M SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan ko Mazan 11

Sponsored Links

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

 

EPISODE 1️⃣1️⃣

 

#Ad

Akwai wani cuta da ake kira da POLYCYSTIC OVARIAN SYNDROME(PCOS) wanda ake samun shi a mafi akasarin mata.

-CUTACE DAKE HAIFAR DA RASHIN HAIHUWA A KASHI 70-80% NA MATAN DAKE DAUKE DASHI.

-CUTACE DAKE HADDASA RIKICEWAR AL’ADA

-FITOWAN GASHI A GEMU,SAMAN CIKI,KIRJI DA BAYA

-TUMBI

-KIBA

-KURAJE A FUSKA

-YAWAN KWADAYI

-YAWAN KASALA

-RASHIN SAMUN BACCI DA DAI SAURANSU .

-SHIN an tabbatar miki da cewa kinada wannan cuta da akema lakabi da PCOS kuma kin rasa yadda zakiyi?

-SHIN kinyi amfani da duk wani mataki da kikasani amma kin kasa cin karfin CUTAN?

SHIN kinata kokari kisamu JUNA BIYU amma har yanzu shiru ba labari?

Toh sha kuruminki,nesa tazo kusa,dan 4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS CHALLENGE DINMU zai taimaka miki wurin samun cikan burinki.

KUMA ABUN ALBISHIR SHINE,ZAKI IYA SHIGA CHALLENGE DIN A PROMO PRICE NA NAIRA 5000 KACAL.

Abunda kawai kike bukata shine JAJIRCEWA da kuma NACEWA. Zaki iya shiga kungiyar mata masu wannan CUTAN a WhatsApp ta wannan link din DOMIN SAMUN INGANTATTUN BAYANAI GAMEDA WANNAN CUTAN ⬇️ https://chat.whatsapp.com/I15myu04O5i8f8DAyTxi1d.

Ko kuma kiyi subscribing YouTube Channel dinmu ME SUNA LAFIYAR MATA TV domin samun video duk sati akan wannan cutan ta wannan link din ⬇️ https://youtube.com/@LafiyarMataTv?si=mugBUh7hcuWFvezV

 

 

Episode 11

Wuraren 4 na asuba wayan Nura yashiga ruri da kyar ya iya yabude idanunshi dan rabonshi dayayi bacci irin mai dadin nan harya manta, hannunshi daya yazare ahankali daga saman ass din Ummi dake bacci ajikinshi sun rufa da bargo yadauko wayan ya kallo screen din ganin Wife yasa yadan danna gefe sabida wayan yadaina ringing ya ijiye, wayan na katsewa wayan yashiga ringing again agajiye yakai hannunshi yadauki wayan tareda picking yakai wayan kunnenshi kafinma yayi magana Hadiza kai tsaye tace “kana ina Nuri? I know ka kwashi yarana baka sanar da ni inda ka kasisu ba but at least nasan kai kana kwana agidan ina kake yau baka kwana gidan nan ba, kana ina Nuri”? Hadiza tamai ihu kaman tana magana da wanda ta haifa, wlh yamanta menene bacin rai arayuwanshi daga jin muryanta har ranshi yasoma baci da asuban farin nan just imagine, daurewa yayi batare daya daga muryanshi ba gudun kada yatada Ummi yace “ina inda nakeda farin ciki da kwanciyan hankali I can’t stand gidan dakika maida bola da abincin dasuka baci a ko’ina” sosai Hadiza taji ranta na tafarfasa tace “kadaisan ni ba kazamiya bace kuma nafi karfin ka kirani kazamiya wlh, yar aiki kuma ana kan nemo mini wata and ba maganan dana kira nayi dakaiba kenan, kana ina? A ina ka kwana eh Nuri? Where are you?” Batare daya daga murya ba yace “baki da hadi da inda nake” yana maganan ya katse wayan daga kunnenshi wani kalan ihu Hadiza tayi tana karabin dakinshi da kallo dataga an chanza komi na dakin hadda penti da furnitures kasa daurewa tayi ta dannamai kira ahankali Nura ya jaye Ummi daga jikinshi yasauka daga gadon yadauki wayan yafita daga dakin yana sauka kasa yadauki wayan ganin bazata daina kiraba tace “Nuri where are you?” Dan tsaki Nura yayi yace “me ruwanki da inda nake? When did you starting caring about inda nake?” Cikin fada tace “I’ve always cared, ya za’ayi mijina bai kwana agida ba kuma bawai cemin kayi zakai tafiya wani wuri ba bazan tambayeka ba, kana ina Nuri? And yanzun nan nashiga dakinka naga ansa new furnitures an ciro komi nada maisa bakasa an chanza funiture gidan gabaki dayaba saina dakinka kadai”? Akufule yace “banga dama ba” dan shiru Hadiza tayi saikawai taji gabanta na fadi tace “Nuri a ina ka kwana?” “Bakida right din sani” wani abu Hadiza taji ya tsayamata awuya abubuwa dayawa na zuwan mata rai, zata sake magana Nura yazare wayan daga kunnenshi ya katse tareda kashe wayan ma gabaki daya cus amarcinshi yakeso yayi in peace barin wayan yayi anan ya hayo sama cikin bacci Ummi taji ana lalubanta dudda ta gaji hakanan ta hakura yanda Nura keyi kaman yanzun ne yafara saduwa da mace bakaramin dadin Ummi yajiba dan batada wani maraba da virgin ga dumi kaman oven.

