Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 31

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣

 

…….Sai da Mommy ta harari Afrah sannan ta sakko AA a bayanta ta miƙama Uncle Muneer da yay magana. Dada ko tai muƙuy tana satar kallon yaron. Kamar dai kunya ce ta hanata cewa a kunnto mata shi. Amsarsa Uncle Muneer yay yana murmushi da tsokanarsa irin na wasar jika da Kaka Mommy na kare masa suna dariya. Cikin murmushi ya dubi Dada da faɗin, “Dada gafa baƙon duniya kinyi sabon ɗa”.
Murmushin yaƙe Dada tayi da faɗin, “Aiko ga shi nan bai baro gida ba, ALLAH yasa iya nan ya tsaya bai ɗakko sauran halayyar ba”. Kowa ya fahimci abinda take nufi, wato kamanin AA da Smart. Amma sai duk suka basar da ita. Ganin bata da niyyar cewa a bata ɗan yasa Uncle Muneer miƙa mata shi. A dai-dai nan Lulu da su Afrah suka kaima labarin zuwan Dadan ta fito. Babu kunya ta zabura gabansu ganin Uncle Muneer na miƙama Dada AA. Cikin sauri take faɗin, “Uncle kai dai ɗauki amma dan ALLAH kada ka bata ta faki idanunku ta kashe min yaro.”
Babu wanda furucin Lulun bai dakarma zuciya ba. Cikin faɗa Mommy ta ce, “Mawaddat mike damunki? Baki gane wacece bane? Dada ce fa!”.
Babu alamar damuwa ko sassauci da ga Lulun ta ce, “Mommy sarai na gane wace. Ko a cikin dubun mutane bazata layance min ba ai ba! Dada bace?. Kiyi haƙuri Mommy ki fahimceni, tayaya zan yarda ta ɗaukar min yaro bayan tun yana ciki aka haɗa kai da ita wajen nema ganin bayansa a gaɓar da daga ni har ubansa bamu san da shi ba saboda tsabar zaluncinsu. Dan haka barni da tsohuwar nan ni na dawo a rakkiyarta. Shin mima ya kawoki gidanmu? Keda kike zaginmu kuma kin rantse ƙafarki bazata sake taka cikinsa ba saboda Daddy da Mommy sun zalunce ki?”.
A daburce Dada ta ce, “Kina da hankali kuwa Mawaddat!?”.
“Sarai nake Dada, kinfi kowa sanin haka kuma. Ko a lokacin da nake shaye-shaye na san abinda nakeyi balle yanzu da nake a cikin hankalina. Yanzu dan ALLAH bakiji kunyar zuwa wai ganin abinda na haifa ba? Abin bai miki wani banbarakwai ba hakannan? Ai nazata ko’a hanya kika ga jinina dana Aliyu kya gudu dan kunya. Baku so ba ALLAH yayi, Aliyu ɗan Aliyu Mawashi ya tabbatar muku shi ɗan halak ne. Kuma ki sanarma ɗayan Mugun ni da shi wasa yanzu zai fara…”
Rawa jikin Dada ya farayi kamar mazari. Tuni hawaye sun cika mata idanu, muryarta na rawa ta ce, “Mawaddat ni kike ma irin wannan ɗibar albarkar haka? Saboda namiji? Namijin ma da bai damu da ke ba bai taɓa sonki ba sai da akai masa tallarki da sunan auren yarjejeniya. Kin bar gidansa bai nemi inda kike ba…”
Cikin ƙyaɓe baki Lulu ta ce, “Wannan gurgun tunaninki ne Dada. Shiyyasa kika zabgan ƙarya Aliyu ya sakan ko kunya baki ji ba saboda kina son na auri shashashan jikanki da baida freedom ɗin kansa sai na ubansa. Yo ai ko maza sun ƙare a duniya gara na mutu babu aure dana auri wannan shakatafin da ko ƙirrar mazan ƙwarai babu a jikinsa soƙai-soƙai kamar wani ɗan talo-talo. Aliyu ya soni ko karya soni wannan ba matsalarki bace ba, jeki fara gyara naki matsalar auren da ya rage saura kwanaki hope ɗinki ya kufce inba haka ba wlhy azumin bana sai mun buga miki gwauruwa tashi gari ya waye….”
