Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 38

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣8️⃣

 

……..Tattaɓa shi ya shigayi idanunsa na cika da kwalla, sai kuma ya rankwafa da ƙyau daga zaunen da ya kai ya manna masa kiss a goshinsa da kumatu duk biyu. Kamar AA yasan mi ake ya wani juya abinsa ya kwanto a hannunsa. Murmushi yay mai kama da ƴar dariya, sai shima kawai ya kai kishin giɗe ya rungumesa a jikinsa sosai yana sakin ajiyar zuciya masu nauyi da shafa lallausar sumar kan yaron da Lulu ta hana a aske, sai gyaran fuska ake masa. Yaja kusan mintuna biyu a haka kafin ya ɗago idanunsa ya dubi Lulu da ke satar kallonsu. Kanta tai saurin maidawa gefe cikin taɓe fuska. A karo na farko yay magana cikin ɗan sakin murmushi. “Irin wannan bazata haka Madam?”.
Mikewa tai tamkar bata jisa ba zuwa inda akwatin kayansu yake, dan ɗaya ta ɗakko jal ita da AA, kayansa ma sunfi yawa dan nata basu wuci kala uku ba sai kayan barci. Sai da ta zuge zip ɗin tana ƙoƙarin ɗaukar kaya sannan ta bashi amsa da “Sai yanzu kasan da ni?”. Bata jira amsarsa ba ta wuce closed ɗinsa hannunta riƙe da kayan data ɗauka taja labulen da aka sa a wajen wai dan karya kalleta.
Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana mai lumshe idanu, ya dai fahimci kishi ake da AA ɗinsa kenan. Mintuna kaɗan ta fito sanye da wando da riga marasa nauyi, sai dai yanda suka bi jikinta da fidda mata surarta fes ya saka zuciyar ƴan maza motsawa. Ga Lulu hakan normal ne, ita batayine dan wani birge miji ba, tun fil azal wannan shine dressing nata. Batare data kallesa ba ta wuce gaban mirror ɗinsa dake cike da turarruka da mayukan gyaran gashi sai abinda ba’a rasa ba. Gashinta taƙe ƙoƙarin tifkewa. Kwanciya ya gyarama AA tare da miƙewa, dai-dai tana tattare gashin cikin hannunta bayan ta zare ribbon ɗin data ɗaurosa da shi sukai ido huɗu da shi a bayanta. Yay wani tsaiwar ƙasaita irin na isassun maza yana kallonta da mayatattun idanun nan nasa. Sosai ta ƙara jin ƙirjinta ya motsa, tai azamar janye idanunta tamkar bata ganshi ba. Idanun ya rufe ya buɗe a lokaci guda yana ɗan ƙara matsawa jikinta daf ya mata runfa, sai kuma ya ƙarasa rungumeta a hankali tare da ɗaura kansa a kafaɗarta. A tare suke ja numfashi da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Yanda yake wani bin wuyanta da shinshina idanunsa a lumshe ya sata jin tana neman zubewa a ƙasa, saurin riƙo hannayensa duk biyu da ke zagaye da ita a saman cikinta tai, hakan ya sakashi sake ƙanƙameta tsam-tsam kamar za’a ƙwace masa ita ya wani busa mata numfashi a cikin kunne….
Harga ALLAH bazata iya ɗaukar wannan salon nasa ba, dan haka tai ƙoƙarin jan jikinta da saurin faɗin, “Wai nikam minene haka?” cikin rawar murya data lips. A cikin kunnenta ya raɗa mata “Saƙon barka da zuwa mana. Haka ya kamata ki tarbi mijinki _My Final Choice_”.
Kanta ta matsar gefe tana taune lip ɗinta na ƙasa, cike da basarwar nan tata cikin son janye jikinta ta ce, “Kama nemo Final Choice ɗin naka bana son iyayi”.
Sake ruƙota yay sosai yana murmushi. Idanunsa ƙyar a kanta ta cikin mirror ɗin ya ce, “Kowa yasan na nemo abita ai tuni. Dan duniya duk ta san Mawaddatan’warahmah ce Heart controller ɗin Aliyu Hydar Mika’il Mawashi”.
“Kai dai ka sani”.
