Entertainment GistKannywoodNews

“Babban Burina a kan Diyata Surayya – Jaruma Hadiza Saima

Sponsored Links

Surayya Hadiza Saima

Hadiza Saima shaharriyar jarumar nan ta masana’anatar shirya finafinai ta Kannywood ta bayyan babban burinta a kan diyarta Surayya.

Kai da gani ba sai an fadi ma ba, Surayya da Hadiza saima tamkar an tsaga kara tsabar kamar da su ke.

Sai dai abin da Saima ta bayyana a kan diyarta da bambanta da yadda mutane ke tunani matuka inda ta ce;

“Lallai babu abin da zan ce da Allah sai godiya da ya nuna mani wannan rana domin wannan abin farin ciki ne a gare ni.”

“A yanzu babban burin da na ke fata shi ne Allah ya nuna mani lokacin auren ta. Ina fatan Allah ya ba ta miji nagari, kuma Allah ya ƙara mana shekaru masu albarka cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.”

Wannan shi ne abin da mahaifayar ta fadi a kan diyarsa, sabanin yadda mutane ke tunani ko sa ran za ta fadi (wato fatan diyarta ta zama jaruma irinta).

To, Allah ya kyauta.

Leave a Reply

Back to top button