Nailah Hausa Novel

Nailah 2

Sponsored Links

 

🌸NAILAH🌸*

 

Related Articles

~*(The abandoned flower🌹)*~

 

 

*Na*

 

*Baebee*

 

~*WRITER OF✍🏽*~

 

*MUSAYAR BURI*

K

*YAN DABA NE (The revenge)*

 

*ZUCIYARMU* *AND NOW…….*

 

 

*NAILAH* ~*(the abandoned flower🌹)*~

 

 

*Wannan labarin da duk abinda ya ƙunsa ƙirƙira ne, idan yaci karo da rayuwar wani ko wata arashi ne a gafarce ni*

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*

 

 

*PAGE 2*

 

 

A Basara Local Government, gidan hakimi Mlm. Abubakar ya kaita ya ma Hakimi bayanin komai sannan ya roƙesa alfarma, shi kuwa hakimi ya amshe ta da hannu biyu ya saka ta a makarantar secondary amma boarding school.

 

 

Da yake bata san wasa ba, bata san shirme ba, bata san komai ba sai karatu, sai ya kasance karatun kawai take yi, karatun da ko ƙwaƙwalwar kifi ne da mutum dole karatun ya shiga ya zauna balle tata ƙwalwar mai saurin kama abu da haddacewa (ko wane ɗan Adam da bawarsa, wannan yana daga cikin baiwarta) haka yasa cikin ikon Allah duk ajin da take koda bata fita a na ɗaya ba, zata zo a na biyu.

 

A haka har ta gama secondary cikin nasara ta fita da sakamako mai kyau wanda ya bata damar samun shiga jerin waɗanda Gwamnatin jiha ke basu scholarship ɗin karatu a babbar University ɗin dake babban birinin ƙasar.

 

Abinda yake bata mamaki tun fitowarta cikin gari sai taga ma masu kalar fatarta sunfi yawa, sannan babu wani nuna banbanci kamar ma basu damu da kalar fata ba, sai dai dukda haka bata iya sakin jiki da mutane ba dan ƙaton ciwon da mutanen ƙauyensu suka mata a zuciya tun yarinta yana nan bai goge ba, har yanxu bata iya magana a cikin mutane, har yanxu bata iya ɗago ido ta dubi wanda yake gabanta, sai take gani kamar za’a jefa mata kallon ƙyama irin wanda ake mata a baya.

 

 

Sai dai abinda bata sani ba wannan lifestyle ɗin nata da ƙoƙarin ta, ya saka da yawan mutane suke matuƙar sonta da respecting ɗinta, da yawa suna so suyi abota da ita amma ba kowa ne take sakin jiki dashi ba, uwa uba yanzu da ta ƙara girma sosai ta goge, asalin kalar fatarta chocolate da kamanninta na baƙaƙen labarabawa ya fito, kyawunta mai sanyi ne, idanunta masu matuƙar haske da take ɗan yawan lumshesu wanda duk balakin mutum ba zata buɗasu duka ta kallesa ba, sune suke saurin fizgar mai kallonta ya ji baya son kauda idonsa daga kanta.

 

 

Sosai tayi farin ciki da damar da ta samu na cigaba da karatu dan a yanxu ta gama fahimtar babu abinda zai bata darajar da mahaifiyarta ke mata fata irin Ilimi, Ilimin Addini da na rayuwa, ta zage damtse sosai bayan sunyi candy ta cigaba da haddar sauran litattafan addini dan a boarding school Alqur’ani kaɗai ta samu haddacewa cikin rarar lokacin da take samu, sauran litattafan kam bata samu wadda ta iya ba balle ta koyar da ita yadda zata fahimta, a fannin ilimin boko kuma ta ɗauki aniyar indai ana tardo ƙarshen biro da takadda sai ta ƙure su InshaAllah.

 

 

A haka har lokacin tafiyar su ya gabato hakimi da ya ɗauke ta kamar yar cikinsa da kanshi yasa aka yi mata komai na shirin tafiya, tun daga kan abinci, sutura masu kyau, takalma da sauran abubuwan da ba za’a rasa ba, muhallin zama dama yana cikin scholarship ɗin sai idan mutum yana buƙatar ƙari ne.

 

 

*Azhar* (The Capital State)

 

Gaba ɗaya fadar shugaban ƙasa ta rikice babu abinda kake gani a farfajiyar Villar sai soldiers da keta kai kawo wasu na shiga mota suna fita daga Villa wasu kuma na shigowa,  ba komai ya haddasa haka ba sai ɓatan ƙaramar yar shugaban ƙasa wadda masu tsaronta suka kaita har makaranta lafiya ƙalau sai bayan an tashi ne suka neme ta suka rasa tun rana har gashi yanxu ƙarfe tara da rabi na dare ta bada baya.

