TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 49

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/13, 7:33 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣9️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Irina ne shima ba wani tarin abokaine dashi ba sai mutum
biyune suka rakoshi zuwa dakin suga angonai adole sun saka babban riga a
jikinsu.

    Ina dan jiyo
muryan su daga can ciki inda nake kwance a makure kaina yana wani irin sara min
lokacin naji muryan hanne tana fadin babu inda zata fito yanzu don tunda aka
kawota kanta yana ciwone.

   Naji Ahmed din na
fadin subbahanallahi Hanne shine baki fada min ba tun dazun na sayo mata magani
ta hade aika san ciwon kan zahra ba irin normal ciwon kan nan bane.

   Ta dai shaka wanan
abin inaga ta samu barci don tun dazun banji motsinta ba haba dai hannatu kika
barmin mata ita kadai a daki kwance.

   Au laifina zaka
gani yanzu Master duk kokarin zama  kula
maka da ita da nayi a,a ai bamu yar haka dake amma dai kin kusa laifi kan a nan
da baki zauna kin tsare mun itaba a ciki.

   Taufa abu yazo ga
masuyi ke nan ashe zamu daina ganin ka yanzu waje kana gida kana gadin gimbiyar
bai basu amsa ba sai jin sallaman shi da nayi a ciki yana kiran sunana da Zahra
?

    Barci kikeyine ko
idon ki biyu yanzun hannatu ke fada min bakiji dadi ba haka haba aida kinsa ta
kirani a waya gashi yanzu dare yayi koda yake barin fita yanzu kila na sameshi
bai shige gida ba.

   A lokacin nace
cikin karfin hali ga murya duk ya dushe min gurin kukan da nasha a wanan wunin
ko wace amarya na farin ciki da walwala a wanan ranan ni kuwa sai bakin ciki da
takaicin da muka gani akaina nida mahaifiyata.

    No ka barshi kawai
yana fada min ai na fada cikin karfin hali dariyan su mukaji daga falon ko ba a
fada ba musan shi sukewa dariyan lokacin.

   Yace baifa tafi ba
har yanzun kike nufi bari kawai na samo maki ki gwada a gani muryan dayan
abokin nasa mukaji daga falo yana fadin .

   Kai mutumina wai
mikakawa zimudi hakana zahra Allah ya nufa yau a gidan ka zata kwan ka shige
kamar wanda ankacewa za a kwacema ita.

  Ka barsu suyi abinsu
Allah ne ya nufa suga wanan ranan don sun zama iccen tumfafiya mai tohurwar
kasa ko an sareka a sannu zata dawowa tsaye.

    Yau ba gashi bayan
wuya sai dadi ba hakkurinsu yakaisu ga zama ma,aurata ga jjuna ai Master ya zan
zakaran gwajin dafi a cikin dubu.

    Hannatuce ke
fadawa abokan nasa haka sai naji Ahmed din ya fito yana fadin  hannatu dare ya soma na sallameku zuwa gida
kada aga kun dade a nan.

    Can naji muryanta
tana fadin kai haba dai Master wanan kudin basuyi yawa ba kada fa mu cikama ido
kai muna kyautan da baka shirya yinsa ba.

    Hannatu ke nan
kada kiji komai konfi haka a wurina idan ina da hali dayafi hakan don ke kawace
ta arzikin da akeson mutum ya samu ai bari wanan ya sauke ku a gida idan zai
tafi yanzu.

   Kai Master kake
kowa koran mu kake sonyi mun rakoka dakin amaryan ka ko da badon yan matan nan
ba babu inda zan tafi yanzu amma kaci bashin hakan gareni.

   Allah dai ya nuna
muna lokaci lafiya naji Ahmed din yana fadawa maishi suka kwashe da dariya
hannatu ta leko daga kofa tana fadin zahra zamu tafi insha Allah da safe zan
taho in dubaki.

    Ki taho ina da
safe wanan mai rawan kan zai barki ki shiga gidanai da safe sai ko kinyi zaman
jiranai a waje indai  Amadina.

    Daga nan naji
fitan su suna mika min gaisuwa suka fice daga dakin can naji shiru harshi falon
yayi tsit can sai naji dawowan shi yana rufe kofan shigowa part din mu alaman
ya gama fita ke nan a ranan.

    Ya shigo dakin da
sallama naji ya rufo kofan falon lokaci guda ina danjin motsin shi a falon can
na yayi sallama ya shigo ya aje abu yana fadin .

