Bakar Ayah Book 2

Bakar Ayah Book 2 Page 17-18

Sponsored Links

Page 🖤17••18🖤

 

***DAWOWA LABARI***

 

Shirye shiryen komawa new side Lubna takeyi,dan bazata fara sabon aikin da boka zulungum yabata a wajenba.
Gobene kuma dawowar Jabeer daga Tafiyar dayayi,kuma goben takeso tasakashi ya kori Bombee daga side ɗin da take,dan da ita yadace badawata can banza ba.
Haka ta wuni tana saƙawa da kwancewa ita kaɗai.
Muryar Bishirah ce ta katseta daga tunanin abinda tashirya gobe tayi,
“Uhm ranki yadaɗe an samo baƙar kuliyar kaman yanda kika ce”
“Yawwa Bishirah na gode,dafatan dai babu wanda yaganki da ita koh”
“Eh babu wanda ya ganni,a cikin kwali na shigo da ita,nasaka mata maganin bacci a kifin kaman yanda kika ce”
“Shigomin da ita yanzunnan”
Fita Bishirah tayi,bata daɗe ba sai gata da mage a hannunta,ta langabe sai bacci takeyi.
Duk da tsoron dayake cinta haka ta daure ta karbi magen tareda nufar ɗakinta da ita,bayan tayiwa Bishirah gatgaɗin kartaji wannan zancen.
Banɗaki ta nufi da ita inda ta ajiye suƙa da kuma maganin. Wanda yake cikin kasko.
Hannunta yana rawa yana komai haka tasaka wuƙar ta yanka wuyan magen,jini ne yafara zuba a cikin kaskon,inda magen tafara shure shure,amma haka ta riƙeta gam da hannu biyu jinin yana ɗiga,a duk Lokacin daya ɗiga sai yayi cuuu kaman ruwa ya ƙone ajikin abu mai zafi. Da haka har ta gama tass kafin ta jefa gawar magen a cikin leda tasaka a durt bin.
Ɗaukar kaskon maganin tayi ta maidashi inda tayi masa kyakykyawar ajiyah.
“Anyi ɗayah,hmmmm duk wanda kuka rabi Jabeer kun shiga uku da baƙin ciki,zanso naga idanuwanku ranar dazanyi masa asirin da ko lasar ƙafata nace yayi sai yayi batareta musu ba. Wuyar wata ukun tacika,zakuga abin mamaki da idanuwanku”
A zaune yake akan gado yasaka fararen kaya marasa nauyi masu laushi na bacci.
Waya ya danna tana ringing amma har yanzu ba’a ɗauka ba,tun kwana uku da zuwansa yagama abinda ya kawoshi,da gangan yaki komawa saboda abinda zaije ya tarar,musamman daya samu suke waya da Jaleelah,koyaushe suna maƙale suna zubawa juna soyayyah.
Wannan lokacin yayiwa Jabeer daɗi da har bayason su shige daga cikin rayuwarsa.
Yana cikin saƙar zuci Jaleelah ta ɗaga ƙirnnasa.
Da sauri yakai kunnensa domin kar yayi Missing zazzaƙar muryarta,aikuwa kaiwarsa keda wuyah yayi kicibis da itah.
“Assalamu alaika masoyina”
Saida ya lumshe ido na tsawon lokaci kafin ya amsa sallamar
“Wa’alaikissalam Sarauniyar zuciyar Jabeer”
Daga nan suka cigaba da hirarsu kaman kodayaushe,maganar aure ta sako masa akan Mahaifinta yace ya turo.
“Yah Jabeer idan har dagaske sona kake babana yace katuro ayi maganar aurenmu,domin na faɗamasa cewar muna soyayya dakai,kuma ya yaba da abin har yayi bincike akan ka”
“Uhhh to shikenan karki,nafiki zaƙuwa wajen ganin na mallakeki a matsayin matata,bakisan yanda nake jinki a cikin zuciyata bane shiyasa,ina mai miki alkawarin cewar dana koma gida zan samu abba da maganar,inshaaallah aurenmu bazai wuce nan da nan Wata uku ba”
“Dama nasan bazaka ƙi amincewa ba,kaman yanda kake son kasancewa dani nima a wajennawa hakan take,ina sonka sosai,ka burgeni matuƙa daka fara zuwaga iyayena kafin a tunkareni,hakan maxa dayawa suka kasa aikatawa”
