TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 35

Sponsored Links

 

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [2/11, 8:25 PM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

 3️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Makewayin ba laifi
don an shafeshi da siminti gashi da gani yana samun kula wajen tsabtaceshi ko
uaushe haka kuma baka ma dauka gidan marasa karfine kake.

   Tufafin jikin shi
ya fara cirewa kafin ya watsa ruwa ya dade yana cuda jikin shi ya kuma ji dadin
ruwan sosai ya kwara ya fito take yaji wani iska mai sanyi yana dukan jikin shi.

 Da dan sauri ya
karasa wanan sakin da Shattu ta nuna mai ya shiga bai sauya kayan ba gadon da
ya gani a dakin yakai zaune a kai.

    Sai lokacin
natsuwa ya fara zuwa mai ya fara bin ko ina na dakin da kallo babu wasu kayan
jin dadi a dakin sai wanan gadon da wani mattacen kujera mai zaman mutum biyu
kawai a dakin.

   A hankali yakai
kwance saman gadon sai lokacin ya gane cewa saman gadon kara yake zaune ashe
saidai yadda yasha gyara ba zaka gane cewa gadon karane hakaba.

   Tunane ya fara yi
kota ina zai farayin abinda ya kawoshi wanan kasan don yadda yaga garuruwan
yana da wuya a iya gano mai mahaifinshi haka kai tsaye.

   Dan dama saukin da
yaji shine cewan da tsohon yayi zaibi masu irin sana,an mahaifin nasa a baya ya
bincika masa.

   Yana cikin wanan yanayin
na tunane har barci mai nauyi ya daukeshi a wurin na tsawon lokaci yana kwance
yana barcin gajiya don akwai gajiya sosai a jikinshi gaskiya.

   Karfe biyu ya falka
koshi ba don yaso ba sai don lokacin sallah dake ratsa jinin mai kula dashi da
duk lokacin yayi zai tashi kome yakeyi yayita a cikin lokaci wanan ne ya falkar
dashi daga barcin nasa a lokacin.

   Shatu kawai ya gani
a tsakar gidan tana yan aikace aikacen ta a lokacin ya nufi ban daki ya kewaya
ya fito ya fara alwala don sallah.

   Yana dakin zaune
har akai la,asar ya fito waje ya samu itama Shattun tana daki lokacin hakan
yasashi fita wajen gidan don dama maza ba a san su da zaman gida ba su sai
mata.

   Sannu a hankali
yake takowa daga inda yake tsaye kofan gidan bayan ya gama bin unguwar da kallo
yana nazarin wurin can ya tako zuwa inda dabbobin gidan suke killace kamar
yadda ya hango a sauran gidajen unguwar suma sunyi.

    Nan ya tsaya yana
karewa dabbobon kallo yana mamakin irin kiwon da suka samu suka cika haka sukai
kyau da dadin gani kafin idon shi can ya sauka kan wata akuya dake kiwo a cikin
awakan dake cikin garken.

   Uwargarke sak
yagani a idonshi saida abin ya firgitashi lokaci guda ga kuma akuyan na kallon
shi ta tsura mai ido kamar yadda uwargarke kan kafa shi idanu tana kallon shi
din wani lokaci.

   Kasa boye
mamakinshi yayi don saida ya furta a fili yana nunata yace uwargarke ke nake
gani ko gizo idona keyine ?

   Yarona ka samu
tashi ashe yaji an fada daga bayanshi jin haka yasashi juyowa yana fadin eh
baba ashe barci na samu nayi tun fitowana daga wanka.

    Ai hakan yana da
kyau sosai gara dai daka dan samu ka runtsa din zaka samu ka dan walwale kadan
gashi yanzu har kazo duban dabbobin mu.

   Eh baba kiwon sun
samu kula sosai gasu sun banje suyi kyau sosai gwanin ban sha,awa tubarkallah
masha Allah.

