Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan ko Mazan 26

Sponsored Links

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣6️⃣
https://chat.whatsapp.com/KO6bdcXjxmh2l6pM6T0meI

In mutum yanason yayi register Kuma yayi siyayyar 🌟3 free registration ne
Kuma Ina adashen products din GHT in mutum beda halin Siya Nan take

08066136431

Note: Ni ba lawyer bace! Though I consulted some lawyers irin su Majal and co😍 Incase kunga mistakes no mind me, I be health personnel ejor❤️

26
Shiga cikin court room din sukayi hada ido yayi da Hadiza dataci gayu yanda kasan zataje gasan kyau tana sanye dawani vilisco embellish atampa maroon ta kafa daure tayi kyau gefenta kuma Zeenah ne zaune itama ta kallo Nuran, dauke kai yayi daga kallonta yawuce yazauna kusa da lawyer shi while Alhaji Musa yazauna a daya daga cikin kujeran dake row din bayansu, Hadiza itama tashi tayi tawuce tazauna kusa da lawyer ta wata attajiran mata ne haka taci glass Mrs Oyenyi Chichi Ebenezar, daidai nan Alkali ya shigo aka tashi akai introducing case din sannan aka kira Nura kanta yafito ya tsaya yayi rantsuwa Mrs Oyenyi ta mike taje gaban Nura ta tsaya tace “Mr Nura kaida Hadiza has been married for 10yrs 9month correct?” Anatse Nura yace “yes” anatse matan tace “describe relationship dinta dakai a tsawon shekarun” dan shiru Nura yayi saikuma ya kalli Hadiza dake kallonshi kyur, Mrs Oyenyi tajuya takalli abinda yake kallo tace “are you trying to blackmail my client Nura”? Dauke idanunshi yayi yace “no” Mrs Oyenyi tace “to bama kotu amsan tambayan da na maka” ahankali Nura yace “relationship dina da ita is just like relationship din any other couples, we live, we share good moments and we have arguments just like every other couples do” Mrs Oyenyi tace “babu any history of abuse ko molestation” Dasauri Lawyer Nura yace “objection my lord, mesa take sa magana abakin client dina is just kaman tariga tai concluding cewa client dina is an abuser” Alkali yace “objection overrule cigaba” Mrs Oyenyi tai murmushi tana kallon Nura tace “ina jinka Nura” Dan shiru Nura yayi sai chan yace “bantaba molesting Hadiza ba or abuse her banda ji…….” Mrs Oyenyi tai blocking nashi tace “matanka tace kasha molesting nata not once or twice ko bataso tai wani abu dakai kanayi” dafe kanshi Alhaji Musa yayi cikeda rashin jin dadi, dasauri Hadiza ta waiga ta kalli Zeenah cikin whispering tace “bancema Mrs Oyenyi yana molesting dina ba what is she saying?” Cikin whispering Zeenah tace “ni nace takara dashi sabida yaji ajikinsa ai kin gayamin abinda yamiki kenan daya auro Ummi” cikeda rashin jin dadi Hadiza zatai magana Alkali yace “silent” akai shiru, Mrs Oyenyi tajuya tadawo gaban bencinta tadauki wani file ta taho ta bayar tace “mai girma mai shari’a Nura yasha yima client dina fin karfi, ihu, harma yakai yana dukanta yanzu, cikin file din nan na dauke da evidence na farko hoton fuskan Cleint dina ne Hadiza da fuskanta dazaka ga yatsu biyar na Nura sunyi jazur a fuskanta wanda har yakaita ga asibiti aka dubata takarbi pain killers, sannan auren Nura yazama babban damuwa ga client dina bata da kwanciyan hankali da peace of mind agidanshi haryakai ga just about a weeek ago tana asibiti for case na heart sabida damuwan shi duk evidence na medical history nata is there, ina mai rokon kotu ta bima Hadiza hakkinta duba da irin fighting datayı for her life a hospital for the past two weeks duka duka yaushe akai discharging nata amman harya mata kalan wannan marin what if marin yayi leading nata takara samin cardiac arrest bayan yasan clearly an fadi a asibiti bazata kara surviving ba??”
Tashi lawyer Nura yayi zaiyi magana da sauri Nura yadagamai hannu alamun baiso yayi magana yazo dashi nan ne dan kawai yamai arranging bail da sauran formalities, ahankali Nura ya kalli Alkalin dake kallonshi ganin yahana lawyer magana yace “Yallabai I am guilty!” Dasauri daga Lawyer shi har Alhaji Musa har ita Hadizan suka kalli Nura dan bata taba tunanin Nura ko lawyer shi bazasuyi gardama ba, dan shiru Nura yayi chan yace “I let my emotions get the best of me, and I sincerely apologize for that” ahankali yadaga kanshi yakalli Hadiza yace “Hadiza am sorry for slapping you and for all d pains dakikace nai causing miki” Nura zai magana Lawyer shi yatashi da sauri yace “Mai girma mai shari’a client dina ya yarda yayi laifi kuma yabada hakuri muna pleading for mercy to pay fine na domestic violence din da duka charges dinma” dan hamdala Hadiza tayi tana karkada cinyoyinta dan feets nata are so cold batason akai Nuran ta gidan yari she’s just hoping ayarda ya biya fine din.
