TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 58

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/22, 11:47 AM] +234 908 769 2191: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣8️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

 

Kokarin dora girki nakeyi da let evening don dawowan shi
lokacin ina tsaye ina kunna gas banji motsin shigowan shi part din ba sai ji
nayi ya rungomoni ta baya yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin i miss you my
princess.

   Idona na lumshe a
hankali don jin haduwan jikin mu da nasa a lokacin dan wani irin shock danaji
har cikin raina zuwa zuciyana lokacin.

   A hankali na sauke
ajiyan zuciya na furta miss you too ya hanya ya karatu ina kokarin jiyowa mu
fuskanci juna dashi a lokacin.

   Saidai bai bani
daman hakan ba don kara matseni da yayi a jikin shi yana fadin kada kice zaki
dora girki bana jin cin komai a yau don sam bana jin dadin bakina two days ke
nan ina hakan.

    Da sauri na kwace
jikina daga gareshi ina kallon shi cikin mamaki tare da fadin master meke damun
ka baka da lafiyane ko me da hakan ya faru ?

    Ina kallonshi ido
da ido ina magana a rude kai ya rausaya min tare da ware hanayen shi ya bata
fuska yana fadin gani nan dai bana dai jin dadin jikinne kawai kuma ba ciwo
nake ji a wani wuri a jikina ba.

   Yana fadin hakan ya
juya zai bar kitchen din yanayin fuskan shi ya sauya a lokaci guda hakan da
yayi ya kara tayar min da hankalina lokacin guda nabishi da kallo har ya
shigewa ganina.

   A hankali na aje
ashanan dake hannuna nabi bayan shi zuwa dakin duk sauri na sameshi a zaune
falon ya zauna ya mayar da kai baya yana tunane a lokacin.

   A hankali nakai zaune a gefen shi ina me kura
mashi idanu kafin nakai hannuna saman kanshi na shafo a hankali ina fadin meke
damuwan kane master ?

   Ajiyan zuciya mai
nauyi naji ya sauke kafin ya dago kai yana kokarin kallona yana fadi wallahi
kawai nake jin zuciyana ba dadi a kwanakin nan biyu.

  Ga yawan mafalkin da
nakeyi mara kyau dana kwanta barci hakan yasa na dawo ko zan daji saukin
yanayin da nake jin kaina din ciki.

  Shiru nayi ina
kallon shi tare da dan kura mai ido don na fahinci akwai abindake damun shi da
yake boyewa a zuciyan shi wanda ya shafi rayuwan shi shi kadai.

  Mikewa nayi a
hankali zuwa ciki bandaki na shiga na hada mai ruwan wanka na dawo na sameshi
yadda na barshi a zaune yana tunane.

    Hannun shi na riko
a hankali bayan na zauna ina fadin shiga kai wanka kafin magariba ya karasa yi
zaifi kadan samu natsuwa sai ya kalloni a hankali yana kakaro murmushi tare da
fadin nagode my princes.

   Yadanyi kamar zai
mike sai kuma yayi zaune ya hade hanayen shi wuri daya tare da dukar da kanshi
kasa kamar me tunane na kura mai ido bansan lokacin dana furta ya salam a fili
ba ya dago kai yana murmushin kake tare da miko min hannuwan shi alaman in
kamashi ya mike tsaye.

   Haka din nayi mashi
ya mike tsaye tare da dan dafa min kafada ya tausa ya shige dakin na bishi da
kallo a raina ina fadin meke shirin faruwane hakan wai ?

  Fita nayi zuwa
kitchen na dora ruwan zafin da zan zuba a flask don shan shayi don nasan kobai
ci komai ba zaisha tea din ya dan ji nauyin cikin shi a lokacin.

   Kafin na fito zuwa
dakin na samu kayan daya cire na dauke zuwa inda muke tara kayan wankin mu a
dakin a daidai lokacin nake jin muryan su Aisha da suka shigo gidan a hargitse
suna fadin.

   Matan yaya kina ina
kisha labari yau mun faso taro muma bakiga yadda ake kallon mu ba a wurin taron
nan har ana wani dan ji damu a wurin yau.

