Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 46

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣6️⃣

…….“Ni kuma gashi gaskiya bazan iya baku Matana ba yanzu dan kaima dai kasan ango nake”.
         Dariya Ahmad ya kwashe da shi da faɗin, “Ɗan iska shegen sama. Banza ta faɗi ko anata kwasar romon dimakuraɗiyya. Sai kaita riƙo ai ko tana nan zata mana aiki”.
     “Shegen sa idon ka dai a kanka zai ƙare. Sai dai fa daga nan ɗin dan mai kawo min mata Nigeria yanzu ban gansa ba”. Ya ƙare maganar yana kashema Lulu dake kallonsa ido. Kanta ta ɗauke tana ɗan murmushi da harararsa. Dan ita ta ƙagara ya kammala wayar ya mata bayani. Sun sake tattaunawa sosai da Ahmad ɗin kafin suyi sallama. Yana yanke wa kiran Uncle Yousuf na shigowa. Tashi yay yabar falon ma gaba ɗaya, Lulu ta bishi da kallo cikin jin tsarguwa. Bai jima ba sai gashi ya dawo. Ganin yanda ta turɓune fuska ya sashi zuba mata ido.
        “Lafiya kuwa Madam?”.
   Baki ya taɓe da ɗauke kanta gefe. A hankali ya kai zaune kusa da ita yana mai kamo fuskar tata. “Please miya faru kar kiyi fushi mana.” harara ta sakar masa da buge masa hannu tana son tashi, yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. Rungumeta yay da ƙyau ta yanda bazata iya tashin ba. Cikin tallafo kanta da ɗaura goshinsa a saman nata ya ce, “Please Baby luv, kin san fa da fushinki gara kawai a tada yaƙin duniya na uku. Faɗamin minene?”.
         “Ba kai bane kake ta wani ɓoɓɓoye abu dan kar naji”.
     “Haba ni na isa. Kikama san Aliyu ciki da bai ɗinsa balle abinda ke a zuciyarsa. Dama fa zan yi maganar dake”.
     “Babu wani ban yarda ba. Bayan tun randa mukazo kaketa wani magana da Ahmad a cuccure, hakama idan Uncle Yousuf ya kiraka sai ka koma gefe ko Daddy”.
            “To yi haƙuri bazan sake ba. Bani ɗan lokaci yanzu zan miki bayanin komai dan kema kina daga cikin tawagar ai. Dama ba’azo gaɓar da naki aikin zai fara bane kawai shiyyasa. Haɗamin coffee yanzu ina zuwa”.
      Babu musu ta miƙe zuwa kitchen, ya bita da kallo har sai da ta shige sannan ya tashi yana sauke ajiyar zuciya. Bedroom ya shiga, babu jimawa ya fito ɗauke da laptop a hannu da Flash drive kusan huɗu. Centre table ɗin falon ya jawo gabansa sosai yana kaiwa zaune da zube kayan hannunsa, sai lokacin idonsa ya sauka akan camara ɗin data ɗakko. Ɗauka yay ya ajiyeta a gefe yana girgiza kansa, sai gata ta fito ɗauke da ƙaramin tray da coffee 2cups sunata turiri.. gefensa ta zauna tana ajiye masa nasa gabansa itama ta ajiye.
      “ALLAH yay miki albarka”.
  Ya faɗa yana ƙoƙarin saka flash a jikin Laptop ɗin. Cikin jin daɗi da farin ciki ta amsa masa. Dan a duk lokacin da yace ALLAH yay mata albarka tana matuƙar jin kanta on top ne. Sai da ya gama saita komai ya kalleta. “Ina son ki nutsu sosai dan maganar da zamuyi mai matuƙar muhimmanci ce”.