“Amma nafaɗamiki fah cewar inada mata biyu,kina ganin hakan babu matsala”
“Babu wata matsala nidai a wajena,dan haka kada ka damu,nasan kanada damar riƙesune shiyasa ka auresu. Allah da kansa yahalattawa na miji auren mata huɗu,idan har zai iya adalci a tsakanin su,dan haka indai zakayi adalci a tsakanin mu shikenan”
Da farko Jabeer baiji daɗin yanda bata nuna kishi ba,duk da kuwa hakan yake fata,amma kuma dayaji bayaninta sai bai kawo komai a ransa ba.
Hirar su suka cigaba dayi har lokacin da zuciyoyinsu suka raya musu su bari.
Wayar ta ce tayi ƙara da misalin ƙarfe takwas na safe,juyawa tayi tana lalumar haidar,bata jishiba dan haka tayi tunanin ko Hilyaan ce ta ɗaukeshi.
Wayar ta ɗauka tareda zame bargon dake jikinta kaɗan.
“Yadai khamees da safennan?”
“Hmm yanzu ne safen koh,koda yake ashe amarya ce fah.
Binciken danakeyi ya kammala,Gen abdu manga shije na biyu a kason Share mai yawa na companyn mijinki, meeting ɗin daya gudana ma kwana uku da suka gabata yaje wajen,wanda inada tabbacin akwai abinda yake saƙawa”
“So yake ya ƙwace companyn daga hannun Jabeer,da farko yayi shurune saboda in Lubnah ta haifi yara one day sune akai,amma yanzu ya sanja plan saboda ƴar sa bata haihuwa dagaske kenan……..sai kuma me,kayi nasarar cire na’urar jikinka?”
“Uhmm nayi nasara,nawa tana hannun dama ne,nikuma ina checking na hagun”
“To yayi kyau”
“Uhm tun kwana uku baya aka gama meeting ɗin,amm mijinki bai dawo ba sai yau,bazaki bincika mai yake ba a wannan lokacin”
“Wannan kuma kofin shayinsa ne,ruwansa yasha ruwan tea ko kuma yasaka madara,baya cikin lissafina a yanzu,bari zanyi plan da wanne zan fara ƳAR KO UBAN.inbaka da abin faɗa zan koma bacci”
“Kutt bazaki fara shirye shiryen taryarsa ba bacci zaki……”
Tun kafin ya gama Bombee takashe wayar tayi jifa da iya,tareda maida pillow ta kwanta.
Abinci na gani na musamman Lubnah ta jaɗawa Jabeer domin taryarsa.
Yana shigowa mamaki ne yakamashi ganin a side ɗinsa tahaɗamasa girkin,taji kwalliya cikin wata doguwar riga ja,ba lafi tayi mata kyau sosai.
Murmushi tayi masa maiɗan ɗauke da alamar takaici,saurin gusar dashi tayi tareda takowa inda yake.
“Sannu da dawowa farincikin ran Lubnah,nasan dama bazakake kaga halin danake ciki ba,side ɗinka zaka fara shigowa,shiyasa nayi komai a nan wajen”
Alama ya nuna narashin kyautawarsa akan hakan,atleast tunda zamansa take,yakamata ya je ya ganta tukunna.
“Kiyi haƙuri luby na gajine shiyasa ban je wajenki ba,amma nayi niyyar idan nagama shiryawa zan shiga ai”
Karya kai tayi irinna ƴan duniya kafin tagyara annunrin fuskarta.
“Shikenan na karbi uxurinka,yanzu tunda ka gani muje na tayaka shiryawa ko?”
“Bayyi mata musu ba,dan yanada buƙatar hakan sosai. Ita ta taimaka masa ya cire kayansa,kana ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗan zafi,babu yadda bayyi ta ita ba kan tazo ta tayashi wankan amma taƙi.
Abin tsoronta ɗaya shine kada taganshi yana wanka zuciyarta ta jata ta aikata abinda boka ya mata gargaɗi akai,na kada ta kuskura ta bashi kanta har sai ta gama wata ukunnan tukunna chass.
Taya fito daga wanka ma bata ɗakin,tana can wajen shirya masa abinci,wanda shikansa yasan ƴan aikine sukayi,ba itace ta dafaba.
Duk yadda taso nuna kisisinarta kan yaci abincin kaɗan yaci ya tashi.