    Kazalika dana ai
kiwo kula sukeso indai ana kula dasu ana basu abinci yadda ya dace sai kaga
Allah ya tarfawa abin albarka kasan kuma mu filani ba a rabamu da kiwo ko da na
kazane kuwa.

   Ya dan murmusa har
lokacin idon shi na kan wanan akuyan yana kallonta cike da mamakin haka a
zuciyarshi.

   Baba dama akuya
sukanyi kama da junane ya tambayi tsohon alokacin da bai shirya hakan ba yaji
tambayan ya fito a bakin shi lokaci daya ya furta hakan ga tsohon.

   Murmushi mai sauti
tsohon ya sake ya dora da fadin yaro mutane ma anyi su da kama balle dabbobi da
halittansu duk iri dayane .

   Sai kuma ya kawar
da zancen ta hanyan fadin yanzu daga wurin abokina nake na soma tambayan shi
labarin mahaifinka ko Allah zaisa a dace amma hakan bai samu ba don ya nuna min
bai san wani wanda ya taba zama a wanan nahiyan na sokoto ba gaskiya .

    Saidai zai saka
bincike a kai shima ta hanyan tambayan mutanen su don shima wani tsohon
mafataucine daya jima yana wanan harkan na sayar da dabbobi a kudu.

   Sosai Ahmed din
yaji dadin jin bayanin da tsohon ke mashi a lokacin nan dai ya kara kwantarwa
yaron da hankali tare da bashi tabbacin cewa ya kwantar da hankalinshi muddin
mahaifin shi dan kasan mambilane za a gano mashi shi in sha Allahu.

  Suna wajen suna hira
har akai kiran magariba abinda yasa su dagawa ke nan shi Ahmed din ya shiga
gida ya debo masu ruwan alwala ya kawo masu.

  Tare dasu akai
sallah jam,i a masallacin unguwar suna cikin wa yanda suka dakata har a idar da
sallah a lokacin bayan sun idar din suka nufo gida kai tsaye tsohon na gaba shi
Ahmed din yana bayan shi.

   Ya dade a zaune
yana maimaita kallon photo don shi kanshi yasan yayi kama da wanan guy din
sosai sadai kamar wanan din zai dan darashi da fari da kuma tsawo haka kuma ya
dan fi shi yasir din dan budawa kadan.

    A ina fattu ta
sami wanan photon kuma wayeshi din na cikin photon da har yake da kama dashi
haka kama ba kuma na wasa ba ?

    Da badon yasan
cewa shine dan fari ga iyayyen shi ba da yace shima wanan din jinin sune don
kamarsu har ya baci sosai.

  To a cikin dangi shi
din dan waye da har bai sanshi ba bai taba jin wani yayi maganan shi ba kuma ko
ta kamanin su duk da dai shi ba wani sanin yan uwama yayi sosai ba.

   Well zai kira Fattu
din yaji waye wanan guy din kila a wurinta zai samu karin bayanin da yake son
sani amma tabbas itama Fattu din taga kamar sune dashi yasa ta turo mai wanan
photon da aka rubutawa Master namu.

   Master ?

Master din me ya tambayi kanshi kafin yaja tsuki yana aje
wayan a gefen shi ya dauko littafin shi yana dubawa.

   Naji dadin zama a
dakin tsohuwar don kuryan ba hayaniya ko gittaiyan mutane kamar wancan dakin
dana baro na farko da muka sauka sai nan din yafi mun can dadin zama.

    Saidai da alaman
abokiyar zamanta a dakin itama tana ji da kanta don tun shigowan ta lokacin
banyi barci ba muna waya da ummah ta shigo muka gaisa bata kara bi ta kaina ba
sai harkokin gaban ta takeyi na shirin kwanciya ta fita batuna nima haka.

   Washe gari ma
hakane mun daiyi gaisuwan safe da ita bayan mun sallame sallah daga haka kuma
bamu kara yin wani magana ba karshema na saka earpiece a kunnena ina sauraren
kira,a nayi barci don haka ban sam me akeyi a gidan ba kuma.

