TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 55

Sponsored Links

 

 ZAINAB IDRIS MAKAWA
[4/22, 11:46 AM] +234 908 769 2191: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Kamar yadda jikina yayi sanyi haka shima na kulla jikinshi
yayi sanyi sosai tun lokacin da abin ya faru har zuwa bayan isha,i bamuyi
magana dashi ba.

   Ya dawo baya  ya shigo ya dauki abu ya sake fita ya dan
jima a wajen ya dawo ya sameni zaune ina waya da Hannatu a lokacin ya samu wuri
gefena ya zauna yana sauraren mu don a zaton shi muna magana ne kan abinda ya
faru tsakanin mu da mahaifiyar nasa yadda wasu mata sukeyi idan matsala ya faru
dasu.

  Sai yaji magana
mukeyi kan test din mu har dai zuwa lokacin da muka gama wayan na kashe ina
gyara zama tare da lumshe idona naji muryan shi yana fadin.

   Zahra na yanke
shawara zan nemi wuri mu koma can nidake don irin wanan matsalan da inna take
yawan maki koda yaushe.

   Bana jin dadin
ganin yadda akan sister dina inna take rufe ido tana fada maki maganan duk daya
zo mata a ranta kandan matsala kadan tsakanin ku raina yana baci da hakan sosai
wallahi.

  Jin abinda yake fada
din yasa na dan sakw runtse idanuwa don na kasa fahintar ko ya fara ganin
laifinane kan matsalan mahaifiyar nasa yanzu dani.

    Da kyat na daure
na iya fadan magana daya da cewa yin hakan kuma shi zai kara haifar da babban
matsala a tsakanin mu dasu.

  Don zasu dauka nice
na baka shawaran ka barsu ka tafi can nisa dasu mu zauna mu kadai ba tare dasu
ba din don nayi yadda raina keso ke nan yadda take zato ina yi a yanzu.

 Koma me zat fada ta
dade bata fada ba don ba zan yarda da irin hakan yana faruwa ba ko yaushe
tsakanin ku.

 Gaskiya niba zan tafi
ba ni dai takewa hakan a kanka kuma zan daure duk wani kiyayyan da take nuna
min a yanzu har zuwa lokacin da zata gane cewa ni din ba haka nake ba a yadda
ta daukeni din.

   Shiru yayi ba tare
daya fadi komai ba sai zuwa can naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin don
Allah ki kara hakkuri bisa wanda kikeyi a yanzu nasan ba a kyauta maki ga hakan
kiyi hakkuri don ni naja maki hakan.

  Ba zakaci abinci
bane sai yayi sanyi na tambayeshi don mu kawar da wanan zancen ya nisa tare da
fadin zanci amma tare dake don nasa baki ciba har yanzu.

  Bana jin cin komai
ne yanzu amma muje in zuba zanci na fada ina mikewa ya jawoni nayo baya zuwa
jikin shi na fada ba shiri.

  Rufoni yayi da
hannayensa yana neman fuskana ya hada da nasa yake fadin princess nasan kina
daure komai ne a kaina don kada naga kasawan ki.

  Kiyi hakkuri don
Allah zahra hakan yana min ciwo matuka a rayuwana ba komai don Allah wata kila
nidin ce nakeyin abu ba daidai ba wani lokacin .

   Ji nayi yace hmmm
kin dai fadi hakan ne yanzu amma nasan abin kema yana damun ki nace toko ya
dameni yaya zanyi tunda matsayin uwancikina take a gareni nasan zata bari wata
rana insha Allahu.

  Sai naji ya kara
rungumeni yana sauke ajiyan zuciya kamar wani zai kwanceni gareshi a lolacin
yadda yake min din.

   Da kyat na samu
nayi mai dabara ya daga mukaje cin abinci ba laifi na dan daure na danci don
hankalinshi ya kara kwanci don hakan ya kwantar mai da hankalin shi .

    Zaune yake yana
tunanen irin mafalkin dayayi a daren yana son tunawa amma kuma ya kasa gano
komai a kwakwalwan shi.

