Bakar Ayah Book 2

Bakar Ayah Book 2 Page 33-34

Sponsored Links

Page 🖤33••34🖤

 

 


Kallonsa take tareda jin sanda zai bata amsar me waɗannan tarin magungunan suke a cikin drawersa,kaman companyn magani.
“Bakace komai ba,da alama waɗannan magungunan duk nasaka baccine,kanaso kacemin su kake sha?
Meyasa to bakada lafiyane na tsawon lokaci ka boye?”
“Uhm duk wannan tambayoyin fah,kin damu dani har hakane?”
Yaƙarisa maganar yana dariyar ƙarfin hali.
“Bafa abune na wasa ba Serious me wannan magungunan suke a wajennan?”
“Sha nakeyi amma bakoyaushe nake buƙatarsu ba sai ina cikin matsanancin yanayi,ba wani abune na serious ba yanda kike tunani ,yanxu dai miƙomin maganin zazzabin nasha,ƙarfina ya zuqe a maganar danayi ɗinnan”
Ajiyar zuciya ta sauƙe,bata sake cewa komai ba ta miƙomasa maganin yasha kaman yanda ya buƙata.
Saida taga yasha kana ta tashi zata bar ɗakin..kamo hannunta yayi ya riƙe gam,ja tayi amma ya riƙe sosai da guntun ƙarfin dayake jikinsa.
“Dan Allah kada ki tafi ki zauna”
“Uhm saboda kana buƙata ta koh,sai nan da sati biyu bazan sake ganinka ba ballanta wani abun ya haɗamu”
“Uhm nan da sati biyu kikace ai ,kafinnan ki taimakamin wajen zama a tareda ni”
“Ina matarka meyasa baka ƙirata ba saini”
“Meyasa kike son maimaita maganar da kin riga kinsanta uhm?”
“To yanzu dai bazan zauna dakai ba,saboda nabar ɗana a ɗaki shika ɗai”
“Idan bazaki zaunaba zan biki to mu tafi sashenki,i hope hidima bazai miki yawa idan mu biyune koh”
Jimm tayi batace ahah ba bata kuma ce eh ba,tarasama mai zatace da taji maganar da yayi.
Hannunta yasake yana ƙoƙarin tashi,batada zabi ta taimaka masa suka nufi sashennata badan tasoba.
A gado ɗayah suka kwanta bayab sun saka Haidar a tsakiyarsu.
Abinda bata tabayi ba tunani ba kenan daga wajen mijinnata na wata shida.
Bayan sallahr asuba tunda koma bacci bashi ya tashi ba saida kukan haidar ya jiyarci kunnesa,buɗe ido yayi suka haɗa ido da Bombee,wacce take ta kiciniyar sakawa yaron diafer,da alama kuma yunwa yake ji ba son saka kayan ba.
Kallonsu yake cikeda sha’awar su,abinda yake mafarkin samu kenan,amma kuma bai samu ba a rayuwarsa,shine ganin matarsa suna zaune lafiya da kuma ɗansa.
Yaron kwata kwata baya kama da itah,illah abu ɗaya dasuka hada dashi shine idonsa kawai.
Kallon fuskar yaron yake ko zai sake ganin wani abu da suka haɗa da Bombee,saidai sabanin ganin hakan saima wani abu daya gani a fuskar yaron wanda yasaka ƙirjinsa bugawa.
Saurin kawar da kai yayi yana jijjiga kai. Inaa rashin samun yaro nasa na kansa,baikamata yafara ganin dan da baisan asalinsa ba a matsayin nasa.
Yana tsoron kar zama da yaron waje daya yasa soyayyar yaron tayi tasiri a ransa.
Yasan ko tsafi yake da baƙar zaba Hajiya zeenah bazata bari yahaɗa alaƙa da yaron ba.
“Tunda ka tashi na haɗa maka ruwanka,ka gama ina jiranka a dining”
“Bazaki tambayeni ya jiki ba”
“Jikinka na ganshi ba buƙatar tambayarsa,Fatan Shine Allah ya sawwaƙe kawai”
Daga haka ta suri yaronta sukayi waje,saida zata fitane ma yakula da kayan dayake jikinta,daga ita sai bom short da t-shirt.
“Ohh Allah ya bani ikon tafiyar da wannan bauɗaɗɗiyar baiwa taka,ba sonta nake ba,amma kuma zama tareda ita yana sakani cikin nutsuwar zuciya,na ganta tana ta hidimarta da yaronta yana sakani jin inama suɗin iyalina ne danake da iko akan su.
Narasa wanne irin yanayine haka nake shiga gameda su”
Bayan ya fito daga wanka ya kalli kayansa nazaman gida,da alama tashigo dakin kenan yana wanka.
Madara take bawa haidar a feeder sa Lokacin daya fito.
“Wannan yaron ya kai cin abincine,bazaki bashi mama ba”
“Na yayeshi wancan satin,madarar formular nake bashi,dama dan jikinsa yaƙi karbar madarane yasa na bashi nono”
Zaro ido yayi jin tsaurinta gameda yaronnata.
“Haba ke kuwa,shiyasa yake kuka kenan,bai kamata ya wannan yaron ki cireshi daga abincinsa ba,abune da kowanne yaro yakeson samu a wajen mahaifiyar sa……….”
