TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 10

Sponsored Links

 

 

<

Tsaye yayi yana karewa akuyar wace ke kwance tana tukan
abincin dataci kallo kafin yaja kafanshi zuwa daki zuciyar shi cike da tunanen
ina tafito gashi

bai san wanan dattijon daya saye taba a cikin unguwansu ba.

   Duk inda ta fito
wuri mai nisace sosai to yaya akayi har ta gane hanyan gida ta dawo haka a
cikin dare har ta shigo gida lalai dabba sai a barta inda aka ganta suma suna
da kwakwalwa ke nan ashe kamar mutane.

   Dukawa yayi ya
dauki takalman shi mafalkin da yayi ne mai kama da almara ya fado mai arai har
ya tashi bai makara ba a lokacin.

   Yaro ga akuyan
kunan na dawo maku dashi har gida na yafe kudin ta halak malak  Allah yasa kudin ya amfane ka kai ya fada
yana mikewa da sauri yayo waje Dije yake kwallawa kira ta fito har yanzu tana
cikin alhinin akuyan tana dakinta tana mita tana fadin dama nasan za,ai haka
dake uwar garke.

   A nan kika bude ido
fa nan kika saba nima tun tafiyan ki nake kewan rabuwa dake sai kuma ki gudu ki
dawo bayan na karbi kudin ki.

   A lokacin ne taji
kiranshi cikin daga murya azotonta ta dauka akuyar ta gudune sai dai ta hangota
a kwance yadda take lafiya Amadi da wanan kiran haka ?

    Lafiya Dije wani
mafalki nayi da asubah din nan yanzu ya fado min a rai wai wanda ya sai akuyan
nan yake fada min ga akuyan nan ya mayar muna halak malak mu rike kinga kuma
gata nan yanzu.

   Kai Amadi ina aka
taba haka kila don zata dawone kayi mafalkin hakan ko saboda sabawan da mukayi
da ita kuma yasa ka fadin hakan.

    Ba hakana bane
yanzu dai nasan mai ita zai dawo insha Allahu ya biyo sawun abinshi kinga sai a
bashi ko bana nan yazo zaki ganshi wani dattijo farine dogo ya dan rankwafa da
farin geme a fuskanshi.

    Wanan kwatance
haka ai karewa halitta kallone bari dai yazo din mu gani idan shine yace to ni
zan tafi sai na dawo ke nan tace Allah ya tsare ka dauki jakka biyar kayi
amfani dashi cikin kudin akuyan.

  Jin haka yasa ya
juyo da sauri yana mata kallo  mamaki
kafin yace Dije ina zan taba kudin mutane ga akuya a hannu  mu yanzu.

    To kudi ai ya zama
namu yanzu albashin idan mai ita yazo sai a bashi abinshi ya tafi ba shike nan
ba a aje kudi ana kallonsune haka ba
tabi?

   Ya dai sa kai ya fice ya barta tsaye tana
magana ita kadai a gidan tana fadin kaji mun yaro waishi ga uzzutazu yasan
Allah ke nan ko ka wani ce kudin mutane mutanen bamun basu akuyan ba sakacin su
yasa suka sake ta ta gudo.

   Meeeeey meeeey
akuyan tayi kuka lokaci guda ta juya gareta tana fadin uwar garke kin min
gafara rashi yasani rabuwa dake amma na kwana dake a zuciyana jiya wallahi.

  Ashe da rabon mu
sake ganawa dake haka ruwa ta diba da guntun dusa ta kai mata tana fadin ci
uwar garke gaki har cikin ki ya fada haka.

    Sauri nakeyi sosai
saboda na dan makara na isa school din a gurguje nake in isa department din mu
muka hade dashi ina kwana nace ciki ciki shima haka ya amsa min din.

   Na wuce da sauri
saidai tun ka  na karasa na hango wasu a
waje hakan ya sanar min da wanda ke cikin ajin ne ya dakarar dasu waje din don
makara.

    Nima danazo yanzu
a nan na tsaya haka na bayana suma suka tsaya kaina yana duke ina jin yadda
sauran ke zagin malamin ban dai kula hakan da sukeyi ba.

    Shine yazo zai
shiga ajin magnet ka roka muna shi don Allah sai lokacin na dago kai mukai
ar,ba da wanda suka kira din da magnet.

    Wanan matashinne
ya shige a yadda yake kamar kullun mutsu mutsu dashi naji wata na fadin amma
dai kai wanan din ne zai roka muna wanan mutum maigirman kai ?