    Yana yawan ganin
matashin a yan kwanakin a mafalkin shi bai masa magana amma yana ganin matashin
kamar yana cikin damuwa sosai game da wani abu saidai ya kasa fahintar damuwan
matashin me zuwa mai da siffan danshi yasir daya haifa.

   Da farko ya zata
yasir din ne yake cikin wani hali amma yana kiran wayan matashin dan nasa yaji
yanayinshi yana cikin kwanciyan hankali sosai lokaci.

  Don haka suka dan
taba hira kafin suyi sallama ya kashe wayan nasa din a lokacin yaci gaba da
nazarin mafalkin da karo na uku ke nan yana yinsa a dan lokaci nan da yake
ciki.

    Gyara zama ya
danyi yana fadi a zuciyar shi shin kodai wanine daga cikin danginshi yake cikin
wani damuwa irin haka alakar jini yake bibiyan shi a yanzu.

    Yasan a yanzu yana
da rauni da sakaci zuwa ga yan uwan nasa da bai kulasu yadda ya dace din saidai
shima yasan cewa haka kawai yaji baya son kula kowa nasa a yanzu.

   Dan daman shi daya
shine alherin sa ga mutanen unguwa da mutanen gari bai kaiga ya fasa dan basu
ihisanin daya kan dan raba garesu ba idan yazo garin duk da yasan bai masu
komai ba a cikin irin tarin arzikin da Allah ya nufeshi dasu a rayuwa.

    Duk da yasan
maidakin shi ma,ana uwargidan shi Yabi da yanzu kusan itace ke juya komai a
yadda takeson ya kasance a rayuwan ta.

  Duk da hjy tayi
kwatance da kokarin rabashi da kowa kamar yadda tayi nasaran rabashi da yan
uwanshi ta hanyar kakabesu kaf a rayuwansu .

  Sai ita da nata yan
uwan da irin mutanen data yarda su zauna a kusa dasu lokacin amma kuma duk da
hakan batayi nasaran rabashi da aminan saba na kurciya da hakkurin su kan irin
wullakanci da suke fuskanta baisa sun gaji sun bar mijin nata da ita ba.

   Wanan abin yana
matukar konawa hjy rai don ta tsanesu kamar yadda ta tsani mutuwarta a lokacin
haka ta tsani ta bude ido ko kunnuwanta yaji mata yana ambatan sunayennsu ko
zai masu wani alheri a rayuwan su.

   Hakama yanzu da
zancen wanan matashin mai kama dashi daya fito yasa hankalin hjy din ya kara
tashi sosai duk da bata sancewa shi wanan matashin wayeba gareshi.

   Tayi kokarin acikin
siri nasa mutanen ta su binciko mata wayeshi amma anyi rashin sa,a har rana ita
yau basu ma ji wani duriya daga gareshi ba balle ganin shi.

  Har tellansu isah da
shima yaga matashin ta bincika a waya amma ya nuna mata shima ganin shi yayi
kawai kuma yaga kaman nasu kamar yadda wasu da dama dake wurin ranan suka sheda
hakan.

   Tun abin yana
damunta a rai har ta dan fara sakewa don ba wani labarin da zai gamsar da ita
akan matashin ta bar abin ga kamace kawai irin na dan Adam wani lokaci.

   Da wanan tunanen ta
manta da zancen saidai bata bar wani kafa don daure mijin nata da takeyi a ko
yaushe na ya zauna under control din ta kada ya tsalake duk wani abinda tace
dashi a rayuwa.

   Ta kumaga nasaran
yin hakan don ko banza shidin ya kasance ba mai hayaniya bane ga kuma asirin
dake aiki sosai a kanshi ko yaushe cikin barbade yake a jefa a filon kwanan
shi.

   A shafa a takalman
sakawan shi a zuba mai inda zaibi duk akan duniya da zai iya bari itama zata
iya barin shi ko wani lokaci amma ta manta da hakan duniya kawai aka saka a
gaba lokacin da nema daga ita sai diyanta kwara hudu data haifa dashi biyu maza
biyu mata.

