Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 34

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣4️⃣

 

……..A ɓangaren Ummah tana shiga ɗakinta ta sake tsagewa da kuka, a haka ta hau neman layin Hajiya Naqiba.
“Na shiga Uku Aminiya Abban Salim ne ya mutu?”. Cewar Hajiya Naqiba a rikice jin Umma na ɓarza kuka.
“Ba garama mutuwar ba zan haƙura dole Aminiya. Ashe malamin nan yaudarata yake shima duk irin maƙudan kuɗin dana zube masa. Gonata ta gado fa na ɗaga na sayar na bashi kuɗin aikin nan amma ace wai duk a banza nayi, yau sai ga shegen yaron nan mai taurin ran tsiya a tsakkiya Turawa kamar zasu cinyesa dan soyayya. Wai wani ƙungiya na kwallo asinal yake ko uwarmi ne ma oho musu suka sayeshi da wani uban kuɗi da har yanzu ma zuciyata da ƙwaƙwalwa ta sun kasa haɗawa dai-dai, wai zai musu ƙwallo na shekara biyar. Shike nan na mutu Aminiya, duk wahalar da nake akan yaron nan dai abanza take cigaba da tafiya”.
“Tofa babbar magana, wai shi Hydar ɗin ne yakai wannan matakin na shiga ƙungiyar Arsenal? Shin ko shine ma ɗazun Maheer ke ban labari cikin zumuɗi wai wani matashi Smart ɗan Kano ya zama babban gwaska a duniya, yanzu hakama yana nan gidan Alhaji Sammani wai suna kallo ko ana nunashi”.
“Matsiyaci haihuwar asara shine. ALLAH ya tsinewa uwarsa ma bashi ba. Na tsani matar nan fiye da yanda na tsani mutuwata, duk irin wahala da kai-kawon da nake a kanta da faɗi tashi kullum abbanza suke tafiya. Narasa wace irin baƙar tambaya ke ga Hafsatu”
“Humm Aminiya kar kice haka, kin manta nasarar da kikaci ta tsahon shekaru yaron nan ko filin ball bai iya shiga, ga tsanar da Abban Salim yay masa. Sannan a yanzu haka fa akwai asirin dake jikinsa wanda ya gagara zama da matarsa waje ɗaya….”
“Na fara ji a raina asirin nan bai kama shegen yaron nan ba, matar tasa kawai ya kama dai kamar, kuma mayen yaƙi sakinta. Malam yana ɓoye mana ne kawai”.
“Tunda dai har ya kama matar tasa ai ya wadatar damu. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH yanzu ma bamu makara ba. Wajen Na-zuru zamu koma tunda dama shine yay masa wancan ƙullin goron na farko, irinsa zai sake mana ko ya shiga filin ya yanke jiki ya faɗi basai muga ta ƙafafa ba. Sannan kisa ranki a inuwa, wannan maƙudan kuɗi da kikaji ba nashi bane ba, haka naji Maheer nacewa da nake masa faɗan shi miyyasa bazai zo ya koya ƙwallon ba.”
“Kai dan ALLAH wai da gaske kike? To kudin na waye?”.
“Ni ban sani musu ba, kamar dai yace wai ko kungiyar daya bari ne ai da kuɗin, shi za’a yanka masa nasa albashinne.”
“Kai amma har na ɗan jin sanyi, shegiyar uwarsa sai muga ta hura hanci, ashema kuɗin na wasu ne shasha ɗan ya koma bawan turawa bata farga ba”.
Dariya suka kwashe da shi kamar suna kusa da juma….

Niko na ce, “Hummm!”.

★Sosai abinda Umma tayi ya tsayama Abba a rai, har ya shiga dogon nazari akanta. Sai dai baicema kowa komai akan hakan ba. Itama baice matan ba. Ya dai ɗauki ɗammarar saka ido a lamarinta domin tabbatar da abinda ransa ke raya masa…

★Ammah kam ko’a jikinta, dan ita zuwa yanzu lamarin Ummah bai wani damunta sosai. Face dagewar da tai da addu’a ita da zuri’arta domin kariya da ga sharrinta. Dan duk yanda Gwaggo Sa’adah taso ɗaukar mataki ta hanata, acewarta su jira sakamako na zuwa akan kowa…..