    Sai wajajen karfe
goma naji ana tayar dani daga barcin na bude idona tsohuwan dakin ne mahaifiyar
su mommy a kaina.

    Da sauri na kai
hannu na cire abinda ke kunnena na dan yunkura ina gaida ita da kwana duk dana
lekata da asuba nagaida ita tana fadin
kina barci haka baki karya ba har wanan lokacin yar nan ?

    Zan karya na fada a
sanyaye ina dan murmushi a fuskana toki tashi ga abin karyawan ki nan uwarki ta
aje maki a falo tun dazun su sun fitane zuwa Na,ibawa gidan wan mahaifinsu.

    Na amsa mata da to
ina kokatin mikewa zaune tana fita take kara fadin idan zakiyi wanka sai in
saka a kawo maki ruwan dumi kiyi hakan yasa na gane ba zan samu ruwa a bayin ba
ke nan lokacin.

    Nace wanka zan
fara saina karya tace barin zo ta fita zuwa can saiga wata matashiyar mata ta
shigo da ruwan wankan tana gaidani na amsa tace ga ruwan hjy tace a shigo maki
dashi nan din.

   Nayi mata godiya
tazo zata fita na kirata na mika mata dubu daya nan take ta washe baki tana min
godiya ta karba ta fita tana murna ni kuma na mike zuwa ban dakin nayi wanka
tare da brush na fito.

   Kamar yadda na saba
idan ba makaranta zan fita ba ko wani waje nakan tsaya in bata lokacina a
daidai wanan lokacin nayi sallah nafila na rokawa kaina saukin rayuwa da dacewa
ga rahaman ubangiji da nemawa iyayyena gafara.

   Nan ma din hakan
nayi don nayo alawala na fito nayi raka,a biyu na zauna ina addua a daidai
lokacin wanan yarinyar da muka kwana saman gado daya tashigo dakin .

   Kallona tayi ta
dauke kanta gefe taci gaba da abinda takeyi har zuwa shiga ban dakinta don ta
kewaya sai gata tafito kuma a lokaci guda tana fadin.

    Don Allah a ina
kika samu ruwan wanka ne nace wata mata ta kawo min nayi daga haka ta fice daga
falo can naji muryanta tana fadin.

    Nima a saka a kawo
min ruwan mana zanyi wankan yanzu kifita min a ido yar nan ko ita wanan bata da
lafiyane kuma bakuwace ita kinga dole nu kula da yar mutane ko.

    Bandai san ya
sukayi ba naga wanan ta dauko ruwan da kanta tashige bayi tana wanka har na
gama shirina na nufi falon tsohuwar bata fito ba.

    Ruwan shayi na
dansha koshi ban iya shanyewa duka ba nabar saura na mike na koma cikin dakin
na haye gado wanan din na sama tana shiri kallo daya tayi min ta kawar da kanta
gefe har tagama ta fice ta barni.

   Ina nan ni kaidai a
dakin tunda ba sanin kowa nayi ba zuwa can rana sosai na fara jin muryan mommy
sun dawo sunawa mahaifiyar su bayani.

   Zuwa can mommy din
ta leko tana fadin daughter na tafi na barki ke kadai sai ta sameni a shirye na
saka wani atamfa blue da adon farin filawa
a jikina sai dan kwalin shi da gyale fari mai kyau a gefena ajiye koda
fita zai kamani.

    To kinyi wanka ko
nace eh hjy tasa an bani ruwan wanka nayi OK kin karya dai ko ta tambayeni eh
na bata amsa cikin ladabi to mike ki fito waje mana cikin mutane ki zauna kin
kunshe kai a daki ke kadai kamar amarya.

   Ko wurin kawar taki
ba zaki fito ba kya zauna ke kadai ina abune a waya aina fita na dai dawone na
fada ina ita maryam din ?