“Nasani Mr CEO sannan koda da lokaci kadan bantaba yin abu danna cutar dashi ba,ina sonsa kaman yanda uwa take son danta,bukatar hakan ce ta taso.
Kuma a yanzu jikinsa ya karbi madarar fiyeda da”
“Uhm”
Shine kawai abinda Jabeer ya faɗa,dan bashida tacewa a ciki,tunda ɗan ta ne kuma ikonta ne.
“Oh barina zo nabawa angon nan da lokaci kaɗan abinci,kar azo biki a ganka a rame”
Gogewa haidar bakinsa tayi tareda bashi abin wasa ta taho inda abincin yake.
Sai da ta gama zubawa kafin ya samu waje ya zauna yafara zubawa cikinsa.
Maganin yasake sha bayan abincin,kafin ya miƙe akan doguwar kujera..
“Naga ka samu sauƙi fiyeda jiyah,ka ci abinci kasha magani,toh bazaka tafi sashenka ba koka fita”
“Uhmm ni bazan tafi ba saina gama warkewa,saidai in korata kike toh”
“Menene amfanin ka taremin a sashe to bayan da naka,nina rasa mai yasa nake ta ɗawainiya dakai ba matar ka ba”
“Kema ai matata ce ina,ko kin sauke auren daga kanki?”
“Hhhhh habadai koda ni matarka ce amma ta wata hanyane daban,ka daina sakani cikin wannan matsayin”
Duk korafin da tayi Jabeer bai bar sashannata ba,dan inda sabo yafara sabawa da halayyarta. Sai wajen yamma kafin ya tafi,bayan ya yi wanka yaci abincin rana,wai suna yana jinya,amma ƙara ƙiba ma yayi fiyeda yanda tazo ta sameshi.
Yana fita itama tafara shiryawa saboda zuwan meeting din da zasuyi itada su Hilyaan,jiya yakamata suyi amma ta ɗaga saboda Jabeer.
“Zancen Dear gaskiya ne data faɗa maka,na fasa ɗora mahafinku akan wanann aikin,domin bazayyi min yanda nake so ba.
Dan haka ka gaggauta dawowa ƙasarnan kafin ba sanja shawara,kana jina koh”
“Ehh zan dawo,waye zaiqi zama ceo na company babba haka,gaskiya you are the best mommy”
“Wanann koɗaɗdiyar matar taka inzata zauna dakai a ƙasarka ta biyoka,in kuma bazata zauna dakai ba ka raba tsakaninku ka dawo gida”
“Kai mommy she have preganant,and you know i love her so much”
“Kai kuma ka sani”
Ta kashe wayar tana tsuka.
“Banda taurin kai irinna yaran yanzu,mai zayyi da wata baturiya oho,hakan ma ba musulma ba,Soon zanyi maka aure da wacce nake so,bazaiyiyu yayanta su gaji abinda nakeson ɗoraka akai ba kam”
“Hajiya akawomiki ruwane ki sha”
“Eh kawomin,da saikin tambaya,zamanki gidannan wata biyu yaci kinsan mai nakeso da wadda banaso ai”x
“Kiyi haƙuri Hajiya kai nne sai a hankali na tsufah,yanzu zaki faɗi magana an jima na manta.
Uhm dama inaso na tambayeki zanje ganin jikokina a wajen mamarsu da yamma Hajiya inba damuwa”
“Rose”
“Yeah Hajiya anything else?”
“Ki bawa Yalwa dubu biyar kudin mota zataje dubo jikokinta,
Ke kuma kidawo da wuri,karkiyi irin wancan zuwan ,mtsww wai nima narasa wanda zan dau aikin gogegoge sai tsohuwa,koda yake ba laifi kin iya aiki”
Taba gama faɗin hakan tashige ɗaki tabar Secatariyarta da Baba yalwan.
Naira dubu uku tabawa yalwan maimakon yanda Hajiya tace,sauran ta soke a nata aljihun.
Karba tayi kaman bata gane mai brr Na’imah tace bataba,godiya tayiwa Rose har ƙasa,inda itakuma take mata kallon raini .
Ɗakin masu aikin tashiga ta shirya kafin ta fito,tafiya take zugub zugub har ta iso wata kwana.
Wata dariyar yan duniya tayi tana kiƙƙifta ido wanda basuyi kamada na tsofi ba,dukkuwa da yanda tayi iya ƙoƙarinta wajen yin kwalliyar dazata tauye mata fuska,ka iya duniyanci mutum bai isa ganota ba.
Ta gefen ido take kallon wanda aka saka yafi bayanta,saida ta kula mota tatareshi tayi wuff ta faɗa wani butique.
Banɗaki ta shiga ta wanke fuskarta tareda saka kayanta wanda suke cikin buhun.
Powder da shafa da kuma jan baki,sai bakin glass tada saka.
Fitowa tayi tana taku irin na ƙwararru,a hanya suka bugi juna da wanda aka saka yabi bayanta,sai waige waige take yana neman tsohuwar dayake bibiya.
“Uhm guys baka ganine kana buge lady?”
“Am sorry madam bangani bane”
“Ohk ya wuce”
Dariyah ta sheqe da ita bayan ta tari taxi ta hau.

