TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 31

Sponsored Links

 

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/2, 10:57 PM] +234 813 274 8094: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

  3️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

 Jin yawan kudin motar
yasa ya fara budan ido yasan dole gari
da nisa sosai da nan din don sai a lokacin yaga kasadanshi na kamo hanya
shi kadai zuwa wanan waje.

  Yanzu yake daya sani
ya sanarwa Dije zancen tafiyan shi din duk da yasan cewa ba yarda da hakan
Dijen zatayi ba.

    Amma a wanan
tafiyan haka mai nisa ya kamata ace ya sanarwa Dije din kafin yazo ba wai ya kamo
hanya haka shi kadai yazo ba yadda yayi din a yanzu.

   Sai Ido yake faman
rarabawa yana kallon gari da ikon Allah gashi tunda ya bargida baiga wani idon
sani daya sani ba a nan hakan yasakashi fara daya sani da ya hakkura ya zauna
inda yafi wayau.

   Saidai a take wani
zuciya yace dashi haba kamar kai ba namiji ba dai Ahmed haka zaka zauna ana ma
gorin iyayye a cikin gari alhalin kana dasu raye.

  Waya sani ko
mahaifin nawa baya raye yaba kanshi tambaya to ko baya raye dai zanga wasu
nasan su su nasani suka tabbatar da ya haifeni a duniya.

   Duk da gajiyan dake
jikin shi bai hanashi sakawa da kullawa ba a lokacin yana zaune a karshen
mazaunin passengers ya kama haban shi da hannu guda .

   Wana  fitowan ba gudu baja da baya gareshi ko ta
halin kaka so yake yaiwa kanshi gata a idon mutanen da yake rayuwa a cikin su
duk da mutane da yawa sun sha sheda shiba shege bane.

  Da ubansa sabani
ra,ayi kawai aka samu yai fushin zuciya bai juyo ga danshi ire iren haka kowa
ke tofa albarkacin bakin shi a kai suna fadin iya sanin su kan matsalan nashi
dashi yake ganin shi kadai ya shafa.

  Don hakane ya yanke
wanan shawaran a zuciyan shi cewa zai tafi har garin ya binciko mahaifin nasa
ko yan uwanshi bisa taimakon wani mutum da akace tare sukazo dashi mahaifin
Amadi din garin suna yara.

   Duk da mutumin ya
nuna cewa shima baisan shi ba haduwa duniyace kawai sukayi a ibadan dashi har
suka zama abokai har yakai sin sami ubangida dan zamfara da suke sana,an
dabbobi tare har yakai sunji dadin mutumin sun biyoshi nan zamfara sun zama
kamar yan uwa dashi.

   Amma shidai ainihin
dan kanone kuma yasan shi mahaifin Amadi din yana fada mai cewa shi dan Mambila
ne kuma ainihi iyayyenshi sanan nune a garin da kace gidan hardo Dume za a akai
ka.

    Wanan zance Amadin
ya rike a matsayin makami a gareshi yaji yana da karfin tafiya a zuciyar shi
koba komai zaiyi kokarin kai kanshi garin ya binciko waye ainihin mahaifin nasa
a nan.

    Haka yasa yai
amfani da daman shi daya samu yanzu tunda ya gama karatun shi kafin ya fara
wani abinda zai samu na dogaro da kanshi ya hada yan kudaden dake gareshi ya
kulla wanan tafiyan a asirce ba tare da sanin kowa ba a cikin dangin shi.

   Tun yana kallon
garuruwa har yayi barci ya falka driver sai faman sharara gudu yake dasu a mota
saidai sun tsaya a wani gari sunyi sallah sunci abinci a garin.

   Dan samakon da
akasarin passinger mutanen motan sukayi a lokacin yasa suka sauka akaci abinci
suka kara daukan hanya kuma.

   Kwance nake ina
barci ni kadai a dakin nawa sai faman juyi nakeyi a gado don mafalkin da
naketayi marasa kyau daya shafeni gudu nake faman yi ina neman ceto.