Ta faɗa tana janye jikinta a nashi. Bai hanata ba ya saketa tare da harɗe hannayensa a ƙirji. Kallonsa tayi ta ɗauke kai da rusinar da idanunta. A hankali ta ce, “Malam matsamin na wuce”. Dan ya tsare mata ko ina. Bai matsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta sama da ƙasa ba. Kallo irin mai haka mutum sukuni ɗin nan da ji iska ma na maka wahalar shaƙa. Ƙoƙarin raɓasa tayi ya tare, ta sake komawa ɗayan ɓangaren, nan ma ya tare, ta koma tsakkiya nan ma ya tare. Sai kawai ta zabga masa harara tana tunzura baki. Hannayensa ya warware da ƴar murmushi har sannan a fuskarsa ya ɗan matsota, baya ta matsa ta manne da mirrorn. Shima sai ya dafe hannayensa a mirror ɗin ta gefe da gefenta ta koma tsakkiyarsa, ya ranƙwafo sosai yana busa mata numfashinsa a fuska. Ga son su haɗa idanu da yake faman yi. Cikin daburcewa ta furta “Aliyu!”.
“Uhmyim Mawaddat!”.
Ya amsa mata kafin ma ta gama rufe bakinta, sai taji ma ta sake daburcewa dan yanda yay kiran sunan nata da amsawa acan ƙasan maƙoshi da busa mata numfashin yasa ƙafafunta ma suka fara rawar son kasa ɗaukarta. Ɗago idanunta da suka tara ƙwallar da ita kanta bata san dalili ba tayi, hakan ya bashi damar ɗaura lips ɗinsa akan nata kamar dama abinda yay target kenan. Kafin tai wani yunƙuri ya tallafi kanta da ƙyau da hannun damarsa, ɗaya hannun kuma ya saukesa akan bayanta. Sam bata da wani sauran ƙarfin yin wani yunƙuri, dole ta haƙura dan tasan wani buyaginta bazai sa ya fasa ba in dai shi ne, sannan ita kanta kawai ƙarfin hali ne tana buƙatar mijinta. Jin tsaiwar na neman gagararsu yay ƙoƙarin tattarota zai ɗaga. Da sauri ta tattaro nata ɗan hankalin waje guda itama ta kai masa ɗan duka a gefen cikinsa….
“Ouch!”.
Ya faɗa yana sakinta yana dafe wajen. Sai kuma hankalinta ya tashi ganin yanda ya duƙe, cikin rikicewa ta ruƙo hannunsa dake riƙe da inda ta bugesan duk da dai ita tasan kaɗan ta masa. Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Please kayi haƙuri ALLAH ban san zai maka zafi ba, wayyo ni”.
Sake langaɓewa Smart yay kamar gaske, ta kamashi ta jinginar da mirror ɗin tare da ɗan daga rigarsa tasa hannunta a wajen tana murza masa a hankali. Sake langaɓe murya yay yana faɗin, “Wayyo zafi Ammah kizo ta targaɗa miki ni”. Harga ALLAH Lulu ta ɗauka da gaske yake, dan haka ta sake ruɗewa har idanunta na tara ƙwalla, duk yanda yaso riƙe dariyarsa hakan na neman gagara, dole ya saketa dai-dai tana kwantar masa da kai a kafaɗarta.
Galala tai tana kallonsa ga hawayen da suka cika mata ido na neman fara zubowa. Cikin son danne dariyar da ke ƙara tunƙuro masa ya ce, “Dama haka kika damu da Aliyu? Madam!”.
Hararesa ta ballara masa da raɓawa ta gefensa ta wuce tana jan ƙafa da ƙyar dan ji take tamkar zata zube ƙasa ma. Shima sai yaja nasa jikin yana murmushi zuwa ƴar ƙyaƙyƙyawar kujerar dake gefe da ɗan table mara tudu dai-dai ita da zaka iya miƙe ƙafa a kansa ya zauna yana sauke numfashi da ƙaramar dariya. Sai da ya bada kusan mintuna biyu hankalinsa ya dawo jikinsa sannan ya tashi zaune da ga kwantar da bayansa da yay ya buɗe idanunsa a kanta. Tama kwance kusa da AA ne idanunta a lumshe ta wani dunƙule jikinta waje guda kamar wata baby. Ƙaramin murmushi ya saki da miƙewa ya fara zame kayan jikinsa da faɗin, “Ya kamata ki fara cin abinci kafin ki kwanta barcin ko”.
Shiru kamar bazata amsa masa ba, sai can a takaice ta ce, “Ba buƙata”.