Sashen su Hajiya zeenah ya nufa domin ya gaishesu,A wajen Alh aliyu mahaifinsa yafi tsayawa suna ta hira,daga baya ya ɗau mota ya nufi wajen Khaleel,zai rakashi gidansu Jaleelah.
A hanyar zuwa gidan ya tsaya yayi siyayya mai matuƙar yawa kafin suka nufi gidan,dama tasan ta isowarsa.
Sauƙa ta musamman akayi musu,basu Jabeer ne suka baro anguwar su Jaleelah ba sai bayan isha,salloli ma duk a unguwar sukayi.
Shikansa Khaleel yana jinjina irin soyayyar da Jabeer yake yiwa Jaleelah.
Lokacin daya shigo sashen Lubnah tana kwance da waya a hannunta,ta saka kayan bacci tana kan gado.
Ɗan zabura tayi tareda ɗagowa takalli Jabeer ɗin,dan gabaɗaya bataji shigowarsa ba sam.
“Uhmm kina wannan chatting ɗin inata sallama koh”
Cikin kasalalliyar murya mai cikeda alamar gajiya da buƙata yayi maganar.
Gaban Lubnah ne ya bada sautin dumm kaman ganga,ganin Jabeer da kayan bacci,dan tasan mai yakawo shi.
Matsowa yayi inda take da niyyar kama hannunta,saurin matsawa tayi kaman taga aljani.
Wanda hakan yasashi yin mamaki matuƙa.
“Lubnah lafiyan ki kuwa?”
“Iyee na’am dama …..dama ina period ne”
“Hmmm period a wannan lokacin,har yanzu bansan yaushe kike period ba,idan akwai abinda yafaru ko wata matsala ki faɗamin ina jinki?”
Yana cewa matsala wata idea tazo kanta,saurin saitawa tayi tareda yin magana cikin sigar tausayi,yanda tasan zai yarda da ita.
“Kayi haƙuri dama banason sanar dakaine kada kaji babu daɗi,na kamu da ciwon sanyine a tafiyar dakayi,to shine dana je wajen maganin gargajiya suka bani wani nayi amfani dashi na tsawon wata uku,amma a wannan tsawon lokacin kada na bari ka kusanceni.
Kayi haƙuri ni kaina da farko nayi tunanin hakan zaisa na shiga haƙƙinka dan haka……….”
“Ahah karki shiga damuwa,lalurine yana iya hawa kam kowa,indai wannan ne babu matsala,Allah ya baki Lafiya,Yakuma kaimu har sai kim warke ɗin.
Ni barina tafi side ɗina toh”
Yaƙarisa maganar yana sumbatar goshinta.
Tashi yayi ya nufi ƙofah,har yayi nisa ya juyo tareda cewa,
“Amma bakya ganin bazamuje kiga likita ba gobe?”
“Ahah sunce kada nayi amfani dana likita har sai na gama tukunna”
Ohk”….yafaɗa cikin sanyin gwiwa,a yanda yake ji yayi zaton zata taimakeshi da wata hanyar,amma sai tama koma kan wayarta hankalin kwance,hakanne yasa shima yabar ɗakin ya nufi nasa sashen.
Da safe bai samu tashi da wuri ba,kasancewar yanda yakai dare bayyi bacci ba yana fama da laluri.
Sai wajen ƙarfe goma ya shirya ya fito.
Da Lubnah yauma yasake yin karo tayi kwalliya cikin lace tana tsaye a bakin dining,wanda yake cikeda kayan karin kumallo.
Murmushi tayi masa tareda tambayar ya tashi lafiyah,shidai a mamaki ya amsa,dan bai saba ganin hakan ba.
Surutu take tayi masa yana cin abincin har ya gama tukunna.
Yatashi zai tafi sai yaji tace.
“Amm Honey Dama magana nakeso muyi mai muhimmanci”
Komawa yayi yazauna domin jin mai zataje,dama yayi tunanin hakan,domin ruwa baya tsami banza.
“Shin idan kanada mata guda biyu,waye yakamata yafara zabar abu a cikinmu?”
“Kece yakamata ki fara zaba”
“To amma meyasa wancar matar taka tafara zaban wajen zama a new side kafin ni”
“Uhm wacce matar kenan”
Dan shi har cikin ransa yamanta wacce take magana akai,saida ya tuna da auren da Hajiya zeenah tayi masa kafin abi ya faɗo cikin ransa.