   Don wani iska mai
kama da guguwa dake bina a guje ina gudun ceto kada ya lailayeni a lokacin wani
gidane a gabana na gani aka miko min hannu kamar an fisgeni da karfi alaman wani
ya ceceni na falka a tsorace.

    Da kyat na bude
idona sai naganin a wani daki na daban sai daga baya na tuna da inda nake na
dade a hakana kafin na mike zuwa bandaki na kewa na fito.

   Duk da ummah ta
fada min na dinga kokarin yin sallah dare amma sai nakejin kasalan yin hakan a
gareni saida kyat nake samun daren da nake rayewa ina tsayuwan daren .

   Hakana koma wani
barcin ya kara daukana wani mafalkin nakeyi saidai wanan karon ganin kaina a
wani waje dake da yawan tumfafiya gasu nan birjit a wurin ba iyaka.

   Na rasa me zanyi a
lokacin in ceci kaina a wurin ina nan tsaye ina tunane sai na kai zaune ga
wirin ba motsin komai ina nan zaune ne na kurawa wasu halita a jikin wani iccen
tumfafiya dake kusa dani ido ina kallo gashi ni ban san me nake a wurin
ba,  sai can naji motsin a bayana na juya
.

  Wani mutum naga yana
nufoni dattijone sosai mutumin yana cikin fararen kaya yana min murmushi tare
da sallama.

   Kaman nin mutumin
yayi min kama da wanda na taba sani ko naga fuskan a wani wuri kafin ya karaso
nake faman tunanen hakan.

   Na amsa sallaman da
sauri cikin damuwa yace zaman ki a nan shine alherin a rayuwan don zaki kubuta
daga sherinsu har abada.

   Don kina tare dasu
ta ko ina baiyanan ki a nan shine alheri a gareki ya zama hanyar kubutanki daga
hannun makiyanki don suna son saka rayuwanki a ukuban su a yanzu na har abada.

Saidai kuma zasuyi ta wahalan cin maki amma ba zasu taba
samun nasaran iya hakan ba gareki don ke din da tsari a jikin ki wanda ba kowa
Allah kewa wanan irin baiwan ba a rayuwa.

  Don ke din kina tare
da tsarin Allah ko yanzunma suna kan neman ki ba zasu hakkura dake ba sai sunga
abinda zai faru ya faru dake zasu dauka sun gama da rayuwan ki gaba daya.

   Basu san cewa kin
riga da kin masu nisa ba a hakan sai daga baya zasu gano hakan gareji lokacin
da basu iya komai a kanki zasu san suyi sake har kinfi karfinsu.

  Kinga hanya nan ya
nuna barin gabas da hannun shi yace ki bishi zai kaiki gidan ku ba abinda zai
sameki in kin shiga gidan in sha Allahu.

 Nuna min hanyar da
yayi yasa na dago kaina ina kallon hanyar daya nuna min din babu komai a wurin
sai yawan tumfafiya gasu nan kore dasu sunyiwa wani irin luf luf a wurin gwanin
ban sha,awa.

    Na dawo da kallona
ga tsohon saidai babu kowa a wurin kamar ba wani mahalukin da ya taba tsayawa
bayan ni har nayi magana dashi a wurin na yunkura na mike haka naja kafata da
kyar na nufi wurin daya nuna min din.

  A cikin ganyayen
tumfafiyan masu tsawo da tsayin duhu nake tafiya da sauri sauri gudu gudu ina
sauri in bar wurin amma bancin ma iyakar wurin ba a lokacin.

    Ban kuma fasa
kutsa kaina ciki  duhun ganyen tumfafiyan
ba sai ganin kaina nayi a gidan kakan Ahmed tsaye ina dan waige waige a tsakar
gidan su din daga haka.

  Har na falka daga
barcin don alam din wayana dake kara a lokacin alaman shidda na safe yayi ke
nan a gurguje na mike na shige bandaki na dauro alwala don na gama makara ga
sallah asuba ranan.