   Saidai iya binciken
ta ita da bokayen nata da malamai Allah ya batar masu da basiran cewa dan nashi
yana raye ko yaushe sukayi mata duba sai suga ai baida wani da a duniya sai
diyan ta.

  Don kamanin danta
suke bata sak da wanda suke gani a duban nasu don hakane hankalinta ke kara
kwanciya don tasan sungama da wanan babin a rayuwanshi ko.

    Bata san Allah ya
riga daya tsago wanan hallitan a cikin jikinshi ba yana rayuwa a wani bangare
na daban a cikin kasa kamar yadda suma suke nasu rayuwan cikin jin dadi a
daulan mijin nata da Allah ya azurta shi dashi ba.

    Ba wani abu takewa
hakan ba tun farko ita da kakanta data bar duniya a yanzu tareda yan uwanta
dake taimaka mata wurin irin wanan halin nason su mallaki duk wani abin
hannasushi tun farko.

   Don irin hakane
yasa tun farko suka nisantashi da kowa nasa bayan sun gano barshin gida a
lokacin bashine solution a garesu ba.

  Yasa suka karya
asirin ya dawo gida saboda sunsan dukiyan ba zata ciyu garesu ba su kadai tunda
ga yan uwanshi da suke uba daya sun mamaye komai bayan batan nasa.

   Yau gidan yana da
jama,a sosai don mijin nasu dake gari don hakane duk wace ke girki bata da hutu
idan mijin nasu yana gari.

   Irin hakane ya
kasance ga ummah da girkin ya fado kanta a washegarin ranan da Abba yazo garin
ke nan zata karbi girki hannun mama wace ita iya abincin dare dana rana zata
girka dashi din.

  Suna kitchen suna
aiki da Tani mai aikinta don tun karfe biyu suka dora girki a gidan suna tsaka
ga aikine yan uwan Abban mu mata suka shigo don ganin Abba din a lokacin don ya
kwana biyu bai leko garin ba.

   Tun bayan auren shi
da hjy karima yanzu Abba din sai ya kwashe kwanaki mai tsawo bai leko Gusau ba
suna can Abuja tare da amaryan shi .

   Ganin tana aikine
basu tsaya a part din ba suka shiga wurin mama sun dan dade tare da mama din
kadin Abban ya sallami wasu bakin da yake ganawa dasu lokacin yace su shigo
gashi kafin wasu su shigo mashi ya tsayar dasu wurin son ganin su din.

    A wanan lokacin
ummah ta shiga lokacin girkinta na ranan don haka ta shigo falon suna ciki da
yan uwan nasa don ta dan rage wasu aiyukan daya shafi rayuwan Abba din da suke
masa da kanau basai sun saka yan aikinsu ba sunyi.

    Gwaggo uwace ke
fadin hjy salma naga fa sai wani sharning kike yi yanzu meye sirin hakanne
yanzu sai gwaggo rabi tace meya dameta yanzu tunda ta aurar da yar mu ai dole
hankali ya kwanta kafin wa yan nan su taso kuma don Amira kan ba yanzu ba kusa
auren ta sai me rabon ganin hakan.

    Gwaggo uwale din
ta kara fadin aiko naga mama da mijinta a mashin zasu makaranta wanan yaron
akwai kokari wallahi haka zai daukota saman yar mashin dinshi ya kawota gaida
mu har gidajen mu.

    Mashin kuma zahra
dince ke yawo a gari saman mashi  ina
motar nata koya lalace ne kuma Abban ya tambaya acikin mamakin jin hakan ?

   Daga inda gwaggo
shafa take zaune tace wace mota kuma yaya motar daka sa a karbe a hannunta tun
lokacin auren su kake rambayan mota kuma yanzu ?

   Ni din nan nasa a
karbe mata mota akan wani dalili ya tambayi su gwaggo din sai gwaggo uwa tace
ikon Allah wanan ai tsohon zancene mota kan an karbe munyi korafin hakan har
mun gaji ai.

