TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 14

Sponsored Links

 

 

 

  Na sayar da wanan
labarin don Allah kada wani ko wata yayi audiovisual din labarin nan don Allah
yin hakan taka dokane.

   Duk da akwai
matsala a tsakani  mama da ummah sai nayi
mamakin ganin ai ummahce mai dawainiya da bakin mama din kuma da duk wani
abinda zasici zasu sha daga wirin umma yake fitowa .

   Naso nayi wanan
tambaya  saida ba fuskan yin hakan gareni
naja bakina nayi shiru  ina kallon su a
fakaice don nikan washe gari tun safe na fita zuwa school ban dawo ba sai
shidda na yamma na iso gida.

   A wajen gidan mu na
samu su Dele sun fito shan iska har na karaso cikin gidan na aje mota idonsu yana
kaina gashi naki jin hakan a rayuwana mutum ya kura min ido ba daukewa.

    Naso sharesu amma
ganin hakan ba zai yuyu gareni ba yasa dana fito na nufi inda suke zaune din
don na gaidasu.

   Tun kan na karaso
kabir kanin Dele ke fadin wow what a beautiful car is this sister kunyi kyau
dake da motar taki baki daya so wanan ce motar da mami jafar ke fadin an saya
maki dama ba a saiwa su Aisha ba gaskiya motar nada kyau sosai wallahi.

    Nagode na fada
kafin na dago kai wurin Dele ina gaidashi ya amsa min cikin dan nisawa yana
gyara zaman shi tare da fadin kin dawo ashe nace eh ya sabon yanayi.

 Sai lokacin ya danyi
murmushin gefe a fuskanshi yace ba matsala ina enjoyed din garin ai don weather
din ku na da kyau sosai.

   Gaskiya yarinya
daddy ku ya fito dake gari dole mamin jafar tace ojuju ku kaiwa daddy ku har ya
sawo maki wanan mota haka mai tsada no warder ta kira mamin mu hankaki tashe
tana kuka wai mamanki dake zaku karbe mata miji a hannun ta .

   Kabir dan uwan nasa
ya fada a dake ya hade hannayen shi wuri daya bai motsa a yadda na sameshi ba
sai idon daya zuba min kawai yana kallona kamar yaga photo.

   Kabir din ya juyo
yana fadin is what they said, now aiba karya na fada ba brother ayi mata magana
su gyara idan sun san sufada don kada suje su kaisu wurim babalawo ya halakasu
a banza.

    Shit kasan sin din
da kake aikatawa kuwa kabir kasan wanan yana iya jawo fitina kai meyasa kake
shiga shirmen matane wai don Allah?

   Na fada maka idan
kaji suna shirmen su ka daina kula balle ka dauka wani abu zai iya faruwa kawai
dai shirmene na mata kawai suke fadin hakan.

  Nisawa nayi na gaida
su suke tambayana daga ina nake nace school kabir bau dadara ba ya sake fadin
lalai mami jafar saida dai tasa kikayi karatu a garin nan ke nan duk da daddy
ku baiso hakaba.

   I don no why  wasu mata suke irin haka kan yayan mijin su
meye laifin dan mijiki gareki ne wai da sukeyin wickedness akan yayan mazajen
sune wai ?

   Murmushi na kakaro
a fuskana tare da fadin har yanzu dai kana nan yadda kake ashe daba mutum
dariya shima murmushin yayi tare da fadin.

   Kina ban tausayine
a cikin su da kawai kizo mu koma lagos muyi zaman mu can ki kyalw kowa a nan
zaifi amma idan that mumu Rukkaiya and Aisha suna ganin ki nan ba zasu bari a
zauna lafiya ba And you know what ?

  Na girgiza kai yace
don kifisu da komaine fa yasa sukejin haushin ki har mami Jafar din Zahar ya
fada daga inda yake zaune na dago ido na kalleshi yace go inside.

    Cikin daure fuska
nasan halinshi shiru shirune sosai shi baya da yawan magana sosai gashi bai iya
bacin rai ba don dukkan su nasan halinsu tun ina karama dama kabir abokin
wasanane idan mun hadu dashi.

   Saidai yanzu dana
girma na rage irin sakewan da nakeyi dasu a baya can don yanzu hankali yazo min
na gane cewa su din ba muharamina bane yanzu.

   Don hakane ban iya sakin jikina dasu a yanzu
jin hakan danayi daga bakin Dele yasa na juya kawai na shige ciki abina na
barsu wurin.

