Bakar Ayah Book 2

Bakar Ayah Book 2 Page 49-50

Sponsored Links

Page 🖤 49••50🖤

 

Rawa jikinsu ya fara suna neman abinda zasu tare jikinsu dashi.
Duk abinda suke bombee tana kallonsu daga inda ta jijgina
“Miye kuke wani karkarwa,ohh da bakusan ba daidai kuke aikatawa ba sai yanzu,ai bakuji komai bama tukunna sai kunji wanene yaganku a haka yanzu.
Mijinku yazo yana murna da farincikin faɗawa masoyiyarsa ya warke,gashi ya dawo gareta,amma mai zai tarar,a kwance yaganta da fitsara da kishiyarta,wato ɗaya matar tasa,shin idan kune wanne hali zaku shiga in kuka ga haka….?”
Shuru sukayi suna saurarenta,zuwa yanzu kowa ta samu towel ta ɗaura a jikinta,wayarta ta danna,can saiga hilyan tashigo ɗakin.
“Kinzo da bulalar?”
“Eh nazo ta ita,gata ma a hannuna,mai suka sata haka? Rabonki dayin amfani da ita kin daɗe sai yau”
“Ba surutu na tsayayi ba anan wajen,na turawa security da khmees kan su bi bayansa nizan tafi naga mai yake faruwa.
Ki tabbatar kinwa ko waccensu bulala ɗari ɗari,bayan sun gama su gyara kaff ilahirin part ɗinnan gabaɗaya,idan suka gama su wankemin kayana gabaɗaya,daga nan kuma zan faɗi abinda zasuyi gaba.”
Har zata fita ta dawo ta kallesu,wanda idonsu ya raina fata.
“Jawaheer ce ta samu ƙarfin halin cewar”
“Mai kike nufi?”
“Bayi bayi kuka zama,da mai kuke tunani sai kawai naje nace ga abinda kukayi,ahah ahah wannan bazai faruba,ni dama na daɗe da sanin abinda kuke,hatta kadarorinku da su asusun bnakinku na sirri duk nasani,sannan kaff sashenku a cike yake dam da camerori wanda sukeyimin record na abinda kuke aikawa.
To ko iya haka na barku kunsan kuna hannuna,laifinku na cin amanar mijinku da sakashi cikin wani yanayi zaku girba.
Hilyan ki cika aikinki,sannan kibasu takardun dukka dukiyoyin da suka tara harda na banki suyimin sign kafin na dawo,duk kuma wacce ta kuskura ta saka ƙafa tabar gidannan batareda izinina ba,hmmmm ta kaɗe har ganye,sannan kuma yana gareku ku bari danginku su ɗau matakin abinda zanyi muku,a ranar zan shaida musu mai kuke.
Hilyan a cigaba da gashi”
Ƙirane ya shigo wayarta,dan haka da sauri ta fita tana magana.
“Me kun bishi baku ganshi ba har yanzu?”
“Ehhh har yanzu fah madam bamu ganshi ba,saidai cctv cameran da muka bi ya nuna cewar hanyar barin gari yabi”
Kashe wayar tayi tareda dannawa khmees ƙira,shima dai har yanzu dai babu wata kafa.
Duba lokaci tayi har an kusa yin la’asar,daga inda take tsaye a falonta tana jiyo ihun su Jawaheer waɗanda suke cin kakarsu a hannun matashiyar sojan.
