M SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan Ko Mazan 1

Sponsored Links

 

💫MATAN??? Ko MAZAN???💫

 

 

✍🏻M SHAKUR

 

 

Chapter 1- FEMINISM

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINKAI.

 

Note: Wannan littafin kagaggen labari ne ba rayuwan wata ko wani narubuta ba, is just fiction danai highlighting major issues dake kawo misunderstanding a aure, I hope we all read and learn.

🙏

 

 

 

 

EPISODE 1️⃣

Zaune suke akan kujerun dake cikin garden din yahuza suya na bayan central mosque. Maza hudu ne, dukansu suna sanye da suit but duk sun ciccire jacket din sun makala jikin kujerun dasuke kai da alamun  daga wajen aiki suke, gasassun kaji ne agabansu da shayi sunasha suna kallon katon TV dake wajen inda ake buga kwallo tsakanin Manchaster da chealsea.

Kana ganinsu kasan suna bala’in enjoying match din dan sai gardama suke suna dariya kyakyakya.

Wayan daga daga cikinsu ne yay kara hakan yasa yakai hannunshi yataba aljihun gaban riganshi batare daya janye idanunshi dagakan TV ba yaciro wayan yajanye kanshi daga TV yakalli screen din ganin Madam yasa yadanyi tsaki ya ijiye wayan yacigaba da ringing sauran mazan dayake zaune dasu suka kalleshi dan yake yayi yakai hannunshi yana shafa kirjinshi yace “Madam ce wlh ke kirana tahanani sukuni” dauke kansu duka sukai daga kallonshi kaman hada baki suka cigaba da kallon match din abinsu.

 

 

Karfe  11:30 daidai aka gama match din inda Manchester sukaci da 4:2, wanda aka kira dazune yatashi yana daukan wayanshi dake ringing har lokacin da jacket nashi duka ya rike a hannu yace “lemme be on my way, inba hakaba Madam zata kashemini batteryn waya wlh, saida safen ku” daya daga cikin ukun dasuka rage zaune shima yamike dasauri yace “nima gani biye dakai Engineer bazan iya da masifan matan nan this night ba tahanani bacci nima” yana maganan yadauki jacket nashi da car key yabi Engineer dasauri zuwa wajen dasukai parking cars dinsu, sake sallama sukayi kowanne ya shige motarshi suka bar wajen.

 