   Ina shiga ina jiyo
hayaniyar su mama a part din su da alama dai akwai bakin da sukazo masu don
gaida mami din da zuwa ke nan lokacin.

   Part din mu nashiga
ummah tana zaune ita kadai a falon nayi sallama ta amsa na karasa ina gaida ita
da tayi min ya karatun nace alhamdullahi.

   Har na juya zan
shige naji tana fadin kinga su kabir kuwa da dan uwanshi a nan yau suka wuni
zaune tun zuwan su gaidani basu

 sameki ba suka zauna
na  basu dade da fita ba ai.

   Suna waje zaune na
juyo ina bata amsa na shige ciki don zuciyana tayi nisa ga tsoron abinda naji a
bakin kabir din kan zancen motana idan nayi tunane dakyau mami Dele tazone kan
kiran gagawan da mama tayi mata ke nan a yanzu.

   Dama nasani ko a
baya idan sun samu wani matsala da Abban mu idan naje hutu wanda a yanzu na
tuno da hakan bai wuce kan zancena zasu samu baraka dashi sai mami Dele din
tazo zasu shige daki su dade a ciki karshe ma su gice gidan tare sai dare sosai
mama take dawowa.

    Don akwai wani
zuwa da nayi hutu lagos din datun wanan lokacin zuwa hutun ya fara fita raina
abinda ya faru shine da lokacin komawana yayi ranan muna cin abinci Abba ke
fadin .

    Maamah tunda zaki
koma

 sai yayan ki musa ya
kaiki shopping ki zabi duk abinda ranki keso ke na  ko kai musa gobe ka fita da ita sai ka sayo
mata duk abinda take so a nan.

   Ai kafin Abba ya
rufe baki mama tayi cikin shi tana fadin na fadama banson hakana wani sayayya
za ai mata kome ta rasa yanzu da za aje kashe mata kudi kuma?

   Can inda suke zaune
da uwarta ba a sai masu abune halan tunda duk zuwa ina ganinta da sabbin kaya
ai kai haba maimuna yanzu yarinya tazo maki hutu tayi wata daya amma ki bari ta
koma haka ba komai daga nan.

   Mikewa nayi na bar
wurin don ganin kaina ana son samun matsala ga ya musa ya fara fadin haba mama
su wa yan nan da ake sayawa fa da cewa su Aisha.

   Sai ita datazo maku
hutu dan sayayyan da za ai mata kuma shine zai zama matsala yanzu kuma haba dai
mama idan hakane ai sai ta bar zuwa hutun tunda zuwan ta duk zata tafi sai an
samu matsala irin haka.

    Fada sosai mama ta
fara yiwa ya musa din yasa na tashi daga wurin cin abincin zuwa sakin kwanan
amma ina jin muryoyin su cikin fada sosai daga dakin.

   Karshe shine naga
mami Dele tazo gidan sun dade da mama kuma suka fita saya  tsaraban da Abba bai mun ba ke nan haka na
dawo tun wanan karon naji zancen mama ya fara fita min zuciya.

   Na shiga part din
mu da sallama ummah tana zaune ita kadai a afalo nayi sallama na shigo ina
gaida ita da gida ta amsa min kamar a cikin damuwa.

   Yadda nake mata
kallon tuhuma yasa tace dani ki shiga ki cire kayan nan kifito kici abinci na
amsa da to ummah na nufi hanyar shiga dakunan kwanan mu.

   Muryan umma din ya

 dakatar dani na tsaya
tana fadin kinga su Kabir a waje ne nace eh umma suna waje tace ai tun karfe
daya suna nan sun shigo su gaidani suke tambayanki nace kin tafi school.

   Shine suka zauna
nan din abincin safema a nan suka karya saidai na ranane gashi nan na aje masu
basu dawoba ko sunci a can ne ban sani ba
?

    Suna waje ummah
yanzun muka gaisa dasu na fada nasa kai na shige dakina dogon riga na saka baka
a jikina sai dan kwalinshi dana daura a kaina nasaka plat shoes dina na zaman
gida wanda iya cikin part din mu nake yawo dashi na fito zuwa falo.

    Dining na nufa don
ban samu ummah inda na barta ba da zan shiga abinci na bude naga sallon girkin
na bakine wanan ke nan ko yau din ummah ce ta girka masu abincin na fada a raina.