“Ohh nunamin zakayi ma kaman baka san wa nake nufiba,taje ta ɗauki side ɗin dani naji shinake so a wajen,dan haka yau ka faɗamata tabar cikinsa ta ɗauki wani,dan wannan nakeso”
“Ina side huɗune,ki dau wani mana a wajen,kowanne ma naga yana da ƙofa ta cikin side ɗina,babu wanda yake gefe,dukka a round suke a wajen”
“Nidai shinake so,domin yafi kusada lambun shaƙatawa,iskarsa ma tafi ta sauran daɗi,kawai ni yafimin shi nake so”
“Uhm kin faye fitina Lubnah keba yarinya ba,wannan side ɗin ba yafi gefe fiyeda sauran,a haka kike sonsa?”
Hanyar ƙofa ta nufa zata fita yayi saurin riƙota.
“Dama babu wanda ke sona a gidanan,a wajenka kaɗai nake samun sukuni,kaima kuma yanzu karamin abu amma ka kasa yimin shi,shikenan to naga matsayina”
“Kibar wannan zancen,indai sashen ne muje yanzu na fitarta a wajen ki shiga,shikenan?”
Goge hawayen Lubnah tayi tareda jijjiga kai,kana ta ƙanƙame hannunsa daya saka a cikinta.
Makullin motarsa ya ɗauka tabishi a baya tana murmushin cin nasara,ba koranta ne batada hanyar yi ba,tafison tasaka mijinnata datake taƙama dashi ya koreta da kansa,taga yaya zatayi.
Shiga motar itama tayi yaja zuwa sabon wajen,a cikin ƙanƙanin lokaci suka kai gurin.
Lokacin sha ɗaya tayi rana tafito sosai.
Itace ta fara fitowa daga motar ta ƙwanƙwasa kofar kafin ma ya kashe motar.
Hilyaan dake jijjiga haidar a hannunta taji ana buga ƙofar.
“Ohh wai har yanzu anty maryam baki gama bane,wasu sunzo nemanki a waje to,ga haidar yana ta kuka shima.”
Hanyyar ƙofar ta nufa tareda buɗe musu ƙofar.
Lokacin data buɗe ƙofar da Jabeer suka haɗa ido,wanda zuwansa wajen kenan ya kashe mota.
Kallo ɗaya tayi musu tareda cewa.
“Ku shigo”
Binta sukayi a baya har tsakiyar falon,wajen zama ta nuna musu tareda dan ɗaga muryarta.
“Anty maryam serious yanzu kam baƙi kikayi,gashi nace miki yaronnan kuka yake tayi”
Muryarta suka jiyo tun kafin tashigo falon.
“Ohhh baby yana missing mommy,Hilyaan ki ɗan bashi ruwa mana,ba yunwa yakeji ba,yaushe ma na zauna yasha”
Shigowa falon tayi ta dawo daga backyard ɗin gidan,tana goge gumin dayake fuskarta da wani ƙaramin towel.
“Kayan workout ne a jikinta baƙaƙe,riga iya rabin ciki,sai kuma wando iyah gwiwa,gashinta kuma ta kama shi da ribbon irin kayan,shima yana dauke da adon fararen star dake jikin kayan.
Kayan sun matseta,sosai fittet ɗin farar fatarta ya bayyana a ciki,ga kuma gumi dayake bin jikinnata.
Kallon mamaki tabi su Lubnah dashi wanda suke tsaye. Yayinda suma suke aikamata nasu kallon mamakin,musamman ma Jabeer dashi ganinta biyu dashi kenan.
Basar da kallon dasuke mata tayi tareda dan juya blue idonta.
“Ohh baƙi mukayi haka,sannunku da zuwa,saidai naga baku zauna ba”
“Hmmmm dama tun kallon danayi miki ranar a bakin gidannan,da kuma kallon danayimiki da daddare,nasan ke ba ƙaramar tatacciyar ƴar bariki bace. Ba kince ranar sai abinda kika ga dama zayyi ba,harda wani ranann nazo nemansa kika ce bazai fitoba,inna isa nima nasaka shi yayi yanda nakeso in yana wajena,to yanzu gashi na sakashi,korarki yazo yi a wannan side ɗin yanzunnan,saboda ni matarsa uwargidansa wannan side ɗin nakeso”
