Nailah Hausa Novel

Nailah 6

Sponsored Links

 

*🌸NAILAH🌸*

 

Related Articles

~*(The abandoned flower🌹)*~

 

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN

ƘAY*

 

 

*PAGE 6*

 

 

Mommy ta lura da yadda Nailah keta ɓoyewa bayan Khairat tunda Eeyad ya shigo falon, shi kuma kallo ɗaya ya watsa mata irin na ke kuma? sannan ya ɗauke kanshi ya cigaba da magana a wayar dan bai gama ba, Mommy ganin abin ba na ƙarewa bane tace “Khairat tashi ki dakko ma yayanku ruwa mana”

 

 

 

Zunbur Nailah ta miƙe itama ganin Khairat na shirin tafiya ta barta nan gurin bayan ta samu ta laɓe a bayanta kuma sai ta tashi ta barta tantarwai jama’a?

 

 

Ƙasa ƙasa tace “muje nima in sha ruwan a can” babu musu Khairat ta juya Nailah ta koma can ɓangaren hannun damarta suka nufi kitchen ɗin tare.

 

 

Sai da suka ɓace ma ganin Mommy sannan ta ɗauke idonta daga kan Nailah tana murmushi, ita dai haka kawai yarinyar ke burge ta ba tun yau ba, tun ranar da ta fara ganinta, gashi kuma tazo da wani lamari mai girma, irin mai shiga lokaci ɗaya ya mamaye abinda yake da wuyar tardowa balle a samu damar kaiwa gareshi.

 

 

 

Mommy ta maido dubanta kan Eeyad tace “ka yi tunani mai kyau, dama ta sanka ne naga duk yanayin ta ya sauya daga zuwanka?

 

 

 

Shiru yayi bai bata amsa ba, har saida ta fidda ran zaiyi magana taji yace ” a Company take aiki”

 

 

 

Tsaki Mommy ta ja na takaici sannan ta sanar mashi da saƙon Abih cewa yana son ganinshi bayan Sallar Isha.

 

 

Suna isa kitchen ɗin Nailah ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta.

 

 

“Ke wai miye dan Allah, daga ganin mutum kin bi kin rikice” Khairat tayi maganar tana ƙure Nailah da kallon tuhuma.

 

 

 

Nailah ta yatsine fuska tana ɗan watsa hannayen ta tace “wai dama Sir ɗan gidanku ne? Shine fa nace maki ya ga wannan katin da Zee ta bani.

 

 

Ɗan baya Khairat tayi kaɗan ta kama haɓa kamar na alamun mamaki sai kuma tace eh mana, ba dai kince a Unigold kika samu aiki ba, kuma dai ai Unigold Company na yayanmu ne.

 

 

Nailah tace to miyasa baki faɗaman ba?

 

 

Khairat da gaba daya maganar ta fara gundurarta tace ” to amfanin miye hakan xai maki, ai na san dai ba kallon shi zakiyi kice masa ni fa ƙawar ƙanwarka ce dan haka ka san matsayin da zaka dauke ni ba.

 

 

Ta nufi hanyar fita sai kuma ta juyo ganin Nailah tayi tsaye taƙi tahowa tace “eh kam gwara ki tsaya dan ko nice abinda zanyi kenan, bari na kai mashi na dawo mu haye sama kawai.

 

 

 

 

Kamar yadda Mommy ta sanar dashi ana gama sallar Isha ya nufo gidan dan amsa kiran Abih, ya iske shi yana cin tuwon dawa da miyar kuɓewa ɗanya wadda ta ji naman kaza, sosai yake son tuwon dawa dan haka shima yayi serving kanshi ya shiga ci har suka cinye suka wanke hannu sannan Abih ya maida dukka hankalin shi kan Eeyad yace “game da maganar matarka ne, nayi magana da mahaifinta, mun kuma tattauna sosai dan samo mafita a lamarin”… Ya kwashe yadda suka yi da Abban Husnah sannan ya dora da faɗin “yanxu kai muke jira daga nan zuwa wata biyun InshaAllah.

 

 

 

Girgiza kai Eeyad yayi yana tunanin anya Husnah ta san da wannan hukuncin da mahaifinta ya yanke, koda yake shi kawai dan mafitar yar shi zai yi ba dan wani abu ba, amma zai yi magana da ita ya ji ta bakinta.

 

 

 

Ya ɗago ya kalli Abih yace “Abih inaso muje wani guri tare da kai jibi InshaAllah”

 

 

Allah ya kaimu lpy kawai yace ba tare da ya tambaye shi inda zasu je ɗin ba.

