TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 27

Sponsored Links

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/25, 10:32 PM] +234 815 085 0067: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣7️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Zahra lafiya kike kuwa meke damun kine yau zaki bar school
da wuri haka don naga kin fito daga aji ana karatu zaki gida ?

   Wani irin faduwan
gaba naji ya ziyarceni lokaci guda ga kunya kuma haka yasa na dan dauki lokaci
ban iya juyowa na fuskance shi ba lokaci guda.

    Kafin na tattaro
karfin halina na juyo tare da fadin ina wuni bana jin dadine yasa zanje gida
yanzu nasha magani indan kwanta nagode sai anjima na fada da sauri na fada
motana ina kokarin tayar da motan.

   Hannuna dake rawa
na kasa saka key din motar da kyau yasa shi matsowa zuwa window motan yana
fadin kina ko cikin hankalin ki zaki iya tukin motan a haka.

   Murmushin dole na
zakulo a fuskana kamar makaryaciya nace meka gani zan iya mana a daidai lokacin
motan ta tashi ban kalli inda yake ba sai horn nayi mai na barshi wurin yana
bina da kallo har na bace mashi.

    Ajiyan zuciya ya
sauke ya juya a hankali ya koma wurin da yafi yawan zama wasu lokuta inda a nan
ne kuma muke haduwa muyi karatun dashi.

    Bai dade da zama
wurin ba su munir suka sameshi gaisawa sukayi dashi manir ke fadin yau master
da kanka karigamu isowa ajin ?

    Dan murmushin
gefen fuska ya sake ba tare da yai magana ba don inda sabo a yanzu sun saba da
hakan nasa na rashin magana wanda kuma a hakan har muka shaku da juna dashi
kowan mu ba mai son yawan magana ba cikin mu.

   Sunyi karatun su na
dan lokaci duk da sun gane karatun nasu yanzu akwai sauyi a cikinshi sosai don
bai yawan nacewa wurin maimaita masu.

   Bayan sun gama an
fara watsewane a wurin tana batun wucewa ya hada kayanshi hannatu ce taki tashi
tana zaune ya dago ya kalleta yana fadin .

   Hannatu lafiya dai
ko yana kallonta ta dan gyara zama tana kalllon shi tace Master magana nake son
yi dakai akan zahra.

   Zahra ya ambaci
sunan a cikin mamaki kafin ya dan kada kai yana sauke murmushi tare da fadin
wani abu ya farune sai hannatun tace a,a master.

   Kasan dai zahra
bata da sata abokiyar data fini school din nan kaf don haka ta fada min duk
abinda ya faru a sallah break din nan da Daddysu yazo.

   Muyi magana ta
fahinta na bata shawara a jiya akan zamu ganka yau mu baka hakkuri kan hakan
sai gashi yau din ta tashi bata da lafiya don haka ta tafi gida tun dazun.

   Eh na ganta da zata
tafi din nake tambayan ta ko lafiya zata koma gida wanan lokacin take fada min
bata jin dadin jikintane.

   Ok ka ganta ke nan
nasan  duk akan matsalan takune bata jin
dadin jikinta amma master sai nake ganin kamar zakuyiwa kanku sakacin da zai
dameku a baya.

  Akan me fa ya
tambaya yana kallonta a cikin mamaki murmushi ta sauke a fuskanta tace haba
master na dauka ai in kun boyewa kowa hakan ni ba zaku boye min ba don nasan abinda
ke tsakanin ku yanzu dai.

   Meke tsakanin mu
din banda abinda ke tsakanina dake shine karatu nan da mukeyi sun kuma ce ta
daina yanzu shike nan kowa ya tsaya a matsayin shi ai.

   Nasan ni din ba
ajinta bane don bankai matsayin tsayawa da yarinya irin zahra ba kema kin sani
abinda kowa ya sani ne kuma don haka kada yanzu kema ki shiga cikin masu ma
alakata da zahra din wani fassara na daban.

    Murmushi Hannatun
ta sauke mekama da yake a fuskanta tace nawa akayi muka gani a garin nan
matsala dai ko wani mahaifi da nasa kalan fahintane .

  Shi mahaifin zahra a
nawa fahintar an kai masa zancen nakune ta baibai yasa ya hau haka ba tare da
bincike ba a kai har ya yanke hukunci irin hakan a tsakanin ku.

   Hannatu na kula
kina son jan zancen da nisa yanzu bayan an rigada an wuce wanan wurin ko nake
gani yace na bar ko wani irin halaka da yarshi na kuma bari.

  Itama din ta bar
hakan ba sai kowa ya tsaya matsayin shi ba yanzu kuma ke kanki kinsan hakan ban
kai matsayin da zan zauna da zahra ba gaskiya kema kin sanda hakan.

  Ita zahran ai bata
dauki haka  ba idan ka duba irin rayuwan
ta na saukin kai a cikin mu sam bata nuna cewa mu din ba ajinta bane take tare
damu.