Ɗakinta ta nufah ta ɗauko wasu takardu ta nufi sashen Hajiyah Zeenah.
Tundaga bakin falon take jiyo maganarsu da kuma ƙarar cokala.
A zaune suke a dinning tunda ga kan alhj aliyu har dasu Abdulmaleek,kasancewar yau juma’a dama tare suke cin abinci idan an saƙƙo a masallaci.
Ƙare musu kallo tayi na takaici kafin ta nufi wajen dinning ɗin ko sallama babu.
Gaban Hajiyah Zeenah taje tayi dire mata takardun dasuke hannunta..
“Sign”
Ta wulla mata biro tana kallonta,itama Hajiyah Zeenah kallon bombee take cikeda mamaki.
“Baki gane takardun bane ko kuma nayi miki bayani tukunna”
“Amma…….”
“Nagama miki aikinki,in baki yarda ba kije sashenta ki ganta da idonki,nice nan nayi kidnapping ɗinta dama bakowa ba,dan haka gatacan na dawo da ita sashenta.
Ɗaiɗaita rayuwarta kikasakani nayi tayanda zata buƙaci saki daga wajen ɗanki da kanta,yanzu ba iya wannan nayi ba,harda karya asirin datayimsa nayi.
Dan haka nina gama aikina a wannan gidan da a waje yakeda kyau amma cikinsa kurkune..
Kin haɗa familynki kuna cin abinci cikin kwanciyar hankali,batareda kinsan inda babban ɗannaki yake ba tun safe,ni kuwa anya ma kece uwarsa? Da alama bakya neman inda yake sai zakiyimasa aure ko kuma zai kulamiki da dukiyar gidan.
Nizan tafi daga nan,mun gama aiki dake tunda na cika aiki,jan jira idan kika samo ɗanki daya fita daga gida dun sassafe a zauce sai ki tambayeshi ya sakeni,inkuma takaicin duniya ya kasheshi matan dakika auramasa kuma sai nayi takaba..
Ga waɗannan takardun(ta faɗa tana sake wulla mata wasu takardun)
“Share ne na Companyn ku dayake hannun brr na’imah,wacce ta daɗe tana shiri na karbar sa daga hannunku,nasakata ta fanshesu da ƴaƴan ta.
Ba iya ita kaɗaiba a kwai sauran mutane irinta masu son Companyn,ni yanzu zan tafi ga nawa iyalan sun jirana,ruwanku ku ɗau matakin da kuma nemo halinda ɗanku yake ciki”
Wani kallo tabi dukkan table ɗin dashi kafin tafita daga cikin falon a zuciye.
Yanda kasan ruwa yazo ya cinye falon haka sukayi.
Dan jin maganganun bombee sukayi kaman a mafarki,lokaci ɗaya kuma suka fara ƙoƙarin yadda zasuyi.
Hajiyah Zeenah kuwa wacce takula da hankalin su yabar kanta,ɗakinta ta wuce da sauri tana yarfe gumin dayake zubo mata,shikenan bombee ta gama da ita a cikin iyalanta,yanzu kowa yasan abinda ta aikata,dama kuwa saida alhj Aliyu ya faɗamata cewar zatayi nadamar kawo bombee cikin gidanta.