 

 

Washe garin ranar da suka zo Khairat ta ja Nailah suka nufi boutique inda suka siyo kaya na ban mamaki tun daga kan dogayen riguna, riga da wando, riga da sket da sauransu sannan suka biyo ta shagunan atamfofi suka siya suka bada ɗinki, Nailah ta kasa ƙiyasta karamci da mutunci irin na Khairat, ta ya zata ɗauke ta kamar yar uwarta ta jini bayan bata san ko wacece ita ba, bata taɓa sanar da ita wani abu dangane da rayuwarta ba balle ace tana tausaya mata ne, abu ɗaya ta sani game da ita shine ta hanyar scholarship da take makarantar daga haka babu komai, shine kuma suma iyayen sun ji sun gani suka riƙe ta hannu biyu duk da ko miye ta silar Khairat ne, ai gaskiya dole ta canja mata suna ta fara kiranta *Khairat yar aljanna*.

 

 

 

Rayuwa ta cigaba da tafiya tuni Nailah ta saba da kowa na gidan, har Abba da ba sosai yake shiga harkar wanda ba na jikinshi ba, amma yanda yake ɗaukarta kai kace akwai wata alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu, a hankali Nailah ta fara tsintar soyayyar uwa, uba, da kuma yan uwa a cikin wannan ahali har take ganin muhimmancin da suke bata ya zarta yadda ta cancanta tun ranar da hutunsu ya ƙare ta tattaro kayanta da nufin komawa estate Mommy ta kalleta tace “yanxu wani abu aka yi maki da zaki tattara kaya kice zaki tafi?  ko wani yace ki tafi, ko kuma dai ki nuna man abinda kika ga dama shi zakiyi? to baki isa ba wlh koda wasa kika ƙara min zancen tafiya sai na saka an zane man jikinki tas, sosai Mommy ke faɗa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba wanda ya saka Nailah da faɗa ke saurin saka ta ruɗewa jikinta na rawa ta ƙaraso ta riƙe hannunta tana fadin “Mommy dan Allah kiyi haƙuri ba zan ƙara ba InshaAllah” sai a sannan Mommy ta dakata tana sassautawa ganin yadda Nailar duk ta rikice.

 

 

 

Yau da ya kasance ranar Laraba a gajiye suka dawo daga makaranta, Khairat dake jin yunwa na neman halaka ta ko hijab bata cire ba ta nufi dining ta shiga zuba ma cikinta, Nailah kau sama ta haye ta shige ɗakinta wanda yaji komai na more rayuwa ta tuɓe kayan jikinta ta shiga wanka, tana fitowa ta iske mommy zaune bisa gado tana duba wayarta, dama hakane duk bayan lokaci haka Mommy ke zuwa babu tsammani tace su bata wayarsu ta shiga dube dube.

 

 

Mommy na ganin fitowarta ta ajiye wayar ta maida hankalinta kanta tace “idan kin shirya kije ɓangaren Abbanku kinyi baƙo a can.

 

 

Da sauri Nailah ta ɗago ta kalli Mommy sai kuma ta kauda kanta tana ayyana baƙo kuma? Ita ko wane baƙo ne zai zo mata babu sanarwa kuma ai ita batada wani wanda har zai zo mata baƙunci kuma gurin Abih.

 

 

Mommy dai tashi tayi ta fita bata bi ta kan Nailah da alamunta suka nuna tana buƙatar ƙarin bayani, a ranta tace idan kin je kin gani, nima yau yan miskilancin irin naku zan taɓa.

 

 

 

Leshi ne peach color ta saka da ya matuƙar amshi fatar jikinta ya ƙawata ta, babu kwalliya a fuskar ta bayan kwallin da ta saka ma idonta, ta saka hijab ɗinta har ƙasa sannan ta nufi ɓangaren Abih tana ta saƙe saƙe a ranta.

 

 

A kan Abih dake zaune bisa daya daga cikin kujerun falon fuskarshi yalwace da murmushi ta sauke dubanta bayan tayi sallama an amsa sannan an bata izinin shiga, sai dai tsinkayo dayar muryar da suka amsa sallamar tare da Abih ya saka ta saurin kai dubanta ɓangaren jikinta na ɗan rawa rawa.

 

 

 

Baba!!! Ta furta a inda take tsaya ta kasa gaba ta kasa baya tana bin shi da kallon mamaki.

 

 

 

Malam Abubakar da shima ke mata kallon mamakin budurwar da aka kira mashi a zuwan Nailah duk da shekara tara ba wasa ba, yayi murmushi yana faɗin “kaga kuma ta tsaya, ko bata gane ni ba oho”

 

 

Nailah ta manta da ko wa yake a wajenta, ta manta da su waye a wajen, ta manta shi din ba muharraminta bane, ta samu damar ɗaga ƙafarta da hanzari ta ƙarasa inda yake tana ƙoƙarin faɗawa jikinsa yayi saurin dakatar da ita yana faɗin “kai kai kai, diyata baki san kin girma ba MashaAllah yanxu idan kika faɗo min ai tsaf zaki ɓalla ni, ko ba haka ba” ya ida maganar yana kama haɓa idonshi kan Abih da keta dariyar Nailah.