         Kanta ya jin jina masa da sake maida hankali garesa sosai. Cikin nutsuwa shima ya fara mata bayani ta yanda zata fahimta tun daga randa Daddy ya fara aiki a maikatar da Alhaji Sufi Garko ke shugabanta, wanda a dalilin haka ne ya ja Daddy a jikinsa, a maimakon aikin gwamnati ya maidashi akan harkokin kasuwancinsa. Yanda abubuwa suka dinga tafiya har zuwa sanda kuɗi suka ɓata da shiga jikinsa da Sulaiman ya farayi ta hanyar nuna masa zai taimakesa da kasuwancin da suka fara tare har zuwa sanda ya fahimci abinda ke cikin business ɗin da haduwar Daddy da mahaifiyarta, da abinda ya faru a dalilin aurensu, fyaɗen da Alh. Sulaiman yay ma Sultana da yanda Daddy ya tayashi ɓoye sirrin zamansa da mahaifiyarta, rasuwarta, mutuwarta, ɗauketa a Nigeria har zuwa girmanta, shigowa rayuwarta da yayi dama kamun da Alh. Sulaiman yay masa har zuwa aurensu da buɗe musu ciki da Daddy yayi akan komai da dalilinsa na ɓoyewa. Yanayi yana nuna mata abubuwa a laptop ɗin nashi, yawanci duk wayoyin barazana ne, da wasu harƙalloli tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman ne, dama hotunan abokan da sukai huɗɗar kasuwanci da Daddyn ya adana matsayin hujjar da ya dinga tsorata su Alh. Sulaiman da tawagar su Nakowa da ita. Tunda ya fara Lulu ke kuka na tashin hankali, har takai AA ma ya fara kuka sai da Smart ya ɗaukesa ya ɗaura a cinya. Jikinta tsuma yake matuƙar tsuma, idanunta sun masifar kumbura saboda kukan da taci. Cikin damuwa ta ce, “Na cikin camara ɗin ma dan ALLAH ka nuna na gani”.
       “Ba yanzu ba”.
   Ya faɗa yana jawota jikinsa ya rungume cikin lallashi. Sai ta sake tsage masa da kuka. Muryarsa a raunane shima kamar zai saki kukan ya ce, “Please mana ya isa kukan haka kinji, mugodema ALLAH tunda babu abinda ya faru da shi. Duk da ina ji a jikina da saka hannun Sulaiman a zuwan Felix gareki, hakama su Alace da Luna da suka koya miki shaye-shaye ina zargin sakasu akayi mawaddat duk da dai bani da tabbaci.”
      Kanta ta sake turawa a jikinsa tana kuka mai cin zuciya. Duk sai hankalin Smart ya sake tashi. Dole ya rufe laptop ɗin ya maida hankali a lallashinta da bata baki. Duk yanda taso suga abinda ke a cikin camara ɗin a yau yaƙi yarda. Da yaga ta damu sai yace mata dole sai an kwashe abinda ke cikinne zuwa flash shiyyasa. Badan ta yarda da shi ba ta haƙura, sai dai ta ɗauka waya tai kiran Daddy. Yanda yaji tana kuka shima sai hankalinsa ya tashi, cikin ruɗewa ya shiga lallashinta da tabbatar mata tayi haƙuri zuwa gobe zai shigo birnin London shi da Uncle Yousuf. Hakan ya ɗan sakata jin sassauci, dan babu abinda tafi buƙata a yanzu sama da taga Daddyn a kusa da ita. So take ta sake tabbatar da babu abinda ya samar mata shi. Uncle Yousuf ma ya amshi wayar ya lallasheta, hakan ya ɗan ƙara saka mata jin sauƙi, bayan ta yanke wayar ta shige jikin Smart tana hawaye. Murmushi yay yana mai ɗagota, cikin zuba mata idanu ya kai lips ɗinsa kan nata a hankali. A nutse ya canja yanayin nasu zuwa wani abu daban, babu kunya a falon akai yaƙin ƙasa-da-ƙasa, sai dai ƙura ta lafa kuma ta koma jin nauyi. Shi kuma yana mata dariya da tsokana wai dama abinda take so kenan ashe. Itama dai yanzu ta zama babbar mayaƙiya. Tashi tai ta bar masa falon bayan ta gama mimmitsinesa da bubbuga masa filo. Da kallo ya bita yana mai jin ƙarin ƙaunarta mai faɗi da girma na sake mamaye sa tako ina. Da ga ƙarshe ya miƙe da ƙyar ya bita bedroom ɗin. Bathroom ya nufa inda yake jinta sukayo wankan tare. Shine ya koma falon ya ɗakko AA da ke barci. Suma dai kwanciyar sukai domin hutawa ransu…..