   Wace maryam na
tambaya cikin alamun rashin ganewa wace kuka kwana a nan tare oho ta fita dazun
na bata amsa.

   Taso muje ta fada
ta juya tana fita daga dakin na mike don dole nabi bayanta wacan dakin da muka
fara sauka muka nufa da ita na zauna a nan wanka mommy din ta shiga ta fito duk
ina zaune saman gadon na dan kishingida a lokacin.

   Hankalina yana ga
wayana ina duban sakonni wanda ya waci da yan course din mune nake charting don
banda wasu abokan kirki da zan rika hira dasu.

   Muryan mommy ne ke
fadin anjima za aje kamu na fada maki kayan kamu wanda mu zamusa yan gidan ango
jin hakan yasa na dago kai na amsa mata.

    Ta shiga ta fita a
dakin har yamma yayi aka fara shirin fita zuwa wurin kamu din lokacin na mike
na koma dakin hjy inda kayana suke yanzu tana falo na gaida ita na shiga.

   Nan na samu wanan
yarinyar maryam tana shiri itama duk da nasan zata girmeni gaskiya ko ba a fada
ba na shigo banyi mata magana ba bayan sallama na shige ban daki dan ruwa kadan
na samu a ciki saidai hakana nayi amfani dashi ina tsanda na fito .

      Falo na nufa na
tambayi wanan matar ina kwatance sai gata ta shigo dakin da gani irin matan
unguwar nan ne dakan dafa wani su samu inda zasuci abinci suma a cikin rufin
asiri don yadda naga tana aiki kuma ana sata yi da wasu aike haka.

  Bayan mun shigo daga
ciki nake fadin kin gane dakin nan nake son a wanke robobin ruwan nan a dinga
saka ruwa ko wani lokaci don Allah.

   Wani kallo wanan
maryam din ta jefoni dashi amma tana ganin na jawo jakka ina fadin don Allah
koda wanine ki saka yayi muna hakan ga wanan kiba maishi don Allah a bar barin
ruwa yana katsewa a ciki.

    Godiya matar ta
fara tana fadin ai angama yarinyar arziki kada ki damu da komai baki jin babu
tunda kema kina bayarwa ai har abinda bakice nayi ba za a dinga maku a dakin
nan insha Allahu.

    Matar ta juya ta
fita tana godiya ina jin muryan hjy mai dakin tana tambayan ta tana fada masu
yadda mukayi naji tsohuwar tace ai tayi maganin ku shine daidai daku.

    Tare dasu mommy
karima zaku fitane naji muryan maryam din dake ji da kai tana ganin tafi kowa a
dakin ta fada na dauka waya takeyi yasa na shareta.

 Dake nake nace da su
mommy zaku fitane ko mu fita tare don ni ba wai nasan su bane sosai nace ayyah
wallahi ban sani ba gashi dai ina shiryawa .

   Maryam din ta fara
saka kaya a jikin ta kafin in saka tana wani zuwa tana dawowa tsakanin falo da
dakin kafin nima na saka kayan na fito shar dani a cikkn tufafin.

   Zuwa lokacin kusan
duk wanda ke gidan ya saka ankon shi a jikinshi ana fita waje mommy ce ta shigo
dakin da sauri tana fadin daughter kin gama shirin kuwa ?

   Eh mommy nagama
mama ai tare zamu tafi maryam din dake saka wani abu a jakkarta ta fada sai
naji mommy tace shike nan ma da kunsan wuri sai nace a baku key kuzo tare da
angone kuma ku shiga cikin su.

    Wa zaija motar
maryam ta tambaya naji mommy tace zahra mana wace keda mota babba na shiga
wurin milayan biyu da rabi naji ance bayan wanan ma kina da wata ko ?

  Na dan gyada kai a
hankali yarinyar ta kara kallona cikin mamaki mommy dai ta juya tana fadin
barin gani ko za a iya yin wani abu ta fice daga dakin kai tsaye .