   Zahra ki tashi ki
danci wani abu sai kisha magani gashi na karbo maki a chemist saidana muskuta
nake fadin ba zan iya cin komai ba a yanzu murya can ciki nake magana.

    Ruwan zafine sai
madara da kaza ko kadan ne don Allah ki tashi ki taba zaifi ki kwanta a haka da
yunwa a cikin ki ai ya fada yana zama kusa dani daidai kafana.

    Na dan jaye kafan
tunda ban zama irin haka da maza dan dama ya musa da mukayi sabo sosai dashi ko
ina kwance ne zai zauna a bakin gadona idan ya shigo dakina muyi magana.

  Saiko yau dashi
Ahmed din yayi hakan gareni sai naji abin wani bambarakwai gareni gashi dai ina
son in daga don hadani da Allah da yayi kuma yayi zaune inda zan tashi din
lokacin.

    Ko yagane me nake
tunanene sai naga ya mike ya nufi bandakin ya dan leka kamar ruwan dake ciki ya
duba a lokacin ya fito daidai lokacin na mike ina dai ganin juwa a idona.

    Sannu yai min daga
kofan bayin inda yake tsaye yana bina da kallo kamar ranan ya fara ganina a
duniya nasan lokacin da da hali dayace zai daukeni ya kaini bayin saidai babu
fuskan hakan gareni.

   Har nakai bayin
yana min sannu ya rufo kofan da kanshi na dan jima a ciki don har brush nayi ko
zanji dadin bakina lokacin sai dana gama na fito.

  Kallo daya nayi mai
na kawar da kaina gefe na dan rabashi na wuce zuwa gado na zauna a bakin gadon ina
mayar da brush din a cikin jakata na samu ya bude kayana ya ciro min rigan
barcina ya dora saman gado.

   Shi kuma yana tsaye
daga shi sai boxer irin na maza da farin singlet a jikin shi abinda yasa jikina
bari ke nan don ban taba ganin wani mahaluki hakan gabana a fili ba .

   Sannun dai ya kara
min yana fadin ga kayan barcin ki nan na fito maki dashi ko wanan din zaiyi
maki ban sani ba nagode kawai nace ba tare dana dago kaina kalleshi ba.

    Ya juya zuwa
bandakin ya jima a ciki don ban debe tsamani idan ba wanka yayi ba a lokacin
sai gashi ya fito yana saye da jallabiya mara hannu brown a jiki  shi da ganin rigar sabuwace a ranan ya fara
sakata a jikin shi.

    Na dan kai
kishingide don yadda yanayin jikina nake jinshi lokacin kallon inda kayan makulashen
daya aje yayi sai naga ya nufi hanyar waje ina jinshi ya bude kofa can ya dawo
ya rufe ya shigo hannun shi yana dauke da plate da cups biyu.

   Ya aje ya bude
ledan ya juye naman da har lokacin yana da sauran zafin shi sai kamshi suya ke
tashi wanda ni kuma a lokacin nake jin kamshin na hawa min kai.

    Ina zaune a inda
nake ina kallon shi ya gama ya kalloni yana fadin bissimillah kona kawo maki a
nan da sauri na tareshi da fadin No ka barshi na taso ruwan zafin kawai zansha.

    Wani kallon mamaki
ya watso min kafin yace ruwan zafi kawai naman fa ba zakici bane don kifa na
sayoshi kuma gashi bakici komai ba ?

   Bana jin cin komai
ne a yanzu don tun safe dana karya ban iyacin komai har yanzu da sauri naji
yace dani what kina jiran me har yanzu oya tashi na baki a baki idan cin yake
maki wahala.

   No ba haka bane
kawai dai bana jin dadin komai ne a bakina yanzu ruwan zafin is OK idan nasha
sai naga ya mike ya dauko cup din ruwan zafin
ya nufoni dashi.

    Yana zuwa yakai
zaune a kusa dani har turarensa na maza daya shafa yana shiga hancina a lokacin
ba kuya naga yana kokarin mika min kofin shayin a baki da sauri na dakatar
dashi daga hakan da yake shitjn yi cikin kunyanshi nace.

   Haba dai zan iya
sha dakaina ai bakya son na baki da kainane kefa yanzu sauraniyatace ke dan
murmushin ciki na sake dkn ni mamakinshi ma ya hanani kara sakewa.