Daya daga cikin biyun dasuka rage zaune ne yakalli dayan yace “karfe nawa zaka bar nan Nura?” juyawa wanda aka kira da Nura yayi kaman bashi akama magana ba yadaga hannunshi sama yakira daya daga cikin yaran dake aiki a Yahuzan da gudu gayen dayakira yazo cike da girmamawa yace ”yallabai gani” juyawa Nuran yayi yakalli mutumin dake kusadashi yace “ya akaro dakai ko zaka wucene kaima?” girgizamai kai yayi alamun a’a hakan yasa Nuran yajuyo yakalli yaron yace “karo mana shayin goruba da kaza asaka masa aciki da gizzard, kasa yaji separately bancin yaji sosai” wucewa yaron yayi yatafi Nura yadauki wayanshi zai fara tabama Musa yace “wai har yanzu kaida Hadiza baku shiryaba? Kai to kasauke girman kanka ka nemeta kuyi sulhu mana” tabe baki Nura yayi yace “wlh ko zan mutu bazan lallashi yarinyar nan ba cus nagaji, any little misunderstanding wanda daga wajetane fa yake farawa amman kullum nike neman sulhu akan wani dalili? She keep taking advantage of rashin son hayaniya na, yo bansan ciwon kaina bane aka gayamata?” Dasauri Musa yace “haba abokina kaima kasan mata da fish brain biyemata zakayi” dasauri Nura yace “bazaka gane bane, duk yanda zan suffanta maka Hadiza bazaka ganeba, she’s so bossy, tanada mentality dinnan na feminism, gani take dani da ita daidai muke shoulder to shoulder, she feels irin india kinada kudinki babu shit din da namiji zai kawomiki kidauka, you don’t need him for anything, she don’t care about me one bit billahillazi kaman ba aurenta nake ba” dafashi Musa yayi yace “chill please kodan yaranku ku shirya haba, Aman is just 4,5yrs ina, little Amal kuma 2 please banson yara tun suna kanana su taso suna ganin iyayensu basa shiri kaji Nura” kabar da hannunshi daga kafadanshi Nura yayi yace “enough Man, talking to Hadiza is impossible, barni nima nabita nazama fish din but saidai ni bazan zama sardine irinta ba mara hankali dake karewa a gwangwani ba, dan trust me mentality feminism nata nan is taking her nowhere, wlh saina gwadamata bonu duk randa takaini bango yar durun uwa” ya kifo uban ashar da hausan shi haba Musa ya kwashe da dariya, dan dariya Nura yayi shima yace “kaikuma meya faru kaima kabiye mini dayin dare awaje yau dan is obvious kaima da naka guntun matsalan kaima” dan tsaki Musa yayi yana tsaida dariyan dayake yace “matata, kaga Maman Shatu I don’t even know idan mace ce ita dan at this point cewa nake anya ba namiji bace itaba kuwa” dan dariya Nura yayi daidai lokacin ana kawo musu ordersu yaron ya ijiye yawuce yatafi, tsiyaya musu shayin Musa yayi yadauki kopin yakai baki yadan kurba ya tsaya kaman mai tunani yace “Bro imagine fa duka duka yanzu fa na shiga 45yrs amman this woman na neman maidani tsohon dole, she hates anything tarayya dani, dazaran nazo saita fara ni bansan yakamata yanzu na soma rage kwanciyan aure da itaba nasomas tsufa, menene menene, wai is high time mufara hakura dayi yara sun girma, Shatu is 16 zata shiga university next month let’s just focus on yaranmu, I was like what da hell! An gayamata ni katako ne ko sotake da tsufana nafara sopy”? Bushewa da dariya Nura yayi harsaida ya yarda naman bakinshi kasa yana nema ya kware, Musa yace “kadaina dariya is a serious matter ni da kai munada banbanci, kai daman bakin zuciyanka da girman kanka bazai barka kanemi Hadiza ba I don’t even know yanda kake surviving wlh, niko bazan iyaba kullum da rokon Allah nake hada matan nan kafin tabari indan taba, da girmana da darajata Maman Shatu ta maidani maibara shine fa jiya tamini karatun Alam Nashara matan nan atafaufau tahanani wai munada budurwa mudaina yi” dariyan da Nura keyi saida yan wasu table suka juyo suna kallonsu dasauri yarage sautin dariyan, kwana nawa kenan kullum cikin kunci yake but yau Musa nabashi dariya sosai wlh he’s so funny and hausan shi is just everything, dole ma kai understanding pains nashi sabida kalamomin dayake using to express it, tsagaita dariyan yayi yadauki nama yakai baki yace “to be honest with you Musa bawai banson nasami natsuwa bane ina so sosai but halinta is making me loose interest and love for her, banmason in tuntubeta da neman kwanciyan aure, itakuma ko oho bata damu dani ba, she no send me fa” cike da takaici Musa yace “I don’t know yaya brain din mata ke aiki imagine fa sun mana laifi but idan sun taru cikinsu they will belike mijina yamin kaza kaza kaza kaga ana kaimu online ana please hide my ID akai karanka amman baza su taba fadin suga kaza kaza da sukema mazajensu ba bunch of hypocrites, masu fuska biyu kawai, banda gayu da nunama kawayensu suna more mazajensu da aurensu babu abinda suka iya, ita kuma dama nafada mata idan bata chanza ba wlh she is on her own, daleliyar kishiya zanyo mata, da kudina da sana’ata wlh bama saina nemi mata ba Gwaggo zan kira a kano asamomin yarinya yar achan achan atoh ni wlh ban tsufaba garau nake, anma kawomin wasu magungunan basir daga Cotonou bazaka sha ba”? Girgixa kai Nura yayi yace “kaidai da shaye shayen magungunan basir din nan” dariya Musa yayi yace “kaima yakamata kasha wlh ya wanke maka mara tastas, fire for fire wlh ka lallasa Hadiza” “inaaa ni bazan biyemaka ba narasa ina zansa kaina, baridai maybe idan komi ya daidaita nazo na amsa”.

Wuraren 1.30AM sukatashi Nura yabiya kudin komi, kowanensu yashiga mota dan tafiya gida, Musa yace “zakazo office kaduba motocin ne gobe sun iso fa” Gyadamai kai Nura yayi yace “inada wani important meeting gobe but zan shigo dazaran nagama” Musa yace “to shikenan nimafa sonake nazo naga site dinnan, terrace dinnan yamin kyau dakukayi” “ba kaki sayaba bakano da son kudi” ckin dariya sosai da barkwanci Musa yace “shikuma bazamfare annubazaranci da kudi, nabiye maka saika karan mini da dan jarin motoci na” dariya dukansu sukai sukai sallama kowa yaja motanshi sukabar wajen.