**

 

Kaman bazata daga wayanta ba saikuma ta daga tace “Ya akayi Hadiza”? Dan shiru Hadiza tayi saikuma chan tace “Anty Jams kinga ko akwai wani kalan silent bakin and cool mugunta da Nuri ya iyamin dake cimini zuciya, yake kuma bakantamini rai” yanayin yanda Anty Jamila taji muryanta yasa tace “yanzu kuma meya faru?” Cikeda damuwa sosai kaman Hadiza zata fashe da kuka tace “tun bayan sakin nan Nuri ya chanza gabaki daya, wlh bana gabanshi at all baya kulani, yau 5days kenan daya kwashe su Amal da Aman I have no idea inda yakaisu, ranan yadawo ya kwana agida to tun ranan bai kara kwana agida ba yau 4days kenan baya kwana agida, kuma bai sanar dani zaiyi tafiya ko zaije wani wajeba, ranan danai noticing bai kwana gidaba I called him da asuba ina tambayanshi yana ina ke kinji yanda yake amsani ne kaman ba Nuri na ba, yana gayamin banda right na in sani daganan ma kashe wayan yayi Anty Jams har yau nakira wayanshi akashe, wani zubin kona kira naji call waiting yana gama wayan dazaiyi saiya kashe, i WhatsApp him, namai dropping imessage, namai sako a IG duka babu wanda bai duba ba yaki kulani, bakiji yanda kirjina kemin daci ba wlh jikina nabani wani abu ina yake? Ina yaje yana kwana? Yana ina?” Duk sauraron ta Anty Jamila tagama tace “meya jawo ya barmiki gidan?” Danshiru Hadiza tayi tace “nasan ina gayamiki zakihau mini masifa but please understand me Anty Jams this is Abuja city of wealth, this is how we roll, Anty Jams kinsan menene yar aikina Ummi nan tayi tafiya zuwa kauyensu an kirata wai kanka ta ba lafiya bla bla bla shine ta tafi, ranan dana dawo kaman yaran nan zasu kasheni da aiki haka na dafa mana indomie Anty Jams wlh ni nama manta yanda ake girki yanzu I can’t even stand heat din kitchen ai sai fatana ya kode bayan uban kudin danake zubawa a skin care dina” “sannu diyar qaruna, idan akaji kina magana wani zai dauka Obasanjo ne ya haifeki ko Bill Gates, Hadiza nasan ni yayar ki ce i oath to support you but listen wlh wlh bazan iya supporting wannan rayuwan dakikeyi ba ayanzu, Hadiza this is not you ba tarbiyan nan Mama tabamu ba, ni kafin kigama bani labarin nama gane karshen nasan kinki yin komine ya kwashi yaranshi yakai inda za’a kula dasu, Hadiza you’ve failed as a wife already, yanzu kuma you are failing as a mother ace yaranki just su biyu bazaki iya kula dasu ba Nura ya kwashesu yatafi dasu wani waje” rai abace Hadiza dake fama da bakin cikin Nura tace “Anty Jams I think this is the last time zan kara kiranki nagaya miki damuwata for crying out loud when will u drop all this sentiments da mentality kusayawa yan kano and just look at me like an educated smart lady data zagaye kasashen waje? Eh fisabilillahi fa, kinzo abujan nan infact kinada friends ma acikinta, kinga yanda muke rayuwa maisa bazaki fahimce ni ba Anty jams? Menakeyi that is wrong eh menakeyi? Ba’a taba kwana agidana babu abinci ba inada mai dafawa, yarana basu taba kwana basu sami wankan safe da dare ba before bed, kome sukeso dafa musu ake, sau nawa ina cire kudi nai order expensive kids wears bama da kudin Nuri ba na sayoma yarana kaya? Bawai ina cewa Nuri baya saya musu kaya bane zai daukeshi da kanshi yakaisu different kids stores kome sukeso ya saya musu but ni kwaso musu uban kaya nake na kyalekyale different things sai kinje wardobe nasu zaki gani, headbands, ribbons menene menene I know how much nake kashema yarana, Aman nada every single collection na kids shoe da gucci suka fitar this year, Little Amal nada birkin ga receipt na handbag din worth millions duk da kudina na saya musu da zinarai, dan kunnen diamond stud ne yanzu haka a kunnen Amal ninai order shi, menene ban musu? I buy heaven and earth for them duk yar aikin dazan dauko da basaso koranta nake straight cus I wanna make my kids comfortable sune life dina, I gave them the best yar aiki dasukai approving, sukeso kuma Ummi can Babansu do that for them?? Nuri baida time na kallon yan aiki na ma balle yasan wanne yaranshi sukafi so I did all that on my own to akanme zakice I failed as a mother ko as a wife? Anty Jams Nuri yataba gayamiki yadawo daga office babu abinci agidan nan? Ba abinci about kala biyu akan dinning cikin warmers?? Ko yadawo yaga dakinshi ko bayinshi da datti ko singlets da boxers nashi ba’a wanke ba? Bazaki taba shigowa gidana ki ga datti ko daya ba akasa ko ki taka kasa, ko issues damuka samu this time kan Mamanshi sabida rainin dayamin ne sai bayan yace suzo zai sanar dani amman tunda mukai aure nataba samin matsala da uwarsa? No, mukaje kano mu sauka agidan nadan wuni daganan na gudo gidanmu so menayi? Police dana dauko is because