Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 37

Sponsored Links

037
___________________
Ambassador kasa bin ta cikin gidan yayi saboda ko rufeshi tayi da duka dai shi ya siya,don haka ya gangara ya shige motarsa ya kame ,alkawari ya daukarwa kansa yau sai yaga abinda ya ture ma buzu naɗi

Ya Sheikh a uzzure ya shige gidan Anty tana zaune tana baiwa yarinyarsa cerelac ya shigo ɗakin yana haki yana wuwwurga ido
Dam! Gabanta ya faɗi ta ajiye bowl ɗin cerelac ta miƙe tsaye “Bro Lafiya?”

“Bata zo ba?”
“Wacce kenan?”

Kafin ya bata amsa wayarsa ta fara ringing ,Sunan salimatu yaga na yawo akan screen ɗinsa .
Dama haka yayi saving number Salima dashi .

Da sauri ya ɗauka “He..Hello Salamu alaikum …kina ina?”

A sanyaye tace “Kai zance kana ina? Na bincike ko’ina nagidan ,You no where in sight ”

“Humm! Gani nan dawowa” Yana kashe wayar ya juya zai fita.

“Aah Bro, dakata wai meke faruwa ne?”

“Laaa bakomai😃Dama Dama wai mun rabu zata zo nan ne shine nazo in ɗauketa ,Kinga gashima tace mun ta dawo gida ,To sai anjima”

“Miqdad!” ras ! Gabansa ya faɗi

“There is something fishy a cikin gidan ka,I need to knw what is it”

“To fa🤔Ita Saliman tace an mata wani abu ?”

“See don’t bit around the bush what is going on!”

“Muyi Hausan dai anty”

Fusata tayi ,shine zai raina mata wayau ,a yanda take ta ɗauki mayafin abayanta ,ta ɗaura akan abayarta ta saka room slippers

Sakin baki yayi yana kallonta kamar wawa .
“Oya muje”

“Ina😳” Ya daƙwalƙwalo mata ido

“Ina zakaje daga nan?”
“Gida mana”
“To nan zan bika,yau kowa sai ya faɗa mun meke faruwa”

“Innalillahi wainnailaihir rajiun ,wallahi da ƙafa na fito ,da keke na taho nan ,kuma shima da yaga halin da nike ciki bai tambayeni kuɗin ba yace inje don wallahi bani da ko sisi a aljihuna ,kinga ma Aljihuna”

Tsayawa tayi tana ma ya Sheikh kallon sakarai yanda yake magana sam babu wayau a tare da shi to meye na fiddo mata fatun aljihun wandonsa? Koda ba abun mamaki bane ba,haka mugayen maza suke ma matansu in suna son hanasu kudin cefane ,nan kuwa kudin yana aljihun boxers.

“Au Rowan naka ma har kanka kake mawa?”

“Kinsan fetur yayi tsada ba rowa bane ba ,motana shan man tsiya take dashi yanzu idan daga gidana zuwa nan na taho a mota wlh ban kunna Ac ba ba komai sai yasha mun mai a ƙalla na 5000# kinga kuwa in ɗan sahu na hau 150# an kawo Ni nan ….Ki gane🧏‍♂️ rayuwar ɗan lissafine ,shiyasa indai ba taron Sa’a da Sa’a bane ,na ajiye motana bana shiga ,babur nake hawa

Ehwooo🥵Lallai er uwata tana cikin masifa kenan ba’a kunna Ac a mota ? Komai ana kididdiga….rumtse ido tayi tana ayyana ga ya Sheikh can akan babur ɗan acaɓa ya figeshi da babbar riga yana tafe huuuu iska na cika babbar rigar ana gudu dashi a kan titin kamar balbela🤓

“Ok ba matsala bane ,muje a motana” ta biya ta gaban center table ta ɗauki car key dinta tayi gaba ,baida zaɓi illah yabi bayanta tunda ba gidan babansa bane ba…

A ransa ya fara zancen zuci “Duk dai Salima taja muna ,dabata fita ba da waye zaice zaizo gidanka kana nafa’e guri guda! Anya ma bata da iskokai?…Ji fa yanda ta fice a tashin hankali mai zaisa ta koma ba tareda ta ƙaddamar da nufin ta ba …hummm lallai sheɗan ya shafe ta….ko kuma dama can barazana tayi mun ta gwada irin son sa nike mata,hehehe Wane ita ai bazata iya rabuwa dani ba ,Ni nasan irin son da take mun😄”

Anty sakate tayi a gaban mota tana kallon Ya Sheikh yana tahowa sai ya ɓata rai kamar zai kuka sai kuma ya fashe da dariya Amma mara sauti .

Tabbas Salima ta auri mahaukaci ! Da matsala !!!

***
A bakin gate ta Parker motar tana jiran Ya Sheikh ya fita ya buɗe masu gate ta shigo da motar tunda basu da mai gadi ,dama duk in zai fita da mota shi yake buɗewa ,itakuma Salima in ya fita ta rufo gate din da ya fita ya bari ta cikin gida.

Anty tana rungume da kambin mota tana jiran Ya tale mata gate Saidai taga ya runtuma cikin gida ya barta a nan.

Ba arziki ta kashe motar ta tako a ƙafa,don tana da garanti ƙwaƙwalwar ya Sheikh akwai motsuwa yau sai yaga Likitar mahaukata kafin ta tafi tabbas!

Dr Adnan wilkawar ya sheikh ya gani da gudu wanann ya sa shima ya tako da sauri a ransa yana ƙiyasta indai ta ɓace bil haƙƙi to yanda ya shiga gidan nan tsaresa zaiyi sai ya kira ƴan sanda sun wuce dashi ,ko banza ai suna da haƙƙi ln maƙofataka.

Don haka shima ya bi bayan anty da ta wuce cikin gidan da sauri ,bata ma lura da tahowarsa a baya ba.

Ambassador dake maƙale a mota kamar munafuki yana ganin ana ta shiga gidan ,shikuwa yayi sukuti kunnuwarsa sai kaɗawa suke da kansu suna motsi ,tsabagen ƙwarewa a son jin munafurci .

Kai ina ! Ko harafi ɗaya banason ya wuceni banji ba . Shima ya rufa ma Adnan baya.

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button