Bakar Ayah Book 2

Bakar Ayah Book 2 Page 35-36

Sponsored Links

Page 🖤35••36🖤

 

Bayan meeting ɗin da sukayi ba ita ta dawo gida ba sai wajen magriba.

Tana zuwa kayan jikinta tarage,nan da nan ta hau haɗa abinci.

‘Wani Lokacin tana mamakin kanta yanda ta damu da rayuwar Jabeer,abinda bata taba yiwa wani ba kenan,ko kai saboda aljanun kanta basa kulawa da tsakaninta da shine kai,shiyasa take jin bond din tsakaninsu yana ƙara tasiri a jikinta.

Tana cikin zurfin tunanin taji ƙarar rufe ƙofah.

“Uhmm ɗazu nazo bakya nan,meyasa in zaki fina bakya sanar dani inda zaki uhm?

Ko so kike kema ki zama iri ɗaya Lubnah akan haka”

“Ba maraba akan hakn,amma kuma akwai banbanci,inda da buƙatar tambayar ma to Hajiya zeenah zan tambaya bakai ba”

“Meyasa ita take aurenki?”

“Wani abu mai kama da hakan dai”

Ganin yanda take amsa masa maganar yasa ya rabu da ita ya watso ruwa ya tafi masallaci.

Lokacin daya dawo ta kammala abinci ta saka a dining,zama yayi ta zuba masa yaci ya ƙoshi kafin ya sake ficewa.

Koda babu biyayya irin yanda yake son macen dazayyi rayuwa da ita ta kasance,amma kuma badai kulawa da cikinsa ba kam,da kuma kayansa da ɗakinsa.

Dan har ya zauna yaci abincin tana ta danne danne a system bata cemasa ƙala ba,yakula akwai abinda yake ranta,dan haka ya fita yabata waje..

Ƙarfe goma ya dawo gidan ya shiga ɗakinta.

Tana kwance daga ita sai wata riga iya gwiwa,wacce ta ɗage saboda kwanciyah,haidar kuma yana cikin gadonsa na yara a gaban gadonnata.

Tunda ya ɗora idanunwansa akan cinyoyinta ya gagara ɗaukewa,abinda ya taru masa tsawon lokaci ne yafara koƙarin taso masa.

A hankali yafara takawa har zuwa inda take kwancen,a bakin gadon ya zauna tareda kaiwa hannunsa kan cinyarta..

Duk da yanda ƙwaƙwalwarsa keson hanashi,amma kuma zuciyarsa tana muradin hakan,kuma tafi da hannayensa.

Cikin sanyi yake shafa duk inda rigar ta bayyana,vai ankaraba yaji caraf Bombee ta tashi tareda riƙe hannunsa,hakan da tayi ne yasa ya faɗa jikinta suka koma kan gadon..

Kallon idonsa take shima yana kallon nata,gashi duk ya bada ƙarfinsa akan ta.

Tana ƙoƙarin tureshi daga kanta shikuma yasamu damar haɗe harshensu waje guda.

Yadaɗe yana sarrafa harshennata batayi yinƙurin hanashi ba,saida taji yana shirin wuce gona da irine ta hanyar son rabata da rigarta yasata ta zame jikinta.

Numfashi yake sauƙarwa mai ƙarfin gaske yana ƙoƙarin saita kansa.

“Please…..mmmmaryam help me please”

Jijjiga kai tafarayi tareda yin magana cikin karyayyiyar murya,wacce take nuna tsantsar tausayinsa.

“Kayi hakuri Jabeer amma bazan iya ba sam,hakan zai karyamin plan dayawa idan nayi”

“Saboda kin tsaneni shiyasa bazaki bani kanki ba,ina buƙatar taimakonki a yanzu maryam a matsayina na mijinki,bakya ganin lokacin da muka ɗauka bai…….”