A bangaren uwar gayyar kuwa direct gidan malamin ta nufa inda mahaifiyar ta take.
A zaune taka akan gado wata mata tana bata shayi a baki,gefenta kuma Inayah ce da innayi suna riƙe da hannayenta ta kowanne bangare.
Tsaida kallonta tayi akan ƙofar inda bombee take tsaye,kana ganin kallon kasan ta dade batayi ba,saidai ta alama tagane ƴar tata sosai.
Hawayene yake zubowa akan kumatun bombee,sai yau tasamu hawayen ta suka zubo,bayan wasu shekaru dasuka shuɗe an hanata sakinsu daga jikinta..
Zubewa tayi a gaban innar tata cikin karayar zuciya,kanta ta ɗora a cinyarta,take kuwa tafara rabzar kuka kaman anyi mata saqon mutuwa,saidai kanajin kukan kasan irin wanda mutum ya daɗe yana tarawa ne.
Ganin hakanne yasa su Inayah da matar da take bata abincin barin ɗakin da sauri,domin su bawa ƴar da uwar waje.
Saida inna Danejo ta barta tasha kukanta kafin ta ɗora hannunta akan bayanta tana bubbugawa.
“Bbb…….bommbeee”
Tafaɗa a hankali cikin ƙaramar murya,kamar mai son koyon magana.
“Inna inna ta kin ƙira sunana innata”
Ɗagowa tayi da fuskar shabe shabe da hawaye tanayiwa inna Danejo dariyah..
Hannu tasaka tana share mata hawayen tareda girgiza kai,alamar ta daina kukan..
“Idan bakyaso na daina bazan sake ba,ya jikinnaki bakyajin wani ciwo koh?”
“Babu abinda nakeji bombee……..kawai kawai bansaba ne ba dayin amfani da wasu wuraren”
“Zaki saba a sannu inna,komai zai wuce kamar bai faruba,duk wanda yace zai sake tabaki bazan barshi ba kowaye inna”
“Uhm naji,to kinci abinci yanzun,an sameshi mijinnaki?”
Jimm bombee tayi jin tambayar da ta aikamata,a ranta tana ƙiran sunan Inayah,tasan ita tafaɗamata mai yake faruwa.
“Ahah ba’a ganshi ba,karki damu inna zasu ganshi na gama abinda yasani zama dashi,yanzu babu komai tsanina dashi”
“Amm…..”
“Inna yakamata ki huta,yanzu kika tashi bai kamata ki dunga damun kanki ba har haka ”
Zama tayi a wajen tana kallonta,har saida ta koma baccin kafin tabar ɗakin..
Falo takoma inda su Inayah suke zaune.
“Yah innan take?”
Innayi ta tambaya cikeda zumuɗi.
“Ta yi bacci kafin na fito”
“Yah Jabeer ɗin kuwa an sameshi,yansu maleekah ma taƙirmu wai gatanan zuwa,da alama bata sani ba sai yanzu”
“Uhm dukka basu sani ba gidan,saida zan fito na faɗamusu,ki daina yimin zancensa haka,yanzu dai kawomin abinci naci nayi wanka kafin na faɗa..
Inna gama shiryawa zamu yiwa malam godiya mu tafi gida”
A cewarta ta rabu da sha’aninsu,amma lokaci zuwa lokaci sai duba waya take,domin ganin ko an ƙirata.
Duk abinda take a cikin motar kowa na kulada ita har suka isa gida.
Har suka isa gida dare yafari amma babu labarin Jabeer ba ɗuriyarsa,ƙiran waya daga wajenta tayi recieving sunfi sau a ƙirga.
A gidansu Jabeer kuwa duk sun taru a falon sayyada-tateen,kowa yayi jugum da abinda yake tunani.
Takaicin ɗaya ma yanda iyab sayyada ta cika musu kunne da surutu.
“Ohh ni sayyada ina jabeeru yashi ga a garinnan haka,anyi nema har angode Allah?”
“Hmmm nifa nafi zargin Wannan matar tasace ta ɗaukeshi,ba tace ita taɗauke lubnah bama,kuga fah irin azabar data ganawa sauran matan ma,duk yanda akayi dasu su fito daga ƙofar akaisu asibiti sunƙi wai ta hanasu fita?
Saida kuma ya bata lokaci guda ta ɗauke ƙafarta tabar gidan”
Lailah ce tayi maganar wanda suke zaune kujera ɗaya da Madeenah a falon.
Duk falon shuru akayi ana jin maganar Lailah,da alama kuma wasu dayawa a falon sun fara gasgata maganar tata,musamman duba da yanda ta zuba musu tujara ɗazu.
“Haba anty Lailah,wlh anty maryam bazata sace yah Jabeer ba,wannan wanne irin zancene?”
“Ke dallah rufemin baki,yanzu haka wani abun take baki a sashenta ta shanyeki kema,gashinan ta sakaki kina kaimata rohoton duk abinda yake faruwa a gidannan.
Ni wlh nafara yarda da zancen anty Lailah”
Madeenah ce tayi maganar tana hararar maleekah,yayinda ita kuma take kallon Lailah,jitake kamar ta tona mata asirin abinda take,amma tasan inta faɗa a yanzu batada hujja.
Tashi tayi daga falon ta nufi sashensu,dan tasan duk tarom da akayi a wajen babu abinda yake tsinanawa Jabeer ɗin,ƙarshema Lailah wata dama tasamu a wajen na yaɗa manufarta.
Ƙiran bombee tayi tashaida mata abinda ake a gidan,daga baya kuma tayi ta roƙonta akan ta dawo,saidai har sannan babu wata tsayayyar makafa.
“Dan allah anty maryam kidawo,nasan idan sunga dawowarki zasu daina yimiki wannan zargin,amma idan har kika tafi a yanzu za’a ce da hannunki a batansa”
“Ohh saboda ba’aga fitarsa ba kome,to duk mai cewa na dawoɗin kada ya fasa”
“Kiyi haƙuri amma gobe zanzo gidan,kema nasan kinaso ki dawo anty Maryam”