  Wanan mafalkin yasa
ni jin wani yanayi na daban a jikina don tun tashina nake jin kasala a jikina
ko ina yana min ciwo zakice a fili nayi wanan gudun ba a cikin mafalkina ba.

   Ranan ban iya
fitowa ko falo ba har su mommy suka fice wurin aikinsu ni kuma ina kwance a
dakina a galabaice sai wajajen sha biyun ranane Tabitha ta leko dakina tana
fadin.

   Anty Anty yau
lafiya kuwa baki fito ba barci nake sosai a lokacin a galabaice nake jin
muryanta sama sama a kunnuwa na hakan yasa ni bude idona da sukai min nauyi a
lokacin ina kallon ta bushi bushi tsaye dan nesa kadan dani.

    A cikon murya mara
sauti nake fadin yau bana jin dadin jikinane nake kwamce ina kokarin son in
juya itakuma tana tsaye a inda take  idon
ta yana kaina tana kallon yanayina tare da fadin ayyah sannu ko .

  Na hado maki ruwan
zafi ki sha shayi ta fada cikin tausayawa nace barin yi wanka na fito kitchen
din tace Allah baki lafiya nagode na fada a daidai lokacin dana samu na mike
zaune.

   Ta juya ta fita na
dan dade a zaune don sanin danayi cewa baida kyau daga rashin ka kace zaka
sauko daga kan gado ba tare daka dan dade a zaune ba na wasu yan mintuna kadan.

  Don irin hakan yana jawa jikin bawa wani
matsala a take attack zai iya kama mutum a wurin yasa na saba da idan na tashi
zan danyi minti biyu ko uku zaune kafin na mike na sauko.

   Bandaki na nufa na
watsa ruwan zafi ko zan samu dan karfi a jikina na fito na murje jikina da
manshafina na fito bayan na shirya zuwa kitchen.

   Ina shiga Janet ta
shiga yimun sannu itama na amsa Tabitha ta fara fadin madam yau ta fita ta
kwashe kayan shayi muma ba a bamu shayin munsha ba.

    Na danyi murmushi
karfin hali ina fadin zakusha shayin ke nan tace in mun samu zamusha mana anty
nace barin zo na juya zuwa daki na dauko kudi na kawo masu dubu uku nace su
karba su sayi duk abinda suke son suci.

   Gadiya suka fara
min na dora idomie a wuta na dafa nan na fara jin gulman mommy da irin halinta
na samu abubuwa da yawa da nake son ji game da mommy din a bakinsu.

   Zaune nake na kasa
cin abinci don bakina da nake ji harshi babu test a lokacin wayana na jawo na
fara neman layin Ahmed saidai computer na fada min not richarble ..

  Kira kusan hudu nayi
mai ban sameshi ba yasa nayi mamakin haka
don yana ganin kirana yaka  dauka
ko ya bari sai ya mutu ya kira da layin shi.

  Irin haka  yasa na kasa fahintar halin shi don shi mutum
ne da sam baison aga gazawan shi a al,amari idan ya taso tsakanin shi da mutum
din.

  Yau kwana biyu ke
nan baya gidan ganin cewa yamma ya soma a rana ta biyun a daidai lokacin dashi
yake can yana kokarin shiga garin yola Dije kuma a nan zamfara ta tayar da
hankalin ta sosai.

   Har yakai ta fita
ta samu malam tanimu da fitosanshi ke nan a lokacin take labarta mashi rashin
dawowan Ahmed din gida da sunan zai shiga kauye ya sayo hatsi kamar yadda ya
fada mata din.

     Dijeki kwatar da
hankalinki duk inda yake in sha Allahu Amadi yana lafiya don ni jikina bai bani
cewa wani abu ya sameshi a can ba kinsan tafiya yadda yake.

    Mai yuyuwa wanan
karon yayi nisane da gida sosai don in kin kula abinci a yanzu yayi nisa sosai
ba ako ina ake samun shi ba haka kai tsaye.

