Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 37

Sponsored Links

 

 

 

Ababa na dawowa dakin ya haska fitila yaga benazir zaune ta sankare da alama Bata hayyacinta ta zaunce ne a take da rasuwar sumayyahn.

Dayan gefen ya haska baiga Annensu ba,
Kokarin haska dakin yafara koina babu alaman Annen
Yana kokarin juyowa yaga kaman sumayyah ta motsa Amma Dayake tashin hankalinsa a yanzu kada Annen tabi hanya yasa ya fice dakin da sauri Yana kwala Kiran sunanta a rikice.

Hande da jaririyar ta isheta da kuka Jin ihun Ababan Yana Kiran Anne yasata fitowa daga daki a rikice rungume da ‘yar acikin zanin uwarta.

Hankali tashe ya sanar da hande Annensu ta bi daji a Daren,

Hande cikin firgici tace

“Mun shiga uku da wannan qaddara,
Daga mutuwa sai hauka ga Kuma jinjirar ‘ya anbarni da ita a hannu wayyo Allah mun shiga uku.

Dakin su Annen ta fada ta fizgo Benazir dake riqe gam da hannun sumayyah suna fitowa tsakar gidan ta dungura mata ‘yar tana fasa kukan sun shiga uku sun lalace ‘danta ya hada iri da Anne me jinin Kaddara baqa iri iri.

Qanqame ‘yar benazir tayi kaman sumayyahnta ce ta qanqame
Ahankali take dawowa hayyacinta tafara Jin sama sama hande da Ababa na ihun Anne tabi daji haukanta ya tashi.

Fizgo tinaninta da hankalinta tayi da qyar tareda shiga girmamammen tashin hankali da masifar rayuwa.

Daqyar taji qafafuwanta a jikinta ta iya motsawa tafara jefa kafa koina ta samu ba nutsuwa ta nufi hanyar bangaren dabbobi Ababan dataga shi da hande sun nufa suna Kiran sunan Annen cikin mamakin ganinta zaune cikin dabbobi tana Kuka kaman ranta zai fita.

Benazir na hango Annen ta qaraso da tsananin gudu ta fada jikinta da babyn a hannu suka fasa Wani tsimamman kukan Daya taba zuciyar hande a Karo na farko.

Kuka sukeyi sosai hande da Ababa na kansu hande na fadan baa yiwa Mamaci Kuka,

Shi kuwa Ababa kokarin Ciro ‘yar daga tsakiyarsu yakeyi kada a kashe masa ita
Ta Daya bangaren baya hayyacinsa Shima kwata kwata sbd rasuwar sumayyahn Neman juyar masa da Kai takeyi,

Kakkarwa jikinsa yakeyi Yana hada gumi Mai tsananin yawa.

Rikosa hande tayi tana kokarin zaunar dashi sukaji motsi can cikin gidan da sauri hande ta sakesa Dan dubowa tana shigowa tsakar gidan bataga kowa ba.

Faduwa gabanta yayi ta waiwaya ta Kalli dakin su benazir saidai bazata iya leqawa ba tayi Ido biyu da gawa Dan haka take tsoro ya Dan shigeta ta juya zata koma Ababa ya iso Yana Neman zubewa qasa sbd jiri da bushewar yawun tashin hankali.

Dakin ta sake kalla tace masa

“A dakin Nan fa Akai motsin dazu fa,
Kodai Bata rasu bane sumayy….Bata qarasa ba Ababa yayi Wani irin zabura ya fada dakin sbd tinawa da dazu kaman yaga motsawanta saidai Yana fadawa ya haska Kansa ya juye take sbd ganin wayam babu sumayyah a dakin koma me Rai koma gawarta.

Hande data biyo bayansa tana ganin babu gawar ta saki Wani gigitaccen salatin dayafi kama da ihun Daya saka Anne da benazir tasowa suka fado dakin gigice tinanin sumayyah ta tashi.

Ganin ba sumayyahn yasa benazir rarraba Ido a dakin tana Neman sake zaucewa.

Anne kuwa fadawa tayi inda sumayyahn take kwance tana lalubawa ko idonta ne Basa ganin gawan Sumayyah hannuwanta suji mata.

 

Sabon tashin hankalin da Basu saka masa rana bane suka samu kansu a ciki na rashin ganin sumayyah ace ta bace bat idan da Rai idan gawar.

Ababa da Kansa ya gama juyewa tsaf lokacin barin kayan gidan yafara yana Neman haukacewa ya dauko bindigarsa ya fito idanuwansa jajir baya ganin ko gabansa ya fita yafara duba zagayen da kewayan gidan da anguwar ko zai San wane balain da masifar ne ya samu Kansa,

Shin guduwa sumayyah tayi itama kokuwa sace gawarta Akai?
To waye yasan da ita da halinda ake ciki da har zai shigo gidan ya sace gawarta.