Tana cikin cin abinci taji falon yayi tsitt,kowa ita yake kallo,ganin yanda take zuba abincin kaman magani. Duk da cewar taki yarda amma duk wanda yakalleta yasan tana cikin damuwa,wanda duk bazai rasa nasaba da bacewar mijinnata ba yau kwana guda.
Jiyama da daddaren hanya ta sanɗa tafita da mota,amma haka ta dawo batareda sanin inda yake ba.
Tunda tatashi har yanzu babu wanda tayiwa magana bayan gaisawar da sukayi da inna Danejo.
Maleekah ma data fito tana kallonta amma batayimata magana ba,kaman bata santa ba.
“Maryam inkin gama cin abincin inason yin magana dake….kafin sannan ke innayi haɗo mata kayanta ta tafi yau zata koma gidanta”
“Amma inna bakiji mai maleekah ta faɗa bane,duk abinda nayimasa wai zargina suke da saceshi”
“Uhm suda suke zarginki shiya zargeki,koda shiya zargeki ai badan shi zakiyiba saidan wanda ya baki umarnin yi. Balanta mijinki a yanzu yana buƙatar komawar ki gidanki,dan haka kishirya ki tafi gidanki,dama tunda dan banida ikon cewa komaine lokacin dakikace wai auren wucin gadi kikayi,da kinsani bazan barki ba sam.
Aure ba abin wasa bane dazaki sakashi lokacin dakika ga dama kuma daga baya ki cireshi.
Sannan banda kin maida mutane shakatafi zatonki waye baisan abinda kike ba,kowa yaganki yaga damuwa ƙarara a fuskarki dason sa a idonki,kawai taurin kai ne yahanaki rungumar hakan.
Indan tani kika ƙi komawa ma to ki manta,dan nan da sati guda wajen nawa mijin zankoma tunda na warke,niba kebace mai juyawa miji baya”
Zumburo baki bombee tayi tareda sunkuyar dakai tana kallon kwanon abincin,ai shikenan kuma yanzu babu freedom.
“Ehh inna wai kina nufin gembu zaki koma?,ai basai kin je ba,nanda jibi ma baba suna tahowa shida muruje,na turamusu kuɗin motama tun a jiyan”
“Ya taho kuma? addah laari fah?”
“Har yanzu baki daina maganar ta,ita kam ai ta daɗe a ƙyauyensu tuntuni,a can take wai ƴan uwanta suna mata magani”
Takarisa maganar irin bata dame taba.
Hannu inna Danejo ta miƙawa bombee tareda cewa.
“Kinci gidanku nan,wai yaushe zakiyi hankali ne kina babba,nakula babu abinda kika koya a wannan shekarun sai yanda zaki kama wancan ki yiwa wancan barazana koh?”
“Ohh inna to shikenan naji ki daina wannan faɗan kada ki samu matsala mana,Naji zan koma amma dole sai an sameshi tukunna inna,idan ba’a ganshi ba babu amfanin komawa ta.
Yanzu dai ke ishashshiya kinyi nasara,saiki tashi mutafi ko na ɗauko kayan haidar a gida na dawo”
Taƙarisa maganar tana hararar maleekah,wacce take ta dariyar komawar bombee.
“Wow you are the best inna,ke kaɗai ce mai tanƙwasa mana ogah,idan ta kafe akan ra’ayinta bata sanjashi da wuri”