         *_NIGERIA_*

    Sau biyu ana ɗorata amma ƙashin ya gagara zama saboda tanada ƙiba, gashi a cinya ta karye. Su kansu malaman asibitin lamarin neman fin ƙarfinsu yake. Ƙaninta dake tsaye kan lamarin nata ne ya yanke shawarar su nemo masu ɗorin gargajiya. Dan mijinta tunda yazo zuwan farko asibitin yaji irin sambatun da takeyi da tona ma kanta asiri ita da aminiyar tata da ayanzu kowa ke kira da Dodo ransa yay masifar ɓaci. Ashe itace ta rabashi da matarsa mai sonshi dan ALLAH tun bashi da komai, sannan ta rabashi da manyan ƴaƴansa da sam yanzu ko kallon arziki bai musu da ma danginsa. Hatta da karatunsu bai saka hannu ba gashi yanzu duk ALLAH ya tallafesu sun samu ayyukansu. Ranar yayi kuka da hawayensa da yin dana sani. Yana zaune da matarsa lafiya ƙyale-kyalen Naqiba da suka haɗu a wajen aiki ya kwashesa har yana kushe matarsa akan bata iya komai ba sai gidadanci saboda kawai batai zurfi a ilimin boko ba. Shagalin biki akai na alfarma lokacin ya zubda kuɗi tare da sakata a danƙareren gidansa da ya gama gini. Itace ta gaban mota idan zai fita, itace ta zuwa jahohi idan aiki ya kaisa, acewarsa itace mai ilimi. Duk da bawai wani mahaukacin kuɗi ne da shi ba yanada rufin asirinsa dan har Saudiyya yaje kusan sau uku, kuma duk tare da matar son nasa Naqiba. Yakan je Dubai kuma saro kaya a yanzu haka, dan yanada manyan shaguna a cikin kasuwar kwari. Yakan yima Naqiba abu sau sama da goma kafin yayma matarsa da ƴaƴansa, a haka har suka haihu ɗaya da ita, dan Maheer kawai ta haifa sai mace ita kuma ta rasu tun tana 3years….

An sake ma Hajiya Naqiba ɗorin gargajiya da taci uwar azaba harda sumanta. Bayan farfaɗowarta ne ta cigaba da sambatu kamar zautacciya. A wannan halin su Abba da sukazo dubata saboda a gidansa ta samu matsalar, yana ta son zuwa sake dubata tun randa suka kawota asibiti tashin hankalin Ummah ya hana shi. Sai yau ne yaga ya dace yazo kar ai abin kunya shine ya kwaso su Abdull suka zo. Anan ne kunnensu ke jiye musu sambatun Hajiya Naqiba da ke fallashe sirrinsu. Ba Abban kawai ba hatta su Mubarak ji sukai ƙasa na neman kasa ɗaukarsu. Bakin Hajiya Naqiba bai mutu ba sai da akai mata alurar barci mai ƙarfi. Tuni Abban ya baro ɗakin ko sallama bai iya yima danginta dake cike da ɗakin suna faman mata ALLAH wadai ba. Cikin sauri yaransa suka take masa baya. A wannan tashin hankalin suka dawo gida, sun iske Yayan Ummah Jibirin ya sake zuwa da wasu malaman yau ma. Sai dai suna jira Abban ya dawo a tunkari Ummhn.
  
       Duk hayaniyar da akeyi Umma na jiyosu da ga falonta, sai dai furucin Abba yasa a yanzu bata iya fitowa ko tsakar gida, dan ya tabbatar mata idan ta sake fitowa ta firgita masa iyali batare da shi yace ba a bakin aurenta. Wannan kalma na ɗimautata a duk sanda ta sake maimaita kanta a ƙwaƙwalwarta. A cikin abinda bai wuce sati guda ba duk tayi wata irin firingau-firingau da ita. Tai muguwar rama kamar mai cutar sida. Kuka kam idanu sun daina sai dai na zuciya. Tunda take ko’a labari bata taɓa sanin akwai makamancin irin tashin hankalin nan nata a duniya ba. Ita a yanzu ma neman hanyar zuwa ga malamin da yay aikin take ya karya shi amma babu hali, tsakar gida ma ya gagari mutum balle ƙofar gida har akai ga shiga mota. Abincin tana cinsa ne kawai dan tsoron mutuwa. Amma badan yunwa ba. A duk sanda ta jiyo muryar Ammah dai ta fashe da kukan baƙin ciki na tsananin jin kishi. Tana jin raɗaɗin tayaya za’ai ace Ammah taci nasara a kanta kenan? Itace fa Yahanasu mai yawan ƴaƴa maza a gidan fiye da kowa, ƴar uwar mai gidan jininsa, tafi kowa yawan ƴaƴa, ita ta fara haihuwa a gidan, tanada power ɗin juya miji a tafin hannunta koda daga baya zai suɓuce mata zata sake nemo hanyar riƙosa. Kowa a waje gani yake itace ke juya gida da miji, amma a kullum sai Hafsatu ta zama sanadin rusa mata plans nata. A kowace safiya tana ji kamar ta kashe matar nan ko zata ji sassauci na zafin tsanar da take mata. Kuka irin mai ƙona zuciya ɗin nan ya suɓuce mata, sai dai babu ɗigon hawaye a cikin idanun sai zafin zuciya da gwara ma kaita hawayen……..✍️

_🥱🥱Jiya kunji shiru ko. Ina nan na dage muku da typing ne nima na ƙagara mu gama🚴🚴._

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button