“Badan na tsaneka bane Jabeer ko kuma dan bana tausayinka,inda inada ikon baka wannan taimakon zan baka kaman yanda na yi maka sauran abubuwa.

Bazan iya baka kaina ba alhali bansan matsayar aurena ba a gareka”

“Kamanya,kina nufin zan sakeki idan na kwanta dake,ko kuma na juyamiki baya,bahaka nake ba maryam”

“Nasan ba haka kake ba,hasalima ba wannan dalilinne suka sakani hanaka kaina ba.

Jabeer aurena dakai yarjejeniya ne na tsawon wata shida wanda mukayi da mahaifiyar ka,banda na maidashi na shekara guda da yanzu saurana wata guda na bar gidannan,yanzu haka ma tana kan bakarta dana gama mata aikinta kowanne lokaci zan bar gidannan..

Dan haka banason ka saka ranka akan macen da koyaushe zata iya tafiya,tunda matarka ta ƙaurace maka,kayi haƙurin sati biyu mata biyu russ za’a baka.

Amma ni tamkar mafarki ce,duk yanda zaka tsaya a ciki dole zaka buƙaci farkawa,dan haka ina taimakonka ne ka farka kafin lokaci ya kure maka”

“Hmmm duk naji bayaninki,nasan bazai wuce saboda kina da zafin zuciya zakiiya korar Lubnah,shiyasa ta auroki,wannan dalilinne kenan kullum take gargaɗina dana nisanceki badan zaki cutar dani ba saidan itake buƙatar hakan.

Nikuma zan nuna miki cewar dasannu zaki zama mallakina Maryam,duk da bansan mai nakeji a kanki ba,amma kuma zuciyata tana bani bazan jure rashinki a cikin gidana ba”

“Wannan duk maganar zuciyarka ce,amma a yau idan Hajiya zeenah taga dama zata iya raba aure mu,abu ɗayane zai hanata yi shine tasan bazan yadda ba,saboda contarct ɗin mu bai ƙareba”

“Shikenan zanyi ƙoƙarin yin nesa dake har saina jaddada matsayin aurena dake Maryam,abu ɗaya nake so koyimin,shine ki yi ƙoƙarin kar mommah ta soke contract ɗin dake tsakaninku”

Ɗaga masa kai Bombee tayi alamar ta yarda,daga nan yadafa yafita daga ɗakin.

Da kallon tausayi Bombee tabishi kafin ta gyara kwanciyarta badan don bacci zaizo ba.

“Kabani lokaci Jabeer kafin nayi tunanin zama dakai ko akasin haka,amma ita kanta mahaifiyar ka saidai kayi haƙuri,amma in shirina yazo kanta bazan ragamata ba sam”

 

 

“Mommy kina ganin zan haska a bikinnan kuwa yanda ya kamata?”

Jawaheer tafada tana dudduba uban lallen da ake zana mata,duk wanda yaganta daƙyar zai ganeta,yanda tasha uban gyara da kuma kwalliyah..

Yaune za’ayi bridal shower,duk da cewar uban gayyar yace babu wani event da zayyi,su dama gidan su Jaleelah mahaifinta bayason wasu bidi’o’i a biki.

“Ƙwarai ma kuwa dear,kinyi kyau fiyeda yanda kike tunani,ina mai tabbatar miki idan ya ganki sai ya rasa tunanin sa”

Murmushin jin daɗi tayi jin abinda mahaifiyar tata ta faɗa,gobene ɗaurin aure,bayan an ɗaura zasu je gidan su na kwana biyu,daga nan su wuce honeymoon na Wata guda,kowaccensu zata samu sati biyu,zayyi sati biyu da Jaleelah sannan yayi sati biyu ma da Jawaheer a ƙasashe daban daban.

A bangaren Jaleelah ma ado na musamman danginnata sukeyimata,na gargajiya mai ratsa jiki,duk wanda ya ganta saiya sake,yanda fatarta tayi sharr da ita tamkar tuffah.