Benazir da Anne kuwa zuwa lokacin Kuka ma Wani gata da arziki ne dayafi karfinsu,
Kukan sukeson Yi Amma babu hawayen idanuwan sun bushe bayan kukan babyn Dayake cika gidan babu me iya ko motsi sbd girma da tashin hankalin lamarin.

A inda benazir take zaune cikin duhun dakin rungume da babyn da har lokacin Bata samu an mata wanka ba,
Qamshin da hancinta ya shaqar mata ne ya sakata miqewa a zabure tana tabbatarda Alh Bilal ya shigo gidan.

Fitowa tayi daga dakin Anne ma ta biyota kaman zariya suka fara ware idanuwa a tsakar gidan cikin duhu Amma Basu ga kowa ko komai ba Dan haka Suka koma bakin kofar dakin suka rakube suna jiran dawowar Ababa da Koda gawar sumayyahn ne.

Shiru shiru babu Ababa babu labarin dawowarsa Yana can yabi hanya Baya hayyacinsa gurin Neman sumayyah ko gawarta,
Tin yana yawon dubawa cikin anguwar harya fice anguwar Bai saniba kaman tsohon mahaukaci haka yakoma acikin tsakar Daren.

Hande dataji jaririyar ta kasa Dena Kuka Kuma makotan kusa zasu iya Jin kukan su San da haihuwar dole ta fito ta karbi yar ta shiga dakinta da ita acan tayo mata wanka ta saka mata kayan da Ababa ya siyo na haihuwar ta fito ta miqawa benazir ita ta sake komawa dakinta sbd sanyi illa zai mata da tsufanta.

Benazir da Anne kuwa suna tsakar gidan Basu motsaba ko Nan da can suna jiran dawowar Ababa zuciyoyinsu na Wani irin tsallan tashin hankali mara misali.

Babyn a cikin hijabi benazir ta sakata ta dunkule sbd sanyi tin tana Kuka har ta Dena tayi shiru tana baccinta da jarirai.

A rayuwarsu Basu taba shiga tashin hankali irin Daren ba,
Yanda suka ga Rana haka sukaga Daren gurin Jiran tsammanin tashin hankali,

Kiran Asuba Akai aka gama har Akai sallah aka fito babu labarin Ababa Suma babu alaman zasu motsa har gari yayi haske tukuna Benazir taja Anne da babyn a dayan hannunta sukaje sukai sallah suka sake fitowa babu me iya ko tsayuwa a cikinsu sbd fargaba da tashin hankalin.

Karfe 6 na safe Ababa ya shigo gidan ko Gani bayayi Yana kawowa tsakar gidan ya yanke jiki ya Fadi.

Hande da gudu tayi Kansa tana fashewa da kuka

Benazir da Bata gansa da sumayyah ba itama sarewa qafafunta sukai ta zube a gurin durqushe tana Neman Kuka ya taho mata ko zata samu sassaucin Abinda take ji a cikin kirjinta.

Anne kuwa a wannan lokacin Ido kawai ta zubawa benazir tana kasa motsawa bare iyayin kukan itama.

 

*********A Kaantes ma a tsaye suka kwana kan ummensu Bilal data rikice gabaki Daya sbd zuciyarta Datake tsinkewa tana shiga tsoro da firgici akan ‘danta.

Duka wayoyin Bilal din Basa shiga hakama ga ummen asthma ya tashi gabaki Daya kaman wadda ta jima tana jinya kiransa DD keyi Yana qarawa Amma Sam wayoyin Basa shiga.

Hakan yasaka dole DD a ranar ya kwana cikin KAANTES Bai tafi gidansa ba,
Dad kaante ma hankalinsa yayi mummunan tashi shikuma dayaga baa samun Bilal din Kuma har tsakiyar dare har Asuba har safiya Bai dawoba Dan haka Suka Yanke shawarar Neman Ababa.

Zazzaune suke jigum jigum kaman gidan makoki a palon dd babba suna jiran dd babban ya kira Ababa Wanda shikuma aketa kira baya dauka.

Daga DD har dad kaante dashi Kansa dd babba harma ummensa zuwa lokacin hakurinsu yafara qarewa suna buqatan Jin komai gameda haihuwar da zuwan Bilal din dama Asibitin da suke.

Kokarin sake saka Kiran dd babba yayi daidai Nan wayar dad kaante tayi ringing cikin zaquwa ya daga Kiran ganin number sbd ko Bilal dinne Dan haka kawai wannan Karan suke Jin yanayi mara Dadi akan lamarin nasa.

