TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 60

Sponsored Links

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/25, 10:45 AM] +234 703 080 4044: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣0️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Mommy daddy lafiya yake kuwa ta fada tana shugowa dakin a
firgice yau bakiji irin voice din da yayi min ba don na sameshi natambayeshi
abinda ya faru.

    Na fada maki aida
baki jeba don akwai matsala dake shirin faruwa da nake hangowa don haka dole
mubishi a hankali har mu gano inda matsalan yake.

   Mommy mu hadashi da
Grandma kawai ita zata taka mashi burki don ba zan juri ganin hakan ba gareki
dolene daddy ya dawo normal.

   Zan fada mata amma
ba yanzun ba sai nan gaba idan abin yafi karfina zan nemi taimakonta ta fada
tana kawar da kai daga kallon yar nata dake tsaye a kanta lokacin.

    Cikin takaici ya
kawar da fuskanshi daga kallonta na dan lokaci kafin ya dora hannayenshi saman
haban shi ya shiga dogon tunane akan matakin da zai dauka yanzu ga iyalin nasa.

    Har daki ya sameta
bayan sun gaisa yai mata ya karfin jiki ta amsa da lafiya Alhamdullahi jiki
yayi sauki sosai na rage wanan mafalkin da nakeyi mai firgitani yanzu.

    Alhamdullahi Allah
tsare gaba saidai inna ya kamata wasu abubuwa yanzu ki daina don in kaiwa wani
ya kyale ka wani ba zai kyaleka ba hakama dabbobi tsakanin mu dasu tausayine da
jin kai.

    Don baka san irin
baiwan da Allah yaiwa wani dabban ba kana tabashi bai baka bashin hakan Allah
ya tsare gaba tace amin ya mike ya shige wurin Dije su gaisa da ita.

    Ya fito daga
sashen sune ya dawo daki ya karya ya fita
don yana son yai sayayya don ya koma makaranta wanda sayayyan duk na
gidane shi a can yakan dan sayi abinda zaiyi amfani dashi.

   Gashi dan break
yazo don matsalan fargaban dake damun shi sai laluran ciwon inna din ya tsayar
dashi har tsawon sati biyu ake nema yanzu sai faman kiranshi abokin karatun shi
keyi akan ya dawo zasuyi test.

   Hakan ne ya daga
mashi hankali yake shirin komawa a lokacin bayan fitan shine ina zaune a falo
ina kallon wasu photuna a wayana na bukin wasu diyan abokin Abba da akayi akai
shagalin karya sosai sabanin na bukin koda yake aurena ne ba ai wanan ba da
aurensu Aisha sun dayi wasu event da akeyi cikin gari.

   Naji wayana yana
kara na dauka na duba ummahce a layi take kirana lokacin na dauka da sauri tare
da sallama muka gaisa tayi min ya mai jiki na amsa da ta samu sauki sosai
yanzu.

   To na kira in fada
maki cewa yar uwarki Aisha ta haihu dazun da safe yanzu haka tana gidan nan sun
dawo daga asibiti idan kin samu lokaci ki shigo ki dubata.

   Murnane ko mamaki
ya rufeni nace ikon Allah ashe cikin dama har ya isa haihuwa to Allah ya raya
yasa dadin musulmine tace amin zanzo ko yau ko gobe insha Allahu.

   To sai kin shigo
kidai ta hakkuri komai na duniya dan hakkurine wata rana sai abin ya zama
labari idan bawa ya iya hakkuri daga jerabawanshi.

   To ummah nagode na
bata amsa tare da fadin zanshigo kafin Master ya koma Allah bada iko ta fada ta
kashe wayanta lokaci guda na lumshe idona har lokacin ina jin wani iri a
zuciyana.

  Kamar yadda duk wata
mace keji a rayuwanta a lokacin da taji wani ya haihu ko wata nada ciki yar
uwan aurenta don abin yana taba zuciyar mace sai dai idan hakan bai sameka ba.

  Gashi yan uwan
master ko ince mahaifiyar master tana ganin cewa nice banson haihuwa da danta
nake planing don kada in haihu dashi har take ikirarin cewa zata auro mashi
wata mace a lokacin duk da bamu dade da wani aure ba.