Bai sake cemata komai ba ya nufi bathroom. Da kallo ta bisa, sai kuma rashin sake cewarsa koman ya bata haushi ta wani tura baki da hararar bayansa tana murguɗawa ta maida idanunta ta rufe. Ya ɗan jima kafin ya fito ɗaure da towel yana goge jiki da ƙarami. Kai tsaye wayarsa da ke ring ya nufa yana ɗan yamutsa fuska da kallon agogo. Bai niyyar ɗauka ba, sai dai ganin Ahmad ne ya sashi ɗagawar tare da ɗaukar bluetooth ya manna a kunnensa ya cigaba da abinda ke gabansa da alama Ahmad ɗin yake saurare.
“Ka kira dai kayi gulma ɗan sa ido”.
Dariya Ahmad ɗin ya kwashe da shi da ga can. Ya ce, “Ai kai dama ba’a maka abin arziƙi. Ni yarona na kira naji yaya yazo bai jigataba dai ko?”.
“Ga shi nan na samesa yana kwasar barci dan sun shigo gidan na fita. Yaya kun gama da mutanen?”.
“Har yanzu dai ana cuɗawa, naga sun ɗauki burin duniya sun ɗaurama wajen. Amma dai za’a dai-daita in sha ALLAH dan naga da Yaya yace zamu haƙura kuma kamar sun damu.”
“Oh kuma dai?”.
“Ai kasan dama irin wannan matsalar ba daga masu kayan bane masu sayarwar ne”.
A hankali ya ɗan furzar da iska da faɗin, “To duk yanda kukai dai?. Ya batun wancan aiki? Yaushe ne kuma shigowar taka?”
“Ai maybe ma na fasa, dan business ɗin bai faɗa ba har yanzu, kasan abinda ma lura da shi komai suna fara yinsa ne a tsare kafin su sakeshi a kasuwa, amma dai shi guy ɗin nan ya tabbatar min zai haɗani da ogan nasu saboda nace masa ni dila ne, sannan pharmacy ɗin nan ya kamata aikinmu ya fara ta kansu dan na sake zuwa da takardar nan still sun saida min jiya. Kaga tabbacin maganarka kenan ta fito”
“Hummm aina faɗa maka dama. Sai dai inaga kafin hakan ya kamata musan mai pharmacy ɗin. Sai Companyn da yafi kawo musu kaya. Dan ina son mu fara da mutuminka ne”
“Uhm wannan ma tunani ne mai ƙyau, sai dai kuma kamar abin zai mana wahala nake ga. Kasan fa kai ka fini dabaru ta irin waɗan nan fannin”.
Murmushi Smart yayi yana ɗan lumshe ido. Cikin ɗan furzar da iska yace, “Kaima zaka iya Ahmad. Ka nutsu na maka bayani, yaro zamu samar da zai nema aiki a wajen, ta silar yaron ma zamu samu abinda bamu hasaso ba ma. Plan a kenan, idan wannan zai ja mana lokaci plan b muja yaro ɗaya dake pharmacy ɗin a jiki, ta hanyar masa alkairi kasan dai yanda mutanenmu suka ɓaci da wannan karɓar na goran, a cikin biyun nan zamu dace da ɗaya”.
“Yess boss na fahimce ka, kuma tabbas wannan dabaran yayi, shiyyasa nake sonka”.
“Ɗan iska waye boss ɗin naka?”.
Dariya Ahmad ya sanya da faɗin, “Kai mana. Zanyi ƙoƙarin nan daga nan zuwa next week, Dan Cameroon ma nake son zuwa kawo shanun nan dai. Ya kamata ka shigo ayi harkar nan da kai ALLAH, dan na hango za’a samu alkairi a ciki.”
“ALLAH mutumina! Kaifa nasan baka wasa dama da harkar ƴan canji. Yanzu yaya za’ayi?”.
Cikin dariya ya ce, “Masheranci, kaima naga ai bawasan kake da su ba. Muyi magana kawai idan ka samu time, yanzu karna shiga lokacin Madam tana amaryarta. A huta lafiya tsohon ango”.
Kafin Smart yace wani abu ya yanke kiran. Ya ɗan lumshe ido da girgiza kansa yana furzar da iska. Yana ƙoƙarin cire bluetooth ɗin idonsa ya sauka akan Lulu ta mirror da ke kallonsa………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button