   Abincin na fara
zubawa a cikin plate a daidai lokacin kuma naji sallaman Dele cikin muryan nan
nasa mai sanyi haka yasani dagowa ina amsawa.

  Yana gaba kabir yana
bayan shi kai tsaye dining din suka nufo yaja kujera daya ya zauna a sanyaye
shima dan uwan nasa yaja yakai zaune kamar wanda ke a galabance dashi.

  Kallo juna mukayi
nida kabir din muka sakewa juna murmushi lokaci guda yace miko masa wanan ya
fara cin wanan da kika zuba sai ki zubo muci tareni .

   Ido na fito dashi
nace naci abinci da kai kato da kai ai sai kasa a dakeni yau ya dago fuska a
daure yana fadin nine kato ko wanan yana nuna dan uwanshi gareni.

   Kaidaine kato amma
ai shi yayanane don haka nake girmamashi ko yaushe saboda ya dauki girma na
kuma sayar mai oh really nace yes ina aje plate din abincin dana sa komai a
gaban Dele din.

    Na juya na fara
zubawa a cikkn wani inda nakesa komai a wadace don nasan yana da ci sosai a
baya ina ajewa yace oya zauna tare zamuci ba wasa nakeyi ba.

   Dole na zauna muka
soma ci tare sai santi yake zubawa wai gaskiya ummah ta iya girki sosai yayin
da nake kara lodamai abinci dana sha sai fira yake zuba muna dan uwan nasa na
shiru.

   A haka Rukkaiya ta
shigo ta sameni dasu take fadin wai ana kiransu Dele din gasu nan zuwa idan sun
gama cin abinci ta juya ta koma part din su.

  Tana fita kabir yace
kinsan me na tsani wanan yarinyar wallahi sjn faye gulma da sa ido yanzu wanan
fita da tayi zataje tayi amebo akanshine.

    Dariya nayi yace
gaskiya nake fada nace yan uwana ba haka suke ba kaima ka sani kawai dai baka
ra,ayjnsune kawai yasa ka fadi hakan.

  Mikewa Dele yayi
wanda shima yasa shi mikewan yana bin bayan dan uwan nasa a kofa suka hade da
Aisha data biyosu ranta bace.

    Duk yadda yaso
ranan  mu hadu bai samu hakan ba don
bubuwa gaba daya sun rikemai a ranan saboda test din da suka shiga mai zafi
kodaya fito ya samu motana baya wajen yasa shi komawa ciki.

   Zuciyar shi ta
bashi shawaran ya nemi number na ya kirani haka kawai zaiyi ya samuyin magana
dani yadda yake so son so yake yaja min kunnem yin hakan saidai yasan a fili ba
zai iya yin hakan ba gareni don yana kallon narkankun idanuna yasan zasu
rikitar dashine lokaci guda.

    Zai iya cewa yana
hanin mata kyawawa da zarra irina mata amma bai taba haduwa da macen data
rikitashi ba lokaci daya irin hakan.

   Yasan dai bai isa
ya nuna so ko shakuwa a inda Allah bai kaishi ba haka kuma shi bai isa yakai ko
matsayin drivern gidan su ba ko mai ban ruwa gidansu ba yadda yaji mutane suna
fadan irin arzikin gidan mayana din a gari.

   Shawaran zuwa
department din mu yayi ko zai ga abokan karatuna hakan yasa ya juya da sauri
zuwa hanyar shiga building din suka hade da hannatu a kofan wace ke fitowa don
zuwa gidan lokacin.

   Tana ganin shi ta
fara sake murmushi a fuskanta lokaci guda tare da fara gaidashi tana fadin
master kayi wuyan gani fa ashe ka shigo yau bamu sani ba gashi harsu zarah sun
wuce gida tunda muka fito dazun tace yau suna da baki a gidansu don haka ta
koma gida da wuri yau din.

   Don Allah ko kina
da lambata ki kira min ita akwai sakon da zan batane eh to nima dai na dauki
lambatane a wayan ta bata sani ba amma dai gashi tasa hannu tana ciro wayan
nata daga cikin jakkarta na hannu ta fara duba wayan can ta miko mai tana fadin
ga layin nata akwai kudi a ciki dazun ta saya min kati.

   Kai wanan ta faye
surutun tsiya wallahi haka ya nasa a zuciyar shi yana karban wayan a hannunta
sunan ZARAH MAYANA yagani da manyan harufa.

