Matan Ko Mazan 1
đ«MATAN??? Ko MAZAN???đ«
âđ»M SHAKUR
Chapter 1- FEMINISM
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINKAI.
Note: Wannan littafin kagaggen labari ne ba rayuwan wata ko wani narubuta ba, is just fiction danai highlighting major issues dake kawo misunderstanding a aure, I hope we all read and learn.
đ
EPISODE 1ïžâŁ
Zaune suke akan kujerun dake cikin garden din yahuza suya na bayan central mosque. Maza hudu ne, dukansu suna sanye da suit but duk sun ciccire jacket din sun makala jikin kujerun dasuke kai da alamun daga wajen aiki suke, gasassun kaji ne agabansu da shayi sunasha suna kallon katon TV dake wajen inda ake buga kwallo tsakanin Manchaster da chealsea.
Kana ganinsu kasan suna balaâin enjoying match din dan sai gardama suke suna dariya kyakyakya.
Wayan daga daga cikinsu ne yay kara hakan yasa yakai hannunshi yataba aljihun gaban riganshi batare daya janye idanunshi dagakan TV ba yaciro wayan yajanye kanshi daga TV yakalli screen din ganin Madam yasa yadanyi tsaki ya ijiye wayan yacigaba da ringing sauran mazan dayake zaune dasu suka kalleshi dan yake yayi yakai hannunshi yana shafa kirjinshi yace âMadam ce wlh ke kirana tahanani sukuniâ dauke kansu duka sukai daga kallonshi kaman hada baki suka cigaba da kallon match din abinsu.
Karfe 11:30 daidai aka gama match din inda Manchester sukaci da 4:2, wanda aka kira dazune yatashi yana daukan wayanshi dake ringing har lokacin da jacket nashi duka ya rike a hannu yace âlemme be on my way, inba hakaba Madam zata kashemini batteryn waya wlh, saida safen kuâ daya daga cikin ukun dasuka rage zaune shima yamike dasauri yace ânima gani biye dakai Engineer bazan iya da masifan matan nan this night ba tahanani bacci nimaâ yana maganan yadauki jacket nashi da car key yabi Engineer dasauri zuwa wajen dasukai parking cars dinsu, sake sallama sukayi kowanne ya shige motarshi suka bar wajen.
Daya daga cikin biyun dasuka rage zaune ne yakalli dayan yace âkarfe nawa zaka bar nan Nura?â juyawa wanda aka kira da Nura yayi kaman bashi akama magana ba yadaga hannunshi sama yakira daya daga cikin yaran dake aiki a Yahuzan da gudu gayen dayakira yazo cike da girmamawa yace âyallabai ganiâ juyawa Nuran yayi yakalli mutumin dake kusadashi yace âya akaro dakai ko zaka wucene kaima?â girgizamai kai yayi alamun aâa hakan yasa Nuran yajuyo yakalli yaron yace âkaro mana shayin goruba da kaza asaka masa aciki da gizzard, kasa yaji separately bancin yaji sosai” wucewa yaron yayi yatafi Nura yadauki wayanshi zai fara tabama Musa yace âwai har yanzu kaida Hadiza baku shiryaba? Kai to kasauke girman kanka ka nemeta kuyi sulhu manaâ tabe baki Nura yayi yace âwlh ko zan mutu bazan lallashi yarinyar nan ba cus nagaji, any little misunderstanding wanda daga wajetane fa yake farawa amman kullum nike neman sulhu akan wani dalili? She keep taking advantage of rashin son hayaniya na, yo bansan ciwon kaina bane aka gayamata?â Dasauri Musa yace âhaba abokina kaima kasan mata da fish brain biyemata zakayiâ dasauri Nura yace âbazaka gane bane, duk yanda zan suffanta maka Hadiza bazaka ganeba, sheâs so bossy, tanada mentality dinnan na feminism, gani take dani da ita daidai muke shoulder to shoulder, she feels irin india kinada kudinki babu shit din da namiji zai kawomiki kidauka, you donât need him for anything, she donât care about me one bit billahillazi kaman ba aurenta nake baâ dafashi Musa yayi yace âchill please kodan yaranku ku shirya haba, Aman is just 4,5yrs ina, little Amal kuma 2 please banson yara tun suna kanana su taso suna ganin iyayensu basa shiri kaji Nuraâ kabar da hannunshi daga kafadanshi Nura yayi yace âenough Man, talking to Hadiza is impossible, barni nima nabita nazama fish din but saidai ni bazan zama sardine irinta ba mara hankali dake karewa a gwangwani ba, dan trust me mentality feminism