“Wlh fadeelah banason magungunan da Inna take sakani sha,ina tsoron fah kada a samu matsala kafin a gama bikinnan”

“Wacce irin matsala,babu abinda zai faru,keda zaki ɗaga dubai kisha amarcinki”

“Uhm ina son zuwa Kam amma fah kinsan bata yanda raina yakeso zanje ba”

“Kibar maganar nan haka kada tayi nisa,kar wani yashigo,muje na rakaki ki wanke lallen kada ya dame.

Ya kiraki ne Mutumin akan zancen sallamar ƙawaye?”

“Uhm munyi waya dashi dasafe,karkiji yanda yake tayimin zumuɗin ya ƙosa na zamo mallakinsa,yanaji dani sosai fa.

Batun sallama kuma kada ki damu kinsan zai baku sosai.

Kikace da yamma makarantarmu zasuyimin walima koh?”

“Uhm zasu haɗa walima,aikin cancanta suyimiki abinda yafi walima ma Hafiza Jaleelah”

Dariya sukayi a tare jin abinda Fareeda ta faɗa.

 

 

“Wai ka warke amma har yanzu naga baka shirin tafiyah sashenka,yau anyi sati biyu kusan.

Koda yake manene na damun kaina,ana kawo maka amarenka ai bazan ganka ba daga nan”

“Haka kike tunani,saidai in baki nemeni ba zaki ganni,bana manta Alkhairi ballanta irin wanda kikayimin.

Ohh tsayah wai kina nufin bazakiyi kewata ba inna tafi”

Ƙarisa saka sarƙar tayi tareda zaran gyalenta zata fita waje.

“Uhm kanka ake ji nina siyayya”

“Amaren zaki yiwa?”

“Saboda kaika bani kuɗin uhm?”

Dariyah Jabeer tareda sake komawa ya kwanta akan gadon nata,aikuwa fass haidar ya mari fusakrsa wanda yake zaune akan gadon.

“Maryam da alama ɗannnan naki shima ke ya iyo,kiga marin dayayimin”

“Ahah ba yanda za’ayi ya iyo ni,inaga ubansa ya ɗauko wataƙila”

Jimm yayi jin abinda Bombee tafaɗa.

“Akwai abubuwa da dama a rayuwarki wanda suke binne a ranki,shin a matsayina na mijin dakike aure bazaki faɗamin yanda kika samu yaronnan ba,duk da cewar alama dayawa suna son nuna asalin yaron bashida kyau,amma kuma zuciyata ta kasa yarda da hakan,kaman yanda takasa yarda da cewar cutarwa kikeson yi a gareni.

Sannan tawani bangaren inajin kaman kusanci tsakanina da yaronki”

“Kayi hakuri amma kozan faɗa maka menene asalin yaronnan badai yanzu ba,sannan inaga zaman dakayi dashine a kusa yasa kaji hakan,amma inkana ganin bakason ɗana bance kasoshi ba,babu wanda na tilastawa ya kalli dana a fuskar so ,tunda ina son abuna ya wadatar.

Batun aure kuma zuwa yanzu kasan matsayin aurenka a wajena,dan haka babu zancen boye boye a ciki,ni ma tafiyace,kowanne lokaci zan iya barin gidannan nan da wasu watanni shida masu zuwa”

“Abinda kike faɗa bazai dameni ba maryam,Saki a hannuna yake ina?”

“Kuma za’a iya saka ka kayishi koyaushe ba?”

Shuru yayi bashida tacewa har ta dauki ɗanta da jakarta tafita.

 

Har takusa shiga mota saikuma ta hango matar da aka kawo leƙen asiri tana leƙa windowanta.

Komawa tayi inda take tsaye tace.

“Ke mekike anan wajen,abinda aka turoki kiyi kenan?”