Shegiyar kanwarsu had the audacity tashigo har gidana ta nemeni da fada tana zagina takuma yakusheni da kumbunan vampires nata, I need to show them no one can bully Hadiza in her house, so Anty Jams menene kike fadamin? Inada damuwa which kinsan bazan iya fadama friends dinaba sumin dariya bayan cika bakin danagama yi na inada karfi da iko agida suga abinda mijina kemin, I called u cus kene sister na and look at wat u are telling me eh, nayi deserving abinda Nuri kemini? Ya dannamini saki daya yanzu kuma ya maidani thrash ya kwashe yarana, shima yabar gidan yabarni ni kadai inata kwana agidan nan kaman mayya, sannan ina kiranshi yana kashe waya kuma nasan yana kunna wayanshi dan nasan dole yakira mamanshi kuma yaga messeges dina yayi ignoring, ina gayamiki kina mini masifa that i failed as a mom and a wife what have I done? Menayi? Eh”? Duk yanda taso ta daure ta rike zuciyanta kartai kuka takasa sai kawai tafashe da kuka awayan ita karan kanta bazata iya misilta kalan zafin datakeji ba na yanda Nuri ke soyata a pan dinan, ance dama blood is thicker that water wani iri Anty Jamila taji hakan yasa cikeda lallashi tace “Hadiza kinfi kowa sanin yanda nake sonki, tun kina yar karama you’ve always being my DiDi, Hadiza mun taso cikin tarbiya mai kyau muke aikin gida I remember lokacin idan yau nine da shara to kene da wanke wanke, the next day nine da wanke wanke kene da shara same goes for girki, Hadiza Baba da Mama nada rufin asiri mun taso bamu rasa komiba but we were trained muma kanmu komi muke wanki, muje aike bamu da yar aiki Hadiza, mun taso munga yanda Mama kema Baban mu girki tabashi, tamishi komi, Nura ya nuna shi girkin ki yakeso yaci how many minutes zai daukeki kimai? Is just breakfast and dinner da rana yana office, Hadiza Nura ba dan Abuja bane that’s wat nakeso ki gane bazamfare ne girman kano, ya nunamiki he doesn’t want the Abuja lifestyle dole ne saikinyi lifestyle din to please your friends and co? This is peer pressure Hadiza, must u do abinda kikaga anayi agarinku? Anyi magana kice feminism you know your rights Nura yafiki sanin rights naki tunda har mutumin nan zai bude miki kasuwanci ya daukeki kuje garuruwa ki samo contact na suppliers ki saro kaya, Hadiza Nura na mugun sonki how many men zasu iya ma matansu abinda Nura yamiki yet baki da wanda zaki cima mutunci sai shi sabida kinganshi shiru shiru baida hayaniya kuma yana sonki saikikai abusing simplicity nashi” hawaye Hadiza ta share cikin muryan kuka tace “Anty idan baka rikema maza wuta ba cin ubanka suke, ga Baraka nan mijinta juyata yake kaman lagwani, yahanata business kudi sai wanda yaga dama zai dan yammata, gashi da mata ihu agaban kowa haka kikeso Nura yamaidani? Ya takani duk sanda yaso? Noo bazan yarda ba wlh, fire for fire yanzu shine new system na zaman lafiya tsakanin mata da miji agidan aure” Anty Jamila tace “Noo fire for fire is never option, look at you yanzu jibi yanda kike kuka kina bala’in son mijinki but girman kai da al’adan yahudu da nasara yasa you are gradually loosing him” dasauri Hadiza tace “I reject it Anty Jams, bazan taba loosing Nuri na ba, yana bala’in sona, duk yan uwanshi ne da Mamanshi suka gama zugashi, Nuri baitabamin hakaba, Nuri kome zanmai baya fushi dani, baida riko ko ijiye mutum azuciya, he will still come back to me and talk to me and call me, Nuri na baitaba shareni ba, wlh all this aikin Maman shi ne da kanwarsa kuma muzuba da ni da su” girgiza kai Anty Jamila tayi zatai magana Hadiza ta tareta tace “karki damu you’ve said enough Anty Jams ko’ina Nuri yaje zaizo har nan har gidan nan yasameni bawai ina kukane sabida abin yawani dameni ba, kukan danakeyi na bakin ciki ne cus nine yakamata na dinga cusama namiji kalan bakincikin nan ba namiji ya dinga cusamin ba ninefa Anty Jams is still me Hadiza bakatakani bama nabaka hot-hot balle kuma katakani, wlh Nuri zai gane ni yagasama aya a heart, saida safe” bama ta jira amsan Anty jams ba ta katse wayan ta ijiye wayan tanabin dakinta da kallo gidan gabaki daya bayamata dadi sabida yanda ba kowa ciki, mutum rahama ne hayaniyan yaranta is something, kawai she’s not enjoying komi, mamaki take take kuma karayi itane Nuri bazai returning call nataba, lallai Nuri don get liver, tasaba saidai ita ta katsemai waya amman wai itane ya katsema waya tun ranan yaki kiranta back, yaki replying messege nata, hmmm takasa yarda ita Nuri zaima haka cus baitaba mata iskancin maza haka ba tunda sukai aure sai yau, da wannan abin har gwara ya mareta ma eh tasan mari ne bakaramin shiganta wannan silent da ignoring attitude din da Nura yamata ke damun zuciyanta ba.