A bakin ƙofar gidan tayi parking motarta,ta daɗe kafin ta fito ta nufi gidan.
Innayi ce ta amsa mata sallamarta wacce take ta karatu,saboda makarantar jami’ar dazata shiga,wacce Bombee tace zata sakata.
“Innayi ykk ya karatu,ya kuma inna?”
“Lafiya kalau addah Bombee,su Hilyaan da inayah suna ciki,amma Maleekah bata zo ba”
“Meyasa bata zo ba,mun fa haɗu da ita a gida zata taho”
“Uhm naji Hilyaan tana cewa wai zasu tahone da khamees kaman”
“Ohh this girl,tanada rigima sosai,bana hanata biyema Khamees bane,su barni naji da wanda yake kaina ma na hidima”
Dariya innayi tayi,daga nan batace komai ba.
Ɗakin inna tashiga ta gaisheta,tana zaune a kan darduma tana jan carbi.
“Inna barka da yamma ykk,nayi magana da malamin dana ce zan kaiki wajensa,watakila sai a dace a wajensa”
Kama hannun Bombee tayi tareda nuna alamar suje su biyu.
“Ahah inna ke zaki fara zuwa,naki zai iya yin sauki yanzu,amma nawa dole sai nayi bincike gameda wacce tayi aikin,sannan kuma naki yafi wahalarwa fiyeda nawa,barina na tafi inna”
“Kitaaaafi anan wajen,bamason kizo wajennan Ta haramta mana kaiki wajen mahaifiyar ki kifitaaaaa”
Toshe kunnuwanta tayi tana cize baki,saboda yanda kan kemata kamar ana doka mata guduma.
Sakin hannunta tayi ta wuri tabar ɗakin,bayan tasake waigawa ta kalleta,tana son kasancewa da mahaifiyar tata,itama kuma tasan tana son ta ganta a kusada ita.
Sai bayan sun zauna sun kusa minti goma kafin Maleekah suka shigo itada khamees,dukkansu idonsu a ƙasa yake,Lokacin dasuka ga yanda Bombee ke aikamusu kallon tuhuma.
“Mal…….”
Da sauri tazo inda Bombee take ta durƙusa.
“Haba antynah karkice haka mana,wlh ina sonshi kuma kinsan bashida wani mungun hali,ko kowa yaki ke mai auramin shine ai”
“Saboda a matsayina nawa”
“Na matar babban yaya mana,allah nasan kinacewa yah Jabeer yabarni tareda shi ta zauna,shikuwa inya faɗawa abba magana ta kare”
“A ganinki ba,Maleekah har yanzu banida matsayin dazan shiga sha’anin danginku,ko kin manta matsayina ne a gidan uhm?
Har raina soyayyarku da khamees ban ƙita ba,amma babu abinda na tsana irin jawo magana,shiyasa nake taka muku birki kafin abin ya fi ƙarfina.
Yanzu dai ba wannan ba,jiya da daddare kin ƙirani kan cewar Hajiyah zeenah bata yarda da abinda kike faɗa ba mai yasa?”
“Uhm mijinkine sila ba laifina ba,kina bashi kulawa da yawa har ya sanja yaƙara kwarjini da fara’ah,shiyasa Mommah tafara zargin akwai abinda yake faruwa,musamman dayace wai a gidansa yanzu yake cin abinci.tasan kuma Lubnah bata girki,shikuma bayason cin na ƴan aiki,shiyasa tafara zargin akwai abinda yake faruwa.
Naji kuma waya da maman Jawaheer kan cewa an samu ƴar aikin dazatayi aiki a sashen,ta yanda zata dunga kawo musu abinda yake faruwa”
Aikinki yayi kyau,Hilyaan fah mai yake gudana a barrak.
“Nothing important,naji dai Gen nacewa shirin daya daɗe yana jiran zuwansa ya rushe,da alama Jabeer bazai halarci meeting ɗin ba,dan haka sun ɗaga shi sai next month”
Dariyah Bombee tayi tareda cewa.
“Uhm kawai ƴar ƙaramar rashin lafiya na haɗa yayi da daddare,shine kawai”
Zaro ido sukayi suna kallonta,musamman ma Maleekah.
“Oh kawai na saka masa grape(inibi)a cikin jus,kuma dama yanada allergy dashi,sai yasakashi night fever da kuma small rash.
Amma naji da komai he is normal now”
“Amma anty Maryam meyasa,muma munsan bayason grape sosai”
“Amma nibai faɗamin bayaso ba,da alama bayaso nasani,shiyasa nayi amfani da hakan na ceceshi.
Mai kike tunanin zai faru inya halarci meeting ɗin,zai rasa kunerarsa a ranar ne,shine abin gen abdu manga ya shirya,tunda basusan muna da takardun Alhaji Abdullahi ba ballantana su dakata.
Inaya fah mai ya faru?”
Tun ɗazu take zaune bata ce komai ba,saida aka zo kanta kafin tayi gyaran murya dan lumshe ido.
“Eh to maganar gaskiya ba gen abdu manga ne zai hau kujerar ba yanda kuke tunani,dan haka aikin Hilyaan ya ƙare na bibiyar Sa a barrack..”
“Mai kike nufi da hakan Inayah?”
“Barr Na’imah itake kalmasa koma daga gida,ganin mijinta bazai mata yanda take so ba,yasa ta yanke shawarar ɗora babban ɗanta waro Ammar.
Wanda ya tare a ƙasar England da matarsa juliet,yanzu haka tana ciki,kuma suna shirin dawowa nigeria saboda yazo yazama CEO yanda ta tsara”
Abinda Inayah tafaɗa gabaɗaya yabasu mamaki,inda basu saka Inayah tajiyo ba da bazasu san barr Na’imah ce ke komai ba.
“Okay Hakane abin,dama nazargi haka,amma ban taba tunanin tsanar da tayiwa ɗannata kaɗan bace sai yau,wato yanzu ta nemeshi tunda zai mat amfani.
Zanga kuwa ta yanda zai zama CEO ɗin inanan.
Mungama meeting daga nan,sabuwar haɗuwa kuma sai nan da bayan zuwan Amarenmu.
Saboda nasan dukkansu zasuyi ƙasa da makamansu saboda zuwan bikin,muma mu huta haka.”