“Mawaddat!!”.
Daddy ya faɗa da ɗan ƙarfi cikin tsawatarwa. Cikin girmamawa ta ce, “Na’am Daddy”.
Kansa ya girgiza mata alamar ta bari. Harara ta ballama Dada ta ɗauke kanta. Mommy da Uncle Muneer abin ai ya girmi kansu. Yayinda Dada ta saki kuka tana nuna Lulu. “Ni zaki cima mutunci Mawaddat saboda na zo gidanku ganin ɗanki. Ni kike nunama kin haihu kin san zafin ɗa?”.
Baki Lulu ta murguɗa mata da taɓe baki. Uncle Muneer ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyara zaman AA a cinyarsa da yin gyaran murya ya dubi Dada. “Dada ya isa haka dan ALLAH miye abin wani kuka anan. Mawaddat yarinya ce ai, sannan irin wannan ranar nake gudun mana dama shiyyasa nake nuna miki ki daina biyewa Yaya da al’amarinsa. Yarinyar nan itace dai zata zauna da Tajuddeen, tun farko da aka ƙulla tace muku bata so, amma kika damu kanki, kuma godema ALLAH rabon yaron nan na namiji ne, da mace ne wlhy komai zai iya faruwa ciki harda iya rasa rai….”
“Yanzu dai Manneeru kana sake goyon bayanta ta cigaba da zagina kenan?”. Dada ta faɗa cikin kuka. Da sauri ya ce, “Sam ba haka nake nufi ba Dada. Taya zan giyama Mawaddat baya ta zageki kuma. Amma kuyi haƙuri. Ina son a gyara kuskuren nan ne saboda gaba. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba yarinyar nan ta kuɓuta a hannun Yaya mi kike tunanin zai faru? Ko kuma data rasa ranta a wajen yunƙurin zubar mata da ciki. Yaya yayi amfani da ke ya barki a ciki. Sannan da mijin yarinyar nan fitinanne kina ganin zai ƙyaleku ne akan yunƙurin zubar masa da ciki har sau biyu? Ga shi kunje kunce mata mijinta ya saketa! Shin aure kan aure kukai shirin mata komi ma wai shin ni na kasa gane muku?”.
Tsigil Lulu ta ce, “Abinda suka shirya mun kenan Uncle, kuma wlhy a lokacin na ƙudiri aniyar suna ɗaurashi zan kashe Tajuddeen ɗin ne sai dai nima a kashe ni!”.
Babu wanda bai kalletaba yanzu ma a razane. Itako hankalinta kwance tama miƙe tana hararar Dada da cigaba da faɗin, “Kuma ko yanzu ba haƙura nayi ba. Dan bana barin bashin gaba. Sulaiman sai yamun bayanin alaƙata da shi da ya addabi rayuwata data mahaifina, dan haka ku jira sammacin kotu dan sai munyi shari’a, idan Aliyu ya iya muku haƙuri da kawai ci ni bazan barku ba”. Daga haka tabar wajen fuuuu. Dada ta zabura zata bita Uncle Muneer ya riƙeta yana girgiza mata kai. Sai ta ƙara fashewa da kuka ta maida faɗan a kan Daddy. Wai duk shi ya kitsama Lulu taci mata mutunci tasan Lulu bata da wannan wayon. Daddy dai ko tari baiyi ba, sai Uncle Muneer ne ya shiga mata magana cikin ɓacin rai akan shi da yasan abinda zatayi kenan da bai kawota ba. Yanda yake faɗa zai tabbatar maka ransa ya ɓaci, dan sosai take cima Daddy mutunci da masa gori. Amma ko tari bai mata ba balle aje ga batun ramawa. Su Amrah ne dai suka sake zuwa suka kira Lulu. Aiko sai gata a fusace. Ranta yafi na kullum ɓaci akan abinda Dada kema mahaifinta, atake na ƴan ƙwayar ya motsa ta rufe ido taima Dada tas har sai da ta gudu dan kanta saboda ganin buyagin Lulu fa ya haifi nata. Dan yanda Lulu ke ruwan bala’i zaka rantse bata taɓa sanin Dada ba a rayuwarta balle tuna qlaƙarsu. Uncle Muneer ransa ya kai matuƙar ɓaci, da yasan abinda Dada zatazo tayi a gidan mutane wlhy dabai kawota ba. Aiko ƙin kaita yay gidan Alh. Sulaiman da tace zata duba Tajuddeen shima.