****

 

Bayan 2weeks

Cur Nura yabuga two weeks yana gogan lafiyayyen amarci shida Ummi, yaki kiran Hadiza ko returning calls nata but yana kiran mai gadinshi everyweek yaturamai kudi ayi cefene wanda dama haka yakeyi dudda yasan ba girkawa zatayiba Mamanshi da yaranshi kusan kullum sai sunyi waya daman.

Lafiyayyen soyayya yake bugawa shida Ummi jinshi yake kaman wani sarki ko shugaban kasa ne ma zai fadi, baitaba sanin yar kauye can give him this much respect, affection, peace and love ba saida ya aureta, wlh ayanda Ummi kemai da ace an halasta a addini cewa mata ta bautama mijinta da Ummi zata bautamai ba tantama that girl is just an Angel, saisa shima he became like a fool kome takeso koda batace tanamaso ba zai mata.

Yau zasu koma Abuja jirginsu is by 1, yadan fita haka yabarta tana yima su Amal wasu kayan zaki a kitchen, dudda she’s hiding it but he could see fear a idanunta.

Tana zaune a kitchen tana kallon wasu cute robobi data jera su Iloka, kwakumeti, tuwon madara, tsami gaye, gullisuwa data musu tayi shiru tana tunani, bini bini gabanta na fadi batasan yaya zata kalli Anty ba, ita tunanin ta kenan danta dauka Nura ya sanar da Hadiza, baitaba mata maganan Hadiza ba ko yace any bad thing about her kullum abunsu suke baya kawo sunan matarshi aciki. Tana zaune taji an manna mata kiss dasauri ta dago kanta Nura ne, robobin ya kwasa dagakan kujeran yazauna yana facing nata yace “ya akayi Hajiya Ummi tunanin me kike”? Murmushi tamai cikeda wayincewa tace “bakomi kawo naje nayi parking a akwati” tai maganan tana mikewa dasauri tajuyar da kanta zata tafi karaf Nura ya kamo hannunta tsayawa tayi batare daya juyoba robobin ya kalla yace “baki amsaba zaki tafi kuma gashi” dasauri takai hannunta tashare hawayen daya zubomata sannan tajuyo Nura yabi kwayan idanunta da kallo hannu tamikamai ahankali tace “kawo” kin bata yayi ya ijiye robobin a gefe ya mike yakai hannunshi kan fuskanta yace “menene? Meke damunki? Talk to me menene damuwanki Ummi”? Girgizamai kai tayi dasauri tana kokarin kauda kanta tanaso ta ture hannunshi saikuma kuka ya kufce mata dasauri ta fizge kanta ta juya tareda kifa kanta a bangon kitchen din yanda yara keyi tafashe da kuka sosai tace “ni banso nakoma Abuja kabarni anan naci amanar Anty bazan iya kallonta ba, nasan tunda ka sanar da ita zancen Auren nan zuciyanta bazai mata dadi ba babu wacce keson kishiya barinma yar aikin ka, wlh wlh Allah ma yaga zuciyana bantaba so na aurema Anty Miji ba Auren kaman amafarki haka nima naga yafaru, banda kirki My Noor, ban kyautama Anty ba” Nura yadade yana kallonta all he sees is tsantsan childishness da rashin wayau, tahowa yayi ahankali wajen yajuyo da ita hannunshi yakai kan fuskanta yana sharemata yace “jibi yanda kika bata kwalliyan dakikamin eh” ahankali tace “kayakuri” murmushi yayi this is one reason dayasa yake kara sonta she apologize to him ko bataimai laifi ba, ahankali tana jikinshi yace “bazan taba iya barin matata awani gari ba ni ina wani gari, maza dayawa na haka but ni baya cikin tsarina Inason duk inda nake iyalina na wajen kinajina” gyadamai kai tayi ahankali, anatse yace “bakici amanan Hadiza ba ni mijin mata hudu ne, nan gaba still idan naji inada bukatan kara aure still zanyi Ummi, so bakiyi laifiba” yayi maganan kai tsaye yace “dake da Hadiza dukanku matayena ne daya kuke awajena babu wacce tafi wata and dukanku kuna karkashina ne, nina aureki bake kika aure ni ba, inma laifine aure kinga kenan nine nai laaifin bakeba dan nine na aureki, idan mun koma gida ki bata girmanta amatsayinta na wacce ta girmeki sannan mahaifiyar su Aman da Amal ban yarda ki mata rashin kunya or anything ba dudda nasan ba halinki bane kada ki shiga harkanta kome zatace idan kinga bazaki iyaba ki shiga daki ki kulle kofa ki kirani muyi waya idan bananan but kada kiyi fada da ita okay” gyadamai kai tayi, ahankali ya manna mata kiss a goshi yace “Ummi ina sonki sabida kina bani kwanciyan hankali kada ki chanza daga hakan okay” gyadamai kai tayi, idanunta dasuka cika da hawaye ya kalla yanda fuskanta ya kwabe sai kawai yaji sha’awanta yakamashi hannunshi yadaga yakalli Rolex dake daure a writs nashi yace “akwai sauran time zoki bani hakkina daman jiya da daddare sau biyu kawai nayi kikahau bacci raguwa”  murmushi tayi tana turamai baki kaman yar yarinya cikeda so tace “nan fa kitchen ne” yana daga riganta sama yace “eh nima ilokan wajen zan dafa a kitchen inci tunda ni bancin na roba ba” dariya Ummi tayi tace “saina cinye bakinka yau” kawomata bakin yayi yace “ai nace nabaki tunda ke kinfi son kiss kan komi kin sa lips dina sun kara pink tsabagen tsotsa oya sumbaceni” kaman jira take dasauri tayi grabbing lips nashi tashiga kissing nashi ya mannata abango yana kissing nata back yana warware wando yana ja kasa……

