Nailah Hausa Novel

Nailah 8

Sponsored Links

*🌸NAILAH🌸*

 

~*(The abandoned flower🌹)*~

Related Articles

 

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*

 

 

*PAGE 8*

 

 

*Wednesday*

 

Duk yinin ranar Eeyad bai samu kanshi ba tunda ya je office saboda meeting da suka shiga daga ƙarfe tara har zuwa ƙarfe sha biyu, sannan suka ƙara shiga wani ƙarfe ɗaya sune har la’asar, ana gama sallar la’asar a masallaci ya koma office ɗin ya zauna bisa daya daga cikin kujerun dake cen gefe cikin office ɗin aka jera su sai TV dake manne a jikin bango da freight a gefe sai gurin yayi kamar falo, ya cire rigar dake sama ya ajiye sannan ya zauna yayi relaxing tare da lumshe ido yana nazarin text message ɗin da Husnah ta tura masa lokacin da suna meeting.

 

 

 

Karon farko yaji yana son haɗa kan iyalinsa ya rayu kamar kowa, haka kawai ya ji kaɗaici irin wanda bai taɓa ji ba a rayuwa bayan rasuwar matar shi ta farko, ya shiga rikici sosai ganin jaririn da ta bar masa wanda ke buƙatar kulawa irin ta uwa.

 

 

A nutse ya janyo wayarshi ya maida reply a message ɗin Husnah kamar haka “kin shirya dawowa ki raine shi a inda kika same shi?

 

 

 

Bayan kamar 2 minutes ta kira shi, dan murmushi yayi ya kara a kunne tare da yin sallama sannan yayi shiru yana sauraren abinda take faɗi daga can.

 

 

 

Saida ta gama sannan yace “uhmm, kin sani kenan.

 

 

 

Ga mamakin shi sai tace “yes ai hakan zaɓi na ne, zan shirya amsar halinku irin na maza.

 

 

 

Wannan lokacin dariya yayi har haƙoransa suka bayyana, bai bata amsa ba ya katse kiran yana ayyana wani abu a ranshi, ya zaɓi yin shiru ne dan shi yafi son yayi abu a aikace ba wai faɗi a baki ba.

 

 

Daga can ɓangaren ma Husnah murmushi tayi mai ciwo, tana jin ciwo a ranta amma magana ce ta gaskiya, idan tana son gaskiya Eeyad ba mijin mace ɗaya bane, koda taƙi gaskiyar ma ita ce a wahalce, ba wai dan yana da nacin abin ba ne, kawai idan har abin ya wakana sai ta yini ta kwana tana jinyar kanta, sannan wani daren ma idan yayi haka zata ƙara wuni ta kwana tana jinya, ita ba haka take so tayi rayuwa ba gaskiya, tanada abubuwan yi da yawa a kowane yini bayan wannan, ba kuma zata ce rashin sabo bane dan a zamansu na tsawon wata biyar tare yaci ace ta saba amma abu idan aka fara tun mutum na jin shauƙi har a saka shi a ukku.

 

 

 

Sai 5pm ya baro office ɗin ya nufi gidan Abih kai tsaye.

 

 

Yana shiga yayi parking a inda sauran motoci suke sannan ya taka a kafa ya nufi ɓangaren Abih, ya iske shi a garden yana hutawa da ni’imtacciyar iskar dake gurin mai saka nutsuwa ga bawa, bayan ya gaida shi ya amsa, a nutse ya sanar dashi lamarin da ya saka Abih hamdala a ranshi yana jin lallai Allah maji roƙon bawa ne, ya jima yana burin ganin Eeyad ya zama cikakken magidanci kamar kowa, sam baya jin daɗin ganin yadda yake rayuwa a yanzu.

 

 

 

A ranar su Khairat suna dawowa daga islamiyya Mommy ta sanar dasu zasu yi tafiya gobe InshaAllah kuma zasu kwana biyu a can sai dai bata faɗa masu inda zasu je ba, dan haka tun da dare suka haɗa duk kayan da suke da buƙata a tafiyar sannan suka kwanta, Arif sai tsalle yake dan an kira shugaban makarantarsu an ɗaukar mashi excuse, ko ba komai zai huta da shirgin makaranta.

 

 

 

Washe gari gurin ƙarfe sha ɗaya kowa ya gama shiri dan tafiya suka fito inda aka jera motocin da zasu kaisu airport.