“Wayyo jikina,wayyo bayana ku taimaka min yana ƙaiƙayi,wayyo zan mutu zan mutu nace”
Duk ihun da Inna laari take babu wanda ya jita,tana ɗakinta a ɗaure da sarƙoƙi.
Gaba ɗaya halittun jikinta sun sanja kamanni,babu wanda zai ganta ya ganeta a yanda take.
Wasu irin ƙuraje sun yayyame jikinta,da fuskarta ta jirkice.
Kurajen sunyi jawur saboda yanda take durja jikinta a duk inda ta samu.
“Nace kuzo ku taimakeni,Zilliyah ta cuceni bayan nayi ta bauta mata shine ta gudu ta barni.
Itace fah nabawa ɗan Danejo jaririnnan taba wa aljanunta suka cinye,nasa ta sakawa Bombee shaɗanu,wanda suke zukata da yi rashin mutunci ta daina tausayin iyayenta da daina sonsu,sannan kuma ta daina tsoron kowa a duniyah.
Nice nan laari nayi komai da komai.
Nina makanta Danejo na kumantata,nasa likita yace ciwone yayi mata haka duk fah nice nayi komai da komai.
Tunda na faɗamuku ku dawomin da ƴata Innayi nah innayi nah.
Nasan idan na kaiwa zilliyah ita ta aurawa ɗan ta,to zata warkar dani nakoma yanda nake,har kashemin Danejo zatayi itada zuri’arta,sanadin ta duk na shiga wannan halin nasan”
Mlm Ahmadu wanda yake bakin windownta yana jin abinda ta faɗa,share hawayen idonsa yayi tareda wurga mata Sinƙin biredin dayake hannunsa.
Tana ganinsa kuwa takaimasa wawura kaman dabba,haka da ledar ta dunga ci saida ta cinyeshi tasss .
Barin wajen yayi dan bazai iya jure ganinta haka ba sam.
Inhar abinda ta faɗa gaskiya ne,to kuwa bashida idon dazai kalli iyalannasa ba wanda suka shiga duniya.

Ke duniya…….!!!!

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button