    Sai zuwa can mommy
din ta aiko wai mu fito mubi wani usman a motanshi driver ya fita da motan da
take son mu shiga din.

   Ba ruwana don haka
yadda sukace zanyi don duk a takure nake zaune dasu mun fito din wani guy ne
wace tazo kiran mu ta nufa tana fadin ya usman gasu nan sun fito.

  Yana magana da wasu
ya juyo ya kallemu suma sauran kallon mu sukeyi a dan sama sama muka gaidashi
ya amsa yana satan kallon mu can yace kune zan tafi daku ko maryam din ta amsa
mashi.

  Nikan baya na nufa
maryam ta bude gaba ta shiga wanan data kiramu itama ta biyo mu muka shiga zuwa
wurin taron kan mu din .

   Wurin ya cika da
taron maza da mata ga motoci nan ko ina ka duba anyi decoration irin na
gargajiya anko kan ba a maganan shi yafi kala goma da idona ya gani a wurin.

  Yadda akai taron ya
nuna angon dan gatane sosai don yannen nasa naji dashi muna tsaye a bakin motan
da mukazo cikin shi don tawagan ango muka biyo mu.

    Wayana ne yake
vibration daga cikin jakata nake laluboshi mommy ce na dauka take fadin kun iso
ko nace eh mommy take fadin ki fadawa maryam cewa zaku shigo da angone akwai
yan matan da zakuzo a tare din kifayi masa liki sosai a san dakin shigo na
danyi murmushi ina kashe wayan.

   Abinda na kula
dashi shine na farko mommy nada son asani sai nabiyu kamar suna da adawa a
tsakanin su da yan uwanta sai kuma nayi tunanen ko don Abba ya ban kudin bukine
a gaban ta oho ?

    Mun kai minti
ashirin kafin ace mu shiga fili amarya naciki aka bamu hanya mc na shelan fadin
ga angonne zasu shigo suyi liki.

   Kidan ya canza
saiga wani da sauri cikin abokan angon na fadin ke dake dake ya nunamu mu hudu
yace wai mune a gaba don Allah ace ni cikin mamaki maryam ta tabani na juyo ina
kallonta.

   Alama tayi min da
ido nace OK ya juya ya tafi haka din kuwa muka shiga wurin muna gaba sauran
tawagan na bayan mu.

   Sam ban yarda nayi
wani rawan zakewaba don dama ba gwanan rawa bace ni din har zuwa tsakiyan taron
angon yazo ya tsaya kusa da amaryan shi.

    Nan wuri ya rude
da rawa na fara ja baya kadan na samu wuri na tsaya ina kallon abindake wakana
a wurin don babu ma yadda zaka shiga kace zakayi liki ai.

   Har yakai mc din ya
roki mutane da a fita a ba amarya da ango fili don Allah saida kyar mutane suka
dan rage wata gwaggonsu ta karbi abin magana tace bata son ganin kowa a cikin
fili sai amarya da angonta kawai a fili.

  Dole mutane suka rage
yawa bayani me gamsarwa tayi wanda yasa mutane suka natsu akaci gaba da gudanar
da event din.

   A wanan lokacin da
akace yan uwan ango su fito su nuna farin cikinsu ga ango maryam data dawo kusa
dani ta tsaya take fadin muje mu dan likawa uncle mu fito.

    Tare muka shigo
duk yadda bakuwa ko bako yake a wuri za ayi saurin gane hakan don daga ni har
maryam din bakine dan dama ita wasu sunsan mahaifiyar ta.

    Amma nikan sai
mamare sukeyi a kaina da tambayan yar waye ni din cikinsu ba amsa don basu tambaya
kusa da wanda ya sani.

    Yan dari biyar
biyar nake masu liki wanan yasa mc tambayan suna aka fada mai Zahra nan yake ta
ambatan zahra Abuja.

 

Leave a Reply

Back to top button