    Danna kira yayi
sunan ya shiga saiga wayan na ringing a daidai lokacin ina kwashe kayan da
mukaci abincin dashi da sauri na aje tarim plates din dana dauka zankai
kitchen.

   Bakon number nagani
na tsaya ina mamaki ciki  tsoro nakai
kunnena a lokacin naji muryan namiji yana kwada min sallama.

   Daga wayan nayi ina
mamaki naji muryan hannatu na fadin zarah nice coursemate din ki master ke son
magana dake na kiraki master na fada cikin mamaki sai naji sallaman namiji.

    Amsawa nayi yace
OK dama naso ganjn ki yau ashe kin shigo har kin fita ban sani ba muna ciki
munayin test bamu fito da wuri ba.

  Saisai dama akan
wanan sakon da kika ban jiyane a cikin envelope naso muyi magana dake don ban
san ko kudin meye haka kika bani ba ?

   No kayi amfani
dashi kawai na bakane kawai nagode sai anjima zaiyi magana nace kaba hannatu na
fada a karshe na hana dama  yin magana a
gaban hannutu din ko godiya.

    Hello Zarah kina
lafiya kalau na fada a gajerce har yanzu kina school ke nan ashe tace yanzun
nan fitowana daga class ke nan zantafi.

  Ok saida safe na
fada na kashe wayan lokaci guda na mika hannuna na kwashi plates din abincin
zuwa kitchen daga nan na koma dakina.

   Ba matsala ko
Hannatu dake kallon shi ta tambayeshi ganin yadda yanayin fuskanshi ya sauya
lokaci daya a wurin duk da bataji ko akan me mukai magana ba a lokacin.

    Hostel din maza ya
nufa bayan sun rabu da Hannatu din don ya yawata ko kayan zasu shiga nan aka
kewayeshi sai gashi kayan sun samu shiga har wasu basu samu ba a wurin.

   Haka yasa yai masu
alkawarin zai kawo masu in sha Allah,
kudin shi mina mina ya kirga sai bakin titi ya hau mashin zuwa kasuwa  inda zai kara saro wasu ya kuma cika
alkawarin daya dauka din wa mai kaya .

    Tun kan ya sauka
mai kayan ya hangoshi ya fara washe baki don lokacin daya bashi ma bai karasa
cika ba ya dawo suka gaisa dashi yace har sun shiga ke nan yace kaya sunyi kasuwa
sosai wallahi.

    Nan ya mike ya
jawo wanda ya boye mai da farko yana fadin kaga wasu yau aka kawosu sai ka hada
dasu zasu shiga sosai wanan  mata da maza
duk  zasuyi saya sosai idan sin gani.

   Zuciyar shice ta
bashi shawara yayi amfani da wanan kudin kawai tunda nace na bashi su koda daga
baya zai zauna dani muyi magana a kansu.

    A take ya biya
kudin kayan gabaki daya yana gyaran kayan mutumin ke fadin daukan kayan nan
yayima yawa da zaka daure ka samu tsohuwar mashin ka saya sai kaji dadin yawatawa
da kayan nan zaifima sauki sosai.

    In,sha Allahu ina
da niyar yin hakan nan gaba amma ba yanzu ba sai kudin sun kara kauri nan zuwa
gaba dai sai nasa cigiya in saye don kayan sun fara min nauyi a kai haka.

    Ya baro kasuwa
zuwa gida da kayansa niki niki yana hanyane ya tuna da alkawarin da tayi na
sayowa dabbobin su abinci kaya kawai ya aje daga kofan yace mai mashi din ya
koma dashi .

   Jin motsin shi da
uwargarke tayine yasa ta mike ta fara kuka sosai lokaci guda kuna na tashin
hankali har saida Dije dake daki ta fito hankali a tashe zuwa wurim garken nasu
tana duban su.

   Kofan shigowa gidan
uwar garke ke kallo tana kuka sosai sai hakan ya dagawa Dije hankali ta nufi
hanyar fita wajen gidan sai kuma taci karo da kumshin kayan shi a ta cikim gidan
.

   Mamakine ya kama
Dijen lokaci guda ita daya take magana dama Amadi ya dawone ashe ko kuwa kayan
a nan ya barsu ya tafi ?

     Lekawa tayi ba
kowa wajen gidan sai yan mutanen dake gittaya jefi jefi a layin can ta hangoshi
tafe ya sayowa dabbobin haki da dusa yana sauka saman mashin yana tambayanta ko
lafiya ?

Leave a Reply

Back to top button