nata nan is taking her nowhere, wlh saina gwadamata bonu duk randa takaini bango yar durun uwaâ ya kifo uban ashar da hausan shi haba Musa ya kwashe da dariya, dan dariya Nura yayi shima yace âkaikuma meya faru kaima kabiye mini dayin dare awaje yau dan is obvious kaima da naka guntun matsalan kaimaâ dan tsaki Musa yayi yana tsaida dariyan dayake yace âmatata, kaga Maman Shatu I donât even know idan mace ce ita dan at this point cewa nake anya ba namiji bace itaba kuwaâ dan dariya Nura yayi daidai lokacin ana kawo musu ordersu yaron ya ijiye yawuce yatafi, tsiyaya musu shayin Musa yayi yadauki kopin yakai baki yadan kurba ya tsaya kaman mai tunani yace âBro imagine fa duka duka yanzu fa na shiga 45yrs amman this woman na neman maidani tsohon dole, she hates anything tarayya dani, dazaran nazo saita fara ni bansan yakamata yanzu na soma rage kwanciyan aure da itaba nasomas tsufa, menene menene, wai is high time mufara hakura dayi yara sun girma, Shatu is 16 zata shiga university next month letâs just focus on yaranmu, I was like what da hell! An gayamata ni katako ne ko sotake da tsufana nafara sopyâ? Bushewa da dariya Nura yayi harsaida ya yarda naman bakinshi kasa yana nema ya kware, Musa yace âkadaina dariya is a serious matter ni da kai munada banbanci, kai daman bakin zuciyanka da girman kanka bazai barka kanemi Hadiza ba I donât even know yanda kake surviving wlh, niko bazan iyaba kullum da rokon Allah nake hada matan nan kafin tabari indan taba, da girmana da darajata Maman Shatu ta maidani maibara shine fa jiya tamini karatun Alam Nashara matan nan atafaufau tahanani wai munada budurwa mudaina yiâ dariyan da Nura keyi saida yan wasu table suka juyo suna kallonsu dasauri yarage sautin dariyan, kwana nawa kenan kullum cikin kunci yake but yau Musa nabashi dariya sosai wlh heâs so funny and hausan shi is just everything, dole ma kai understanding pains nashi sabida kalamomin dayake using to express it, tsagaita dariyan yayi yadauki nama yakai baki yace âto be honest with you Musa bawai banson nasami natsuwa bane ina so sosai but halinta is making me loose interest and love for her, banmason in tuntubeta da neman kwanciyan aure, itakuma ko oho bata damu dani ba, she no send me faâ cike da takaici Musa yace âI donât know yaya brain din mata ke aiki imagine fa sun mana laifi but idan sun taru cikinsu they will belike mijina yamin kaza kaza kaza kaga ana kaimu online ana please hide my ID akai karanka amman baza su taba fadin suga kaza kaza da sukema mazajensu ba bunch of hypocrites, masu fuska biyu kawai, banda gayu da nunama kawayensu suna more mazajensu da aurensu babu abinda suka iya, ita kuma dama nafada mata idan bata chanza ba wlh she is on her own, daleliyar kishiya zanyo mata, da kudina da sanaâata wlh bama saina nemi mata ba Gwaggo zan kira a kano asamomin yarinya yar achan achan atoh ni wlh ban tsufaba garau nake, anma kawomin wasu magungunan basir daga Cotonou bazaka sha baâ? Girgixa kai Nura yayi yace âkaidai da shaye shayen magungunan basir din nanâ dariya Musa yayi yace âkaima yakamata kasha wlh ya wanke maka mara tastas, fire for fire wlh ka lallasa Hadizaâ âinaaa ni bazan biyemaka ba narasa ina zansa kaina, baridai maybe idan komi ya daidaita nazo na amsaâ.
Wuraren 1.30AM sukatashi Nura yabiya kudin komi, kowanensu yashiga mota dan tafiya gida, Musa yace âzakazo office kaduba motocin ne gobe sun iso faâ Gyadamai kai Nura yayi yace âinada wani important meeting gobe but zan shigo dazaran nagamaâ Musa yace âto shikenan nimafa sonake nazo naga site dinnan, terrace dinnan yamin kyau dakukayiâ âba kaki sayaba bakano da son kudiâ ckin dariya sosai da barkwanci Musa yace âshikuma bazamfare annubazaranci da kudi, nabiye maka saika karan mini da dan jarin motoci naâ dariya dukansu sukai sukai sallama kowa yaja motanshi sukabar wajen.