 

 

Saura kadan suyi missing flight nasu amman Alhamdulillah sunkai on time daman business class yabiya nan da nan sukai boarding, ashe ranan nan data daure sabida mutane ne yau harsuka sauka Abuja tana rungume ajikinshi sunyi kyau daga ita harshi ruwan amarci yasa Nura yakara haske yana sheki yadan kara kiba sabida abincin dayake samu akai akai itakuma Ummi kaman ba itaba fatanta ya goge tana sheki hannunta rikeda Samsung Z-flip dan kaita shago yayi yace ta zaba shita zaba wai sabida yanda yake budewa yana rufewa ya saya mata shikuma yana rike da hannunta suka fito suka shiga jeep dake jiransu wanda yaron Nura ne na office ya gaida Ummi akunyace ya amsa dudda tana shakkan zuwa su gida amman daurewa tayi ga mamakinta wani gida daban sukaje Nura yace “muje Muga Hajiya ko sai mu dauko yaran mu anjima saimu tafi gida” gyadamai kai tayi parking sukayi gidane babba mai kyau suka shiga suna sallama a babban falon inda su Aman da Amal ke wasa da guje guja dawata karaman yarinya dasu Hajiya da Meena da Matar Baffan shi yaran suka juyo wani irin ihu da Amal da Aman sukayi suka taho dagudu bude hannu Nura dake gabansu yayi suka taho aguje ga mamakinshi wucewa sukayi suka rungume Ummi Amal sai kawai tafashe da kuka shima Aman haka Ummi kawai ta yarda handbag da wayanta ta rungume yaran itama saiga hawaye shiru daga Nura har duka yan dakin sukayi suna kallonsu Nura saiyaji yakara jin dadi da natsuwa dakuma hamdala da auren Ummi dayayi da kyar Ummi ta iya sakinsu cikeda dabara tace “ga Dadyn ku bakumai oyoyo ba” sakin Ummi sukayi da sauri sukai wajen Dadyn su Ummi kuma tazo wajensu Hajiya ta duka ta gaishesu bayan anyi gaishe gaishe aka kawo abinci sukai nak Nura yafita sallan la’asar itama Hajiya tace bari nayi, Ummi taje  ta cewa Meena pls Meena je mota ki bude akwatina akwai wani leda shine a saman kayana ki kawomini abin Hajiyane” murmushi Meena tayi tace “nifa” dasauri tace “naki na handbag dina” wucewa Meena tayi tafita bata wani jimaba takawoma Ummi ummi ta karba Meena tace “je daki ki kaimata mana kina kuma jin kunya ni natafi kitchen” wucewa Meena kitchen tayi Ummi tawuce dakin, Hajiya na zaune kan dadduma Ummi tayi sallama Hajiya tace “shigo mana Ummi aiba saikin jira nace ki shigo ba shigo shigo maza” dakin Ummi tashiga har gaban Hajiya ta duka akunyace tabama Hajiya ledan tace “Hajiya ga tsaraban dana yo miki ba yawa” dasauri Hajiya tazaro idanu tace “laaaaaa Ummi harda wani yimini tsaraba ikon Allah, toooo Allah yayi Albarka Ummi, Allah yakawo kazantar daki” bude ledan tayi wasu manyan atampopi ne guda biyu akwatin nan da Nura yakawo gida ranan kayanta ne daya sayomata su kafin yamata proper akwati, an dinka wasu some baa dinka ba amman tadauko atampopi wayanda sukafi kyau aciki guda biyu, tasama Hajiya wani soft silipas dan madina blue da ake saidawa akauyensu tasayo, da irin dankwalayen nan na tsofaffi kallabi masu kyau guda uku daban daban, ga mamakin Ummi sai kawai Hajiya tafashe da kuka sosai tana kallon kayan tace “Ummi ni kikasiyoma duka abubuwan nan”? Adan tsorace Ummi ta kalleta danta tsorata kartaga kaman ta rainata tanada yara masu kudi yarta na Egypt amman tazo tana mata kyautan danmadina, sai kawai taga Hajiya tahau kwalama Meena da matan baffansu kira dasauri suka shigo cikeda kukan farin ciki tace “Karime, Meena ku kalli abinda yarinyar nan tasayo mini, babu wanda yataba siyamini tsaraba irin wannan daya faranta mini rai haka, nadade ina neman dan madina sabida ciwon kafana kinsan takalmin da laushi duk silipas da ake sayomini saidai nasa ba yanda zanyi, jibi kalluba ku kalli atampopi na, Allah miki albarka Ummi, yanda kika faranta mini ubangiji Allah ya fara tamiki” sai kawai sukahau yima Ummi godiya akunyace ta tashi tafita Meena tabiyota sukaje dakin da Meena ke kwana sai Meena taji takara sonta sabida yanda tasaka Hajiya farin ciki kuma tai alkawari zata kira su Ya Aisha dukta fadi musu dudda tasan ma Hajiya zata fadi, dan babu wanda bazaiji labarin kyautan nan ba yau haka Hajiya taje bata boye abin arziki.

