TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 21

Sponsored Links

 

 

Tsoki naja nayi wurgi
da wayan ina dana sanin zuwa wanan gidan a ranan da banje ba da hakan bai
sameni ba ai sai naji duk wani farin ciki da dan walwalan dana samu ya gushe a
zuciyana sai zallah takaici da haushi tare da wani kunci daya tokare min
zuciyana.

Ban iso gida ba sai
wajajen magariba ganin kofan gidan namu ba yawan jama,a yasa na gane cewa Abba
ya tafi ke nan shi da Amaryan shi.

Gwiwa mace haka na
fito daga motan na rufe na rataya jakata zuwa cikin gidan namu da sallama na
bude kofan part din mu da ake rufe tun shida kamar yadda musulunci ya koyar
ayi.

Ummah ne falon
zaune da kanne na jin karan bude kofan yasata dago kai gareni tana fadin yau
ina kika tsaya haka baki dawo da wuri ba ?

Dan daburcewa nayi
kafin na samu natsuwa ajikina nace mun tsaya summit din assignment ne ummah
bana son wanan dadewan haka a waje kisani dai ke mace ce.

Toh ummah na fada
don a matse nake na isa dakina ina shiga jakka da yan takardun dana riko na
wurga saman gado na fada ban daki fitsari nayi sosai kamar ba zai tsaya ba a lokacin
yadda na zubashi.

Sai lokacin na fara
samun sa,ida a jiki na mike kayan jikina na kalla kafin nayi shawaran kwabesu
cikin bandakin tare da wankan dana darji jikina da kyau da soso da sabulu masu
kamshi na fito na saka doguwar rigana a daidai lokacin an fara kiran sallah.

Don haka na tayar
da sallah dama da alwala na fito daga bandiki din ban fito ba saidana sauke
isha,i nayi addua na mike na fito don na samu abinda naciwa cikina.

Dining na nufa na
bude abinci ina diba kani dake bi mun yazo yana fadin anty zarah nima ki zuba
min banyi magana ba amma ji nayi kamar ya dora min wani aiki mai nauyi akaina.

Na jawo plate na
zuba mai nasa sanin halinsu yasa na zubawa kowa nasa a lokacin bankai ga zama
ba sauran suka fito wurin dan suci abinci basa wuce takwas zuwa tara basu barci
ba sai ummah kadai muke bari tana tsabgoginta.

Nan muka fara cin
abinci sai karan cibi kakeji a wurin da dan surutun yaran dake tashi ummah ta
budo kofa tafito daga daki zuwa falon .

Ai ki basu abincin
ne ashe yasa najisu shiru basu shigo damuna ba munan tare dasu tun dazun na
bata amsa auta da kanki kikecin abincin ta kalli yar kanwar mu dake ci a
wahalce.

Kafin nayi magana
kanin mu ke fadin ummah tace bata son anty ta batane karban spoon din tayi
hannun yarinyar ta fara bata daga can kanina yace ummah yaushe Abba zai dawo ?

Ummah wai sun
tafine na tambaya ina kallon fuskan ummah din a inda take zaune, tace dazun da
karfe hudu suka tafi take naji wani iri a raina lokaci guda.

Don gaba daya na
kula wanan zuwan na Abba iyayyen mu gaba dayansu basuji dadin zuwa  nasa ba don sai shi da Amaryan shine da
yanuwan dake sintiri a gidan namu da sunan zuwa ganin amarya don ace tana raba
masu kyauta idan sunzo yasa sukai ta tururuwan zuwa ganin ta din.

Lokacin na fahinci
cewa da wata manufa sukayi hakan duba ga yadda a dasuke bin mama suna banza da
ummah watau sai inda akalan Abban ya juya a nan suke suma ke nan don neman abin
duniya.

Magana ummah take
min amma sai taga ba saurarenta nakeyi ba na shiga dogon tunaneni a lokacin wai
me kike tunane haka wai ?

A,a ummah na fada
ina nisawa kafin naci gaba da cin abincin dake gabana ummah tacigaba da fadin
ai gara da suka tafi yau din don zaman su zai iya jawo fitina a gidan nan tunda
dan zuwan nan nasu Allah kadai yasan iya fitinan da hakan ya haifar a gidan
nan.