    Kai gaskiya yau
kin fitar damu fili mun haska sosai wallahi naji dadi ashe sutura shine mace
sai yau nasan da hakan wallahi suna fada cikin jin dadi da yadda mutane suke
wani bamu girma kawai don basu ga wurin raina mu ba yau.

   Gyaran muryan da
yayine daga ciki yasasu natsuwa suna kallona Asmau take fadin yaya ya dawone
halan tana tambaya ?

   Kai na gyada mata
alaman eh a hankali suka mike suka fara kokarin barin dakin ina masu dariyan
hakan tare da fadin baku tsayawa ku gaisa dashi .

   A lokacin ya fito
daga dakin yana kallon su juyowan da Aisha tayi tana fadin bari mu dawo sukai
arba dashi tsaye yana fadin barin dan fita daga masalaci zan tafi unguwa daga
can.

   Yaya ina wuni an dawo
lafiya ta fada lafiya inna ta dawone ya tambayeta tace a, a tana can sai sun
kai amarya zata dawo tace Asmau ma ta dawo suka gaisa daga hakan suka fita
dakin.

  Nayj mai a dawo
lafiya ya fice na mike na shiga na gyara dakin har bandakin lokacin anyi kiran
sallah na dauro alwala na fito.

    Na idar har isha,i
bai shigo ba can naji muryan inna ta dawo suna hira da Dije don haka na fito
don nagaida ita kada inyi laifi ga hakan .

   Na samu sun baza
abinda ta samo a wajen bukin kamar yadda yaran dama suka fada muna da hanne
cewa ko zasuci abin dadi na bukin sai inna ta dawo da dare don yanzun haka tana
nan tana tara komai a cikin jakkanta.

  Gashi ko na gani an
baza a yanzu gabanta can nayi sallama kasan murya na suka amsa min haba haba
kamar basu ba Asmau harda fadin matar yaya keta ?

   Nakai zaune a kasa
gefen su nace inna an dawo ina wuni ya gajiyan jama,a Allah yasawa aure albarka
ta amsa da Amin tana mikawa yarta abu.

   Na dan zauna shiru
ina kallon yadda sukeyi kafin Dije ta fito daga daki kila sallah ta idar tana
fadin shi bai dawo ba har yanzu ko yace bayajin dadin jikin nasane.

    Na dan juyo tare
da fadin bai dawoba har yanzu yace daga masalaci zai tafi unguwane daga can ya
dawo ankace ko halan missameshi uwar ta tambaya har lokacim hankalinta naga
ledan datake kokarin budewa a hannunta ashe alalaine a ciki ta mikawa yar nata.

   Dijece ta bata amsa
da fadin wayasan komi ka damunshi tunda ba fadawa mutane yakeyi ba so  nasan ko matar shi ba fada mata zaiyi ba..

  Nayi mamakin yadda
batai wani nuna damuwanta ga hakan ba saici gaba da harkan gabanta tayi a
lokacin na dan jima kadan na mike ina masu saida safe.

    Ina tare da imanin
matar a zuciya naji muryan Asmau a ranan ita ke fadin matar yaya zaki tafi baki
tsaya anci kayan bukin dake ba mana nagode nace masu nasa kai na suce zuwa ciki
abina.

   Ina shiga sai gashi
an biyoni da kayan wanda alalaine sai wani guntun tuwon amala bakikirin dashi
miyar ma ba komai a cikinsa baida dadin gani a ido.

    Karfe tara da rabi
na dare ya dawo ya samu ni har na kwanta a lokacin bayan ya shigone yake fadin
har kin kwantane princesses ?

    Na dan dago ina
fadin eh ban dade da kwanciya ba ki tashi ga abu nan a falo muci ya fada yana
kokarin rage kayan dake jikin shi a lokacin.

   Duk da banjin cin
komai amma haka na mike ina fadin ba zakasha tea ba ke nan ashe da har na
zubama ruwan zafi a flask ai.

    Wanan ma idan na
samu naci zai wadaceni ba sai nasha tea din ba zan kwanta akwai dai bread a
cikin kayan idan zaki shane ya fada ya shiga bayi.