Tass Alkali yagama rubuce rubucen shi kafin yadago yace “kotu ta yaba da yanda Nura bai bawa kotu wahala ba, ya karbi laifin shi sannan yabada hakuri, duba da baida wani bad record kotu ta yanke hukuncin rike Nura harsai yabiya fine na naira dubu dari uku, 300,000!” Dasauri Alhaji Musa yace “Alhamdulillah” Alkali yace “idan akwai wanda keda wani magana cikin parties din zasu iyayi” hannu Nura yadaga hakan yasa Alkali yace “ina jinka” tashi Nura yayi ya kalli Alkali anatse yace “inason kotu ta shaida ni Nura na saki matata Hadiza SAKI DAYA!” Wani kalan dum! Dummmm! Hadiza taji azuciyanta yayi dawani kalan sauri tadaga kanta takalli Nura hannunta na rawa rawa, Nura na kallon Alkali yace “inason kotun nan tazama shamaki tsakanina da ita, kada Hadiza tasake daga kafa ta taka gidana! Duka wani abu nata na cikin gidana daidai da cokali zan tattara nasa a mota yau ba gobe ba na aika gidan iyayenta inda na aurota, sannan kada ta daukan mini yarana! Alkali inaso kamin katanga da ita!” Hawaye Hadiza taji zasu zubo daga idanunta tarikesu gam tana fuzgar da iska da baki kirjinta kaman ana barza masara dasauri Zeenah tazo ta bayanta tana mata whispering “kada ki kuskura ki nuna kinji wani abu dan dadi zaiji, abinda yakeso yagani kenan” daurewa Hadiza tayi ta rike hawayen Alkali yagama rubuce rubuce yace “you can sit” yakalli Hadiza yace “kaman yanda kikaji mijinki ya sakeki kuma yamiki shamaki da gida wanda yake nashi, dan haka kada ki kara sa kafa agidan shi kikai haka zai iya daukaka kara akanki, zancen yara kuma dake da shi zaku iya daukaka kara kuyi case na custody yara” cikeda karfin hali Hadiza tace “no need yara nawa ne ko suna hannunshi ko suna hannun uban idan inason ganinsu zan kirashi shiya kawominsu, kuma dama koda bai sakeni ba ni zancemai ya sakeni, me akeyi da namiji mai dukan mata” wani dadi Zeenah taji hardama Hadiza tafi kasa kasa Alkali yace “kotu tazo karshe” yatashi yafice police sukazo aka wuce da Nura lawyer shi da Alhaji Musa suka bisu, court room din yarage saura su Hadiza, hawayen da Hadiza ke rikewa ne suka zubomata wlh bazamata iya describing in words how she’s feeling right now ba, bata taba expecting Nura zai saketa ba sabida ta makashi a kotu, tunanin baimazo ranta ba yanzu Nura yamata saki biyu kenan, Mrs Oyenyi da bata wani san komiba ita she’s just a lawyer tace “why are you crying? You should be happy a man like this dayayi inflicting so much pain in you yasake ki infact this calls for celebration ma” Zeenah tace “owooo tell her oo Mrs Oyenyi, I don’t know why Hadiza base her whole life on this guy not knowing yanzu ne zaki fara cin rayuwanki da kyau dakuma tsinke, ni dayama miki biyu yacikashe” dasauri Hadiza tadago jajayen idanunta takalleta Zeenah tace “yes you should be free of this Nura for good haba yanzu kuma abin takaici kina wani zubar da precious hawayenki sabida namiji wlh tir Hadiza kinji kunya, you are a disgrace to mata damukasan ciwon kanmu, you are a disgrace to all feminist out there” hannu Hadiza tasa ta share fuskanta tass tai murmushi tace “ba ina kuka sabida Nura yasakeni bane Zeenah, kuka nayi sabida kalman saki feels somehow ajikin mata, but danya sakeni sai mene harda wani amini katanga da gidanshi tunda gidan dirhami gareshi ko gidan sarkin dubai ne dashi ko prince of Saudi useless Man gidan da I can buy like 10 of it” Zeenah tace “owooo, tashi mutafi jor let’s go and celebrate book hotel and sleep today kafin gobe muje house hunting” dasauri Hadiza tace “gidan ki fa? I thought anan zan kwana”? Dan murmushin yake Zeenah tayi tace “ohh my bad ni nama manta ba matsala saiki kwana agidana, muje let’s call Baraka and pick her up a hanya” tashi Mrs Oyenyi tayi sukai sallama daman sun gama biyanta suka wuce ahanya suka dauki Baraka wacce Sam bataji dadin labarin ba amman ina ruwanta, deep down Hadiza is so worried amman Zeenah taki bata room to show how worried she is kuma itama din batason suce tacika depending on a man ko she’s a disgrace to feminist.
Sai bayan magrib suka tafi gidan Zeenah, babban gidane mai kyau but baimakai gidan Hadiza girma da kyau dinba dudda matar minister ce, shiga sukayi ciki, Zeenah na murmushi tace “ai you are full ko kina bukatan abinci naga munci mun koshi a inda mukaje bari nabaki ruwa kinsan ni yan aiki na basa kwana da yamma suke tafiya saisa kikaga zan baki ruwa da kaina” Gyadamata kai Hadiza tayi Zeenah tadauko ruwa taba Hadiza tace “muje na kaiki dakinki” dan kallonta Hadiza tayi saitaga kaman she’s rushing ko ruwan fa bata budeba amman bata damuba ta tashi tabita sukaje sama takaita wani daki tace “to saida safe”gyadamata kai Hadiza tayi dudda she wanted su danyi hira har zuwa irin 12 din nan nadare but she guess tagaji tunda tun safe suna tare wucewa Zeena tayi agurguje ta sauko kasa ta kwashi takalmin Hadiza dake gaban kofa tashigo dasu da sauri ta wuce kitchen dinta taboye takalmin abaya shi kofa sannan tashiga kitchen agurguje fa tashiga hada girki.