  Balle yanzu taji
cewa Aisha da akai muna aure rana daya da ita harta haihu ni ko batan wata ban
taba yi a gidan nasu ba ai nasan zata sake min zance a ranan.

   Nisai nasan Master
gwarzo a wurin kwanciya duk da yasan nidin ba gwanan hakan bane amma bai
kyaleni sai bukatanshi ya biya yakan barni.

   Don haka nasan abin
na Allah ne shike bayarwa a inda yaso kuma yaga daman hakan ga bawanshi a
lokacin da kuma yaga dama.

   Anan ya dawo daga
kasuwa ya sameni saida ya nuna mamakinshi a fili yake fadin badai wai har yanzu
kina wurin nan zaune ba ya fada.

    Na dan rausaya kai
tare da fadin harka dawo ina nan ina kallon waya photuna bukin gidan Dr nake
kallo tundazun sai naga yayi murmushi tare da fadin ance ansha buki kan gaskiya
a wurin.

    Ga kayan nan ki
duba abinda na manta sai na koma na sayo ya fada a lokacin da nake mikewa zuwa
kitchen ruwan da muke sakawa a gora na dauko mashi tare da cup na kawo mai duk
da baida sanyi sosai.

    Ya karba tare da
godiya yana sha na bude kayan ina duba tare da fadin ai akwai komai nake gani
yace a,a ki dai duba naga kamar na manta da wani abu a ciki.

   Idan na tuna sai in
aika asayo min ai a, a na fada maki banson kina min ciko komai da yake hakkina
ki dinga fada min in saya don Allah don in sauke nauyina akanki.

   Sabulu da omo ya
rage na fada yace da man shafaki naga ya kusa karewa ai eh amma akwai wani
wanda ban budeba ai yana cikin drower aje.

   Ok ita inna tace
saina karo masu kayan miya don in na wuce sai ta saya wani abin wani lokacin
wai ina bambanta sayaya in sayo maki mai yawa su kadan bai kaisu har inyi sati
biyu in dawo.

  Tana ganin kamar
nafi sayo maki kaya mai yawa fiye dasu kinga dole in koma kasuwa in karo masu
in ba hakaba magana zai zama min nan gaba.

  Murmushi nayi nace
nace a fili dole kan ai sai an kara don suna da yawa balle mace sai tayi cikon
wani abin dama girki ke kammala.

    Amma kinga abinda
na sayo masu kuwa hali daine irin na inna nason kure mutum don har Dije saida
tayi magana kan hakan itama amma bari dai din na karo.

  To shi dai yafi
gaskiya inda hali ka karo masu ai ba komai bane ina fadin hakan na bashi ina
kwasan kayan yace yanzu dana huta zan koma na sayo masu ai.

    Ya fada akasalance
nasan ya gajine sosai lokacin yana so
hutu nidai na dauki kayan na nufi kitchen dasu nakai kofa na juyo tare
da fadin.

  Aff kaga na manta
ummah ta bugo waya dazun tana tambayana jikin inna, kafin naci gaba da magana
yace Allah sarki ummah akwai kokarin kulawa wallahi nima takirani shekaran jiya
tana tambayana jikin nata ai.

   Tace Anty Aisha ta
haihu yau da asuba ta samu ya mace har an dawo da ita gida tana nan gidan ban
karasa ba yace wace Aisha dai kike magana wai ?

   Nace Anty Aisha
tamu dai ta gidan mu mana ita nake nufi ta haihufa kikace yana kallona cikin
mamaki nace kodai baka gane Anty Aisha din bane ?

   Nagane mana gani
nayi dai tare akai bukin mu aiko nace ashe kaganeta yace shine kuma ta haihu
yanzu ko wata takwas din bamu cika sosai ba ai don saura kwana goma sha yanzu
mu cika wata takwas.

   Gabanane ya fadi
don sai lokacin nagane mai yake nufi ai da sauri nace to shine abin mamaki mata
da mijinta yanzu ina abin mamaki ciki .

  Kuma kasani dan wata
bakwaine yaron yace zai yuyu kuma gaskiya Allah ya raya nace amin a sanyaye
gabana yana faduwa.