  Saboda abubuwan da
yake min a yanzu zakace munyi irin sabon hakane dashi tun farko don gaba daya
ya juye min ya koma wani Ahmed din na daban ba wanda na sani a baya mai alkunya
ba.

    Hannu na mika ya
sakarmin cup din na dan kai bakina ba laifi don da dan zafi kuma naji dadin
hadin sosai saboda kamshin kayan yajin dake tashi a ciki.

   Na kurba yakai sau
uku yana zaune ya kura min ido yana kallkn yadda nake kurban ruwan tea din sai
nayi kokarin ajewa saboda naji ya isheni a lokacin.

   No shanyeshi fa
zakiyi sai ki dan ci naman nan na baki magani sai ki kwanta nace don  Allah ka barshi wanan din ma is Ok ai basai
naci nama  ba.

   To ki kara ruwan
zafin ga maganin a hannuna sai kisha don dole naci gaba da kurban ruwan shayin
har saida na kusa shanyewa na miko mashi cup din a lokacin ya miko min maganin
daya bare dole na karba nasha da kyar don banson magani a rayuwata.

    Karban cup din
yayi ya shanye sauran wanda na rage din a ciki sai mamakin hakan da yayi ya
kamani bayan yashane ya mike daga inda yake zaune yana fadin .

    Bari na saka wa
yancan a cikin fridge kada su lalace da safe sai ayi amfani dasu ya kwasa ya
fita ya dan jima bai shigo dakin ba don koda ya dawo har barci ya daukeni
lokacin.

   Ya gama abinda
zaiyi ya kashe wutan dakin tare da hawowa gadon daga can barin gefen da nake ya
kwanta ya fara karanto muna adduan kwanciya don yasan yadda nake din nan karfin
hali kawai nakeyi ba lalai bane na iya yin addua a lokacin.

   Ban tashi farkawa
ba don maganin ciwon kan da nasha sai wajajen
karfe uku da rabi na dare koshi fitsari ne ya falkar dani lokacin na
tashi.

    Dakin da duhu
sosai sai gabana ya fadi don sam lokacin na manta da inda nake a ranan ga nauyin
mutum da nake ji a kusa dani lokacin.

  Nan na fara dan
lalaben wayata dana aje a gefen gado na jawo na haska a hankali tare da tuno a
inda nake a lokacin ne naga yadda muka kwanta a gado daya tare dashi.

   Don kusan jikin mu
yana hade da juna dama nayi tunanen hakan don dana falka naji nauyin mutum a
kusa dani saina fara kyarma.

    Muryan shi naji
daga gefena yana fadin lafiya dai ko da kyar na iya bude baki nace dashi ina
son in shiga bandaki na kewayane.

   Mikewa yayi zaune
kafin na tashi ya jawo wayan shi ya kunna touchlight din shi yana fadin na
rakaki bayin ne zan iya na bashi amsa da sauru na samu na mike zuwa ban dakin
ga wani irin barci a idona lokacin.

    Ban jima ba na
fito na kwanta can kafin barcin ya daukeni naji mikewan shi ya shiga bandakin
bandai san fitowan shi ba ashe alwala yayi yazo ya tayar da sallah.

    Yana nan zaune
akai kiran sallah farki ba a jima da kira ba yaji ana kwankwasa kofan dakin
namu daga waje bai daga ba kuma baiyi magana ba.

   Can kuma kamar
bayan wasu yan mintu ya kara jin a kara dukan kofan a lokacin ta mike yayi
gyaran murya yana mamakin hakan yau gareshi.

  Shida zai bugawa
mutane kofa su tashi shine akazo aka bugawa kofa ya tashi waye da wanan aikin
garwshi haka sai yaji ranshi ya baci da hakan da akai muna din.

    Ban dakin ya koma
ya shiga ya sake dauro wani alwala ya fito ya dan shafawa jikinshi turare kana
ya nufi kofan ya bude ya rufo daga baya ya barni a ciki.

    Jin fitan shi yasa
nima na mike na shiga nayi alwalana na fito na zo na tayarda sallah daidai da
lokacin an fara sallah bayan na idar na dan dade a zaune wurin ina adduan samun
zaman lafiya a tsakanin dama sauran mutanen gidan.

   Na shafa ban koma
na kwanta ba saida na gyaro dakin ko ina na saka kamshi nayi wanka har lokacin
bai dawo part din namu ba na samu wuri na kwanta again sai barci.