*_6 MONTH’S LATER_*

Abubuwa da yawa sun faru masu tafiya da nasarori da kalubale a cikin waɗan nan watanni da suka kasance kusan tara da haihuwar Lulu. Ƙalubalenta na farko mai kuma girman gaske shine shiga tsakaninta da mijinta uban ɗanta da akai ta hanyar sammu mai ƙarfi. Nasararta ta farko komawa islamiyya neman ilimin addini tuƙuru tare da maida hankali matuƙa duk da ta koma bakin aikinta. Sai wannan gaɓar ta kuma samu nasarar kafa ƙungiyar da take buri data samu tallafin ƙarfafa gwiwa da ga iyayenta da kakanta har ma da ƴan uwan haihuwar makaifiyarta. Nasara ta uku kafa business ɗinta data jima tana buri na turare, tana kawosu daga ƙasashe daban-daban, ana kiran ƙaton shagonta da suna *_LULU’s ƘAMSHI_*. Nasara ta huɗu ƙyaƙyƙyawan yaronta da kamaninsa ke ƙara fitowa dana mahaifinsa nata ƙara wayo gashi cikin ƙoshin lafiya da kuzarinsa. Alhamdullah kuma yana a cikin kariyar UBANGIJI shikam. Dan duk da irin hare-haren da su Umma suke kawo masa ALLAH ya kiyaye abinsa yaron nan ko gezau. A yanzu haka ya fara miƙewa ya ɗan dafa kujera alamar dai yana son taka ƙafa. Ana kaisa wajen Ammah ya yini abinsa, kasancewar yana shan koko kuma gashi baida damuwa akwai haƙuri yasa sai ya yini lafiya sannan a maidosa. Itama su Asma’u kanzo su yinin mata anan. Su aunty Bilkisu kansu kan zo suga AA da gasiheta lokaci-lokaci. Itama kuma tana zuwa gidajensu har ta yini. Can gidan ne dai bata iya zuwa. Dan kota gwada hakan baya yiwuwa. Wannan abu na cimata rai dan tana so da ƙaunar Ammah a ranta. Wannan soyayyar da ga ALLAH ce. Shiyyasa itama Ammahn kan leƙosu lokaci-lokaci musamman idan ance AA na mura haka ta haƙora. Sosai shaƙuwa ta shiga tsakaninta da dangin Smart. Dan hatta samarin su Mubarak sukan zo gareta a ɓoye batare da sanin iyayensu mata ba. Duk watan duniya kuɗi kan shigo account ɗinta da ga Aliyu, sannan akan kirata da number ƙasar England. Sai dai kota ɗaga ba’a magana, sai ita zata dinga hello-hello da ga ƙarshe a yanke kiran. Takan ji haushi tace bazata sake ɗagawa ba. Amma da an kira bata iya haƙuri sai ta ɗaga ɗin…

★A gidan su Smart kam nasarori da ƙalibalen suma dai basu tsallake su ba. Sai dai Alhmdllh a ɓangaren Ammah babu abinda zata cema UBANGIJI sai godiya. An tsaida Ranar auren Maryam da Ahmad. Yayinda ɗaukakar da ALLAH ya bama Smart ta sake fiddota a cikin ƴan uwa dama jama’ar gidan har da dangin Abbah. Smart ya dakatar da Abbah fita kasuwa duk watan duniya ya yanka masa albashi shi da Ammah a cikin albashinsa da ake biyasan duk sati-sati. Sannan Ahmad zai kawo kayan abinci bisa Umarnin sa.
Wannan abu na ƙara ɗaga hankalin Umma har ma da Mama. Sai dai banbancinsu ita mama kan balbale nata yaran da faɗa ne akan suma su san ciwon kansu su dinga ma mahaifinsu in ba hakaba smart zai ƙwace dukkan power ɗin su, sannan ita bata bin malamai, kishi ne dai irin na matan bahaushe da jin ƙyashin cigaban kishiya. Itakam Umma tsantsar hassada da baƙin ciki sunbi sun kanainaye mata zuciya da ruhi. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Duk ɗan abinda ta samu suna a yawon malamai da bokaye ita da Hajiya Naqiba aminiyarta. Aikin suke iya ƙarfinsu amma basu sake jin wani sabon abu ba bayan zaman Lulu gida. Ga malamin nata ya tabbatar mata akwai fa matsala idan aikin bai kama Smart ba shi. Dan su duka biyun akai musu ai akan su tsani juna. Wannan dalilin yasa take ta faman bibiyar al’amarin Smart dan taji shi ya wajensa yaya akan matar tasa amma ta kasa samun kowacce irin mafita. Ga lamarin Huwaila na caja mata kai. Dan ta girmi Maryam amma har yanzu babu tsayayye, saka auren Maryam kansa ya hargitsa mata lissafinta. Balle da taji cewar itama mai hannu da maiƙo zata aura. Wayyo ina wuta ta saka Ammah ne. Ta rasa wane irin sirri keda Ammah ɗin da dukkan ƴaƴanta suke auren ƴaƴan masu kuɗi. Yanzu dai abu biyu ta saka a gaba. Wato tarwatsa rayuwar Smart da rusa auren Maryam. Duk ta fige ta lalace a tsaye saboda saka wa kai musiba. Itace kullum faɗa da ƴaƴa akan su bata kuɗi, musamman ma Salim dake nuna mata shi fa ya gaji da wahalarta, mitake da kuɗi wai kamar wata ƴar caca..
Duk abinda take a yanzu idon Ammah ƙyam yake a kanta, dan haka ta dake dagewa da addu’oi da sadaka.. Tare da kiyaye duk wani abinda Umma zata basu koda abincin gidanne yanzu ranar girkin Umma sai suka daina ci, miya Ammah ke musu mai yawa tasa a freight, duk ranar da Umma tai girki sai tayi musu abinci a a ɗaki suci, na Ummar a fitar waje aba mutane cikin hikima.. A tunanin Ammah Abbah bai san mike faruwa bane, sai dai idonsa na akan komai yana dai biye yaga iya gudun ruwan kowannensu musamman ma Ummah..