Kinason magana dani M shakur??? Chat me up by clicking on this link
wa.me/+2347012181461
Parking yayi agaban wani babban gida wajajen 2 nadare. Sauka yayi yana kallon wata sabuwar red 2024 Toyota grand highlander dake pake akofar gidan duka duka last month ya chanza mata mota 2023 Toyota Camry hybrid wato bai mataba shine maybe ta saida tasayo wani, dan murmushi yayi yawuce yana ciro key dinshi yabude kofan yashiga ciki yamaida kofan yarufe yajuyo yakunna wuta lafiyayyen hadadden classic falo ne, ijiye key yayi kan tray dasuke ijiye key yaduka yacire covershoe kafanshi yasake juyowa yabi falon da kallo dayake tsaf tsaf banda motan Aman dake kan kujera hannu yasa yakashe wuta sannan yawuce yahau stairs harya fara tafiya yaji kukan Amal chak ya tsaya cus badaga sama yakejin kukan nan ba and dakin Amal na upstairs, shiru yayi jin magana kasa kasa. âsorry Amalulu, Amalilin Mommy, Amalilin Aman, Amalulu na Amalulu yar lukuta, kiyi bacci zakiji sauki gobe kinji, zazzabi ne saina zane zazzabin nan dake damun mini yarinya naâ muryan Amal yaji tafashe da kuka sosai cikin muryan yara tace âMomyyyâ dasauri yajuyo yashiga saukowa daga staircase direct hanyar dakin yar aikinsu yayi dake kusada store room na gidan, tsayawa yayi gaban dakin yasa hannu yakunna wutan wajen sannan yayi knocking kofan tareda bude kofa atare dasauri sabida yanda yakejin kukan Amal, wata yar budurwa ce doguwa tsaye tagoya yar yarinya dabazata wuce 2yrs ba abayanta, wata yar karaman katifa ne adakin ta yan boarding sai ganamasgo saikuma kwalayen magunguna da flask na ruwan zafi da gwangwanin cerelac da bowl da spoon duka akasan dakin, adan tsorace yar budurwan ta duka kasa goye da Amal abayanta ganin maigidan dabai taba zuwa nan ba tace âina yiniâ gabanta na faduwa dan yaune rana da farko da Baban su Amal yataba zuwa wajen nan, sosai yake kallonta baima tsaya amsa gaisuwanta ba yace âme Amal keyi anan da daddaren nanâ? Tana duke akasan still jijjiga Amal dake kuka take abayanta tace âbatada lafiyane Alhajiâ âMamanta faâ? Dasauri tace âAnty tadawo daga aiki tagaji bacci zatayiâ ranshi abace yace âita tace ki kawota nan dakinâ? Gyadamai kai tayi batare data kalleshi ba tace âehâ âbani ita nanâ batai musa ba tashiga kwanto Amal dasauri, yarinyar was looking so weak sai kuka take ta yarda zanin tadauketa ta taso ta taho har inda yake tsaye agaban dakin takawomai ita, itama Amal tana ganin babanta takara fashewa da kuka tace âDaddyâ zafin dayaji ajikinta saida yadan firgita ya rungume yarinyar da sauri ajikinshi yace âmy princessâ yakalli yar aikin dahar takara dukawa anan gabanshi yace âwani magani tashaâ? Dasauri tace âAnty tace nabata wayanchanâ? Tanunamai magungunan dake gaban katifar ta, Ibuprofen suspension ne dakuma Tuxil D na mura da tari, jiyayi ranshi na tafasa dan yaranshi are his life, cikeda takaici yace âhow many mil ma kika bata? Tun yaushe take wajenkiâ? Dasauri tace âtun wajajen 9 Anty takawomin ita, cikin marfi Anty tace nababbata zatai bacciâ âmaisa baki kaita da jikinta yayi zafi haka ba akaita asibiti tun 9 har 2 nadareâ kanta na kasa still da zuciya daya tace âAnty tace karna kawota bacci zatayi tagaji ta kwana awajenaâ kallon yar aikin yayi takaici yasa kawai yajuya yawuce yahau staircase rikeda Amal dake kuka sosai ajikinshi, direct dakin Maman yawuce bude kofan yayi kai tsaye yasa hannu ya kunna wutan dakin, wata kyakkywan faran mata ne kwance kan wani makeken lafiyayyen gado tarufa dawani beautiful bargo AC na aiki dan dakin sanyi tana bacci mai dadi, wucewa yayi gaban gadon ya bubbuga filon da kanta kekai yace âHadiza, Hadizaâ firgigit tabude idanunta dasukai ja cikin bacci tabishi da kallo tana mika tana kallon Amal dake kuka sosai tana miko hannu kaman zata kamata, cikin muryan bacci tace âNuri lafiya zaka kawomin Amal ina bacci batana wajen Ummi yar aikinmu ba pls kamaidata I need to sleep na