  Ai akwai diyan
attajirai irin ta masu jan aji cikin makarantan nan wasu ma basu ko kai matsayi
irin nata ba amma suna ji da kansu cewa su din diyan wasu kusan garine su.

    Ni a ganina
gaskiya ya kamata ku tsaya ku fahinci juna kai da Zahra tunda kuna son junan ku
a yanzu kowa kuma yasan da hakan gareku.

    Haba hannutu ban
zaci wannan zancen zaki zo min dashi ba a yanzu don da ban tsaya sauraren ki ba
gaskiya mutumin nan yai min iyaka da yarshi fa tare da kakausan murya kan
hakan.

   Itama yar nasa da
alaman tabi umurnin mahaifin don haka kibar wanan zancen don Allah ta tafi
hakana don gujewa matsala nan gaba kan hakan.

  Abu daya nasani
shine idan naganta a cikin matsala zan iya taimaka mata final yana fadin hakan
ya fara tafiya da niyar barin ta surin zaune yaji muryan ta na fadin.

   Saika shirya karban
mumunan labari game da zahra don kuna kiris da jin abinda bashi ba a kanta nan
da yan kwanaki kada  don hakan yanawa
rayuwan zahra barazana a yanzu.

   Juyowa yayi da
sauri yana kallon ta kafin ya bude baki yace me hakan ke nufi ke nan tace
abinda idon ka ya gano maka dazun game da ita.

  Ban fahince ki ba
hannatu kaje kayi tunane a kai ta bashi amsa ta mike ta bar wurin da sauri ya
bita da kallon mamaki kafin shima yasamu ya daga kafanshi ya bar wurin cikin
damuwa.

    Tunda na dawo na
fadawa ummah banda lafiya ta ban magani tare da zaton ko ciwon kainane yake son
tashi min har hayaki da shakawa duk saida ummah ta tsareni nayi.

  Kafin na shige
dakina nayi sallah na kwanta sai barci mai nauyi ya daukeni ban falka ba sai
karfe shidda da rabi da kyar na iya mikewa na shige ban daki na dauro alwala na
fito.

   Ban daga ba saida
nayi magariba da isha,i lokacin har ummah ta leko ta gani kona tashi daga
barcin da nakeyi saita samu ina sallah.

    Abinci na fito
naci tare da kannena na koma daki don jikina da ya danyi min nauyi a ranan
wanka nayi nashirya kwanciya tareda karanto adduan kwanciya nakai kwance.

  Kamar ana jiran in
kwanta a lokacin wayana ya danyi tsuwa alaman kira ya shigo saidai flashing ne
kiran nayi mamakin hakan amma sai na zaci hannatu ce ke min hakan don itace me
dabi,an flashing a kira.

   Bandaga inga mai
mun kiran ba lokacin naci gaba da abinda nakeyi nakashe bedside lamp dina na
lumshe idona a hankali.

   Amadi dake tsaye a
kofan gidan su wanda dawowan shi ke nan unguwan tasu wuri  ujulanshi ya sake danna ma lambana kira karo
na biyu gaban shi na faduwa sosai lokacin.

   Saidai kwarin
gwiwan shine zancen su da hannatu don ya karkare wunin ranan da wanan zancen
arashin da hannatu tace idan baison ya rasani yai wani abu don ina gab da
salwanta rayuwana.

  Gashi basu samu
tsayawa da ita yaji ma,anan fadin hakan ba tayi tafiyanta ta barshi da tunane a
zuciyar shi wanan ya sakashi a cikin damuwa sosai a ranan .

  Don haka yaga
dacewan ya kirani yaji meke faruwa saidaya danna kiran farkone yaga mezaice
dani din bayan warning din da mahaifina yayi mai a kaina cikin kakausan murya
da cin zarafi.

   Har ya juya zai
shiga gidane wata zuciya tace dashi ya sake kirana ko zan dauka din zuciyan shi
na bashi cewa anyi min kakausan warning a kanshi don yadda yagani a idona
lokacin.

  Don hakane ya daure
ya danna kira a wayan nawa yagani ko zan dauka in sauraren shi sai yaji kiran
ya shiga saidai wayan yana ringing ban daga ba ga zuciyar shi sai bal bal
yakeyi yana tsaye a cikin duhun unguwan shi kadai.

    Salamu Alaikum
yaji daga bangarena cikin muryana mai sanyi ina mashi sallama hakan yasa ya
gane banyi blocking din layin shi ba ashe kamar yadda ya zata.

    Ya amsa da
wa,alaikis salam zahra ya jikin naki da sauki ko ya fada don bai san me zaice
dani ba a lokacin sai yaji nace.

   Ohh master ne naji
sauki wallahi nagode ya kake ya kaka a gaida ita kaka tana lafiya zataji ya
fada a bangaren shi .

  Sai kuma mukai shiru
na dan lokaci shi baiyi magana ba ni kuma ban kashe wayan tasa ba lokacin
lokacin ina sauraren shi don ina gudun kashewa ya dauka wullakancine hakan .