Zaro ido Jabeer yayi tareda kallon Bombee,jin abinda Lubnah take faɗa wanda bashida masaniya akan sa,ko kuma yaushe akayi shi. Ita ɗinma shi takalla tareda yimasa kallon basai ya sani ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci tajuye zuwa nata salon.
Hannu tasaka a kunkuminta tayi wani malƙwaɗa tareda turo ƙirji gaba kaɗan. Yanda tayi sigar ko ƙwararriyar ƴar bariki albarka,musamman kuma data ƙara dawani rishe ido.
Lokaci ɗayah Jabeer yaji kamar wutar lantarki ta huda daga kansa har ƙarkashin ƙafarsa.
Lanƙwasa harshe tayi tareda yin taku biyu zuwa gaban Lubnah daff,harsun jin hucin juna,bakinta takai kan kunneta tareda yimata magana yanda babu wanda zaiji,tanayin magana idonta yana kan Jabeer wanda takafe idonsa a cikin nata,ta yanda bashida ikon ɗaukewa.
Saurin matsawa tayi da baya tana jijjiga kai.
“Wlh baki isa ba,ina ina kinyi kaɗan”
“Nayi kaɗan,to faɗawa mijinnaki kiji idan ƙarya ne,in kuma bazaki faɗamasa ba to yana nuna kin yarda dabinda na faɗa kenan.
Shin ya shiryah korata na bar shashennan?”
Harara ta bankawa Bombee tareda shikansa Jabeer ɗin,kana ta bangajeshi tabar shi a tsaye anan kaman mutum mutumi.
Bayan ta tafi idonsa ya maida kam Bombee tareda tunanin shin mai ta faɗawa Lubnah daya sanja ra’ayinta haka.
Itakuwa tana ganin Lubnah ta tafi ta maida ainihin fuskarta ta Bombee kaman ba itace take rausaya ba.
Samun waje tayi ta zauna tareda karbar haidar a wajen Hilyaan.
Nono tacire tasaka masa a baki nan da nan kuwa yayi shuru,faruwar hakan duk akan idon Jabeer,da sauri ya runtse idonsa ya bar falon bayan idonsa yayi tozali da abinda bai kamata ya ganiba,wanda yake da tabbacin yanda ƙwaƙwalwarsa tayi record ɗin hoton,ba lallai ya bace nan kusa ba,musamman dayake matse dama a kwanannan,Lubnah ta baro masa ruwa.
A haka yabar wajen kansa cikeda tambayoyi fall na mai yake faruwa,tukunna ma shin wannan amaryar tasa wacece ita?…
Bayan sun tafi kallon alamar tambaya Hilyaan ta jefi Bombee dashi,
“Anty maryam me yake faruwa mai kika faɗamata haka,kuma shikansa mutuminnaki naga da alama so kike ki jurashi a tarko,shin kin sanja plan ɗinki ne”
“Uhmm kinada tambaya Hilyaan,so nake kawai naga ya zayyi,sannan daga kallon danayi masa kamar Lubnah bata bashi lokacinta yanda yadace,duk wacce take son cafkar zuciyarsa zata samu a yanzu cikin sauƙi.
Magana kawai na faɗa mata,kuma da alama tayi tasiri a ranta fiyeda abinda kowa zai faɗamata.”
Lokacin data kai bakinta wajen kunnen Lubnah,ƙankance murya tayi tareda cewa.
“Wai har yanzu baki ɗago lamarin bane uwargidan angona,a tunaninki idan kika koreni anan bazai so hakan ba,zamu baje lokacin mu tareda shi a sashena,sannan kuma idan kina nan ma duk lokacin dayake wajenki,zan yi irin wanann shigar nazo wajennan da suna motsa jiki,kaman yanzu daya kafeni da ido,kina ganin zaki iya jan hankalin sa ya ɗauke kannnasa daga gareni uhm?”
Juyawa Lubnah tayi ta kalli idon Jabeer wanda yake tsaye kyam a cikin na Bombee,take wani ƙululun baƙin ciki ya shigeta,ganin tafara samun galaba akan ta yasa ta ƙara dacewar.
“Shikenan zan koma sashe na gaba wanda yake kusada shi,sannan zan dunga zuwa nan ina motsa jiki a bayan sashenki,wazai ƙi lokaci guda biyu na mijinsa. Hakan zai mana daɗi nida shi,in kuma baki yarda ba ki tambayeshi yanzu kiji,shin idan nazo motsa jikin bazai tayani muyi ba ranar dayake wajenki uhm”