balaâin gaji wlhâ tai maganan tana hamma zata kara jan bargo azuciye Nura ya fizge bargon ya yaye yace âwai whatâs is your problem Hadiza? Kinyi neglecting your responsibilities towards me yanzu ma yarana wulakanta mini su zakiyi, this girl is sick baki kaita asibiti ba, baki kirani kin sanar dani ba, kin barma yar aiki ita da magungunan acika marfin idan tai overdosing yarinyar nan faâ? Hamma Hadiza tasakeyi tarufe bakinta sannan tadan yunkuro kadan takalleshi tace âlook Nuri banda lokacin fada dakai yanzu Allah ma yasan I donât have time, dare mahutan bawa ka maidama Ummi yarinyar nan tasan yanda zata kula da ita, sheâs great da yara bakaga duk cikin yan aikin danayi tafi dadewa ba almost a year take nema yanzu agidan nan, and my children loves her sosaiâ wani kalan kallonta Nura yake yace âda ace bani nakaiki asibiti kika haifi yaran nan ba danace banaki bane Amal is just 2 sheâs sick crying for you jibi yanda take kuka take miko hannu ki dauketa kina cewa akaima yar aiki, what kind of woman are you da bakijin tausayin yarankiâ? âoooohhhhhhhh! Ohh-ho-hooo!â Hadiza tabuga uban ihu tana daura duka hannayenta saman kanta irin ta shiga uku din nan, cikeda gajiya tace âwai all this while so kake muyi fada naki biyemaka cus am busy da work dina baka gabana whatâs the meaning na zuwa tashina tsakar daren nan kana neman balaâi na eh? Nace ka maidama Ummi yar aikina Amal for Godsake this is her job we pay for it ba kyauta take mana ba, idan bazaka maidata ba I can call her da wayana tazo sama ta dauketa sutafi, please pls banson problem Nuri, banso, just get out of my room pls katafi dakinka, haaâa kawai katasheni tsakar daren nan da balaâin ka wannan wani kalan neman rashin zaman lafiya ne iyye? Pls kafitan mini daga dakina nace and nagaji nadawo daga aiki ka maidama Ummi Amal sheâs good with kids zatasa yarinyar nan bacci pls go away from hereâ kawai tsayawa Nura yayi yana kallon Hadiza yanda take magana zaka dauka itane mai gidan nan ko itane take putting food on the plate jibi yanda take cemai yafitan mata daga daki kaman itace ke aurenshi ba shi ke aurenta ba, ganin ya tsaya kallonta yake yana jijjiga Amal dake kuka sosai barinma yanda taga Mommy ta na masifa yasa ta buga tsaki. âMtswwww, kada Allah yasa kafitan nina barmaka dakin, kajika da ruwa kashaâ ta tashi fuuu azuciye tasauka daga gadon tawuce tafita daga dakin tana mita,
yana ji tashiga wani daki ta bugo kofan tarufe tana murza key jiyayi kaman an dauramai dutse a kirji kallon Amal dake ihun kuka yayi tana kokarin sauka daga hannunshi tana kallon kofa tana mika hannu tanaso tabi mamanta Ya jijjigata yace âsorry Amal, Daddyâs princess stop crying, mujeâ wucewa yayi yafita daga dakin dakinshi yaje da ita ya ijiyeta kan gado yawuce bayi yatara ruwa yadawo kayan jikinta yacire mata da pampers yadauketa zuwa bayi wanka yamata tsaf kana ganin yanda yake kasan mutum ne mai tsananin son yara fito da ita yayi daure a towel yawuce yafita yaje dakinta hadadden daki komi pink ga zane komi organize wani shimi yadauko yasamata da pampers yace âzakisha tea Princessâ? Girgizamai kai tayi aâa, yace âjuice, cheese balls, rice, omeletteâ gyadamai kai tayi dasauri daya fadi omelette hakan yasa yadauketa sukaje kasa ya kunna wutan falo ya shiga kitchen da ita baimasan ta yanda zai fara mata omelette dinba, tsaki yayi yafito yaje gaban dakin yar aikin yayi knocking bude kofan tayi adan taushashe yace âdanzo ki soyama Amal kwaiâ Amal na ganinta tamika mata hannu dan tadauketa dasauri Nura yace âwait Princess aiki zatayiâ dasauri yar aikin Ummi tace âai na iya aiki ina dauke da ita kawotaâ dan kallonta yayi sai kawai yabata Amal din ta karbeta tana murmushi ya matsa gefe fitowa tayi tana tafiya tana kallon fuskan Amal tace ânamiki omu omuâ? Dasauri Amal ta gyada mata kai tace âomu omuâ Ummi tace âto muje namiki mai dadi koâ? Amal tasake jinjina mata kai.