   Falon na fita na
samu leda guda biyu saman table ya aje na bude tun ban kaiga karasa budewa ba
na fahinci abinda ke cikin ledan namace gashin maza.

    Sai youngt mai
sanyi da tarkacen zaki da bread guda biyu a ciki na fita zuwa kitchen na dauko
plate na juye dayan ledan kazan a ciki an yanka tun a can wurin daya sayo din.

   Ya fito ya zauna a
lokacin nake fadin kun gaisa da innace tadawofa daga gidan bukin ban shiga ba
saida safe ya fada yana daukan goran freshmilk daya daya sayo duk da tsadan shi
hakan wata rana zai kwaso muna shi asha.

  Duk cikin kokarin
shi na ganin cewa ya kula da ruwana kada ya kasa da abindana saba dashi a gida
duk da yasan cewa ba damuwana abubuwan sukayi bana sha koda ya sayo din.

    Kallon shi na
sakeyi ina fadin za a dibanwa su innane ko ina nufin abinda ya sayo din yace
badasu nasayo ba kina iya basu inna ta raina gobe dai zan sayo masu nasu idan
na fita.

    Ganin baici ba
yasana zage ina ci ina mika mashi hakan yasa ya danci sosai yasha yought din
muka kwanta.

   Na fahinci dan
raman da yayi a jikin shi amma naja bakina nayi shiru ban furta hakan ba a
lokacin saidai ina tunanen meya sameshi haka cikin dan lokaci har yayi rama
hakane ?

    Can cikin barcin
mu nake jin kamar ana hayaniya a kaina da kyar na iya bude idona shine ke wani
irin mafalki a gefena lokacin da ganin kasan yana cikin wani irin mawuyacin
hali a mafalkin da yakeyi din.

 A hankali nakai
hannuna saman jikin shi ina dan bugawa tare da kiran sunan shi ya amsa a
firgice nace ka kwanta da kyau kana wani irin mafalkin da ban tsoro.

  A daidai wanan
lokacin ne bakar akuyan nan nasu mai kukan tsiya ta dauki kuka da bata daina ba
har gari ya waye tana faman abu daya gashi ya fita zuwa wurinta tunda asuba
amma hakan baisa ta daina kukan da takeyi ba aranan.

   Ni kaina kukan nata
yakai min ko ina ballesu da na kula hankalinsu ya tashi da hakan can nake jin
muryoyinsu na jiyo muryan inna na fadin .

   Ai na fada maku ku
sayar da bakar akuyan nan tunda ba haihuwa takeyi yanzu ba anki meye amfanin
aje akuya hakane sai kudi ake kashe mata.

   Ba za,a sayar ba nace ba za,a sayar ba tunda
yaron nan ya fahintar damu illan sayar da dukiyan daba namu ba a yanzu.

   Gara mu barta nan
muna kallonta ko shekara nawa zatayi a nan din kamar yadda ya fada sai inna din
tace wahala ko bai kare maku ba ashe don mu ta ishemu gidan nan gaskiya.

  Ta shigesu tana
fadan bakar magana kan akuyan da dan nata ke kokarin dura mata magani a baki
amma akuyar tana bin inna da kallo zakace mutum ne ita lokacin.

    Aiko haka aka wuni
da ita yana faman kula da wanan akuyar tasa mai abin al,ajabin sai zuwa  rana takai kwance ta bar wanan kukan da
takeyi din.

    Shima din sai
wanan lokacin yayi wanka ya fita bayan nayi sallah na samu na kwanta don akwai
barci a idona sosai a ranan.

    Bayan la,asar ya
dawo da cafamen shi kamar yadda ya saba kashi biyu nasu da namu bayan nayi
sallah na dora muna girki kamar yadda na saba.

   Har lokacin banji
duriyan inna ba na dauka ta fitane a lokacin ashe tana daki ba lafiya tun wanan
lokacin datayi wanan maganan ta shiga ta kwanta shine zazzabi ya rufeta zuwa
yamma kuma sai ga zawo ya biyo bayan hakan .