Hadiza datagaji dan bayan tayi sallan isha’i bacci yayi awon gaba da ita cikin bacci mai nauyin gaske taji hayaniya da kaman karan fashewan abu hakan yasa ta bude idanunta ahankali baccin na fita daga idanunta muryan namiji taji yana cewa “takalmin waye wannan Zeenatu? Wakika kawo gidan nan bayan nagaya miki banason ana zuwa mini gidana?” muryan Zeenah taji kasa kasa bataji metake cewaba saikuma chan takarajin karan fashewa abu kaman plate haka ko glass cup yayi ihu yace “ubanwa yace ki kawo mini wata kawarki gidana I don’t care if she’s squatting here sabida mijinta yasaketa, are you deaf? Are you stupid, gidan ki ne? Is this house yours? Who do you think you are Zeenatu dazaki dinga shigo da mutane ba tareda kin sanar da ni ba? Oya go and call her ta tattara yinata yinata tabarmin gidana inba hakaba wlh kema koranki zanyi yanzun nan” zaro idanu Hadiza tayi saikuma ta dafa kirjinta Zeenah ne da mijinta ke fada haka akanta ake magana ko wata kawan daban? Tashi tayi ahankali tabude kofan dakinta tafito tayi tafiya tadan leka downstairs ta yanda basa ganinta Zeenah tagani tayi kneeling awajen dinning da duk an faffasa plates tahada hannunta biyu harda kuka tana rokon wani attajirin mutum dabai wani tsufa ba kaman Nurin ta yake, murya kasa kasa tana cewa “dan Allah karufamin asiri kada ka tozar ta ni kabarta ta kwana gobe zata tafi i promise” kana ganinshi kaga masifaffe har zufa ke keto mai a hanci da goshi, ga takalman ta dataga an wawwatsar a falo mutuwan tsaye Hadiza tayi dataga yadauki cup yakara bugawa a katsa ita kanta Hadizan saida ta firgita kaman glass zaizo nan sama inda take ya shiga jikinta cikin fushi yace “stop begging me useless woman who are you dazaki dingayi yanda kikaga dama agidana, jeki kira kawar naki kubar gidana dagake har ita” hannu Hadiza tasa ta taushe bakinta mamaki sai kawai ta juya fuuu cikeda zuciya dan tafi karfin wulakanci akan wannan kurkukun gidan tawuce dakin datake tadauki handbag nata kawai tashiga saukowa jin tafiya yasa dukansu suka juyo dasauri Zeenah ta mike tana goge fuskanta ta kakalo murmushi cike da duniyanci tace “Hadiza zoki gaisa da Baby hala karan plate ya tadaki daga bacci ko dan dazu na leko naga kinyi bacci, wlh bari mukayi yanzun nan” wani kallo Hadiza kema Zeenah yanda tayi just now kaman hawainiya sai kawai ta tsinke da lamarinta batace komiba tace “ina key motata”? Center table Zeenah ta nuna mata Hadiza na tsallake tsallake kwallaben dakenan har falon tawuce tadauki key motanta ta kwashi takalmanta tai wajen kofa cikeda zuciya Mijin Zeenah ya nuna Hadiza da hannu yace “jibi mara kunyan da kike cewa ta kwana agidana taganni bata iya gaidani ba” azuciye Hadiza ta juyo tace “anki agaidakan mata mutuncin mahaukac…….” “Hadizaaaaaaa!!!!!!” Zeenah tama Hadiza wani kalan ihu kaman zata tsaga gidan tace “karki kuskura ki zagin mijina wallahi cus zakiga other side of me” baki Hadiza tabude completely flabbergasted tana kallon Zeenah, saikuma chan ta nuna kanta tace “Zeenah you, me!” For the first time in history the chatterbox Hadiza was speechless tama kasa constructing sentence tsabagen shock tana kallon camellion Zeenah, Zeenah tace “yes zaki shigo har gidana ki zagi mijina are you okay an gayamiki irin ex mijinki ne shi Nura”? Shiru Hadiza tayi tana kallon Zeenah, zata sake maganan mijin Zeenah yace “kneel