Kinason magana dani M shakur??? Chat me up by clicking on this link

wa.me/+2347012181461

 

Parking yayi agaban wani babban gida wajajen 2 nadare. Sauka yayi  yana kallon wata sabuwar red 2024 Toyota grand highlander dake pake akofar gidan duka duka last month ya chanza mata mota 2023 Toyota Camry hybrid wato bai mataba shine maybe ta saida tasayo wani, dan murmushi yayi yawuce yana ciro key dinshi yabude kofan yashiga ciki yamaida kofan yarufe yajuyo yakunna wuta lafiyayyen hadadden classic falo ne, ijiye key yayi kan tray dasuke ijiye key yaduka yacire covershoe kafanshi yasake juyowa yabi falon da kallo dayake tsaf tsaf banda motan Aman dake kan kujera hannu yasa yakashe wuta sannan yawuce yahau stairs harya fara tafiya yaji kukan Amal chak ya tsaya cus badaga sama yakejin kukan nan ba and dakin Amal na upstairs, shiru yayi jin magana kasa kasa. “sorry Amalulu, Amalilin Mommy, Amalilin Aman, Amalulu na Amalulu yar lukuta, kiyi bacci zakiji sauki gobe kinji, zazzabi ne saina zane zazzabin nan dake damun mini yarinya na” muryan Amal yaji tafashe da kuka sosai cikin muryan yara tace “Momyyy” dasauri yajuyo yashiga saukowa daga staircase direct hanyar dakin yar aikinsu yayi dake  kusada store room na gidan, tsayawa yayi gaban dakin yasa hannu yakunna wutan wajen sannan yayi knocking kofan tareda bude kofa atare dasauri sabida yanda yakejin kukan Amal, wata yar budurwa ce doguwa tsaye tagoya yar yarinya dabazata wuce 2yrs ba abayanta, wata yar karaman katifa ne adakin ta yan boarding sai ganamasgo saikuma kwalayen magunguna da flask na ruwan zafi da gwangwanin cerelac da bowl da spoon duka akasan dakin, adan tsorace yar budurwan ta duka kasa goye da Amal abayanta ganin maigidan dabai taba zuwa nan ba tace “ina yini” gabanta na faduwa dan yaune rana da farko da Baban su Amal yataba zuwa wajen nan, sosai yake kallonta baima tsaya amsa gaisuwanta ba yace “me Amal keyi anan da daddaren nan”? Tana duke akasan still jijjiga Amal dake kuka take abayanta tace “batada lafiyane Alhaji” “Mamanta fa”? Dasauri tace “Anty tadawo daga aiki tagaji bacci zatayi” ranshi abace yace “ita tace ki kawota nan dakin”? Gyadamai kai tayi batare data kalleshi ba tace “eh” “bani ita nan” batai musa ba tashiga kwanto Amal dasauri, yarinyar was looking so weak sai kuka take ta yarda zanin tadauketa ta taso ta taho har inda yake tsaye agaban dakin takawomai ita, itama Amal tana ganin babanta takara fashewa da kuka tace “Daddy” zafin dayaji ajikinta saida yadan firgita ya rungume yarinyar da sauri ajikinshi yace “my princess” yakalli yar aikin dahar takara dukawa anan gabanshi yace “wani magani tasha”? Dasauri tace “Anty tace nabata wayanchan”? Tanunamai magungunan dake gaban katifar ta, Ibuprofen suspension ne dakuma Tuxil D na mura da tari, jiyayi ranshi na tafasa dan yaranshi are his life, cikeda takaici yace “how many mil ma kika bata? Tun yaushe take wajenki”? Dasauri tace “tun wajajen 9 Anty takawomin ita, cikin marfi Anty tace nababbata zatai bacci” “maisa baki kaita da jikinta yayi zafi haka ba akaita asibiti tun 9 har 2 nadare” kanta na kasa still da zuciya daya tace “Anty tace karna kawota bacci zatayi tagaji ta kwana awajena” kallon yar aikin yayi takaici yasa kawai yajuya yawuce yahau staircase rikeda Amal dake kuka sosai ajikinshi, direct dakin Maman yawuce bude kofan yayi kai tsaye yasa hannu ya kunna wutan dakin, wata kyakkywan faran mata ne kwance kan wani makeken lafiyayyen gado tarufa dawani beautiful bargo AC na aiki dan dakin sanyi tana bacci mai dadi, wucewa yayi gaban gadon ya bubbuga filon da kanta kekai yace “Hadiza, Hadiza” firgigit tabude idanunta dasukai ja cikin bacci tabishi da kallo tana mika tana kallon Amal dake kuka sosai tana miko hannu kaman zata kamata, cikin muryan bacci tace “Nuri lafiya zaka kawomin Amal ina bacci batana wajen Ummi yar aikinmu ba pls kamaidata I need to sleep na bala’in gaji wlh” tai maganan tana hamma zata kara jan bargo azuciye Nura ya fizge bargon ya yaye yace “wai what’s is your problem Hadiza? Kinyi neglecting your responsibilities towards me yanzu ma yarana wulakanta mini su zakiyi, this girl is sick baki kaita asibiti ba, baki kirani kin sanar dani ba, kin barma yar aiki ita da magungunan acika marfin idan tai overdosing yarinyar nan fa”? Hamma  Hadiza tasakeyi tarufe bakinta sannan tadan yunkuro kadan takalleshi tace “look Nuri banda lokacin fada dakai yanzu Allah ma yasan I don’t have time, dare mahutan bawa ka maidama Ummi yarinyar nan tasan yanda zata kula da ita, she’s great da yara bakaga duk cikin yan aikin danayi tafi dadewa ba almost a year take nema yanzu agidan nan, and my children loves her sosai” wani kalan kallonta Nura yake yace “da ace bani nakaiki asibiti kika haifi yaran nan ba danace banaki bane Amal is just 2 she’s sick crying for you jibi yanda take kuka take miko hannu ki dauketa kina cewa akaima yar aiki, what kind of woman are you da bakijin tausayin yaranki”? “oooohhhhhhhh! Ohh-ho-hooo!” Hadiza tabuga uban ihu tana daura duka hannayenta saman kanta irin ta shiga uku din nan, cikeda gajiya tace “wai all this while so kake muyi fada naki biyemaka cus am busy da work dina baka gabana what’s the meaning na zuwa tashina tsakar daren nan kana neman bala’i na eh? Nace ka maidama Ummi yar aikina Amal for Godsake this is her job we pay for it ba kyauta take mana ba, idan bazaka maidata ba I can call her da wayana tazo sama ta dauketa sutafi, please pls banson problem Nuri, banso, just get out of my room pls katafi dakinka, haa’a kawai katasheni tsakar daren nan da bala’in ka wannan wani kalan neman rashin zaman lafiya ne iyye? Pls kafitan mini daga dakina nace and nagaji nadawo daga aiki ka maidama Ummi Amal she’s good with kids zatasa yarinyar nan bacci pls go away from here” kawai tsayawa Nura yayi yana kallon Hadiza yanda take magana zaka dauka itane mai gidan nan ko itane take putting food on the plate jibi yanda take cemai yafitan mata daga daki kaman itace ke aurenshi ba shi ke aurenta ba, ganin ya tsaya kallonta yake yana jijjiga Amal dake kuka sosai barinma yanda taga Mommy ta na masifa yasa ta buga tsaki. “Mtswwww, kada Allah yasa kafitan nina barmaka dakin, kajika da ruwa kasha” ta tashi fuuu azuciye tasauka daga gadon tawuce tafita daga dakin tana mita,