   Allah zai bata
insha Allah da yake yaran daga ita har mijin nata ai ba masu rawan kai bane
kaga basu damu da hakan ba gwaggo shafa ta fada .

   Idan yana gari ya
kaita da yar mashin dinshi in baya gari kuma tace mai mashin ya nema mata da
yake kaita ya dauko ta har lokacin da zai dawo daga wurin nasa karatun.

    Ni din nan na saka
a karbi mota ya kara fada cikin zafin rai da jin hakan ya dora da fadin towama
na aiko ya karbi motan a hannunta wai ?

    Yaya gambo mana
tazo ta karba tace hjy maimuna ta turata kace a karbi key a hannun  zahra din gwaggo shafa ta fada.

    Salma salma ya
kwadawa ummah data shige kira a hasale saiga ummah din ta fito yace kinsan da
wanan zancen cewa Mamah bata da mota a hannun ta dama tunda tayi aure ?

   Dan murmushi tayi
kafin tace na sani mana bani na karbi key din na bayar a kawo maka ba a daudai
lokacin mama tayi masu sallama falom itama ta shigo.

   Dana aikowa a karbi
key din motan ko zahra ta auri yaron nan a cikin fushina tunda ta nace sai shi
aidai zahra diya tace har yau kamar dukkan diyana a garin nan.

   Ke maimuna ya akayi
har Gambo ta karbi key din motar zahra akan wani dalili waya turata ta karbo
key din yanzu kuma ina motar nata ?

   Wanan kuma saidai
idan ka manta don munyi maganan hakan da kai kace baka ga ranan bata mota ba ai
don in ya bace ba zaka gyara ba ko mjjin nata ba zai samu kudin gyaran
wana  motan nata ba.

   Ok da mukai hakan
sai nace a karba a hannunta ko me don ban gane kan wanan zancen ba dama kin
fada min hakane don kisa a karbi motan a hannun yarinyar a tozarta ni a gari ko
me ?

    Wanan wani zance
ne kuma haka kake min ni zanda a tozarta ka ko yar ka data auri fakiri a cikin
garin nan ita bata tozarta kaba sai ni zan saka a tozarta ka ?

   Na yaushe kuma
tunda girma ya gama zubewa a idon jama,a yanzu kowa yasan haka ai tunda hakan
baifi karfin ka ba ummah ta fada tana kokarin wucewa cikin dakin kwanan Abba
din.

   Tare da dorawa da
fadin ni dai nasan kaddaran mutum baya ketare shi mamah kuma yarkace koka saka
ai maka haka  abinda na sani dayane shi
mahakurci mawadacine idan yayi hakuri ga komai fatana dai ta zauna lafiya a
dakinta.

  Wanda bakiwa fatan
zaman lafiyan bama sun zauna lafiya dakunan su ai dama nasan duk wani shege da
ficen da kikeyi salma akan yarana ba yau ba na sani.

   Saidai ki sani haka
zaku kare dake da yar naki a wahalce gidajen auren ku yanzu kin fadane don nayi
bayanin hakan kome wai ?

   Allah sarki ni da
kika gani nan ban taba bin dan kowa da mugun nufi ba balle diyan ki ga Allah na
dogara da komai nawa ba wani ba nasan kuma Allah bai manta da muba ga hakan.

   Zancen mota kuma a
inda akayi ta dagani har mamah din a nan muka bar zancen don haka ki nemi wanda
ya tayar da zancen a yanzu gareshi.

     Tana fadin hakan
tayi shigewanta ciki ta barsu a nan Abba din
ya bisu da kallo kafin ya hade wasu yawun takaici yana fadin ji nan
maimuna kada ki mayar dani karamin yaro don Allah ?

    Nafa san abinda
nakeyi bawai ban sani bane ta ya zan sakaki ki karbi mota a hannun yata bayan
bansa kin karbi na sauran yan uwanta ba ?

   Kedai kawai kinyi
hakan ne dan wani manufa taki can na daban sanan abinda ya ban mamaki cikin
zancen nan da ba wanda ya fada min komai kan hakan sai yanzu nake jin hakan
daga bakin ku wai ?