 

Nura na shigowa gidan Hajiya tace “Nura kalli tsaraban da matanka tayomini ohhh Nura yarinyar nan Ummi saidai Allah ya yimata albarka kawai, kasan yanda silipas din nan da kalluban nan sukamin dadi kuwa, gashi yamin chass akafa, achan achan Masha Allah kaga kiramini kanwarka Aishaa nagaya mata abinda matarka tamin” yana xaune nan yana taya Hajiya dialing numbers saida takira yaranta uku mata ta gayamusu sukace asa Meena ta tura musu lomban amaryan Ya Nura duk zasu kira sunata godiya.

Yanda Hajiya ke murna tana fadama kowa kyautan nan sai shiwa Ummi albarka take bakaramin dadi Nura yaji aranshi ba yana kallon atampopin, shine yasayo su anan Adamawa abinda yafi bashi mamaki yanda sunfi kowani atampa kyau cikin kayan daya sayo mata, design nasu is so beautiful but suta dauka tabawa Hajiya kuma wlh bata fadamai ba, baimasan tana tareda takalman nan ko kallbin nan ba that means tun akuayensu tasayo, kawai saiyaji yakara respecting yarinyar imagine ko shi baisayo musu tsaraba ba shi dama ansanshi baya tsaraba bai iya riko tsarababa amman yatashi sayo abu zai shiga super market ya jido kaya, abin really touched him bazaima iya misilta dadin dayaji ba, duk wanda zai tayashi da Hajiyan shi farin ciki babu abinda bazaima mutumin ba cus Hajiya number 1 ce arayuwanshi.

Zama yayi abinshi tareda Hajiya anan dakin nata sunata hira bini bini ta shiwa Ummi albarka har abin yasa yasomajin kishi maisa shima bai kawo tsaraba ba yasami kalan addu’an nan da Hajiya kema Ummi haka?  Kawai abin saiya zama kaman eye opener dagayau duk yayi tafiya kobaiso saiya sayo tsaraba yakawo shima In sha Allah Ummi takoyamai something in this his old age.