A kunnensa ya Kara wayar tareda cewa hello da sallama.

Wani bayani aka fara Koro masa Daya sakasa yin shiru Yana kasa tanka kalma ko Daya sbd jinsa Daya fara daukewa kafin ganinsa.

Subucewa wayar hannunsa tayi yafara kokarin Kai hannunsa kirjinsa ya Dafe zuciyarsa Amma Bai karasa Kai hannunba ya Yanke jiki ya Fadi

Abbakar da DD sukai Kansa shi Kansa dd babba zuwa lokacin gab yake da samun attack Dan haka da sauri Abbakar ya dauki wayar dad kaante din ya miqawa Dd babba Amma ya girgiza masa alaman ya amsa wayar.

Cikin karfin hali da jarumta Abbakar ya gama sauraron bayanin da jamian tsaron suka gama jerowa ya kashe wayar zufa na tsinke masa sharkaf tareda tsananin tausayi da jimama harma da tashin hankali Amma Kuma ba dalilin boye zancen tinda dole aji,

Sauke Kansa yayi cikin raunin murya da tsananin bayyanarda damuwa yace

“Sir Bilal ne ya samu hadari motarsa ta Kone kurmus,Ansamu konanniyar gawarsa a m…..

Bai qarasa ba suka ji Wani irin Kukan Umme Daya saka kaantes din dauka tsit baka Jin motsin komai.

Mum Khadija ce matar qanin dad kaante dasuka iso gurin tare ta riqota jikinta na daukan rawa itama da mummunan labari tashin hankalin da babu wanda ya saka masa rana.

DD kuwa kasa gasgata Abinda aka fada din yayi sbd yanda jikinsa yake wata irin rawa idanuwansa dake farare masu tsananin kwarjini take sukai jajir ya fice palon da sauri ko gabansa baya Gani ya fito Ya nufi motarsa Naseer Dayake shigowa Yana hangosa ya taho da sauri ya Bude masa motar Bai tsaya cewa komai ba yace su nufi hanyar barin gari inda accident din ya afku.

Umme kuwa Wani irin Kuka takeyi Dayake tayarda tsikar jikin Masu jinta
Dad kuwa tini Akai part dinsa dashi sbd likitocin da aka kirawo har biyu da zasu dubasa Dan take numfashinsa ya tsaya.

Dd babba ma zaune yake Amma duk ilahirin hannuwansa da kafafunsa rawa sukeyi,
Zuciyarta tayi nauyi baya iya motsawa kowane lokaci attack zai iya samu Dan haka Shima take akai ciki dashi Dan jiran likita.

Zeenah dake Kuka sosai da mum Khadija harma da wasu daga masu aikin gidan suka kama Umme Akai ciki da ita,
Bata taba saka ran mutuwar danta ce ta sanyashi fita yabar gida ba da bazata bari ya bar ko kofar part dinta ba,
Irin Kukan datakeyi ne yasa mum Khadija fashewa da kukan tausayinta sbd kowa ya sheda soyayyar dakewa danta wadda ya kasa samu gurin kowa daga familynsa.

 

*****Koda DD ya Isa Shima Saida ambulance tazo ta daukesa daga gurin da hadarin ya faru sbd gawar Ta Kone kurmus ta yanda baa ganeta motarce kawai ake iya Ganewa itama sbd kafin konewar da alama ya daki Wani abin ne lambar motar ta fita harma da baya motar Shima ya balle ya fita.

Hakan yasa Akai saurin Ganewa aka kirasu sbd matsayinsu.

Rasuwar Bilal kaante a cikin Bata rufa awa biyu ba labarin ya bazu koina
Aka fara kokarin saka lokacin janaiza, manyan mutane kuwa tini suka fara kira da Kuma fara Siyan tickets na zuwa gaisuwa da janaiza.

*****A lokacinda labarin rasuwar ya shiga kunnan Ababa a lokaci Daya shi da benazir wannan Karan suka Yanke jiki suka fadi sbd sani da tabbacin Data Basu na cewan Bilal ne ya dauke sumayyah.

Anne da zuciyarta ta qyame kyam a tsakanin Daren jiya zuwa safiyar itace ta zubawa benazir ruwa ta farfado itama tata zuciyar na qamewa tana tashi daga tsoka.

Ababa kuwa Yana farfadowa ya sake yanke jiki ya Fadi sbd ta tabbata sumayyah da Bilal sun mutu sun bar duniya.
38👇👇👇👇👇👇
##MAMUH#
#BENAZIR
#ABABA
#AMNAH
#DD KAANTE
#MARRIAGE/LOVE/ROMANCE

Leave a Reply

Back to top button