Dariyah Hilyaan ta fashe da ita dataji abinda Bombee tafaɗawa Lubnah.
“Uhm na gane,wato zakiyi amfanine da kishin dayake mata ki wanata a haka koh?”
“Yess haka abin yake,tunda zata dawo nan ,dole shima nasan zai dawo nan,abin zaifi tafiya yanda nakeso”
Takarisa maganar tareda dariyar da ita kaɗai tasan ma’anarta.

Tuƙin tuwo take magriba ta gabato,rana tayi ja a yamma.
Murya taji kaman ana ƙiranta a bayanta,bata kawo komai a ranta ba tacigaba da tukinta,domin tasamu ta gama da wuri,tsayawa tayi ta juyah muciyar tareda zare ido.
“Laariiiiii nasan kinji kirana,amma kike so ki juya bayanki daga gareshi,maza kizo ga kirana yanzunnan,ranar wanka tazo ta,duk yadda kika so da boye cibi a yau bazai boyu ba,inaso ki zo kiga mijin Innayi a yau”
Jikin laari rawa ya kama kaman mazari,jijjiga kai tafarayi hawayen takaici na zuba mata,amma tasan a gaba jeji baya tsiyaki take,babu hanyar dazata bi wajen bullewa daga halin ƙaƙani kayan data tsinci kanta ciki,wanda daman tasan da zuwansa tun ran gini da kuma ranar zane.
Hnayar dakinnata ta nufah tana jan kafa kaman ƙwai ya fashe mata a ciki.
Cikin sanyin jiki ta dauki tsinken turaren ta kunna,yana bugar madubin kuwa Zilliyah ta bayyana a jiki tana dariyar mugunta.
“Laari kenan,nayi zaton ai bazaki amsa kirana ba tunda nayimiki rana?”
“Ina na isa uwar matsafa mai daraja,gani gabanki na miƙa wuyah”
Innayi wacce sai yanzu tashigo gidan ta dawo daga gidan ƙawarta,duk yawancin ƙawayenta anyi aurensu,itace kawai tasaura a gida,ko kare bai taba shinshinarta ballanta na kuma murum yace yana so.
Abin ya daurewa mutane da dama kai,ganin gata kyakykyawa dakuma ilimi,batada makusa ko kaɗan,amma yanzu ko magana mutum bayaso mlm Ahmadu yayi masa akan Innayi,saboda yana tsoron kada yace yabashi ita.
Tukunya ta gani akan wuta da tuwo a buɗe ba a gama tuki ba,waigawa take ko zata ga inna laari amma bata ganta ba,ɗakinta ta nufah,har zata shiga saikum taja ta tsaya jin tana magana da,wata mata da bata san muryarta ba.
Abinda taji an faɗane yasaka gwiwarta yin sanyi tareda zubewa a wajen,ko kaɗa kunnuwanta sun kasa gasgata mata abinda take jiyowa.

 

 

 

 

 

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button