yana ji tashiga wani daki ta bugo kofan tarufe tana murza key jiyayi kaman an dauramai dutse a kirji kallon Amal dake ihun kuka yayi tana kokarin sauka daga hannunshi tana kallon kofa tana mika hannu tanaso tabi mamanta Ya jijjigata yace “sorry Amal, Daddy’s princess stop crying, muje” wucewa yayi yafita daga dakin dakinshi yaje da ita ya ijiyeta kan gado yawuce bayi yatara ruwa yadawo kayan jikinta yacire mata da pampers yadauketa zuwa bayi wanka yamata tsaf kana ganin yanda yake kasan mutum ne mai tsananin son yara fito da ita yayi daure a towel yawuce yafita yaje dakinta hadadden daki komi pink ga zane komi organize wani shimi yadauko yasamata da pampers yace “zakisha tea Princess”? Girgizamai kai tayi a’a, yace “juice, cheese balls, rice, omelette” gyadamai kai tayi dasauri daya fadi omelette hakan yasa yadauketa sukaje kasa ya kunna wutan falo ya shiga kitchen da ita baimasan ta yanda zai fara mata omelette dinba, tsaki yayi yafito yaje gaban dakin yar aikin yayi knocking bude kofan tayi adan taushashe yace “danzo ki soyama Amal kwai” Amal na ganinta tamika mata hannu dan tadauketa dasauri Nura yace “wait Princess aiki zatayi” dasauri yar aikin Ummi tace “ai na iya aiki ina dauke da ita kawota” dan kallonta yayi sai kawai yabata Amal din ta karbeta tana murmushi ya matsa gefe fitowa tayi tana tafiya tana kallon fuskan Amal tace “namiki omu omu”? Dasauri Amal ta gyada mata kai tace “omu omu” Ummi tace “to muje namiki mai dadi ko”? Amal tasake jinjina mata kai.

Leave a Reply

Back to top button