down ki gayamin wace jakace wannan mara tarbiya kika kawomin gida, and you leave my house kafin nakira bodyguards dina a kulleki” ya nuna Hadiza da yatsa cike da wulakanci kaman kashi yakema magana, Hadiza ga mamakinta kneeling taga Zeenah tayi agabanshi kaman baiwa sai kawai tajuya da gudu sosai fa tawuce motanta da dazu Zeenah tayi parking achan bayan gida sai yanzu tagane mesa tai parking awajen ashe batason mijin yasan takawo wata gida ne tashiga motan da sauri ta tuki tafito around 12:15Am nadare kawai tahau kuka cus from just little abinda tagani dudda mijin Zeenah is a minister tafi Zeenah enjoying rayuwa in every aspect starting from gidama, maybe halan ya ijiye Zeenah a wannan gidan sabida itane Amarya kuma batada yara but still she expect gidan minister yafi gidan mijinta that is into real estate girma da komi amman gidan ta yafi gidan nan da girma da komu har interiors na gidan ta yafi na Zeenah kyau, not to talk of babban gidan da Nura ke gina mata da ba’a gamaba lokacin daya kaita gidan ita kanta saida tai ihu wani kalan design na gini yake da bata taba ganin kalanshi a abujan nan ba, look at yanda Zeenah ke living in fear tun a kotu data cemata zata kwana agidan ta ta lura da wani abu, look at yanda take baiwa in her own house kneeling agaban miji yana fashe fasten utensils agabanki what if tasami injury, sannan bataga yar aiki ko guda daya ba halama batada yan aiki, jibi yanda mijin keta ihu akan me zata kawo wata gidanshi batare data fadamai ba ita look at yanda take kawo kowa gidanta ba ruwan Nura itanema Nura bai isa yakawo kowa bai fadamata ba, Zeenah has been lying to them all this while tana zuga ita da Baraka suci uban mijinsu yanda takeyi so dama karya take, imagine Zeenah data gama zugata dazu harda cemata she’s a disgrace to all feminist out there, look at Zeenah miji ke bossing around yana sata kneeling kaman student, Zeenah dake gayamata taji kunya tana kuka kan namiji look at Zeenah da life datakeyi! Ya Allah! Daidai Hadiza na parking acikin Hilton hotel tadade a mota tai kuka harta godema Allah gash Anty Jams sun kirata bata dauka ba, bawai tana nadaman abinda tayi bane for slapping her da Nura yayi he deserves to be thought a lesson but she’s just hurt yanda Zeenah made her look so stupid and a fool bayan tafita more gidan miji in every aspect dudda tana auren minister, but Zeenah made her look kaman itace the unluckiest wife in history, koda yaushe ji take she wants to be rulling her house kaman yanda Zeenah ke gaya musu tanayi, and abinda ke faruwa is bata cika zuwa gidansu ba cus kullum tana shago kawancen su is suzo shagonta ayi hira a fita, sudanje occasion ko outing that is it, Hadiza batada yawon zuwa gidan kawaye business nata baya barinta saisa batasan actual condition na gidan Zeenah ba, mesa Zeenah zata zugata bayan itane ke facing abuse ma agidanta not she dan Nura bai taba fasa plates a inda take ba, Zeenah lied to her and betray her, tazugata and made her look so stupid, fool, and immature.
Hadiza taci kuka ta koshi sannan tafito taje tai booking daki jin kanta na sarawa ta tsani karya da yaudara dan ita kozata mutu bata karya, bata yaudara, bata pretending to be who she’s not, she’s just herself aduk inda zataje a duniya be it to mijinta, relatives nata ko friends natama, ganin kanta zai tsage yasa taje ta kwanta.