Yanzu zama yake
sosai a cikin gidan nan tunda an hada hardani waini makirace tunda na girka
abinci dasu kamar yadda yabada umurnin a girka masu har kwana nawa zatayi ta
tafi inda tafito da zan tsaya yin kishi da ita.

Ita bata gane cewa
hakan yafi muna rufin asiriba da ace sai an dauko abinci daga gidan hjy an kawo
nan mu muna kallo zaifi zafi da cin zuciya a garemu.

Yanzu ba gashi sun
tafi ba an dai rabu lafiya aurene baka da hujjan hana namiji yin abinsa idan ya
tashi don me zan tsaya fadan kan abinda nasan bada maganin sa .

Iyaka dai inyi fatan
Allah ya hau dani saman kansu duk wani sheri ko mugun fata mutum ya nufeni
dashi ya koma kansa ni kuma ubangiji Allah kada yabani ikon tunanen da zan
cutar da wani a cikin su.

Amin na fada ina
lumshe idanuna lokaci guda kafin nace sai azumi ke nan Abba zai dawo yanzu bana
ba zai  fara azumi tare damu ba a nan ke
nan ?

Tunda yana da mata
a can yanzu ba zaizo nan ba sai azumi ya raba tsakiya ke nan zaizo rabon sallah
ga mutane yadai bada sakon ku nan ya bayar a baku yana hannuna.

Mungode muka fara
fada duk da Abban bai kusa damu a lokacin amma hakan bai hana munyi godiya
gareshi ba yadda muka sabayi a gaban shi.

Ummah mutanen nan
dana kaiwa kaya dazun suna ta godiya sosai wallahi tundai tsohuwar nan dana
kaiwa gidanta tayi tasa albarka sosai wallahi tana maku addua.

Kallon mamaki
ummah ke min a lokacin kafin tace dani wace tsohuwa ke nan kika kaiwa sadaka na
dan natsu nace kakan wanan din Ahmed din na
na school din mu wanda ya taba taimakona din nan har ya kawoni gida.

Kinsan gidansu ne ta
tambayeni nace eh mun taba zuwa da yawan mu gidan mu gaidashi don shike taimaka
muna a school sosai sai muka hada kudi dubu bibiyu mukaje gidan gaidashi.

Maamah kin fara yawo daga school ba tare da
sanina ba ke nan da sauri nace a, a ummah wallahi banda nan ban taba zuwa gidan
kowaba wallahi ko in group mukaje yau kuma tare dasu hanne kawayena mukaje
gidan.

Ban dai son hakan
idan zaki wani wuri daga school ki dinga fada min na sani kada ki kara zuwa
wuri ba tare da sanina ba a gidan nan nace kiyi hakkuri ummah.

Daga hakan ba wanda
ya kara wani magana kuma a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi
kan hakan daga baya ne na mike nabar falon zuwa dakina.

Wajajen karfe hudu
na asubahi Dije ce kwance tana barci a dakinta sai tayi mafalki ga mutum tsaye
a kofanta yayi mata sallama ta dago ta amsa mai yace.

To uwargidan mu ni
zanyi tafiya ga amana nan na bari a hannun ki duk da nasan kina da rauni a wani
fannin amma ki kula ki kara kulawa  don
mai yuyuwa zan dauki lokaci ban leko nan din ba.

Baki na rawa Dije
ta tambayeshi yace amman dai aiba wani sabo bane a wurin ki illa amanan wa
yanda kika saba riko gidan nan ga tsiro nan garine wurin wanda yafi garin ga
baki daya a wurin nan.

Idan kunyi gigi ko
gangancin cireshi kunyiwa kanku hasara mai dinbi yawa a nan Allah ya kaddara
saduwan mu wani karon idan da rabon mu sake ganawa a duniya .

Kamar zai tafi ya
tsaya yace kibada goyon baya ki karfafawa mai rauni zuciya ki daure ki bashi
goyon baya alheri hakan zai zamo maku wara rana.

Yana fadin hakan
tanemeshi ko kasa ko sama bata ganshi ba bataga inda yabi ba adaidai lokacin ta
falka daga barcin kunnuwan tane ya fara jiyo mata kiran sallah ladanin can
kasan unguwar su yana kiran sallah.

Ga wani zufa
dayake karyo mata ko ina a jikin ta sai zancen mafalkin ya fado mata a rai take
takai kallonta ga kofa kofan yana rufe yadda ta turashi ta tangale da katon
kuttuture ice yadda take turawa idan zata kwanta.

