Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 16

Sponsored Links

Volume:16 Briden Monster
D’agota yayi yana kallon yadda jikinta ya mutu likis,”kina son na daina?” Sharrr hawaye ya zubo mata, domin abin da Malik yake da yatsunta tunda tazo duniya babu wanda ya taɓa mata haka, dakyar ta ja shashekar kuka tare da zare hannunta, ta ja dakyar ta koma kuryan gadon. Ta haɗe kai da gwiwa. Shi kan mamaki take bashi, komawa kekenshi yayi ya bar dakin, stiret dakinshi ya wuce, bai tsaya a ko ina ba, sai ban daki, ya sauka akan kekenshi, ya cire wayarshi ya cilla kan keken, jan wani igiya yayi rufa me dumi ya shiga zuba mishi kai.
Cizon fatar bakinshi yayi ya sakarwa kanshi ruwan, yana zuba kamar me. Amma babu wani cigaba, kashe me dumi yayi ya sakarwa kanshi na sanyi, amma babu wani abu, dole haka ya fito ya kure sanyin Ac ya koma yana me cire kayanshi. Dan janta da yayi a jiki ya saka shi jin wani irin dumi yana ratsa shi, shiga cikin closed Dinshi, side din Jallabiya ya bude, ya ciro wani Morocco jallabiya, ya saka sannan ya fito. Rage karfin ac din yayi ya koma gadon shi ya kwanta.
Kiran Elbashir yayi, yana dauka ya ce masa.”Ya gaya maka inda kudina yake?” “A’a bai gaya min ba, ina fatar da ya gaya min.”
“Tsoronshi kake ji ne, da ba zai gaya maka inda kudina yake ba?” Kamar ya rusa ihu ya ce mishi. “Malik zai faɗa idan baka yarda ba, zan zo na kai ka sai ka ji.” Duk da ba wani magana me zafi ya faɗa ba, amma kuma kwarai Malik yaji haushin kalaman Malik. “Baka da hankali be zaka gaya min magana?” “I’m sorry Malik..” “sorry for yourself! Idan ka sake na hadu da shi, sai dai Uwarshi ya haifi wani!”
“Kayi hakuri!” Katse wayar yayi yana huci.

Kwanciyar shi yayi, yana duba wayar. A hankali barci yayi gaba da shi. Itama Zeeno barci ta sha, tana farkawa wanka tayi da alwala ta gabatar da sallah Azhar, tana idarwa ta duba a cikin kayanta, ta saka riga da wando, sai hula da top har gwiwarta. Gyara fuska tayi ta saka kwalli a idanunta. Ta fito falo babu kowa can tsakiyar falon ta je ta zauna tana me. Fitowa me girki yayi ya gaishe ta.
“Ma, ina ta jiran ki fito baki fito ba, me za a girka?” *Yau muna da baki!* Maganar Malik ya fado mata. “Ayi fried rice and veggies chicken. Sai abin da bLota a rasa ba.”
Gyada kai yayi yana faɗin. “Ok Ma” ya juya zai tafi ta ce mishi. “Ko zaka yi da wani abin sha?”
“Ok Ma!”
Kwanciyarta tayi tana sauke ajiyar zuciya, Malik ya shigo falon yana kallota, wani hade rai tayi tana wani dauke kai. Yana zuba ya kunna tv yana kallon labarai. Wayar shi tayi kara. “Ok ku shigo!” Ya faɗa yana kallonta, sai wani cika take tana batsewa, dariya yayi a kasan ranshi. Allah ya gani shi ba matashi bane balle ya ce zai iya rike kanshi, shi dattijo ne shi yasa bai sake ya lalata tsufanshi tun daga yarantar shi ba. Tana zaune a wurin aka bude mishi kofa, yan mata da sama ne. Suka fara shigowa da kayan. Suna dubawa a falon har izuwa gaban Zeeno.

