TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 18

Sponsored Links

 

 

Labarin nan bai shafi yan jahan zamfara ba ko kadan muyi
amfanine kawai da sunan gari da title din don bada labarin ba,ayi don wani ko
wata daya fito a zamfara ba.

   Munyishine don yan
zamfara dake fadin ba a labari da muna a cikin rayuwan mu sai bawa ya hade ya
shanye ya dawo tankar bashi abubuwa suka faru a kanshi ba Allah yasa mu dace da
rahamomin sa amin.

   Abinda yasa nace
hakan yanzu an fita zancen ummah mu din
duk da itama ana dan waiwayanta tunda ansancewa dai tana tare da Abban
mu taki fita gidan shi duk irin ukuban da ake gwada bata tun farko.

  Don haka ake jefa
mata makarun durkushewa a ko yaushe tako wani hanya don kawai tayi baki ta
dandani wahalan duniya da sunan kishi.

    Yanzun kuma dana
taso ni yarta a kaina mama ta mayar da akalan aikin ta gareni badon komai ba
sai don tagana durkushe a rayuwana.

   Na zamo ban dago ba
bankai diyanta daraja ko kima ba a idon jama,a da har za a sanda ni a cikin
diyan Abban mu a gari saidai nata diyan kawai take bukatan su daga.

    Wanan shine abinda
mama ta saka a gabanta take kuma kanyi a yanzu tun bayan sayan motar da Abba ya
canza min ya zamo  mama masifa abinda ya
zo ya tsaya mata a zuciya yanzu,

    Sai ta mayar da
hankalinta a kaina sosai fiye da farko da take min tsana na iya zuciya kawai
yanzu tsanan bai tsaya a zuciyarta ba har fili take nuna min hakan.

   Wanan tafiyan Lagos
da sukayi na batan Dele wanda ashe tafiyan shi yayi ranan da suka isa a ranan
shi kuma ya daga zuwa Canada yabar Nigeria.

   Bayan sun nasu sun
huta kafin mama ta dawo gida sun ziyarci bokan su na lagos din ta kuma bada
sunana ai mata aiki a kaina.

  Bokan ya danyi dube
duben shi na fara aiki ya danyi ihu yana cewa wanan tana da abin mamaki sosai a
tare da ita.

 Jin haka nan hankalin
mama ya tashi ta nemi sanin meye abin mamakin nata da har yasa boka yadan
razana yana sake ihu tare da ja da baya kandan yana gyara zama.

    Yace wanan din ita
tauraruwa ce mai witsiya ko ina tana kada jelanta kuma zai zami mata alheri
idan ta kada bazan boye maki ba ita din jinin ta nada karfi da wuya wani sheri
yayi saurin kaiwa a jikinta.

   Idan dai bayi mata
gagatumin aiki an kife ta ra baya yadda abubuwan zasu zo mata ta birkice shine
kawai mafita a kanta yanzu amma yarinyar nada baiwa tare da masu tsaronta.

   Budan bakin mama
tambayanshi tayi da cewa kana nufin cewa ita din zatafi duk yayana dana haifa
kome ta kafeshi da idanunta tana son jin amsar da zai bata a lokacin, gabanta
sai faduwa yakeyi cikin tashin hankali.

    Dagowa yayi daga
shi sai dan walkin fata da yayi bante dashi a jikin shi sai wani digo digo dake
jikin nasa zuwa samanshi wuyan shi na rataye da farin kudi couriers irin na da
can baya ga dakin da duhu sai haske kadan ake gani.

  Kwarya ya jawo daga
gefen shi yayi saddabaru a ciki kafin ya ya fara wani irin surukulen magana
makin fuskana ya fito sai fuskan akuya ya gani Orrishi ririshi ya fada yana ja
baya tare da fadin kai taba yarinyar nan fa fitinane a wurin ki.

   Nan maman Dele hjy
Rafat ke fadin koma meye ayi a dakusheta kada ta haska zamu kifeta na lokaci
don yaranki su samu su haska mu saka mata bakin jini ga kowa ta rasa wanda zata
raba taji sanyi.

   Saidai fa amma idan
zata bullo duk zata dakushe hasken yaran ki ga baki daya lokaci guda saidai
akwai lokaci mai tsawo  gareta kafin
hakan ya faru da ita idan hakan yayi maki zan maki aiki kan hakan yanzu.