   Saboda wanda ya
kula da kai har yakira yaji lafiyan ka ya gama maka komai a rayuwa ai don
hakane na jira naji har ya kashe ko kuma yana da abin fada min lokacin.

   Zahra!!! Duk da
mahaifin ki yai min iyaka dake yace ni din da sana,ata da komai bankai matsayin
koda sabulun wankanki banyi darajan shi ba balle nace zanyi soyayya dake a
rayuwana ba.

  Duk da naso fadawa
Alh cewa ni din ba wai soayya nake yi dake ba a lokacin zaman amana da mutunci
mukeyi saidai daddy bai bani daman yin hakan ba gareshi.

   Yace ni din banda
asali da arziki da zance zanyi mu,amula dake don matsayina baikai ga hakan ba
saboda haka in rabu mashi da yarshi ko kuma yasa a wullakantani da kowa nawa a
garin nan.

  Ido na runtse ina
jin wani irin zafi a raina yayin da sautin muryan shi ke amayar min da zancen
Abba na ranan gareshi don haka zahra kada ki dauka cewa na sherekine don son
raina ko rashin damuwa da lamarin ki .

   Allah ya gani zahra
ke haskene a cikin rayuwana don haduwa dake ya zamema rayuwana alheri a yanzu
koda kon barni zahra ba zan taba mantawa da alherin ki gareni ba don kece kika
haskawa rayuwana fitilan hanya madaidaiciya a yanzu haka.

   Enough Ahmed enough
ka dauka cewa ba maiyiwa wani sai Allah a rayuwa  bayinshi anyi hakan ne don aga an hanani
farin a rayuwana ko uwata tayi baki ciki kamar yadda akeson ganin mu kullun.

     Abu daya na sani
na kuma rike har in ina son kane da gaske ba wanda ya isa ya hana wanan a
tsakanin mu don kawai kai din baka nuna hakan bane na kuma san bashi mukeyi ba mutuncine
kawai.

   Naja bayane kuma
don nasan Abba ya saka muna ido don kada najawa rayuwan ka matsala kana gab da
gama karatun ka a yanzu din don hakane banson najawo maka matsala.

    Murmushi naji yayi
kafin ya sauke wani ajiyan zuciya da har nake jinshi yace zahra banda wani
matsala indai a kankine duk abinda Abba zaisa amin idan har zan samu zuciyarki
na dauki hakan a mukadarine a gareni kan samun ki.

    Idona na lumshe
ina jin wani iri a zuciyana yaci gaba da fadin tsorana daya a yanzu shine kada
na nace akan abinda zan dawo ina wahala daga baya kanshi ya kasance cewa ke
baki min irin son da nake maki a zuciyana .

    Har yayi ya gama
ban samu bakin fadan komai ba ina dai sauraren shi ga hawayen daya wanke min
fuska ni kadai a daki ina tunane saida ya ji shirun yayi yawa yake fadin kina
jina zahra ?

   Hello Zahra kina
tare dani kuwa ko kin daukane na amsa da ina ji Ok kin fahinci me nake nufi
kiyi hakkuri da hukuncin Abba a kan mu ba sai mun hadu bane alakan mu zai daure
dake matukan waya yana aiki zamu iya gaisawa har zuwa lokacin da kika shirya
hakan jin nayi shiru ba amsa yace

  Kina jina zahra nace
naji idan mun hadu zamuyi maganan sai anjima na kashe wayan yabi wayan da kallo
na dan lokaci kafin ya aje ajiyan da dan karfi ya fara kokarin tura wayan cikin
aljihun shi.

   Daga kai yayi ya
kalli hanyar daya ratsa ta gaban gidansu sai yan mutane dadaya ke wucewa a
lokacin hakan yasa yasan dare ya fara dan nisa ya cire kafa ya daga da niyar
shiga gida a lokacin Dije data gaji da zaman jiranshi ta leko daga cikin gida
suka hade.

    Amadi lafiya yau
kakai wanan lokacin baka dawo gida ba tana tambayan shi cikin nuna damuwanta
gareshi a lokacin.

   Yanzun ba gani ba
Dije, na dan tsaya yin wani abune a nan waje ai tundazun ina kofan gidan nan
bandai shigo bane ciki ya bata amsa yana skn su shiga cikin gidan nasu.

   Amadi Dije ta
ambaci sunanshi a sanyaye ya juyo yana kallonta tare da fahintar akwai wani
abinda ke faruwa da tsohuwan zomu shiga ciki yace da ita ta fara takawa zuwa
shiga cikin gidan nasu tabiyo bayan shi a baya.

    Kayan daya dauko
ya fara ajewa kofan dakinshi kafin ya dago ya dan duba bayan shi har lokacin
Dije tana biye dashi kamar jela.

  Muje daga ciki yunwa
nake ji Dije banci komai yau tun wayewan gari sai kunun tsamiya danashi kafin
na shiga makaranta.

Leave a Reply

Back to top button