Kafin wata gogaggiyar mace ta shigo, tana murmushi. “Barka da hutawa Mayor!” “Barka dai Madam Zakiya!” Murmushi tayi ta kalli Zeeno ta ce mata. “Amaryanmu!” Yake Zeeno tayi, tana satar kallon Malik. Bata san shi ita ma yake kallo ba, ko da ta ɗan waiwaya suka yi idanu biyu da shi kauda kanta tayi. Cike take da lots of curious. Yadda yake wani abu ita kan tsoro yake bata. Shafa kasumbarshi yayi yana mata wani irin kallo, da sauri ta dauke kai. “Zakiya ya kwana biyu?”
“Alhamdulillahi! Na gode da choose mall din mu” “ita zaki godewa!” Ya faɗa yana kallon Zeeno, yake tayi ta ce. “A’a ba sai ta gode min ba” sai da suka gama bude kayan sannan ta ce mata. “Ma ko zaki duba gayan?” “Yanzu wadannan kayan na meye?”
“Zamu yi baki an jima ne yasa aka kawo kayan da zaki saka.” Kallon shi take baki sake. “Ma zamu iya shiga ki sauya kayan.” Haka ta mike kamar doluwa ta bi yan matan, ta shiga saka kayan tana fitowa, yana zab’a. Sai da taji kafarta ya fara mata ciwo ta saka kayan karshe, wani Iran gown ne me had’e da hijab yaji stones, kin fitowa tayi ta zauna abinta a dakin tana matsa kafarta kasancewar ta saka hill ne a kayan. Tana zaune ya shigo yana kallonta. “Kin yi kyau! Ashe yar kwaila ta wuce a kira ta da kwaila Masha Allah. Madara kenan!”
Da sauri ta kare kirjinta, tana faɗin. “Bana son haka billahi!” Murmushi yayi ya matsa gabanta. “Kin san me? Wata rana da kanki zaki bini na sha ni kuma nayi ta ja miki class.” Kamar ya fasa kuka ta kare kirjinta. “Ni bana so!” Ta faɗa tana kare kirjinta. “Me kike so nayi?” Share shi tayi tana faɗin. “Ban sani ba, ka fita ka barni.” “Babu inda zani!” Ya faɗa yana murmushi. “Ni bana son haka!” “Ni ina son haka. !” Kasa magana tayi ya mike zata bar wurinshi ya taka mata gown ɗin. Faduwa zata yi ya riko ta. Ta zauna akan cinyarsa. Hannunshi ya kai ya zagaye kugunta.
“Me yasa baki so?” Ya sumbaci kafadarta. “Mayor!” Ta faɗa tana son tashi.”kin san me? Bana son kina min haka.” “Me na ma…..” Hannunshi ya kai kirjinta, bata san lokacin da ta zille ta mike tsaye tana faɗin.
“Dama sune damuwarka? Dama ai ta gaya min bukatarka zaka biya ka watsar da ni! Idan da don shi ne da ka gaya min na baka a waje ka kyale ni. Ka sani duk abin da kake ba zan tab’a baka kaina ba!”
Tabe baki ya ce mata. “So what? Ni tsafi zan yi da kirjinki na bawa dodona bayan na gama sha, idan yaso kika mutu sai na kara auren, itama ya mutu na kara auren haka zan ta aure na zama Dodon Amare!”
“Allah ya min tsari, ba iya ni ba har da sauran Amaren!” “Amma sai na shanye madara na.” Mikewa tayi ta bar shi, A wurin tana hararanshi. Kamar ya fashe don dariya domin kuwa ta masifar bashi dariya musamman yadda take nuna yarintarta.

Fita yayi daga dakin, sai da ta gama uzurinta, ta fito ta cire kayan tana kokarin duba wani riga mara hannu ya kutsu kai domin dai bai rufe kofar ba, daga ita sai pink pant, sai bra irinshi da sauri ta tsalla ihu tare da rarrumar rigar ta shige ban daki, wanna karon kan dariya ayi sosai. Yaki fita a dakin yana jiranta, har bayan minti ashirin bata fito ba, dole ya fita ya bar dakin. Shiryawa tayi ta fito dake lokacin la’asar tayi, ta fita zuwa falo ta samu baya nan, kitchen ta leka ta samu ana kan abincin. Sannan ta juyo da niyyar komawa dakinta, kawai suka yi kicibis. “Babbar mace an fito ne?” Ya tambaye ta yana murmushi. Kin d’ago kai tayi. “Ai oho kina nufin baki magana ne, tow shi kenan” daga haka ya matsa ta wuce, shi ba yaro ba ne kuma ba waliyi ba ne. Sannan ba mahasumi ba ne da zai ga mace ace kamfanin sadarwan shi bata dauki chaji ba. Ta gama guje gujenta yana kallonta.
Haka suka yi ta wasan boya har dare yayi, bayan Isha bakin suka iso . Manyan magidanta ne da matansu, har su sha biyu. Tsabar kishi irin na Malik har dakin ya biyota bayan sun tarbi bakin ya shiga duba mata wani abaya ya mika mata. “Bana son ki kara saka kayan nan matukar ba iya ni dake ba ne!”
Bata rai tayi tana me saka abayar, kallona yayi ya mata. “kin ajiye mazaunai kamar agwagwa ba dole ki tashi kaina ba!” Da sauri ta juya tana kallonshi, d’age mata gira yayi yana fadin. “Ce miki aka yi ni matashi ne? Koda bana cikin jerin matasa amma jini na yafi nasu tafasa. Don haka a kiyaye kada a lalata min tarbiyya!” Gyada kai tayi bata kuma kula shi ba. Domin da gaske Malik ya fi ƙarfinta. Yana magana kamar wanda ake zura mishi magna dama haka yake ko yanzu ne yake da magana haka? Haka suka fito falon suka samu ana ta hira matan da mazajensu. “Sannunku kunsan sabon ango yadda yake, shi yasa ban dawo da wuri ba, Madam ki mana jagora kan table din ki mana.”
Murmushi tayi ya ce musu. “Bismillah!” Ta koma bayan Malik tana tura mishi keke, fuskarta a sake. ” Madam da fatan yau zaki cika min cikina da abinci, yo Ina sabon ango dole na ci me nauyi!” “Ai sai na baka da na yau da na gobe, domin ka cika cikinka” haka suka yi ta hira da raha, har table din abincin, aka shiga zama. Daga yadda ta ga suna kasa kasa tun da suka fito ta fahimci ba karamin girman Malik suke gani ba. Don haka itama ta shiga rigar nutsuwa, har suka gama cin abincin, ta mike ita da mata shida suka nufi falon sama. Suna barin wurin Daya daga cikin bakin ya ce. “Yallabai muna tayaka murna auren da kayi.” Murmushi yayi yana goge gashin bakinshi ya ce musu. “Na gode!”
“Hmm! Malik dama Malik akan Lalla Salmah ne, ayi hakuri a d’aga mata kafa. Al’amarin yayi mata tsauri!” Shiru yayi yana sauraren su. Har suka gama magana bai ce uffan ba, sai dai yana binsu da idanu ne. “Yallabai baka ce kome ba, kayi hakuri tayi kuskure. Amma a d’age mata takunkumin yayi mata tsari ba zata kuma ba.
“Shi kenan zan duba lamarin!” “Mun gode!” Daga haka ya kira suka yi yar hira sannan suka tashi zasu tafi, ta hannun Malik suka mata kyauta da tukwaici. Kiran matansu suka yi, a tare suka sauko tare da Zeeno. Bayan sun fito ta shiga dakinta. Ta sauko musu jakunan kayan nan, ta basu da turaruka. Har suka rabu da dadin rai. Mutumin da ya zo da batun Lalla Salmah ya dawo yana me cewa. “Amarya don Allah ga yallabai nan, ki saka baki ya dawo mana da Lalla Salmah, tayi danasanin abin da ya faru ayi hakuri.”