   Ayi duk abinda za
aimata ta dakushe a wurin kowa ta koma abin kyama a wuri  kowa yamana ba inda zata dafa taji sanyi daga
ita har uwarta ta zauna a cikin ukuba mai wahala yace angama saidai idan na
hada ina son kada aikin ya wuce kwana biyu yakai jikinta .

    Ma,ana zakusan
dabaran da kukayi kika shafa mata shi a jikinta bukatan mu dai kawai shine ya
samu taba jikinta suka kalli junan su mama ta bude baki tace angama.

     A daidai lokscin
ummah ta idar da sallah nafila hanayenta a sama tana roka muna Allah tsari daga
duk wani sherin mutum ko aljan ko wani daba daga dukkan abin cutarwa ta shafa.

    Addu,n iyayye nada
tasiri matuka don koda mukaddarine sai abin yazo a cikin sauki ga bawa matuka
uwa tana tsaye a ksn danta da addua da ya waita sadaka.

   Bayan ta gamane ta
fito zuwa kitchen tani na tuka tuwo suka gaisa ta gaida ita da aiki harta juya
zata tafi take fadin Tani idan zaki tafi gida don Allah ga kudin nan ki karba
ki mun sadaka ki sayi tankwa ki bawa mabukatan layin ku sadaka.

   Kiwa Allah ki
tabbatar da kinnmun wanan sadaksn takwan don hankali bai kwanta da tafiyan
mutanen nan ba sam saina dinga ji gabana yana faduwa lokaci lokaci haka kawai.

    In sha Allahu hjy
za a saya ayi yanzun nan kuwa bari nayi sauri kada yamma yayi ban fita ba dare
yayi ban samu badawa ba a yau din nan.

   Tani ta karbi dubu
biyu ummah din ta kara miko mata wani dubu daya tace wanan kibawa yar jagoran
makaho wanda mace ce ke masa jagora da sanda koda yarinyace ko babba indai har
mace ce a bata.

   Hjy sarkinda akaiwa
ya sani Allah ya tsare ya karba muna ummah ta amsa da amin tani ta juya ta koma
cikin gida tani na gamawa ta yiwa ummah sallama ranan da wuri ta bar gidan namu
yar kasuwa ta biya ta sayi tankwa na daidai kudin kulin dari dari tun a hanya
ta fara rabawa wanda tagani da alaman bukata har zuwa gidajen shiyansu.

   Washegari kuma
tunda safe ta taka zuwa gidan sarkin makafi ta kai masu don tasan da yaran shi
mata yake yawon bara shi sai wani zubin ne zaka ganshi tare da diyanshi maza.

    Sai karfe tara ta
shigo gidan mu ta fadawa ummah tayi duk yadda tace din lokacin ne ummah taji
shakat a zuciyarta irin yadda take jin kunci a cikin ranta din nan.

   Hakan baisa tayi
sakaci da  ibadanta ba don tasan irin
abin rashim imanin da akanyi don kawai kishi da rashin hankali gashi a jirace
take da mama ta dawo daga lagos din tace zatayi mata magana kan case din Dele
din.

   Sai gashi mama
tadawo din munji shiru saida sabon halin da aka dawo dashi tun bayan dan
rikemin hannun da tayi danaje gaishe ta ban kara ganin fuskan mama kuma a gidan
mu.

  Haka abubuwan suke
tafiya  a garemu dadi da rashin dadi duk
muna hakkuri muna shanye komai a cikin mu bisa jagorancin mahaifiya a garemu
ummah .

   Wace ke hanamu yin
wani abinda ba daidai ba kamar yadda yan gidan namu suke abubuwansu muna kallo
komai yinsa sukeyi a gadarance don wani lokaci ko mota na parker zasu sa a
kirani wai a nan suke son aje tasu motar na jayetawa.

 Ire iren hakand dai
na nuna gadara da isa ga kowa yasa ummah kawar muna da idon mu kan komai a
gidan namu  yanzu muna komai cikin rashin
issashen yanci muda gidan mahaifin mu din.

    Ya kasance weekend
don haka tun dana shige dana dawo ban fito ba ina part din  mu sallaman yan uwan Abban mu naji sun shigo
suna gaida ummah.

    Hakan yasani
fitowa daga daki don na gaidasu a daidai lokacin da gwaggo shafa ke fadin wai
makulin wancan dayan part din naku yaya yace muzo ki dauko muna a dakin shi.