“Uhm Hajiya Maryam barka da fitowa,naga na gama aikin aka banine,shine nakeson na tambaya koda aikin dazan yi miki”

“Miye sunan ki?”

“Uhm Sunana Zaleeha hajiya”

“Toh Zaleeha (kallon mamaki tayiwa Bombee ganin takira sunanta kai tsaye batareda sakayawa dukkuwa da ta haifeta)

……miye kike yimin wannan kallon zatonki zance Inna ko kuma baba,uwata ce ke komai,kicire wannan a ranki,bana wannan shishshigin,ki nutsu kiji abinda zan faɗamiki.

Karki sake koda wasa ki tsallake layin dana shata tsakanina dake,kiyi aikin da ita uwar mai wajen tabaki,inkinga dama ko numfashi nayi kije ki sanarmata bai dameni ba,saboda kaff gidannan ba wanda nake tsoro.

Amma kika kuskura na kamaki kina shiga lamarina saina sanjamiki kamanni,ba ruwana da tsufanki”

Tunda Bombee tafara balbalamata masifah kanta yake sunkuye bata ɗaga ba,har saida tagama dan kanta ta tafi.

Sai bayan tashiga mota tatafi kafin Zaleeha tabi motar da kallo tareda yin wani shu’umin murmushi.

“Hmm yarinya kenan,kina tunanin zanyi wani abun dazan bar kusada abin farautana yake,da sannu zaku zo hannu na dakake har su innayin,kuɗin mallakina ne,jininku fansa ne gareni nida aljanuna,anriga an bani,kijira yanda zan wargaza rayuwar daga no kina ginawa mai ɗauke da haske a cikinta”

 

Tun Bombee bata shagon dataje siyyaya ba taji wayarta na ƙara a jakarta.

Fitowa da ita tayi ta kalli sunan Hajiya zeenah a jiki,ɗagawa tayi domin jin mai zatace mata.

“Hello Hajiya zeenatu ya akayi?”

“Uhm tunda kika samu part kike zuba fantamawarki banganki ba,zan turo miki address kizo zamuyi tattaunawa gameda aikinda kikemin”

Tana sauƙar da wayar taga address ɗin gidan Hajiya rabi,dariya tayi tareda nufar gidan dasu innayi suke..

Sharp sharp ta sanja kayanta zuwa wasu masu mungun kyau a cikin waɗanda ta siya,A wajen Hilyaan tabar haidar ta nufi gidan,domin zai bata mata budget idan ta tafi dashi.

Riga da wando ne kayan na sai farin kimono data ɗora akai,bakin farin glass tasaka tsanrparent mutun ba ganin blue iris ɗinta,bakin takalmi tasaka hight heel mai matuƙar tsini,sai jaka ƙarama mai adon fari da baƙi.

Gidan a cike yake da mutane kasancewar gobe ɗaurin aure,duk inda ta keta kallo ake binta dashi harta shiga falon Hajiya rabin,daga gani private falor don ba kowa a ciki sai su biyu..

Fararen kujerune a ciki kawai da TV da Fridge ƙarami.

Ko sallama.

Kafin tashigo ɗin da Jawaheer ta haɗu,wacce har yellow take saboda Gyaran data sha.

“Bride to be zan iya sanin inda iyayenki suke?”

“Ke kuma mai kike a gidannan yanzu,ko baƙin ciki kike zan zama matarsa ke kuma aikinki ya ƙare zakiyi waje?.

Samun gu naga har kuɗinsa kike ɗauka kina facaka dashi koh?”

“Ba wannan na tambayeki ba,tambaya nayi ina uwarki take,ta buƙaci ganina idan kuma har na zuwa to ba wanda ya isa yasani dawowa”

“Kut harke wacece dazaki dunga yin magana da mommy haka”

“Ishashshiya ce,wacce ta isa ita uwar taki wacece daba za’ayi magana da ita haka ba iyee ko uwatace kai”

Mari Jawaheer takaiwa Bombee,a tunanin ta ai gidansu ne babu abinda zata iya,tun kafin takai hannunta Bombee takifeta da nata marin saida ta hantsila.