   Idan hakane kuwa
akwaita kenan na fada a zuciyana na shige kitchen din mu ina aje kayan don a
nan nake akewa duk da nagane ana diban min wasu kayan aikin nawa wani lokaci
idan na aje a nan irinsu maggi tomatoes curry da mai tundai mangyadana na miya.

  Don hakane su na
barsu a dakin sai na dawo na adana a cikin dakin gashi na fara jin inna tace
abinda aka sayo masu baya isa kenan dama da nawa ake karawa ayi yanzu kuma nayi
wayau ina sakawa daki dukda haibaicin da inna kan min da ba kayan gidan ubbana
bane dai saukin abin.

  Nasaba da irin gorin
inna son haka abin bai damuwa nake shayewa sai in nuna kamar bansan dani takeyi
ba ma idan tanayi don kawai a zauna lafiya.

    Kodana koma dakin
yana zaune yana gyagyadi lokacin  ya ban
tausayi nasan in nayi motsin daukan ledan zai iya falkawa don haka nabarsu a
wurin na shige uwardakan mu na jawo wayana.

   Hannatu na kira na
samu ta dauka na fara labarta mata zancen haihuwan Aisha din amsa dayane tabani
irin nasa cewa wata Aisha dai kike nufi zahra ?

   Tamu mana sai naji
tace innalillahi auren kufa baiko cika wata takwas ba sosai nace ba a haihuwa
hakane wai hakamafa master yace min da nake fada mai zancen haihuwan.

   Wallahi akwai
rikici har in yar nan ta rayu don ko saidai idan da cikin tashiga gidan dama
nace don Allah kibar zancen nan wani iri nake ji a zuciyana tace na bari amma
dai akwai magana gaskiya.

   Bari na kira ummah
naji na fada sai naji da sauri tace min ki rufawa ummah asiri don Allah don
baki san dasuwa take ba yanzu tunda haihuwane.

   Muka dan taba hira
can naji motsinshi ya tashi ya shigo dakin nayi mata sallama ina cewa ka falka
ke nan yace wallahi nagajine ga zafi kuma koma na tayar da injin din nan ne
yanzu ?

  Da darefa idan ka
tayar yanzu yace saina nemi kudin wani mai mana a saya nace ai kaji zancen muje
falo kawai ka kwanta nayima fifita zaifi.

  Da sauri ya juyo
yana fadin wa ki rufa min asiri kada anji ki kaini asibiti kuma kice ba lafiya
ai gara naje darbejiyan  malam Tanimu
insha iska zaifi.

   Ni kumafa na fada
cikin gatse yace shine kuma ai to mu zauna din ta waje amma gaskiya zafi nakeji
sosai wallahi aiko da mamaki son yau gaskiya ba zafi yadda kake nufi na bashi
amsa mu kafita na dauko center carpet dina na shimfida muna muka zauna a dan
barandan mu akwai iska sosai a wurin dake hurowa daga baya ta inda dabbobinsu
suke.

    Barci ya samu
sosai ni kuma ina aikin girkina inayi ina dan dubashi har lokacin da na kusa
sauke girkin nawa din duk yana kwance yana barci son sanyin wurin.

  Ina mamaki a raina
don ban taba ganin shi yana barci ba haka da rana irin wanan ranan don hakane
abin yake ban mamaki.

   Na fada maku ku
kwantar da hankalinku indai wanan aikin ne ba a wuce sati biyu insha Allahu
bukata bai biya ba irin hakan.

   Tunda har kunce ya
fara kiranku alama ya nuna aiki yana kyau ke nan insha Allahu saidai mu jira
muga ikon Allah yanzun kam.

   Har in bai kiraba
yau zai kiraku zuwa gobe da yardan Allah son duk inda yake yanzu shima a matse
yake cikin kunci don aiki ya fara aiki a jikinshi sunan Allah aiba wasa bane.

   Hakane malam musa
ai don shine mukazo yanzu mu fadama abindake gudana jn akwai wani sadakan da za
a karayi sai mu bayar ayi muna akai.

   Kai ya girgiza masu
yana fadin kwandala naku na fada maku banso cikin zancen nan don nima ina son
in samu ladan da zaku samu ga wanan niyar don nima alkawari na daukarwa yaron.

  Godiya suka kara mai
sukayi sallama dashi cike da mamakin shi gashi dai bako a garin amma bai hurda
da kowa akace sai makwabtanshi da suke dan gaisawa dasu amma kuma yana da halin
kirki.