“Ka sanarda Hadiza kayi aure Nura?” Dasauri yadago kanshi daga katifa yakalli Hajiya jin tambayanta ganin yayi shiru yasa tace “baka kyautaba Nura ai kome Hadiza tamaka ba’a haka, bai dace kawai taga mata daga sama ba dan haka ka sanar da ita yau, sannan ka kira kanwarka Aisha ko ita ko Maimuna ko Matar Baffan ka Karemi kabasu kudi ahadoma Ummi da Hadiza akwati, sannan kaji tsoron Allah kayi adalci atsakanin su dan rashin yinsa zai kaika wuta, ka manta duka halin Hadiza na baya ka bude sabon chapter yanzu and treat them equally kada ka cutar da Hadiza sannan kada ka bari ta cutar da Ummi dubada tafita wayewa dakuma shekaru, sannan kada kabari Ummi ta raina Hadiza ganin itace amarya ko ka nuna mata kafifitata kan Hadiza, kada ka kuskura ka rike matanka ahaka kowacce ka rike sirrinta azuciyanka kada ka sanar da Hadiza kanada matsala da Ummi haka kada kasanar da Ummi kanada matsala da Hadiza, ka kama girmanka kayi tsayin daka akansu, ka tsare hakki dakuma mutuncin kowa kanajina Nura” Gyadamata kai yayi ahankali yace “naji Hajiya” kanshi ta shafa tace “kayafema Hadiza kome tamaka kada ka riketa da laifinta please sannan yau karaba musu kwana, tunda baka gari kuma duk kana tareda Ummi ne lokacin yau kashiga dakin Hadiza kajini”? Gyadamata kai yayi yace “naji” ahankali tace “Allah yamaka Albarka Nura, yanda kake kulawa dani dinnan ka tsaya akan lamarina, kabani ci kabani sha kamin duk abinda nakeso sannan kaji magana ta Nura ubangiji Allah ya saka mata da aljanna” murmushi yamata yace “Ameen Hajiya nagode”  murmushi tamai tace “idan naji sauki komi ya tabbata saika gana da yaron dake neman Auren Auta ko”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya amman tana aure xakibar kano ki dawo gidana da zama bazan barki ki zauna ke kadaiba gaskiya” dasauri Hajiya tace “kai barni da Abujan nan wlh ba sonta nake ba nafison kano” dasauri yace “Hajiya akwai flat dinki daban agidana, nan da wata biyu za’a gama komi bazaki zauna ke kadaiba a kano gaskiya” ahankali tace “to baridai lokacin yayi sai muyi wannan maganan, tashi kaje masallaci an tada salla leka min Meena da Ummi kagani Allah sa sun tuna sun hada kayan su Amal ba sun tsaya hira ba” wucewa tayi yafita dakin da Meena take yaje yadaga labule yayi Ummi kadaice adakin tana shirya kayan su Aman bama tasan da zuwanshi ba sai aikin take harta ga Amal zaune gefenta hannunta da tuwon madara tanasha dan murmushi yayi akan Ummi yasoma sanin akwai wacce zata iyaso yaranka tsakani ga Allah koda ba ita ta haifesu ba saidai basu da yawa a duniya, gyaran murya yayi dasauri Ummi tadago kanta ta kalleshi folding hannu yayi akirji yace “awanki nawa baki sani a ido ba”? Murmushi tayi kaman mai tunani tace “uhmmmm awa biyu da minti ashirin da uku da sakan shidda kenan bansa Dadyn Amal a idona ba” dasauri yace “shine kuma kike murmushi” hadiye murmushin tayi tace “tuba nake nadaina Yallabai” kwafa yayi yace “kinci sa’a akwai Princess anan” dasauri tajuya taja hancin Amal tace “ai princess zaki dinga cetona koda yaushe ko?” Amal tace “yesssss Anty Ummi na” dariya tayi takalleshi tace “kaji ko” hararanta yayi yana murmushi yace “kuyi salla ku shirya nadawo zamu tafi” gyadamai kai tayi tace “to mijina, adawo lafiya asamu a addu’a fa idan kana cikin jam’in nan kaji” juyawa yayi yace “naji matata” yayi murmushi yawuce Meena tazo da gudu tace “ke Ummi haka kuke soyewa keda Yayana, zona koya miki zama da Hadiza……..”

 

 

Yana dawowa aka zuba komi a mota harda abincin dare Hajiya tasa Meena tazuba musu a babban kula dantasan matan gidan bata dafaba kuma bazatazo Ummi tahau aiki da daddaren nan ba suka musu sallama suka tafi saida ya tsaya yayi salla ma……….

 

Parking motarshi yayi Ummi taji gabanta yafadi kallon gidan tayi takasa fitowa su Amal dake tareda ita sukace “Anty Ummi muje gida” daidai lokacin Nura na bude musu baya yakalleta suka hada ido yace “muje” gyadamai kai ahankali, ganin yanda tayi yasa yamika mata hannunshi ahankali takama yafito da ita sannan yadauki Amal itakuma takama hannun Aman gateman namusu sannu da zuwa yana bude boot na mota dan kwaso akwatinan su, bude kofan falon Nura yayi ahankali da sallama abakinshi Hadiza na zaune kan kujera daga ita sai wani material data saka na batic mai shegen kyau gown yana walkiya walwal kyau purple hannunta rikeda wayanta dake kunne tana magana ga MacBook nata kan cinyanta tana aiki tadan saka farin reading glasses a idanunta kanta da kalaba yan kananu ganin Nura rikeda Amal yasa dasauri tace “I will call you back Hajar just send the order ta IG ko WhatsApp me” takatse wayan dasauri tayi tana kallon Nura dashima yake kallonta batare datacemai uppan ba dan fushi take dashi sosai sabida abinda yamata, shigowa Nura yayi saikuma yajuya yakalli Ummi data tsaya gaban kofan batare data shigoba Nura yace “shigo” gyadamai kai tayi tashigo ahankali kanta akasa tana rikeda hannun Aman Hadiza tabita da kallon mamaki irin mugun mamaki daidai nan Gateman na shigo da akwatinan su yabarsu anan falo yawuce yafita bayan yagaida Hadiza dako kallonshi batayi ba balle yasaran zata amsa, ahankali Ummi kanta na kasa tace “ina yini Anty” har lokacin Hadiza kallon Ummi data chanza mata take a ido sosai ganinta tareda mijinta a ina yaganta? Taya suka hadu? Tayaya suka dawo gidan tare? Yarinyar dake kauye? Yanda tambayan ke cinta arai yasa batare data amsa gaisuwan ba tace “meya hadaki da mijina dakuka shigo gidan tare ko ince kuka dawo gidan tare? Kumama bance kada ki kara dawomin gida ba tunda kin tafi ganin kakarki nariga nakoreki, na sallameki me kike dawo yimini agida kuma sannan kika shigo tareda mijina”? Sauke Amal Nura yayi yakalli Aman yace “kuje dakinku asama kujira gani nan zuwa” dasauri Amal tace “Daddy zakazo ka karanta mana stories?” Gyadamata kai yayi dasauri sukai stairs suka wuce sama without saying a word to Maman su kaman ma bata falon.