   Malam Tanimu Amadi
bai tafiya irin  haka yakan danjene ya
dawo gida don haka donle in damu da rashin dawoawan shi haka yaufa kwana biyu
ake nema ga tafiyan nasa.

   Namiji nefa Dije
don Allah kijeki ki kwantar da hankalinki insha Allahu yana nan lafiya ba
abinda ya sameshi a can saidai muyi adduan Allah ya dawo dashi lafiya yanzu
kan.

  Wanan  zancen nasu da malam tanimu yasa ta danji
hankalinta ya dan kwanta ta ta koma gida da dan kwarin gwiwa ba kamar yadda ta
fito ba da farko.

   Kowa ya fito a
motan ga yamma da yayi sosai a lokacin don har wasu sun fara shirin alwala
shima fita  yayi da dan jakkarshi na
ratayawa kalan ta maza a kafadan shi.

    Wurin wani dan
Union ya nufa da yake gani dattijone a
wurin yace don Allah malam tambaya nakeyi mutumin ya juyo don jin hausan
shi yana kallon shi.

   Yake fadin mabila nake son zuwa don Allah ko
za a samu motan da zata tashi a yanzu zuwa can ?

   Malam da yamman nan
kuwa gaskiya yana da wuya a samu motan da zai tashi yanzu zuwa can don yanayi
hanyan a yanzu.

   Amma ka dakata mu
gani nan zuwa dan anjima amma da zaka bi shawarana ka bari sai zuwa safe kabi
motan farko ka wuce kasan yanayin boko haram din nan da muke ciki ya fara kawo
muna nan.

  Jin hakan yasa jikin
Amadi din yai sanyi shi yanzu idan yace zai kwana a ina zai kwana ke nan don
haka bashi da zabi in mota ta samu zai dauki kaddara hakana yabi hanya Allah ya
tsaresu.

    Kaje can ka zauna
mutumin ya fada yana nuna mashi wani benci a wurin Amadin yace bari nayi sallah
a can na fito zan dawo yanzu in sha Allahu.

    Jeka Allah yasa mu
samu motan mutumin ya kara fadi shi kuwa Amadin ya nufi wajen da yaga wasu na
zuwa don yin ibada.

    Har ya idar ya
fito ya dawo wurin ba alaman mota  har
lokacin yaja ya zauna a nan inda mutumin ya nuna mashi da farko kafin yaje
sallah.

    Bai dade da zama
wurin ba wata mota ta shigo cikin  tashan
yaji sunawa drivern kirari ana gaisawa dashi wanan dattijon yaje gurin shi
shima suka gaisa.

  Daga can yaga
mutumin yana masa hannu ya taso da sauri zuwa wurin su ya iso mutumin ke fadin
kayi sa,a ga mota nan har gaba da mambila ya nufa shi sai su sauke ka su tafi.

    Kudin mota dubu
biyu da dari biyar ne ka kawo a bashi dama mutum biyu yake nema ya cika kuma ya
samu don ga wani dattijo can shima gembu zai tafi yace.

  Hannu ya saka a
cikin aljihun shi ya ciro kudin ya mikawa mutumin saura dari biyu ya sake mika
yace babba ga wanan kasha ruwa.

   Godiya sosai
mutumin yai mashi don shi tausayi dattijon ya bashi a rayuwa yafi tsanan wanan
aikin na Union din tasha sai yake ganin shi ga aikin malalatane.

   Sai kaga mutum har
mutum.daya dace ace yana aikin karfi amma ya buge ga yin kamisho din mota ana
bashi taro sisi zuciyarshi ta kara mutuwa .

   Wanan din ma ya
ganshi ya dan tsufane yasa yaji tausayin shi haka kuma ya hango idon mutunci ga
mutumin tun shigowan su cikin tashan dama shiyasa ya nufi wurin shi.

   Ba bata lokaci
bayan shiganshi motar yana rugume da yar jakan shi motan ta tashi suna daga
masu hannu da alama wanan drivern sananene sosai a cikkn tashan yola din.

Leave a Reply

Back to top button