“Ba kome, ya wuce.” Ta faɗa tana kallon Malik, kauda kai yayi yana me cewa. “Ku gaida gida.” Ya musu sallama, saboda dare ya fara nisa don har goma ta wuce. Suka juya cikin gidan, a ranshi yake jin yau zai fara gwada lafiyarshi domin yana da burin cin amarcin shi me lasisi.
Table din ta wuce ya shiga hada kayan, tana murmushi domin taga sun ci abin sosai. Shigowar Lalla Salmah a hargitse ya sata sake flat a kasa tana binta da idanu. Gaban Malik ta nufi ta zuba gwiwarta tare da fashewa da kuka. “Malik ka gafarce ni, Nadrah tana asibiti she committer suicide.” Bai san lokacin da ya nufi hanyar waje ba, ya manta da wata Zeeno. Tun tana saka ran ganin shi da suka fita har ya hakura ta zubawa kofar idanu. Haka ta kwashe kayan ta nufi kitchen ta gyara gidan tsaf sannan ta dawo falo tana zaman jiranshi, duk da tana son kiranshi amma me zata ce mishi?
A can asibiti kuwa, ba karamin wahala suna sha ba, kafin ta dawo duniyiyyar rayayyu. Kiran Elbashir yayi yaji wayar a kashe, haka ya hakura, sannan ya nufi wurin zama ya zauna yana tambayar Lalla Salmah”me ya faru?”
“Tunda honorable jafar ya gaya min cewa kace sai kayi nazari, ya ce Zata tafi ta bar min duniyar ma sai nayi yadda nake so da shi. Matukar ta rayu a gidanka zata dawo da zama, ban san ya zan yi da Nadrah. Na yi kokari na fahimtar yanzu kan bata da ikon zuwa wurinka. Amma yarinyar nan taki tunda nace maka an tsige ni ta ce matuƙar ban dawo da matsayin,sai hm kashe kanta zatayi me yasa take haka , nasa kai nawa laifi amma ita yake fushi da ni, na kasa fahimtar me damunta. Don Allah Malik ya zauna kafin na koma wurin da nake aiki kayi hakuri, ba zan kuma ba.
A can gida kuwa, zaman da Zeeno tayi sai ta baka tausayi domin kuwa ta gama zaman jiranshi. Amma har wurin karfe sha biyu. Abin tausayi bata taɓa sanin haka mata suke jiran mazajensu ba, idan suka futa daga cikin gidan, ganin haka yasa ta mike ta bar falon ta tafi dakinta, tayi wanka ta kwanta, daga ita sai towel. Ta kwanta tun tana jiranshi har ta kai barci yayi gaba da ita.
. …. Malik bai dawo gida ba, sai karfe hudu na asuba, lokacin da ya shigo ya hango ta kwance towel din ya zame daga kirjinta….
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button