  Manufar me kana son
ka dora laifin hakan yanzu a kaina kana denarying cewa baka sani ba ya kallota
yace maimuna halinki yanzu wanene ban sani ba ?

    Kedai kinyi hakan
dawani manufa taki kuma ki kawo min motar na gani kafin na wuce inda gyaran da
za aiwa motar ayi kafin akai mata abinta.

    Yana fadin haka ya
mike ba tare da sunyi zancen daya kawo yan uwan nasa ba wurin shi sai cewa yayi
shafa koma meye ya kawo ku inji a wurin hjy gobe in na shigo ta fada min komai
koke dake kusa in na shigo ki shigo muyi maganan dake.

   Wanan zancen nan
take ya bazu a cikin dangin mu yan uwa suka fara fadin albarkacin bakinsu kan
haka har saida yakai kai ya rabu biyu a tsakanin su.

   Har yakai labari
yazo kunnen mu cewa ai mama itace tayi makarkashiyar karbe mota a hannuna wanda
sai yanzu Abba din ke samun labarin hakan da akai min din.

  Ban san a ina
mahaifiyar Ahmed ta tsinto wanan labarin ba na daiji tana yada habaici a tsakar
gida da fadin dama na sani ko a gidan ba wata tsiya bane ashe ?

    Ba a bakin komai
mutum yake ba dama ina za a dauki yarso aba mutum irin yaron nan da baida komai
dole sai abin banza irin haka ai.

   Dije ko ta fito ta
bata amsa da fadin ai sun zama banzaye ke nan har dan naki da kike shirin
aibantawa a yanzu don ba yar mutane kike wa wanan zance ba in kina da hankali
dabaki fadi ba.

  Ai tayi muna komai
keda uban dan ya gudu ya barki da dan shekara da shekaru babu waige a gareku me
kuka zama a idon jama,a yanzu ?

    Sai amsan Dije din
yai mata zafi tana fadin inna nidai bance ga wanda nake wanan maganan akamshi
ba  inma ubanshi ya gudu ya barmu ai
hakan bayin kan mu bane nidashi.

    Har dai zancen ya
kaisu ga bacin rai wanda a karshe yana dawowa yaji wanan labarin a bakin
makwanta suna sheda mai abinda ke faruwa yanzu a gidan ba dadi.

  Saboda makwabta sun
fara gane irin zaman da akeyi a gidan nasu yanzu wanda mahaifiyar shice ke jawo
hakan ko yaushe.

   Nikan na gama duk
wani abinda zanyi a ranan na samu wuri na kwanta don ya fita da sunan samo muna
shelto a fesa a dakin har barci ya far daukana ina dakon dawowan shi bai shigo
ba.

    Ya dawo yake tayar
dani na koma falo ya fesa muna a dakin na mike da kyar na fito falon ya fesa a
ciki har bayi can sai gashi ya fito dagashi sai dan boxer na maza a jikin shi.

    Duk suran jikinshi
a waje lokacin saidai kallo daya zaka mai ka fahinci zuciyar shi babu dadi a
lokacin na saba da ganin hakan idan wani abu ya bata mai rai.

  Dan zamana dashi da
mukayi yanzu ya zaune kusa dani a inda nake kwance jin hakan yasa na jaye
kafana daya dan zauna a kai.

   Zahra wai sai
yaushene inna zata daina halaiyanta irin haka a kan mu wai ace kamar inna tana
zama tana sa insa da mahaifiyar ta wanda gaskiya ada can baya bansan ta da
wanan halin ba haka?

   Tayi wani abinda ba
daidai bane kuma tayi mana duk daku baku fada min ba duk da nasan kedin ba fada
min zakiyi ba har dije din da sukai hakan da ita.

   Meya shafi inna da
zancen motarki da aka karbe a gidan ku har suke sa,insa da Dije akan hakan ?

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/22, 11:46 AM] +234 908 769 2191: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

Leave a Reply

Back to top button