Har suka isa gidan bombee batacewa Maleekah komai ba,tana yin parking ta shige sashenta.
Itadai banda dariya babu abinda take yiwa matar yayannata.
Kayan haidar ta haɗa a ƙaramin trolly ɗinsa,har tazo fita saikuma ta juya wajen drawer da take ajiye abubuwa muhimmai aciki,harda su takardun Jabeer masu amfani da kuma nata..
Magungunan data ɗebo a ɗakinsa rannan tagani a ciki,tana cewa zata tsaya tayi bincike akan namenene har yanzu bata samu dama ba,saidai haka kawai jikinta yake bata bana lafiya bane.
Ɗaukar su tayi tana duddubawa,wata takarda ce ta faɗo a ciki kaman ta gida.
Ɗauka tayi tana nazarinta,lokaci ɗaya wani abu ya faɗo mata,da alama wannan gidan nasane tunda ga sunansa a jiki,sannan a cctv camera tanuna hanyar barin gari yabi,wannan address ɗin shima ba’a gari yake ba..
Saurin maida takardun tayi ta rufe tareda zarar key ɗin motarta,indai ba ɗaukeshi akayi ba kokuma yayi hatsari,to lallai yana can.
A ƙanƙanin lokaci ta isa gidan saboda gudun datakeyi.
Wata ajiyar zuciya tasaki lokacin da taga motarsa a wajen parking na gidan.
Ƙofar falon ta tura a hankali ta shiga,tsitt kakeji kaman babu mutum a cikin gidan.
Wucewa falon tayi ta nufi ɗakin dataganshi a buɗe.
Tun a baƙin ƙofar tafara cin karo da fankunan magani,hadda ƙwayoyin maganin irin wanda ta boye a gida.
Duk anyi zubar dasu birjik a cikin ɗakin.
Zaro ido tayi tareda rufe baki,ganin Jabeer a sheme a ƙasa bakinsa yayi shuɗi(blue)kumfar datayi fita daga bakinsa ta bushe,da alama ba sannan tafara fitowa ba.
Zaman durshen tayi tareda ɗagoshi jikinta tana jijjigashi,ta ƙira sunansa yafi sau a ƙirga amma shuru kaman maye yaci shirwa.
Ƙarar wayarsa tagani da alama ƙira yana shigowa,kuma wayar ba wacce yake amfani da ita bace,sunan data gani a jikine yasakata saurin ɗagawa har tana shirin sakinta a ƙasa.
(My doctor)
“H….ello”
“Hello hello ina Jabeer ɗin yake lafiya ƙalau kuwa yake,jiya naga ƙiransa da daddare,kuma naji numfashinsa yana ƙasa da sama,kuna ina yanzu haka”
“Muna…..amm wani gidansa ne nima sai yanzu na ganshi tun jiyan,yanxu haka baya motsi,bakinsa sai kumfa yakeyi”
“Innalillahi yanzu maza ki kawoshi General hospital,neorological ward yanzu yanzunnnan akwai problem babba”
Yana gama faɗamata hakan yakashe wayar.
Tashin hankali ba’a saka masa rana,bayan ta ajiye wayar rasa ma mai zatayi tayi,hatta fatar bakinta ma rawa takeyi.
Kinkimarsa tayi a jikin kafaɗarta ta fito dashi daga gidan,buɗe bayan motar tayo tana nishi tana komai tasakashi a ciki.
Babu bata lokaci tayi asibitin nan ma da wani gudun
Tun kafin su isa dama doctorn nasa ya shiryah tarbarsu,dan haka direct emergency akayi dashi babu bata lokaci.
Sai bayan an shiga dashi kafin ta tuna da wani abu waishi ƙiran wayar familynsa.

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

Leave a Reply

Back to top button