Ladanin masalacin
sune yayi kwance kwance ya kira sunan ubangiji da karfi har ta dan kadu don
firgicin dake tare da ita a lokacin.

Motsin fitowan
Amadi daga dakinshi taji hakan yasa hankalinta dan kwanciya budan kofa tayi
saidai bata fito ba tana ciki tana dan kimtsawa saida taji fitowan jikan nata
daga bandakin tafito daga dakin nata.

Kin tashi Dije ya
fada yana kaiwa duke eh barkan mu da fitowa an tashi lafiya yaya daren me
yuyuwa iya gaisuwan da zasuyi ke nan a ranan sai kuma dare su kara tashi.

Tambayan shi takeyi
da ba a daiga wata ba ko yace wallahi Dije har na kwanta na dade banyi barci ba
ina dako ki za,ayi shelan cewa anga wata mu dauki azumi sai naji shiru.

Toh gamu dai sai mu
kama baki zuwa safe mu gani ko zamu samu labarin ganin watan a gari tunda mu
nan bamu da redio ko abin sani tashige bandaki yayi akwala ya shige dakin shi.

Wayan shi ya dauko
ya haska sako ya gani a wayan da baisan da shigowan shi ba tun daya na dare
sakon ya nuna ya shigo mai number zarah ce take sanar mashi da cewa anga wata .

Da sauri ya fito
yana nufar inda Dije din take zaune yana fadin Dije wai ashe anga wata tun jiya
amma ba a sanar ba ko meyasa basuyi yekuwan cewa anga watan ba yadda aka sabayi
a baya can.

Ikon Allah anga
watan ke nan ta fada saimu wuce da saje ke nan don yanzu ba halin cin abinci
don kadan ya rage a kira sallah.

Duban lokacin yayi
yace zaki iya gagautawa ko ruwa kisha don akwai kusan minti ashirin yanzu kafin
a tayar da sallah.

Hakan sukayi shi
dai Amadin ruwan fura yasha sai ruwa daya kora bayan niya daga haka ya fice
zuwa masalaci yayi sallah itama Dije ta shige dakinta ta fara gabatar da Nafila
lokacin.

Garin yayi tsit
baka jin motsin mutane ko ina haka ba yawan mutane a titin sai jefi jefi haka
yan makaranta da ma,aikatan dake fita aiki suke dan fitowa a gidajen su  zuwa wajajen tsabgogin su.

Haka na shigo
makarantan shima shiru ko ina kamar ba mutane
mota na parker na fito ina kullewa naji muryan shi a bayana yana fadin.

Barka da fitowa Zarah
na sheda muryan shi don haka na juyo ina fadin ina kwana brother lafiya ya bako
jiya kin taimakemu sosai wallahi da yau saje zamuyi dagani har tsohuwar kakata
a gidan mu.

Ban tashi ganin
sakon ba sai bayan har nayi alwala ina shirin fita sallah na dauko waya nagani
mun gode kwarai Allah ya nuna muna karshen shi lafiya nace Amin.

Kana ta godiya
kamar wani abu wanan hanyace ta taimakon juna ai nasan ko kai kaji zaka aiko
muna da hakan ya dan murmusa kafin yace.

A gaskiya zarah
naso ganin ki dama muyi magana kan wanan dawainiyar da kika dauko yi muna a
gidanmu haka ina gudun abinda mutane zasu fada kan hakan .

Gara mu tsaya da
mutunci haka a tsakanin mu don kinsan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba a
duniyan nan hakan zai jawo dan tsegumi da zai iya bata muna suna ga alakan mu
dake.

Ban tsanmanin duk
abinda da za a fada na bataci ne a tsakanin mu don kowa yasan mutuncine
tsakanin nida kai hakama wasu dauka suke cewa mu yan uwane na gaskiya dani
dakai din yanzu.

Don ganin irin
mutuncin dake tsakanin mu dakai so duk abinda zasu fada su fada nidai nasan
nice ke karuwa dakai yanzu ba abinda kake gudun su fada ba din ne.

Amma dai duk da
hakan don Allah ki dan rage nayi murmushi kafin nace dashi abu daya zai saka na
rage shine wanan akuyan dake firgitani gidan ku da ba hakan ba kullun sai
nakaiwa kaka abin shan ruwa da kaina gidan ku.

