Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 14

Sponsored Links

014
____________________
Fashewa da dariya yayi yana nuna mata kansa alamar ba lafiya
“Dubu goma ne ,za’ayi karamin tukunyar shinkafa ?ko dai walima zasuyi?”

“Shinkafar cup biyu ma kuwa ,gaskiya daga gani bai da maƙo sam! Zaiyi sakin hannune da alama”

“Ke jeki dai Ni don ba yarda zanyi ba”

Kallonsa tayi kawai ta girgiza kai ,ita ba wannan ma ya dameta ba,katoɓarar da tayi na yabon wani namiji a gaban idonsa sannan kuma har tana cewa ya bata tayi masa girki ta aza zai ji haushi ya nuna kishinsa koma suyi faɗa fata fata ,saidai ga alamu ma sam bai dauki maganar da muhimmanci ba.

Wani abu mai nauyi ne yazo mata maƙoshi ya tsaya ,daga zaran namiji ya daina kishinka tabbas kodai ya rage sonka ko kuma sonka yana dab da ficewa cikin zuciyarsa.

“Tukunyar gidan biki na dafa masa ,kaji ko”
Ta maida masa magana a harzuke

Buɗe baki yayi hagaga
“Topah meye na baƙar magana ,tsigai!”
***
Sayyida tana idar da sallar Magrib ,tana zaune akan praying mat da counter dinta tana ɗan yin azkar na tsakanin magrib zuwa isha’i. Taji wayarta dake kan dressing mirror Yana neman agaji da har bazata ɗauka ba,sai kuma ta miƙe ta cire hijabin taje gaban wayar ,tana ganin sunanta ta washe baki

“laaa hajjaju ne….Hello Salamu alaikum hajjajuna ,sabran…sabran (sorry)…Kin riga kirana ,wlh jira nayi in idar da sallah sai in kiraki inji ko kun isa lafiya…”

Murmushi tayi mai sauti irin tasu ta manya

“Hum Salimatu baiwar Allah ! Ni kina tsaye a ƙoƙon zuciyata ce shiyasa na kira ,naje gida da dimbin tausayinki salima…”

Dariya Salima tayi
“Laaa Hajiya na me ? Halan kinga na rame?”

“Wannan ya wuce rama Salima kin lalace ,nasan yarona yana azabtar dake ko baki faɗa mun ba zan iya perceiving hakan saboda na zauna da marigayi babanshi ,ga kudi har kudi amma yanda Kasan zumbuli ! Rowar tsiya ba’a cin kudinsa ….. A lokacin nan idan Alhaji ya mun wani Halin Addu’a nakanyi Ubangiji kasa halinsa ya tsaya a kaina kar yarana su gajeshi , so unfortunate miqdad shine hak muke kama dashi amma ƙarƙaf halin maƙon babanshi ma sai yace babansa bai komai ba….tun yana yaro akwai madda! Ina yawan yi masa faɗa gadonsa har yau kobo bai taɓa ba,ina miqdad zai kai dukiya ne wohoho Ni zuwairatu!”

Raurau idon Salima ya kawo ruwa “Hajiya Ni maƙonsa baya damuna ya tankacin rashin abinci! Daidai da shinkafa sai ya auna mun adadin da zan dafa,Hajiya jakar maggi star dole yayi mun wata guda ,idan kuwa ya kare saidai in siya da kudi na, mangyaɗa hmmm Hajiya abincina ba daɗi ” shiru tayi saboda yanda muryarta ke rawa zatayi kuka

“Kiyi hakuri ,nima ko nace ,wannan cefanen girkin bazai taba badawa ayi ba,nifa naga duk kin wahale ba gayu Ni tsohuwa nafiki shiga me kyau ”

“Hajiya in zansa kayan gayu sai yace wannan na fita unguwa ne ,me yasa zan sa?!…in zanje kitso yace aah yafiso ya ganni a haka ,in zanje saloon yace ba kyau ƙona gashi haramun ne….wlh ko cikin kawayena bana son shiga ,a dangi nuna Ni akeyi ,wai na fiye rowa har kaina nike cuta duk na sukurkuce basu san shine yake sawa ba,ga aiki ya hanani zuwa wai haramun ne cuɗanya da maza! Ya zanyi Hajiya ya zanyi?”