    Ke kika ganshi
mutsu mutsu ajiyan Allahne wurin nan baki sani ba don kaf department din nan na
science babu kamar shi akace shine yasa ake kiranshi da magnet don kokarin shi.

   Wanan din ta
tambaya a lalace yace shikuwa da kike gani nan kinsan haka Allah ke abinshi shi
bai damu da irin wa yan nan karyan na zamani ba.

   Ya fito tare da
malamin saida sukazo gap damu malamin ke fadin wacece sister din naka sai ya
nunani yace wanan yau ya akayi kika makara tana da kokarin shigowa da safe ai.

    Ya dubemu yana
fadin ku shiga tunda wanan ya roka maku kunci albarkacin sister dinshi mungode
na riga kowa fada a wurin yace ba matsala hope dai kina da kokari irin yayan ki
?

     Murmushi kawai
nayi na shige na barsu a wurin tsaye
sauran ma suka biyo bayana muka shiga tare dasu aka zubo muna ido wuri
na samu na zauna na fara fitar da takarduna.

   Saiga malamin ya
dawo yake muna fadan makara ga dalibi kamar bai dauki abinda muhinmanci bane
yaja muna kunne sosai a haka  har period
din shi ya cika ya fita.

     Sai lokacin na
samu natsuwa kafin wani ya shigo muryan wanan guy din naji yana fadin ashe muna
tare da kuraye ne ajin nan bamu sani ba kanwar over role student a cikin class
din nan .

    Kai na dago na dan
kalleshi yana kokarin zama inda na kusa dani ya daga yana fadin to amma wai dai
na tambayeki wai da gaske don Allah yan uwa kuke keda Ahmad ne ko kuwa dai ?

    Amsan dana bashi
shine ba kaji ya fada da bakin shi ba dazun wani amsa kake son ji yanzu kuma ya
kalleni kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru.

   Kafin yace amma shi
yaya na ganshi haka koda yake baku da zubi daya alamu ya nuna dai irin zumuncin
nan ne kawai a tsakani ku ?

   Don Allah idan ba
laifi ki muna hanya mana a wurin shi mu dan rika ganin shi yana muna group sai
mu dan rika masa wani abu don ance gaba daya department din nan ana ji dashi
saidai don ya kasance shiba dan kowa bane haka yasa ba a sanshi ba.

    Shiyasa nayi
mamakin jin ya kiraki da kanwarsa dazun har nazo na tambayeki ai yanzun zaki
masa magana ko yaya ya tsureni da ido yana son jin amsata.

   Nisawa nayi nace
masa ka bari nayi shawara duk abinda ke nan zan sanar maka gobe ya mike daga
rankwafowan da yayi yana fadin to shike nan saina jiki goben amma don Allah ki
taimaka muna ya yarda kinsan mutumin hutsune sosai don shinema bai kula kowa
wanan kan halin ku yaso yazo daya.

    Daure fuskana nayi
na mayar da hankalina kan karatun daya sama ina yi da farko ganin hakan yayi
min sallama ya tafi ajiyan zuciya na sauke .

    Na dawo gida da
yamma lis nan Tani mai aikin mu ta tareni da murna waina bata goron albishir na
dauko dubu daya a jakkata na mika mata ummah na zaune tana karatun wani
littafin addini na addu,oi.

    Bayan na bata take
fadin yar lelen masu gida albishirin ki aina baki goron na fada a gajiye tace
uwar dakina yau mun samu karuwa wani motar kuma yayan ki musa ya turo maki
dashi yau din nan har wanda ya kawo ya juya ya koma Abuja dazun.

    Mota na fada ina
kallon inda ummah take zaune tace ke dai bari yau nayi murna nayi guda a gidan
nan kamar ba gobe wallahi wanan shi ake kira da dan da Allah kewa fada bayayin
fada .

   Kana zaune arziki
ke sama  ka har gida yau ai tunda aka
kawo motan nan mutanen gefe ke cike da bakin ciki a gidan nan ko motsin su
bakya ji tun dazun nasan ana can ana kitsa wani sherin ke nan kuma ?

   Suwa ke nan na
tambaya da mamaki tace yan hana ruwa gudu mana na gidan nan dkn ita giwanyan
tamaki fitowa taga motan sam sai cewa tayi mota wani irin mota kuma ya saya
maki yanzu.

   Kai Tani uwar
tawace ke bakin ciki don yaya musa ya saya min mota kada ki mata sheri mana na
fada ina nufar inda ummah take zaune na ajiye jakkata kafin nakai zaune.

    An maki albishir
baki ko je kinga motar ba kin zauna yanzu da a gaban shine haka zaki nuna mashi
ke nan ina hanaki wanan rayuwan ko in kula naki do  ba halin kwarai bane hakan da kikeyi .