BECAREFUL WITH FRIENDS MATAN AURE!!!!
SOME FRIENDS ARE EVIL!! SNITCH!! ENVIOUS!! WISE!! AND CROOKS!!!
Zeenah is just one!!! Now ku fadamin mesa Zeenah tama Hadiza what she did to her??? Please kubani amsan nan!

MATAN AURE KUDENA FADAMA KAWAYEN KU MATSALOLIN KU wani zubin daka fadama friends your issues gwara stranger na rantse, bawai ina cewa all friends are bad bane no! But some friends basason suga progress arayuwanki ko cigaba.

Dan Allah kubarni nayi this book yanda na tsara nace zan muku magana akan major abubuwan dake kashe aure ayau which the most common one is FEMINISM wanda shine nake nuna muku abubuwan dayake causing arayuwan mu na yau, look at inda Feminism yayi landing Hadiza, this book is not for enjoyment or catching fun novel nope! Idan irin wannan kukeso I have them very tantalizing ma ga dadi check my wattpad page Mshakurworld. This novel is an educating novel dayake nuna illolin of some actions na both side, look at how nake rubuta this book any action na mutum ina nuna how that person thinks and see things, still ina nuna muku idan kina kaza it can leads to this and this and this, this novel is about auren mutum biyu Nura and Hadiza, life nasu, origin na problem din, kaza kaza kaza, I break everything down for you, and I can tell you for free Nura is the origin na this issues for not teaching Hadiza and guiding her as her leader, ya saki Hadiza dayawa, yabata freedom da yawa, saisa hakuri ma da shiru shiru idan yayi yawa is a disease, lokacin dazakace okay bari nafara gyara karfen yariga yanuna harma ya nika, please masu cewa am bias am this and that look at this book from different perspectives and you will see abinda nake kokarin yi.
This is a wake up call to all of us mata cewa mu gyara, and this is a wake up call to maza na idan matanku nayi ba daidai ba correct them dan ba soyayya bane dan kayi letting go of mistake na mata infact cutar da ita ma kakeyi indirectly.

Anata cewa shi mutum baya chanza wa menene menene, kowa aduniya na da tendency chanza wa either from good to bad or from bad to good, wasu they just have to experience life outside the box kafin suyi tunani, look at Hadiza yanzu just few minutes datayi agidan Zeenah she saw rayuwan wasu couples and tafara tunani this that and this, Hadiza will change guys I know abinda nakeyi but mubarta tayi rayuwan da babu Nura aciki muga how things goes and I sincerely hope you will understand cewa littafin nan nayi shi ne for the betterment of our society in general both daga bangaren mata da bangaren maza Thank you.
Allah yamana albarka gabaki daya, yau nabude layina you can either call me or drop a message kota whatsapp kota text 07012181461.

Zaku shiga shiga group na matan aure na with just 2k. Chat me up idan kinaso.
THANK YOU ❤️

Leave a Reply

Back to top button