 

 

 

A can cikin Villa kuwa shugaban ƙasa da ya gama rikicewa da sauri yake neman kwacewa daga riƙe shin da C.O.S Ahmad yayi yana faɗin kaga Amadu ka barni nace inje da kaina tunda naga duk sojoji da yan sandan da muka aika lusarai ne basu san kan aiki ba, karfa su cutar min da yata.

 

 

 

A nutse a kuma tausashe irin yadda zaka yiwa shugaban ka magana C.O.S Ahmad yace kayi haƙuri Sir kaga ba isasshiyar lafiya ce da kai ba ga kuma jikin girma babu yadda za’a yi mu barka ka fita, hakan zai iya janyo matsala ga lafiyar ka, idan ka bani dama zanyi magana da *Colonel Eeyad.

 

 

 

 

Shugaban ƙasa da yake neman mafita ta kowane hali da sauri yace ok…ok.. ka kira shi mana ai ni na zaci ma ya sani shiyasa ban kira shi da kaina ba.

 

 

 

A office kuwa yana ajiye wayar da ya gama amsa kiran C.O.S Ahmad ya ƙwala kiran Yaƙub lokaci ɗaya kuma ya dawo ya zauna dan yana ƙoƙarin tashi ne kiran ya same shi, Yaƙub ya shigo yana ƙamewa dan bashi girmansa yace Sir sai kuma ya saki jikinsa ya karasa kujerar dake kallon wadda Eeyad ɗin ke bisa ya zauna.

 

 

 

Eeyad dake ɗan jujjuya biro a hannusa idanunsa a rufe ya buɗe ɗaya ya kalli Yaƙub a ɗan fizge sai kuma ya buɗe su duka lokaci ɗaya yace “kana da labarin abinda ya faru da shugaban ƙasa?

 

 

Yaƙub ya ɗaga kai ya kalli sama kamar mai tunani sai kuma ya girza kai yace a’a bani da labarin abinda ya faru da sirikinka gaskiya.

 

 

A hankali Eeyad ya ciji leɓenshi na ƙasa yana jifar Yaƙub wanda yake mataimakin sa sannan amininsa da wani mugun kallo irin na kafa kiyayi kanka sannan ya buɗi baki yace” sun kyauta ai da basu fito da labarin duniya taji ba, ƙaramar yar shi aka ɗauke a makaranta shine Ahmad ya kira ni.

 

 

“Suhanallah” Yaƙub ya furta yana dafe kai sai kuma ya miƙe da sauri ya nufi hanyar fita yana faɗin bara naje na shirya sojoji ai bamu ga ta zama ba.

 

 

Eeyad dake  binshi da kallon kai kuma fa,    ya katse shi da faɗin tsayamin dan Allah malam, bance ka tarkato man kowa ba.

 

 

 

Dawowa Yaƙub yayi ya dafa table din dake gabashi yana kallon Colonel Eeyad  yace mi kake shirya wa?

 

A taƙaice Eeyad yace” zan je mu ɗan zanta dasu muga ko za’a samu daidaito”

 

 

Murmushi yayi jin wai zasu zanta a samu daidaito, yo Eeyad ne zai tsaya jin ta bakin mai laifi, shi da idan yaga mai laifi jikinsa har ɓari yake tamkar mayunwacin zaki yaga nama, amma sai ya kauda tunanin ya koma ya zauna har yanxu fuskarshi ɗauke da murmushi yana karkaɗa ƙafarsa yace” to dan Allah amma da wace niyya zaka yi wannan aiki? A matsayin ka na wanda haƙƙin tsaron al’umma ke kanka kodai duk cikin salon biko ne dan a taimaka a maido maka matarka?

 

 

Ya kai maganar karshe yana kauda kanshi gefe ganin yadda hancin Eeyad yayi jaja jur alamar ya shaƙa kuma gab yake da amayarwa sai dai  ya dauki aniyar ba zai kula shi ba dan ya fahimci Yaƙub shaƙiyyanci yake ji shi kuma yanada aikin yi gaskiya.

 

 

 

 

A nutse yace ” babu damuwa Yaƙub idan kayi wasa zan tura ka kaje kai kaɗai kuma in hanaka tafiya da bindiga tunda kai ba biko zaka je ba”

 

 

 

Zunbur Yaƙub ya mike ya ɗaga hannuwansa sama yana faɗin na tuba Sir dan Allah a min afuwa sharrin shaidan ne wlh, kaga bari ma na tafi matata tana can tana jira na, yana gama maganar ya fice dan sarai ya san Eayad zai iya aikata abinda ya faɗa kuma dole yaje ɗin tunda a gaba yake dashi.