 

 

Nailah da ke sanye da riga da sket na atamfa da suka matukar kawata surar jikinta, yanzu kuwa mayafi ne a jikinsu daga ita har Khairat sai mai ɗan girma ne babu laifi, ta tsaya cak sakamakon idonta da ya sauka cikin na Eeyad dake tahowa zai shiga daya daga cikin motocin, bayanshi kuwa kartin sojojin nan ne irin shi da take jin kamar ta shaƙe su duk lokacin da zasu fita suka bisu a baya kamar jela.

 

 

 

Ɗauke idanunta tayi tana tunanin ita rabonta da ganinshi tun ranar da taje ta jaddada mashi ta fa daina zuwa aiki, saboda tun ranar da tazo Mommy tace mata babu wani aikin da xata kara zuwa, ta zauna ta maida hankali kan karatunta kawai, sai dai duk da ta daina zuwa ɗin bata daina ganin shigar albashinta ba, dan haka ta same shi ta faɗa mashi dan ƙila ko bai sani ba hala.

 

 

 

Eeyad dake mamakin tsohon rainin hankali irin na Nailah, to idan ma ta daina zuwa sai yanxu ne da aka shafe kusan wata uku a lokacin, sai a sannan zata faɗa mashi itafa ta daina zuwa aiki, bai yi magana ba sai taɓe baki da yayi yace “Uhmm” yana binta da kallon nan na ƙasa ƙasa irin yanda take ma wasu.

 

 

 

Ta ɗauke idanunta daga kanshi ta isa bakin motar da su Mommy ke ciki ta  shiga tana tunanin ina ne kuma za’a je har da Sir, ga Abih da kuma aminin Abih suma suk harda su.

 

 

 

 

Tafiya ce suka yi ta minti arba’in a cikin jirgi suka isa garin Aksur, daga nan suka ɗauki hanyar da ta saka Nailah zaro ido zuciyar ta na wani irin tsittsinkewa.

 

 

 

Ba shekara tara ba, ko shekara ɗari tayi ba zata manta wannan hanyar ba.

 

 

 

Jikinta na rawa take nuna ƙofar gidan hakimin Tayra, lokaci daya kuma ta kalli Mommy tana faɗin “n..n..nnan…nan…?”

 

 

Ta kasa magana, ta rasa minene zata ce, kamar ta mance yadda ake magana dan haka ta buɗe marfin motar da sauri ta fita sai kuma ta tsaya a gurin ta daga kanta sama ta shaƙi iskar garin tana murmushi.

 

 

 

Ganin tayi gaba zata shige gidan hakimi sai Khairat da Mommy suka fito suka rufa mata baya suka shiga a tare.

 

 

 

Sun jima a gidan hakimi dan a nan suka ci abincin rana da aka dafa masu mai rai da lafiya, matan suna cikin gida, mazan kuwa suna ɓangaren hakimi, Inna matarshi kuwa sai bin Nailah take da kallo tana ayyana rayuwa kenan, dukda itama lokacin da Nailah ke ɗan zama gidan idan sun samu hutu daga boarding ba wani janta a jiki take yi ba, babu ruwanta da ita sannan bata hantararta, amma sai ta ga Nailah tana ta bata girman ta, kamar ta manta yadda ta mu’amalance ta a baya, lallai yarinyar tanada wani nau’i na halin girma.

 

 

 

 

Sai bayan la’asar suka isa ƙauyen Dosan bisa jagorancin Mlm. Abubakar da Hakimi, a hankali Eeyad ke bin ƙauyen da kallo a ranshi yana ayyana “wai a nan ta rayu? A nan ɗin ma kuma a ƙaskance? Ya salaam, lokaci ɗaya yaji baya ra’ayin ƙauyen sam, yaji baya marmarin sake waiwayar shi har abada.

 

 

Kauyen yana nan bai canja daga yadda ta sanshi ba sai yan gidaje da aka kara ginawa suma ba wani da yawa ba, tunda aka tsaya a ƙofar gidansu Mommy ta zubawa Nailah ido tana kallon yadda jikinta yayi laƙwas, kallon ƙofar take tana haɗiyar yawu daƙyar ta kuma kasa motsi balle ta bude motar ta fita.

 

 

 

 

Kamo hannunta da Mommy tayi ya saka ta ɗan zabura sai kuma ta kalli Mommy.

 

 

 

“Mommy ina ne nan? Who are these people?