   Ba laifi suma basu
zauna ba don suna da dan rufin asirin su daidai gwagwado hakana saboda basu
zaunaba akwai sana,anyi ga kuma kiwo da suka dukufa gayi har yanzu dama ba a
raba bafilace da kiwo.

    Kamar abin almara
wayan Alh jauro ya dauki kara yasaka hannu yana laluben wayan ya duba kamal
farko da tafito mai a bakinshi shi Allahu akbar kunga dan halas yana kirana
yanzu.

   Waye suka tambaya
yace dangaske wallahi shine ke kirana da sauri dayan yace kaga kada ka nuna mai
muna tare don na fahinci baison muji maganan.

    Ya dauka suka fara
zolayan juna da fadin kai jiya da yaukan naci da fari wanan amini yana tunawa
dani yace ko yaushe ai ina tunawa daku ban manta da kuba.

    Jiya muna magana
wayan ya katse dan gasken ya fada hakane na dauka aikai ka kashe wayan yace
saboda me nidana kiraka zan katse yanzu dai munyi maganan kai tsaye kaji
damuwana.

   Wallahi jauro na
fada maka ina cikkn matsala sosai kwanan nan in gajarcema dai wani bakon yanayi
ke shiganaga don na kasa fahintar ko wani yarone nake yawan mafalkinshi
kwanakin nan sosai.

   Don a iya tunanena
na tuno sosai ko akwai yaron da muka taba zaluntane muna yara ke neman hakinshi
a kaina naso ace kana tare da yan uwa a yanzu ko cikin ku akwai wanda zai iya
tuna wani abu na kurciyan mu.

   Jam Jam yaro kuma
yaro wa muka cuta irin haka da har zai dinga dawo maka yanzu a rayukan ka kaiko
dangaske saidai in wani abokin aikin kane nan ?

  Abin ya daure min
kai sosai jauro naso ace kana kusa dasu bande da Jabbo ko Allah zaisa su tuna
wani abin na baya da mukayi.

   Aiko ina kusa dasu
na tashi amma barin samesy in masu bayani sai na sake kiranka yana fadin haka
ya kashe wayan.

   To masu karatu ku
farga da iri  haka ku kula idan zaki
wayan siri ki natsu ki fahinci da wanda kike waya idan abin na boyene kisan
abin fada don baki san wanda ke kusa da maishi ba a lokacin.

  Don hakanne ya
kasance ga Alh dan gaske da ace wani abu mai muni ya fada game da sauran da
sunji a lokacin sai aka samu ya nuna taimakonsu yake nema gaba daya a lokacin.

    Jin hakan yasa su
jin tausayin dan uwan nasu don sunsan irin halin da yake ciki a lokacin nan
sukai shawara kawai su fada mai gaskiya inda Jabbo yace su bari shi da kansa
zai mashi magana idan ya bugo.

   Hakan akayi lokacin
da suka idar da sallah la,asarne suka samu wuri a natse suka bugawa layinshi ba
bata lokaci kamar yana jiran kiran nasu lokacin ya dauka sai yaji muryan Jabbo
a layin yana magana.

   Suka gaisa akai ya
kwana biyu nan yake tambayanshi ko yaji sakonshi wurin jauro yace eh shinema
dalilin kiran naka yanzu don ka kara muna bayani da bakinka.

  Yadda ya fadawa Alh
jauro haka ya karanto masa shima yai shiru yana sauranren shi cikin tausaya
masa sosai a fili sai bayan ya gamane yace dashi ina fatan kana saurarena kaji
mezan fada maka.

   Ni a tunane da kuma
abinda muka hango wanan mafalkin naka yana nunine ga danka daka watsar a cikin
duniya ko zaka iya tunashi yanzu ?

    Idan baka manta ba
tunda ka barshi ka dawo mambila ban tsamani ka taba tuna wanan yaron a
rayuwanka kuma alhalin kasa dankane na cikin ka.

   Cak yaji kamar ana
zare mashi numfashi lokaci guda hankalinshi yana kokarin gushewa a jikin shi a
haka wayan ya fadi a hannunshi ba tare daya sani ba.

Leave a Reply

Back to top button