“Ashsha! Ashsha!! Na lura wlh ,saboda ai nima uwace kuma jinki nake Salima tamkar ƴar cikina kiyi hakuri kinji ,…yanzu bari in tambaye ki?
Salima kefa wayayyiyace yar boko hakane?”

Jinjina mata kai tayi kamar tana kallonta tasan bayan hannunta tana goge hawayen fuskar ta

“Ina kika baro Dan kissanku na mata? Ina kika bar yanda ake ribatar miji a ɗan Oza room dinnan? Naga duk maƙon namiji ta wannan harkar ai ana samun kuɗi dasu…anya kina shan en kayayyakinmu na mata ? Salima maza irinsu miqdad ba’a cin kudinsu a kwance ,sai kema kin zage kin koyi salon kula da miji ,kin watsar da uztazanci ,Kar in sake zuwa gidanki in ganki da hijabi biya biya ,kina tsutsukewa kina fente fuska da powder da janbaki….ha’ahh wai saima na ko ya maki ,Dan kwarkwasan nan da iya tafiya ,ya dawo kin je ɗas! ɗas! Kin amshe jakar kin rungumeshi ka dawo Barka da zuwa rayuwata ,fitilar…” fashewa da dariya Salima tayi ƙyal ƙyal ƙyal har tana dukan ƙafa

Turo baki Hajiya tayi “Au to shikenan nasan duk kin ma sani ,wannan namune dai na tsoffin da ,Plz Inason ganin sauyi a gidanki Salima ta kinji?….”

“To Hajiya Inshallah ” ta fada a kasalance tana tuna wata rana da ta zauna a gaban mirror tana gayu ,tana cikin fesa turare ta nuna masa kwalbar turaren a shagwaɓe

“Sweet tularena ya kare ko zamu biya kadan siyo mun….buɗen bakinta sai ya daka mata tsawa ,ke Ni dama kin saki baki kin mun magana sak irin na mata don Ni kirsan mace da kisisina baya sa inji ko ɗar a zuciyata ,kuma Ni mace ko tayi gayu ko kar tayi gayu uwansu ɗaya ubansu ɗaya …..”

Jan ajiyar numfashi tayi bayan kiran sunanta da Hajiya tayi ta waya “Hello kina tare Dani?”

“Eh inaji”

“Yanzu ki turo mun account Number dinki ,zan saka jiddah ta sako maki dubu hamsin ,sai ki danje ki ,wankin gashi da kunshi ,ki ɗan siya turaruka da dai kayan gyara kinji Salima na”

“Aah Hajiya ki barshi wlh haba dai!”

Rarrashinta ta shigayi
“Habawa Salima na ,nifa na baki,ba kudin miqdad bane ? Ko kina fushi dani ne ? Ko kin raina ne kiyi hakuri ”

“hajiya kibar bani hakuri kinasa inji sani iri wallahi”

“To ina jiran ki ki turo yanzu kinji? In kinje karki kashe duka ki ɗan rage wanda zaki ringa siyan abun da kike so in miqdad din Bai Baki ba kinji….Allah ya shige mana gaba ,Ubangiji ya daidaita zamanku ,ki mike wurjanjan wajen tsamo mijinki ga halaka kinji ƴata!”

“To Hajiya Nagode Allah ya ƙara girma”

“Amin ƴannan kira shan madara da Nama ,in sun Kare Kar kiyi ƙoron Baki ki fada mun in Kara maki wasu kedai karki bari ya sani ,kaiii yau da na ganki saida tsikar jikina ya tashi ,mamanki in tazo ta ganki a haka ai mun bani!”

Sosa ƙeya salima tayi “Kai Hajiya sai zagin mun miji kike,zai fa gyara”

“😃😃Ƴar nema ,tare ma mijin naki zakiyi ,auuu ina tare maki zaki nuna mun Son miji?!🤭To shknn Allah yayi Albarka ki turo number ina jira…”

 

 

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button