 

 

Arif ya faɗa yana bin mutanen ƙauyen da tunda motocin suka shigo suke binsu da gudu har suka tsaya sannan suka yi cirko cirko suna kallo kai kace sun ga abinda ya zo daga wata duniyar, koda yake haka ne babu shakka, sun ga abinda basu taɓa gani ba a cikin ƙauyen.

 

 

 

Nailah ta kamo hannunshi tana murmushi ta nuna gidansu tace “nan ne gidan mu Arif, ba kace kanaso kaga ummana ba, ummana tana nan ciki.

 

 

 

Zaro ido Arif yayi tare da ƙyalƙyalewa da dariya ya buɗe motar ya fice da sauri yana faɗin “sai na riga ki ganinta, sai na riga ki ganinta”

 

 

 

Dariya suma duk sukayi sannan sannan suka bi bayanshi.

 

 

 

 

Babu kowa a tsakar gidan sai Asma da ta gama wanki tana shanya taga shigowar Arif da gudu yana dariya, sai dai ganinta ya saka shi tsayawa a gurin yana kallonta yana tunanin kodai ba nan bane, dan ya ga wannan ai balarabiya ce ba irin Aunty Nailarsa ba.

 

 

 

Itama kallonshi kawai take yi tun daga fatar jikinshi dake fresh, kayan jikinsa da kuma yanayin halittarsa dake nuna zallar hutun da yake ciki, sai kuma ta mayar da idonta kan Mommy da ta shigo yanxu Khairat na biye da ita.

 

 

 

Wadda ta gani a irin wannan lokacin, a irin wannan yanayin ya saka ta sakin rigar dake hannunta zata shanya, a rikice ta ƙwala kiran Ommi.

 

 

Ommi dake ɗaki da sauri ta fito gabanta na faɗuwa na tunanin ko wani mugun abu ya faru da Asma, sai dai ganin waɗanda ke tsaitsaye ya saka ta tsayawa a gurin tana ƙura mata ido tun daga samanta har ƙasa.

 

 

 

Da rawar jiki, da gudu Nailah ta isa inda mahaifiyarta take ta rungume ta tana sakin kuka mai sautin gaske, ta shiga fadin “Ummi na, mama na”

 

 

Ommi a hankali take shafa bayan Nailah sannan ƙasa ƙasa kusa da kunnenta ta furta “mintuna, awanni, kwanaki, satika, watanni, shekaru, dare da rana *Agla*.

 

 

 

Sun jima a haka, sannan ta saki Ommi ta taka a hankali tana nufar Asma da itama ke tsaye har yanxu tana kallonta, ta tsaya a gabanta tana mararin rungumar ƙanwar tata sai dai bata san ko zata buƙaci hakan ba.

 

 

 

Murya a raunane Asma tace “yaya” sannan faɗa jikin Nailah tana sakin sassayan kukan da ya saka Nailah ƙankame ta da karfi ƙirjinta na harbawa da sauri”

 

 

 

 

Sai a yanzu hawayen da Ommi ke ta rikewa suka samu damar silalowa saman kumatunta, ta goge su da sauri ta karasa inda su Mommy suke wanda tuni Khairat yar aljanna ta fara hawaye itama, Mommy ba zaka fahimci komai a kan fuskarta ba, Arif shi kuma sai faman zare ido yake ganin ana kuka, sai kuma ya ruga yayi waje da nufin faɗama su Daddynsa kuka fa ake ta yi cikin gidan nan.

 

 

 

Ommi sosai ta saita yanayinta ta tarbi su Mommy bayan ta shimfida masu babbar tabarmar kaba ƙarƙashin inuwar bishiyar dake cikin gidan mai cika da kuma sanyi.

 

 

 

A sannan Nailah ta sanar mata su Abih dake can waje suna jiran iso, lokaci ɗaya kuma tana ta wurga idanu ganin bata ji motsin Abansu ba.

 

 

 

Saida suka kimtsa aka ƙara shinfida wata tabarmar sannan aka shigo da su Abih dake ta mamakin mutanen wannan ƙauye yana ayyana to dama a ƙasar nan za’a iya samun garin da babu bakar fata ko ɗaya? Koda yake ai ƙauyen ne ya cika ƙauye gashi ba wani girma ne dashi ba, babu mamaki mutanen cikinsa duk ahali ɗaya ne idan aka bibiyi tarihi, to amma idan haka ne miyasa Nailah ta kasance mai duhun fata?………………✍🏽

Leave a Reply

Back to top button