Lulu kam da bayan fitarsu Daddy ya hauta da faɗa sai ta sakar masa kuka. Dole ya fice cikin ɓacin rai dan duk da yayi shiru kalaman Dada sun matuƙar zafar masa zuciya shima, amma bazai so Lulu ta cigaba da mata tsiwa ba matsayinta na kakarya. Ya danne ne kawai saboda dattako. Lulu na komawa ɗakinta kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Ɗauka tai kawai ta fashe masa da sabon kuka. Ƙirjin Smart yay wata irin harbawa. Dan dama kiran nashi ne bana Uncle Yousuf ba. Haka yake yi sai ya kirata da layin Uncle Yousuf ɗin yaƙi magana. Taita faman sallama yay shiru har sai ta gaji ta katse, wani lokacin tabi kiran wani lokacin ta share. Ko tabi baya ɗauka kuma sai dai ya bama Uncle Yousuf ɗin. Dama shi burinsa jin muryartane, wani lokacin ma yakanyi sa’ar jiyo AA na kuka musamman idan darene a Nigeria kasancewar AA ɗin ya dage da musu kukan dare yanzu. Da ance ɗaya tayi babu sauran zaman lafiya kuma sai anyi sallar asuba. Wani lokacin har Daddy fitowa yake ya ɗaukesa aita masa addu’a da rirriga amma yaron nan ko’a jikinsa. Mommy tayi, Ummita tayi Iya Tabawa tayi. Lulu kam sai dai tayi tagumi kawai yana kallonsu, wani lokacin ma ba’a tashinta sai idan kukan yayi nisa ne sosai ace ta tashi ta shayar da shi. Amma yaron nan ko’a jikinsa, wani lokacin ma dan zuciyar tsiya irin ta uban baya ko kamawa.
Kasa sauraren kukan nata Smart yayi ya yanke kiran, cikin tashin hankali da damuwa ya nufi Uncle Yousuf kamar zai fasa kuka ya ke faɗin, “Kuka takeyi, ka kira kaji mike damunta Please Uncle”.
Shima Uncle Yousuf hankalinsa ya tashi, dan yasan duk abinda ya saka Lulu kuka ba ƙarami bane. Wayar ya kira tare da saka Hans-free. Kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauka. Tambayoyi Uncle Yousuf ɗin ke mata cike da kulawa batare da ko jiran sun gaisa ba. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar masa. Smart ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanunsa da suka kaɗa sosai. Shi dai tunda ba wani abu ne ya sameta ba ai da sauƙi. Lallashinta sosai Uncle Yousuf yay, sannan ya mata faɗa da nasiha akan rashin kunyar da taima Dadan. Ya ce karta sake babu ƙyau hakan. Dada tamkar mahaifiya take a gareta. Ta bashi haƙuri da tabbatar masa bazata sake ba. Amma a ranta fa tasan ita da Dada fa ai haihata-haihata (🤣😂 ALLAH ya ƙyauta su Lulu an san daɗin ɗa🥱🚴👏).
Cikin tsokana Uncle Yousuf ke duban Smart yana faɗin, “Darun matar nan taka sai kai Aliyu, ni dama nasan wlhy bazata ƙyale Dada ba. Kuma duk a wajensu ta kwaso wannan masifar ai dan mudai a family namu babu mafaɗaci”.
Murmushi kawai Smart keyi, a ransa yana sake jinjina hali irin na Lulu. Yasan tabbas yaransa sun bani da masifa tunda shima dai ba raga masa ake ba. Wani lokacin idan tana faɗa har mamakin wai kanta baya ciwo yake yi. Tana da tsiwa sosai, ga shi sam babu tsoro a idanunta. Ita dai kawai zaman lafiyarka da ita kada ka shiga gonarta ne kawai……….✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button