Cikin ƙanƙanin Lokaci har shatun hannunta ya fito a fuskarta.

Duk abinda suke akan idon Hajiya rabi wacce fitowarta kenan jin hayaniyar Bombee da Jawaheer.

“Innalillahi yauni naga fitsararriyar yarinya,yanzu ƴar tawa kika sheƙawa wannan marin har cikin gidana?”

“Ko zaki rama mata ne kai,ina ruwana da ƴar taji toh,ki koya mata tarbiyya idan bakyaso ta sha wuya intazo sashena. Hadda tadaina shiga abinda bai shafeta ba zaki nuna mata”

“Shigo muna son magana dake,yau za’ayita ta ƙare ma”

Babu ko ɗar kuwa Bombee tabi bayan Hajiya rabi hankalin ta kwance,bayan ta watsawa Jawaheer kallo wacce take dafe da kuncinta masu aikinta sun tafi da ita.

Kujera ta nufa a falon ta zauna tareda ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Inda harara tana kisa da Bombee ta mutu sau ba adadi a wajen su Hajiya zeenah.

Tissue paper ta ɗauka a gefen kujerar ta goge hannunta tareda cewa.

“Mtsww waccar ƴar taki ta ahafamin wannan yellown abun a hannuna,daga ji ma ƙarni yake,wai a hakan kuma za’a kaita wajen miji,ohhh Jabeer kaga taikanka kaikam”

“To nunamin Kinibibi irin naku na ƴan bariki,kinaso kice ba’a kyautamasa ba komai,kinada wannan huruminne a matsayinki na bare”

“Banida shida mai ɗa,dadinta dai nima inada ɗan ba juya bace,sai kiyiwa matar ɗanki wannan maganar baniba.

Back to business meyasa kuka kirani wajenanan,inda abinyi na kasheshi in bakuda tacewa zanyi gaba”

“Batun contract ɗin da nayi dake sauran wata ɗaya da satuka ya ƙare,inaso ki gaggauta fitarda Lubnah daga cikin gidan ɗana kafin Jawaheer ta dawo daga honeymoon,daga nan kuma kema na sallameki ki tafi kamar yanda mukayi”

“Idan naƙi yin hakan kuma fah”

“Zaki dawomin da ƙudaɗena a yanzunnan ki tafi nafasa aikin”

“Hhhhhh Hajiya zeenah kenan,kin manta na maida contract ɗinmu shekara guda,kuma kin yadda da hakan,sannan kuma a shirin mu babu zancen janyewa daga gareki.

Mai kika maidani bansan mai nake ba?”

“Kinyi kusan wata biyar a gidana,amma har yanzu babu wani yunƙuri dakikayi akan Lubnah,kina nufin kicemin bazaki tafiba ne komai,wai tukunna ma mai kike shiryawa wanda ban saniba.”

“Dama to menene abuna da kik sani bayan labarin da Umaruje ya faɗamiki,kuma nina sakashi faɗamuku labarin,ba ra’ayin kansa bane,da ban sakashi ba babu abinda zaku sani gameda ni.

Hajiya ta wani gun bake kaɗai kika nemeni ba,nima na nemeki dana gane mai kikeso namiki,dan haka maganar tafiyata bata hannunki tana hannuna.”

“Baki isa ba toh,yau innaga dama zansa ya sakeki”

“Nikuma na saceshi na sace amaren ma,ke harkema na daukeki na kaiki dajin dakika ratsa kika shiga inda nake,inna ɗaureki ko ihu bazaki iya sakewa ba harki mutu.

Saiki zaba,nina tafi saina jiki sweet in law ta”

Maida glass ɗinta tayi tana murmushi tabarsu a zaune Sukuti kaman gumakai.

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button