   Ummah na gajine
sosai yau wallahi barin cire kayan nan naje na duba na leka mama a dakin in
fada mata da bakina kada tayi min fadan rashin sanar mata da kaina.

   To ki gwada ki gani
ai hakan yana da kyau ban wani dade a dakin ba na fito cikin wani simple riga
irin na zaman gida waje ire iren su ummah ke sayomin muna Abuja don ban faye
saka kayan dake matseni ba duk da ina dasu ban damu da sakasu ba.

     A hankali nake
takowa daga cikin gida na nufo waje lalai bana cikin hankalina lokacin dana
dawo school zan shiga gida tunda har banga wanan farar motar ba parado dake aje
a wajen gidan mu lokacin.

   Parado ce karama
fara kal tana daukan ido a hanzarce na karasa wurin zagayen motar na farayi
kanne suna bina abaya sai ihu sukeyi har na zagayo zuwa kofan motar na tsaya
kafin naje gaban motan dake dauke da lamban Abuja a gaban shi .

  Tsoro da mamakine ya
kamani lokaci guda nakai hannu na dafa motan a hankali tare da bissimillah
idanuna na runtse inawa Allah godiya.

   Ako yaushe ubangiji
abin godewa ne a gareni irin yadda yake min baiwa iri iri a duniya a saukake
naci gaba a rayuwana wanda alokacin ban san dalilin shi ba sai nan gaba.

   Ummah ummah ummahn
mu nake kwalawa kira tundaga kofa a cikin murna da daukin ganin motar ummah da
ke shirin alwala zata dakanci magariba tayo waje wurina a cikin tashin hankali
ta dauka wani abune ya sameni har jikinta na bari muka hade a falo.

   Ummah wai kinga
motar nan kuwa kaf gidan nan fa babu me ita har mama kai amma naji dadi wallahi
ya musa Allah ya saka mai da alheri.

    Dan Allah maamah
yanzu murnane haka kika dagawa mutane hankali da magariban farin nan haka haba
maamah naki kala  farin cikin ke nan haka
?

  Makin ki godewa
Allah ta hanyan nafila ko daga hannu ki kara neman kari a gareshi tare da
godiya ga ni,iman daya wadatar dake haka a cikin yan uwan ki.

    Ummah zanyi in sha
Allahu don ko a waje nayi zanje nayi sallah yanzu don naga lokaci ya gabato
kamin na gama fadi har ummah ra juya ta shige cikin dakin ta ko a lokacin.

   Sallah na idar a
cikin doki don har lokacin kamar a mafalki nakeyi nake ganin kaina wata iri ni
fatimatul zara,u nice Allah yaiwa wanan daukakan haka lokaci guda.

   Don wanan aiba
karamin cigabane na samu lokaci guda haka don banyi tsamanin motar mama tafi
nawa wani tsada ba don farkon fitowan motar ne lokacin ashe da gaiya ya musa ya
zabo min shi duk da uban kudin dakega motan lokacin.

   Shiga gidan da uwar
garke ya fara tozali tana kwance yarda ya barta tano tuka da hakoranta yadda
dabbobi keyi idan suna gyaran abinci ya fada masu a ciki.

   Ikon Allah ya fada
a ranshi ya karasa wurin turken da sauri yana fadin Dije mutumin nan bai biyo
sawun akuyan nan bane har yanzu ?

   Sai lokacin Dije
tasan da dawowan shi gidan tafito tana gyara daurin kallabin kanta tana fadin
tun safe nake zaune ina saka ido naji sallaman shi har yanzu banji kowa ba
saikai dinnan daka shigo yanzu.

  Ina zuwa Dije tace
ya juya zai fice daga gidan tace cikin daga murya ina kuma zaka ko kasan
gidanshine dama ?

   Wurin malam Tanimu
zan tafi ya bata amsa yana tafiya bai tsaya ba ya fice daga gidan kai tsaye ta
figi zani a rataye tabi bayan shi itama.

    Malam tanimu dake
zaune a kasa buta a gefen shi yana shirin alwala ya hango Amadi din ya nufo
inda yake zaune kamar hankali a tashe.

    Hankalinshi ya
mayar kan matashin dake tafe wurin shi tunkan ya karaso yake tambayanshi da
Amadi lafiya kake tafe haka ?

   Wallahi malam
akuyan nan uwar garke na dije da jiya bakon ka ya saya shine ta gudo daga gida
shi ta dawo gida mun dauka zai biyo sawun ta yau sai gashi har yamman nan na
dawo na sameta a gida baizo ya dauka ba.