    Ni bansan abin
dake faruwa ba har lokacin ina tsaka da aiki a kitchen naji ihun Asmau hakanne
ya dauki hankalina da sauri na fito kitchen din hankali tashe.

   Sai muka hade dashi
ya shigo part din da sauri ashe kudi zai dauka su tafi asibiti da ita lokacin
nake tambayan shi ko lafiya a gurguje ya bani amsa da innace ba lafiya.

   Salati na saka na
fita da sauri tun dana nufi part din na hangota a yashe kasa tana kakarin amai
gwanin ban tausayi na karaso ina mata sannu sai gashi ya iso wurin yana fadin
ku kamata a fito da ita.

   Nan suka kasa
kamata din gashi shi kuma ya rigada ya fice a lokacinko ganin yadda suka kasa
kamata din dole yasa na yunkura zuwa wurin ina fadin Aisha ta tallaba gefe mu
cicibata.

   Amma kuma sun kasa
hakan don inna ba karamar mace bace gaskiya don tana da jikinta ba laifi gashi
kuma ta sabe babu lakka a jikinta saita kara nauyi.

   Ganin shiru ba a
fito da ita ba har lokacin yasashi shigiwa yana fadin ku kamata mana sai ya
ganni da ita na tallabota a firgice.

    A cikin tsawa yana
kallon kannen nasa yake fadin ba zaku kama mata itaba kun barta da ita haka ina
zata iya daukanta ita, , ,

   Aman da inna din ta
sharo min a jikina ya dakatar dashi ga fadan da yakeyi da kannen nasa yana
fadin subbahanallahi da sauri ya karaso ya kamata daga hannuna ya fita da ita
daga gidan.

    Hankalina duk a
tashe yake duk da kyakyamina lokacin ban damu da aman dake jikin nawa ba sai
binsuma da nayi zuwa kofa ina kallo suka wuce da ita dukan su zuwa asibitin.

   Sai lokacin na tuna
na koma na gyara jikina a lokacin jin kazanta yazo min Allah yasa dan rigan
shan iskane a jikina lokacin don haka na daure na wankeshi na fito ina shanyawa
dije ke fadin.

    Duk ta bata dakin
nasu gaau su kuma sun kwasa sun bisu asibitin ba wanda ya tsaya ya gyara dole
nice na shiga na gyara dakin nasu na saka kamshi a ciki don ya canza kamshin
zuwa najasan datake fitar wa lokacin na fito na koma part dina don karasa aikin
dake gabana na girkin dana dora .

   Basu dawo gidan ba
don an bata gado dole abincin da nayi na saka aka kai asibitin tare da wasu
kayan bukatu muka rufe gidan har dije muka tafi dubanta.

  Gaskiya taji jiki
sosai zakace ciwon kwana biyu tayi ta zabge haka da zamu dawone muka dawo da Asmau
muka bar Aisha can zata kwana a wurin mahaifiyar tasu.

   Kwanan ta biyu aka
sallamota ta dawo gida dole aiki yai min yawa din zatace wanan take so ko
wancan haka nayi ta fama da dawainiyar su sai hakan yasa ban samu komawa
asibitin dubanta ba wai ashe kuma nayi laifin nan kuma ga hakan.

   Shine naji yana
fada tsakar gida yana fadin in ba,a godewa kokarun yatinyar gaba ai abin ya
zama ganin iyaka kuma ?

    Tana gida tana
girki ga wasu aiyukan za ace zuwa dayan da tayi dubuta hakan bai wadatar ba kuma
kashe kanta ake son tayine ina part dina ina jiyo abinda suke fadi.

   Koda ya shigo banyi
magana ba don nagama sharan hawayena ke nan ya shigo shima bai dadeba ya fita
na karasa abincin rana nakai masu nasu a part dinsu.

   Tana wani shan
kamshi dani nidai na kara mata ya jiki na fito abina ashe wasa sabon girki sai
cikin dare bayan kowa ya kwanta ta fara kantara ihun azo a ceceta wata bakar
mace zata kashe ta.

 

Leave a Reply

Back to top button