Haka kike da kafiya
ba kafewa bane na bashi amsa ina dan murmushi nace idan munbi ta mutane ko
gaisawa zai zama matsala a tsakanin mu nan gaba don ko yaushe idon su akan
gulma yake.

Tare muka jera har
kofa  building din mu ya kaini mukai
sallama ya juya ya wuce wanan rana shine zance rana ta farko da muka tsaya
nidashi mukai magana mai tsayi a tsakanin mu irin hakan.

Bayan shan ruwane
da yamma suna zaune tare da Dije a kofan dakin Dije din da suka shimfida
tabarma su biyu a gida ya dauki waya ya danna kira a layina.

Na dauka naga
sunan shi na danna dauka yayi sallama na amsa yake fadin Allah yasa nine mutum
na farko dana fara maki barka da shanruwa kada wani ya rigani samun ladan dake
cikin hakan ?

A gaban ummah nake
hakan bai hanani yin murmushi ba nace ai kuwa kayi sa,a kaina na farkon kirana
amma ga hannatu nan yanzun tana kirana kuma.

To ki gaidasu mama
ina masu barka da shan ruwa Allah ya bamu ladan dake cikin sa ya yafe muna kura
kuran mu yasa muna cikin yan tattatun bayinsa na amsa da amin mukayi sai anjima
dashi.

Na dauki wayan
hanne nan ta hauni da fadin ke mutumiyar ina ta kira kina busy haka ko kiyi
sabon kamune banda labarin hakan .

Mikewa nayi nabar falon ina fadin ke dai
hannatu haka zaki kare da sheri har da watan nan mai albarka sai kinyiwa mutum
sheri.

Brother ne fa ya
kirani yau yana min barka da shan ruwa muke magana zakice wani sabon kamu kai
kice master da kanshi ya kawo gaisuwan girma ashe shima muka taba hira sosai
kan lecture din ranan kafin mu kashe wayan nikan na kwanta ban sake fitowa ba
saida asuba da muka tashi yin sahur.

Yana aje wayan ya
kalli inda Djje take tana cin abinci yace wasu mutanen akwasu da kirki tun suna
kanana yarinyar nan fa dije yar gidan mai kudine da garin nan ake ji dashi amma
bata dauki duniya da girma haka ba.

Idan kin ganmu da
ita saiki dauka ba yar kowa bace ita din don sam bata nuna hakan hakama yanayin
shiganta kulun na mutunci ne.

Ai wasu sun san ya kama ko a cikkn yara sai
ka samu masu hali irin na dattako garesu yace hakane ko kudin nan ban fada maki
bane natane ta ban na kara nake jan wanan jarin dashi .

Ranan da naje
kauyen nan buhun gero hamsim na sayo maiwa ashirin sai masara moto guda na
dauko ni kadai aka sauke min kaya kuma duk sun shige washe gari mai kudi kuda
ya sayesu ya bani kudina kasa wallahi.

Amadi kace arziki
ya budu muna har kana iya dauko abin dubu dubbai haka ka sayar yanzu a garin
nan wallahi Dije haduwana da zarah ya zamo min alheri sosai a rayuwana Allah ke
nan.

Kaga ubanka yayi
watsi dakai a duniya ya manta da zancen ka a cikin duniyan nan gashi Allah yana
taimakon rayuwan ka ta hanyar da ba a zata ba.

Shiru yayi don ya
tsani Dije ta dauko mai zancen iyayyen shi idan suna magana idan ba don Allah
da ita Dijen ba sai yace ai shikan baiyi dacen iyayye ba don ko ita mahaifiyar
nasa daya sani ya bude ido da ita mijin da take aure ya yanke alakanshi da ita
yanzu.

Don kuwa ta zabi bin
mijin ta can dajin Niger state inda yake noma suke zaune har suka hayayyafa
dashi yanzu bata zuwa gida kai da kai saita dibi shekaru take leko su tayi
kamar wata daya ta koma garin sai kuma bayan wasu shekaru masu tsayi take
dawowa garesu don haka ba zaice shi yasan dadin mahaifa ba saidai kakan shi
mace itace Dije.

   Kawar da zance yayi da fadin waiko yau u

Leave a Reply

Back to top button