________★

A garko family kam abubuwane keta ƙara tsamari. Abu na farko shine Baba Garko dai tunda ya tsallake bayan kama Sulaiman bai sake dawowa ba, sai labarin a washe garin da Dada taje gidan su Lulu suke jin cewar an ɗaura masa aure matar ma ta bisa. Ranar sunga abinda ya girmesu a wajen Dada. Dan zaman ƴan bori tayi a gaban surukai ta saki ƙaƙƙarfan ihun da ya nema girgiza ginin gidan. Ba ita ba su kansu yaran hankalinsu ya tashi, a ganinsu mi mahaifin nasu zaiyi da wani aure a shekarunsa haka, kuma abin mamaki wai ma budurwa ya aura sa’ar ƴaƴan cikinsu. Matansu kam dai wannan al’amari yay musu daɗi, sai dai suna ƙoƙarin dannewa a gaban mazan nasu.. sai an koma gefe asha gulma da dariyar Dada..

Sai da Baba Garko ya kwashe watanni kusan shida da amaryarsa suna yawan hutawa a ƙasashe sannan suka dawo Nigeria da cikinta da ya fito kowa na gani. Ƙyaƙyƙyawar mace ƴar gaye mai tarin ilimin addini dana boko. Sannan gata yarinya ƙarama, dan bazata wuce sa’ar Lulu ba ma. Da gani dai kasan kuɗi ta gani ta shige, duk da dai Baba Garko ba baya ba wajen ƙyau amma tsufa ai ya ƙwace komai sai godiyar ALLAH kawai. Wannan ciki ya saka ƴaƴansa jin matuƙar kunya, sai dai babu damar yin magana ya maka wankin babban bargo, dan shi ko’a jikinsa. Kuma yace dole su girmama masa mata. Suna son sake bashi haƙuri akan mahaifiyarsu suna jin tsoro, dole sukai gum da bakunansu.
Washe gari Daddy da Uncle Yousuf sukaje gaishesa suma da masa murnar aure anan ne su dai suka fidda kunya da tsoron suka roƙesa akan yay haƙuri itama Dada ta dawo. Ai an mata gargaɗi. Shima Alh. Sulaiman ai masa afuwa dan ALLAH ya dawo cikin iyalinsa. Bai tanka musu ba dai, sai sakawa da yay Uncle Yousuf ya kira masa Smart a waya. Yako kira masa shi suka gaisa. Yana jin ƙaunar yaron matuƙa yanda yake bashi girma. Yay masa faɗa akan rashin kiransa su gaisa, tare da tayasa murnar cigaban rayuwa da ya samu. Yace shi ai bai sani ba sai kwanan da ya gansa ana hira da shi ya shiga mamakin kamannin har yay kiran Daddy shine fa yake tabbatar masa da shi ɗinne. Haƙuri Smart ya bashi cikin girmamawa da tabbatar masa zai gyara insha ALLAH. Cikin gamsuwa Baba Garko ya sake saka masa albarka. Sai kuma ya tambayesa yaushe ne zai zo ya ɗauki iyalinsa. Ɗan jimm Smart yay na wani ɗan lokaci, kafin ya firzar da numfashi yana jan ajiyar zuciya. Cikin tausasa harshe ya ce, “Baba yanzu ni lokacin nawa ne sai a hankali, dan gashi ana tsaka da fara buga wasan premier link ne. Sannan kuma itama bana son a takura mata har sai idan itace da kanta ta yarda zata nemeni nake ganin hakan zai fi zama masalaha, itama bazataga an takura mata ba kamar farko”. Murmushi irin na manya Baba yayi. Tare da cewa, “Shike nan shawaranka yayi sosai”. Daga haka suka ajiye wannan maganar Smart ya koma bashi hakuri shima akan maida Dada da sakin Alh. Sulaiman. Acewarsa shi ya yafe komai ya wuce a tari gaba……..✍️
 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button