 

 

Zama tayi gefenshi tana dariya Abih na ganin haka ya tashi dan basu guri su yi magana a nutse.

 

 

Mlm. Abubakar ya ƙura ma Nailah ido yana ayyana lallai Allah mai hikima ne, wato gaba ɗaya ta canja ba zaka taɓa tunanin ɗiyar Mlm sagir ce haka ba, ta ƙara girma, fatarta mai duhu ta washe, nutsuwarta tun ta yarinta tana nan tare da ita har yanxu, idan ma kayi ƙoƙarin cewa ta taɓa zaman ƙauye za’a iya yi maka kallon maƙaryaci.

 

 

Yana cikin tunanin ya tsinkayo muryarta tana fadin “Baba ina su Ommi da Abbana? Abbana baya sona har yanxu ko? Ina su Mariyama? Ina……

 

 

“To ki tsaya in dinga baki amsa mana sannan ki ƙara yin wata tambayar” ya katse ta daga tambayoyin da take ta jero mashi ba ƙaƙƙautawa, ta saurara tana kallonshi ya cigaba ta faɗin “Ommi da Abba suna lafiya, Mariyama tayi aure, Asma ce batayi auren ba har yanzu, sai kuma mi?

 

 

Ya tambaye ta yana kallon yadda ta turo baki, to ta ya zai bata amsa a duƙunle, koda yake da mi zai faɗa mata bayan haka, ta san namiji dai kuma babba ba zai zauna ya dinga bata labarin rayuwar gidansu ba dan haka tace “Ommi bata baka saƙon komai ka kawo min  ba?

 

 

 

Mlm. Abubakar yace ai basu san nazo ba, nima wani uzuri ne ya kawo ni shiyasa kika ganni kamar daga sama, a ranshi yana kokowa da wani lamari mai girma da yake son ɓoye mata amma zuciyarshi na kokonton anya idan yayi haka ya kyauta kuwa, sai dai idan ya tuna abinda ke ɗaya ɓangaren sai yaga ai komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah.

 

 

 

Sun ɗauki lokaci a tare sannan yayi mata sallama dan zai tafi, Nailah dake jin inama zai tafi da ita tace “Baba dan Allah zan bika in je ko sati ɗaya ne in dawo”

 

 

Malam Abubakar ya kama haɓa yace tofa kin mance maganar da mahaifiyarki ta faɗa maki, ranar da zamu taho da kunnuwa na naji tace tana so ta ganki cikin darajarki, to idan kika koma haka salim alim mi kika yi kenan?

 

 

 

Nailah da bata gane maganarshi ba tace Baba kenan har yanxu ban samu darajar ba?

 

 

Malam Abu ya maida hankalinshi kanta yana murmushi yace tabbas kin samu daraja, irin wadda wani bai taɓa samu ba a ƙauyen Dosan dan kin nemi ilimi, kinyi karatun Addini da na rayuwa karatu mai zurfi, kin samu wayewar rayuwa kin zama ta musamman ko a cikin birnin balle a ƙaramin ƙauye irin namu, tabbas mahaifiyarki tana maki fatan wannan darajar amma akwai wata darajar da zata idasa cike wannan, ki cikata Nailah, ki cika ta sannan in sada ki da mahaifiyarki, nafi so ki koma da cikakkiyar darajar yadda zata yi cikakken farin ciki.

 

 

 

Nailah da Mlm. Abubakar ya ƙara saka ta a duhu da maganganunsa dan ta kasa gane wace darajar kuma yake nufi tace to baba InshaAllah, sannan tayi mashi Addu’ar sauka lafiya ta miƙe jiki babu ƙwari ta fita.

 

 

Sosai Abih ya yiwa Mlm. Abubakar alkhairi sannan aka kaishi har Airport saida suka ga tashin jirgin suka dawo.

 

 

 

Tana komawa ɗakin Mommy ta nufa kai tsaye, tana zuwa ta faɗa jikinta ta saki kukan da take ta riƙewa, Mommy kuwa baiwar Allah duk ta ruɗe tana tambayar mi aka yi mata, ita da ke jiranta ta dawo da farin ciki sai ta dawo mata da kuka?

 

 

 

Cikin shassheka Nailah ta cigaba da faɗin “wai Baba ba zai kaini gurin Ommi na ba sai na ida samun daraja, kuma ni ban san wace daraja yake nufi ba, shine kuma bai gaya man ba”

 

 

Mommy a ranta tace “an zo gurin” sai kuma ta ɗago fuskar Nailah da tayi shaɓe shaɓe da hawaye tana kallon ta tace wannan shine abin kukan? Abu ne mai sauƙi fa yana nufin sai kinyi aure ko kuma sai kin samu mijin da zaku je can a ɗaura maki aure shine fa kawai.

 

 

Nailah ta ɗago da sauri tana kallon Mommy tace……….✍🏽

Leave a Reply

Back to top button