  Duk lokacin gari bai
gama haskawa ba ya dawo gidan ya shigo a zaton shi zai samu banyi sallah ba har
lokacin  sai ya samu nayi sallah don
idonshi ya fara tozali da gyaran dakin da nayi ga kuma kamshi na tashi tun daga
falon.

   Ya karasa ciki ya
ganni a kwance na dunkule da alaman barci nakeyi a lokacin don haka baiyi wani
dogon motsi ba ya koma falo ya kwanta shima.

   Dije kega mutumin
ki ko yau ko lekomu baiyi ba kuma naji dawowan shi tun dazun gashi matar nashi
har gari yayi haske haka bata fito ta gaida mutane ba.

   Haba haba yar nunu
yaushe gari ya waye da kika hwadin wagga maganan  indai Amadina yasan abinda yakai ba sai an
koya mashi ba.

    Wane har yaushe
yake ni gudu nake yazo ya saba da hakan daga baya kuma yazo ya damai keki
rabani da wagga maganan don Allah har yaushe muka fara tantance haline akan
matatai yanzu.

    Shiru tayi don
bata so jin hakan ba daga bakin mahaifiyar nata so tayi ta mara mata baya
suyiwa tufkan hanci don kada ya zarce da hakan saboda yaran masu kudi sai suyi
kokarin mayar da miji bawa garesu.

    Balle wanan da
ubanta yake hamshaki kowa ya sanda hakan dole ta dinga sashi a hanya don in
tabi ra dije biye mashi zatayi suyi abinda ransu keso ana kallon su.

    Shara ta farayi na
gidan kafin can taji bundan kofan part din yaran bata dago ba don taga ko waye
saboda tasan kowaye ma zata ganshi yanzu ai tunda taji motsin mutum zai fito.

   Inna ina kwana ta
dago tana amsawa kafin ya katseta da fadin su hauwa suna inane suka barki kina
shara da kanki haka ?

   Kwana sukai basu
tashi ba na kuma wurin duk yayi ba dadin gani kada a shigo a samu wurin ba
gyara amma ai inna ya kamata a tashesu hakana tunda gari ya waye ko ?

    Ai tashin su zanyi
suyi sallah yañzu idan na gama yasa kai ya wuce ba tare da yayi wani magana ba
sai jin muryanshi tayi yana tayar da yaran nata.

    Haka sunka saba
dashi tun can kamar yaran nan ace ayi sallah suna kwance suna kwana sai lokacin
da sunkaga dama sunka tashi don kansu.

   Dijece tsaye daga
kofan ta take fadin hakan shi kuma yace gasu hauwa a gida ance sai inna tayi
shara da safen nan .

    Haka tagga dama
dauri ta koya masu komai amma yanzu haka gozai gozai yaushe zasu iya hakan nan
dai yayi masu fada ya fice daga gidan can andan jima sai gashi ya shigo da leda
biyu a hannun shi ya shiga ya aje masu guda ya fito ya shige part din mu da
dayan a hannun su.

    Inna keji kamshin
kwai a ledan da yaya yya hita dashiya karamar nanwar shi ke fadin hakan sai
uwar nasu tace kona jiya a a zanyi ?

   Tunda mu kauyawana
bami iya shan shayi da kwaina sai bussashen burodi tunda anga na kawai ta fada
tana wani yatsunan fuska lokacin.

    Inna a dauko kofi
a raba muna ko diyar ta sake fada kai kawai ta gyadawa yar nata don takai cin
da ya kume mata zuciya lokacin .

  Kafin ma tayi magana
yar nata ta mike zuwa dauko kofin ta sai ganinta tayi ta dauko tace su bude su
fara zubawa tana bude kofan saiga kumshin kwai suma a cikkn nasu.

  Lah inna ke gani
ashe muma yasa a faso muna kwanan yarinyar ta fada tana rawan jiki zata bude
ledan daga inda dije take zaune a kofanta ta fara fadin waga diya akwai bakin
kwadai gareki.

    Uwar garke dake
gefe can ta baya yanzu don sai idan kamar zaka bayin su Dije a nan zaka gansu
an dan sakayasu a wurin.

   Kuka akuyan keyi
sosai har suka mayar da hankalinsu garesu suna fadin dabbobinga kukan mi sukai
da safe haka.

    A can cikin
barcina kamar a dakin akuya ta shigo sai zabura nayi na mike don kukan akuyan
daya daki kunnena lokaci guda na mike ina waige waige a tsorace daidai nan yayi
sallama ya shigo dakin.

 

Leave a Reply

Back to top button