 

 

 

Yana fita Eayad ya taka a hankali inda ya sagale  rigar saman uniform ɗinsa wadda aka rubuta Colonel Eeyad daga gefe ya dauka ya ɗora a kan ƙaramar dake jikinshi wadda ta kama shi tsam saboda yanayin ƙirar halittar jikinsa sannan ya fice daga office ɗin.

 

 

 

Duk kiran da Alhaji Abdulkareem (retired Brigedial General) ke jejjera mashi babu wanda ya ɗauka dan bai ma san ana kira ba, a halin yanxu da ya kasance 11 na dare yake zuƙa uban gudu bisa lafiyayyen bike ɗin da yake hawa a duk lokacin da hakan ta kama, bai tsaya ba sai a inda location ɗin da yake bibiya ya nuna masa amma ga mamakinsa wayar kawai ya iske a ƙasa cikin unguwar da za’a iya kiranta sabuwa dan gidaje kaɗan ne aka gama, sauran yawanci duk kango ne sai waɗanda har aka kai rufi amma ba’a shafe ba sannan gurin shiru babu alamar mutane.

 

 

Sakkowa yayi ya ɗauki wayar yayi dan tsaye yana tunani, har zai koma ya hau bike ɗin ya lura da abinda ya saka shi saurin dawowa baya yana bin sawun motar da ya gani.

 

 

 

Su bakwai ne a cikin incomplete ɗin ginin gidan mai girman gaske suna tsaka da surutansu sai gani suka yi mutun ya diro masu ta saman ginin dan baima tsaya knocking ko ƙoƙarin ɓalle ƙofa ba.

 

 

Duk miƙewa suka yi ko wane ya ɗauki makaminsa suna kallonshi da mamaki  ganin yadda suka zazzaro wuƙaƙe bai sa ya tsaya ko yaja baya ba saima cigaba da takowa da yayi ya samu guri ya zauna yana yi masu nuni a kan suma su zauna.

 

 

Dole su tsorata da wanda baiji tsoron mutane masu ban tsoro irinsu ba, saima suka fara tunanin ko aljani ne dan haka babu musu suka zauna amma duk basu mayar da makamansu ba.

 

 

 

Tunda Alhaji Abdulkarim yaji labarin Eayad ya tafi shi kaɗai ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake a babban falon ƙasa har zuwa yanxu da ƙarfe biyu na dare ta buga, yasan Eayad sarai idan ya saka kanshi abu koda zai wahala sai yayi abin nan, abin tashin hankalin baisan ko su waye ba, bai san mi suka taka ba amma ya kama hanya ya tafi sai kace wanda bai san darajar ranshi ba.

 

 

Ƙarar buɗe ƙofar falon ya saka shi saurin juyowa idonshi ya sauka a kan Eeyad da ya saɓo Ikhlas a kafaɗar shi saboda baccin da tayi ya taka a hankali ya kwantar da ita a kan kujera shima ya zauna gefe yana kai dubanshi kan Abih da tunda yaga shigowar Eayad ɗin ya zauna yana ƙure shi da ido.

 

 

Sun dan jima a haka kafin Abih ya buɗe baki kasa ƙasa yace “mi kayi kenan? Kai baka tunanin rayuwarka shine zaka kaɗa kai kaje kai ɗaya.

 

 

 

Eayad ya dan sauke ajiyar zuciya sannan yace Abih idan aka yi gayya zasu cutar da ita.

 

 

Sai kuma ya dan kauda kanshi gefe yana kaɗa ƙafa yace ” kuma ba maganar rashin tunanin rayuwa bane dan ai kai na gado, Abih kaifa lokacin har aljanu kake faɗa dasu bama ta karan mutane ba” yayi maganar cikin sigar da kana jinta ka san iya shege ne irin na ɗan yau.

 

 

Abih ya watsa mashi daƙuwa yana fadin kaci gidanku Eayad watau yaran zamani iyayenku ma kun mayar da su kamar kakanni ko, to in ba haka ba yaushe ka taɓa ganin nayi faɗa da aljani? Abih ya bashi amsa tare da miƙewa ya haye matatakala ya nufi dakinsa cike da samun nutsuwar ganin ɗan nasa yana lafiya…….✍🏽

Leave a Reply

Back to top button