 

Dudda Nura yaji ciwon ko gaidashi batayi ba balle amsa sallaman dayayi ko cemai sannu da zuwa batayiba amman saiya daure yakalli Ummi yace “zoki zauna nayi magana daku” Ummi kanta na kasa ta taho Hadiza jitayi jikinta da kafafunta sun fara rawa hakan yasa tasauke MacBook nata dake kan cinyanta ganin wani attention da care da Nura kebama Yarinyar nan wanda bata taba ganin yayiba tsawon kusan a year datake aiki agidansu, shida ko kallo yar aiki bata isheshi bama, ganin Ummi takasa motsi yasa Nura yazo da kanshi ahankali yakai hannunshi yakama hannunta dawani kalan sauri Hadiza tamike tsaye tana kallon Nura dataga yariko hannun Ummi, shigowa da Ummi yayi cikin falon yazaunar da ita kan kujera shikuma yazauna kan 1 sitter yana facing nasu yakalli Hadiza dake tsaye yace “sit” cikin bugawan kirji trying to calm herself down but takasa sabida yanda kirjinta ke tafarfasan bala’i ganin yanda yakamo hannun yar aikinta tace “Nuri just say abinda kakeso kafadi basaina zauna ba cus I don’t understand sa yar aikin nan zama kan kujera na dakayi kana rike mata hannu, maganan me zakamin eh”? Sosai Nura ke kallonta ganin rashin mutuncin ta da rashin kunyanta na nan dudda yadan punishing nata kwanan nan saikuma anatse yace “Hadiza Ummi ba yar aiki bace yanzu, naje har kauyensu na nemi aurenta an bani, yau kwana goma sha hudu da daura mana aure! Ummi is my wife!”.

 

 

 

 

 

Today da Matan Auren gidan nake when was the last time kika daga waya kika kira Maman mijinki just to say Hi Mama yakike?? Makesure kin kira yau🥰

 

 

Idan kuna gari daya when was the last time taci abincin ki?? Yau weekend yi lafiyayyan girki ki aikamata 🥰

 

When was the last time kika siya mata gifts? Kikai making nata happy??

Do that yauma😎

 

Ance akwai a thousand ways to zuciyan miji and one of those ways is when you carry his Mom asaman kanki, lokacin dazaki dinga kula da mahaifiyarshi kaman taki.❤️

 

Like I said still yau zan fada this book badan fun ko dadi nayi ba nayishi ne for US maybe this book yarage rate na divorce da ake samu Kwanan nan agidajen aure.

Everything in this book is a lesson not just the kishiya part, zamantakewa, kyautatawa, soyayya, yara da sauransu duka nakawo.❤️

 

I have a question for Mamas, duba da maganan na batai failing as a Mom ba cus tana sayama yaranta heaven on earth and tabasu the best yar aiki dasuke so inaso naji view naku kuna ganin GIFTS kesa yara su shaku da Mom nasu ko spending quality time dasu??

And is it possible yara su fison wacce ba ita ta haifesu ba kan wacce ta haifesu????

Maisa Aman and Amal prefers Ummi to Maman su?????

 

 

WEEKEND PROMO💃💃

 

I have special announcement masu son shiga class na MATAN AURE you can all pay 1k now kafin Monday yakoma 2k, registration is still ongoing kafin murufe.

🔊🔊🔊🔊🎊🎊🎊🎊🎊

 

Don’t miss MATAN AURE dina class for anything, I will give you all!!

Sirri zan baku da dama

Zan koya muku how to love mijinki in your own way kaman yanda Ummi keyi.

Shagwaba, iya magana 🥰

Uwa uba iya kwanciya❤️, yanda ake siyan zuciyan miji, how to steal heart na Inlaws naki and so much more.😍

Idan kina tunanin asiri ko kayan mata ke siyan zuciyan miji come to my group na nuna miki gaskiya.

HAUSA CLASS NE BA TURENCI BA

 

REGISTRATION IS 1k NOW

 

6353995766 M Shakur world Moniepoint

Send ur evidence of payment ta PC zanyi adding naki a group.

click on this link and chat me up directly

wa.me/+2347012181461

Leave a Reply

Back to top button