   Bako malam tanimu
ya maimaita cikin mamaki yana kallon Dije dake biye a bayan Amadi din tafe
itama a rikice ta karsso tana fadin malam tanimu ka ganmu a wanan lokacin ba.

    Ina ya fadama
akuya dai ta dawo yanzun haka tana gidana nayi bata abinci wunin yau taki cin
komai saidai ta sunsuna ta kawar da kai gefe daya.

  Gaba dayan su
kallonta sukeyi lokacin suna sauraren bayanin ta kafin malam tanimu da yaji tayi
shiru yace.

  Bako gaskiya banyi
wani bako da kuke wanan zancen ba,  eh
malam Tanimu gaskiyane jiya yazo nan ya sameni ni kadai a zaune lokacin na dawo
daga gidan jabbi mahauci nakai masa tallan akuyan na samu yaje kauye.

   Na sake zuwa gidan
yanka shima bayanan ya shiga gari shine na dawo na zauna nan inda kake hutawa
ban dade da zama ba wani dattijo yazo yai min sallama yana neman ka.

   Nace nima ban
sameka ba bari na sallama na tambaya mashi shine na shiga akace dani baka nan
kaje daji daukan ice na karbo mashi ruwa na kawo mai.

   Shine yake fada min
yazo wurin kane ka taimaka kai masa jagora yazon sayen dabbane gashi kuma bai
sameka ba ni kuma jin hakan yasa na tallata masa uwar garken mu yace a kawo mai
ya duba.

    Bayan na kawo
mashine yace ai masa kudi daga sama na yanka mai amma ya tsaya a nan bai nemi
ko ragowa ba har dubu biyar na mayar mai daga ciki amma yaki amsa haka yasayeta
jakka arba,in cif.

    Ikon Allah to waye
wanan malam tanimu ya sake tambaya cikin mamaki yace dogone fari ya dan
rankwafa yana da farin gemu a fuskanshi.

    Dewa ya,i ni wanan
mutum wanene kuwa don wallahi ban gane shi ba sam kuma dana dawon iyali basu
fada min zancen wani yazo nemana ba.

   To shine shi Amadi
ke fada min dazun wai yayi mafaki mafarki da asuba da mutumin na fada mai cewa
ga akuyar nan ya dawo muna dashi kudi kuma tayi amfani dasu yabashi su halak
malak.

   Kai malam Tani ke
faman juyawa kafin yace lamarin da daure kai yake don sam ban gane waye wanan
mutumin ba anya ba buda ido akai makaba kuwa Amadi.

   Kamar ya buda ido
kuma dije ta fada a dan firgice ko hasale bayan ga kudi a hannun mu mutumi ya
bayar kuma ya tafi da akuya dawowa tayi kawai.

   Watau Dije zancan
nan ne da daure kai yake don sam na kasa gane mai wanan kwatancen da Amadi yai
min yanzu.

   Saukin abindai yaga
gida koda ya dawo ya sallama za a bashi abinshi kudi kuma wanan mafalkin wanan
abinda zai farune kila yasa kayi wana
mafalkin haka.

   Don haka ba laifi
bane indon wanan ne sai kuyi laluran gaban ku da kudin koma waye tunda yasan ni
ai ya kwana gidan sauki ga kuma akuyan shi nan a daure sai ya dauki abinshi.

   Yanzun lokacin
sallah ya gabato don haka ku koma gida sai aje ai hakan nasan maishi zai dawo
neman ta nan kadan wanan ba abin damuwa bane ai.

   Allah ya kyauta
Dije ta fada ta juya zuwa gida tana magana ita kada tana ganjn laifin su ga
sakacin da sukayi na barin akuyan ta dawo gidan nasu tunda yanzu ba hakkinsu
bane uwar garken .

    Shi kuma Amadi ya
tsaya sukayi alwala da malam tanimu su mike zuwa masalaci don yin sallah
magariba da aka kira a lokacin.

    Ina idar da sallah
hijsbi na kwabe zan nufi part din mama don muyu zancen motan da ita saidai ina
fitowa fallon ummah na zaune ta zubawa yara abinci.

   Haka nazo na wuce
ta na ji muryan ummah din na fadin ina fatan baki dauki key ba zuwa wurin ta
ba,  juyowa nayi ina fadin a, a ummah ban
dauka ba ai yana nan dakinki.

  A to idan dai kikaje
mata dashi karbe key din zatayi a hannun ki wanan karamin  aikinta kin sani wurinta haka mai saukine.

Leave a Reply

Back to top button