    Gwaggo ina kwana
au mama kina ciki ashe suka fada na karaso ina gaidasu da kwana har kasa don
basu girman su a matsayin iyayye a gareni suka amsa min cikin sakin fuska tare
da tambayana karatu.

   Naji ummah tace
dasu Toh key din part din nan kuma wani abin kuka samu ke nan kuma suka kwashe
da dariya tare da fadin aikin sanmu ba raggaye muke ba mu.

    Ke zaki bamu don
Allah bamu son dogon tone tone kizo ki saka muna hannu a kai kuma yanzu kima
ihu suka kwashe da dariya ta mike ta shiga daki ta dauko key din part din Abba
ta fita.

    Gwaggo sa,ade ta
kalli sauran tace ai kunga haka yafi da wacan mukaje karba da yau sai mun raina
kan mi gidan nan don gadara da isa da samun waje.

    Yanzun dai ai sai
tabi wani sarkin kuma a sake sabon danmara tunda ga wata zata shigo wanan kan
suna daidai da ita ai in tace ita goganyace yar kano ai ba wasa bace.

    Gabanane ya fadi
dam lokacin guda don na fahinci Abba aure zai kara ke nan kuma abubuwan zasu
taru suyi muna yawa ke nan yanzu don bamu san wace kala zai kwaso muna ba kuma.

   Mikewa nayi na koma
ciki har suka tafi ina jin sunata raha da ummah din suna tafiya na fito ina
fadin wai Abba aure zaiyi kuma ?

   Budan bakim ummah
sai cewa tayi Allah yasa hakan shi yafi alheri Allah ya hau damu kan ko wacece
ya karemu daga sherin dake cikin haka.

  Na amsa da amin a
sanyayye shiru nayi ina tunane kafin na mike nashiga bayi don naiyi wanka daga
cikin bayin ne na dinga jin murya na tashi dana saurara sai naji muryan mamane
ashe.

    Har na fito na
zauna na shirya mama nakan nakinta na fito falo na nemi abinci naci nidai banyi
gigin fita ba lokacin don irin ashar din da mamake lailayowa a bakinta lokacin.

   Har tana fadin wai
Abba da yake da irin mu a gida har uku shine yake zancen kara aure a yanzu ba
zancen auren yaran shi bane a gaban shi ke nan.

    Ta koma fadin
saime ba za a taba ganin bayanta ba dai inma anyi don ta saidai mutum ya karawa
kanshi takaci ai don ita a shirye take da kowa a gidan nan.

    Tsuki naji ummah
tayi ta mike ta shiga dakinta tana fadin kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa
ko dumi bayayi dan sheri kika matsa muka dawo garin nan muka zauna.

  Alh ne zai iya zama
shi kadai ba tare da mace tana masa miko min ba yi wancan yi min wanan yanzun
dai ai kanku akeji nabi ummah da kallo .

  Don na kasa fahintar
ajin da take lokacin shin taji zafim abin itama ko kuma hakan bai dameta ba
take nufi don banga alaman komai ba ga jin hakan.

   Ina nan falo ni
kadai naji an turo kofa na dago kai mamace tsaye a kofan ko wanka batayi ba
lokacin don masifa ke ina uwarku tana daki na fada ta bini da harara tare da
daka min tsawa tana fadin ba zaki shige ki kira min itabane ?

   Na mike tso na
shiga na samu mama tayo alwala na fada mata tace nace gata fitowa saida ta dan
gyara ta fito don ni dana fadawa mama dakina na shige ban tsaya ba.

   A nan ummah ta
sameta tana fitowa tace salma kada ki dauka ni kadai Alh yaiwa haka ki dauki
auren nan da zai kara ba ruwan ki kema din da ruwanki har da tsaki kuwa don har
kina rawan kan dauko masi key ki basu don kawai a cusguna min ko ?

   To bari kiji abinda ya kawoni dama ki sani ke
din nan sai kinfi kowa matsuwa a cikin maganan ki rubuta ki aje na fada na kara
banga matar da Alh zai auro gidan nan ta daga min hankali ba.

    Tana fadin hakan
ummah tace wai maimuna mai kika daukeni a gidan nan ne don Alh zaiyi aure sai
ki dauki kowaakiyin ki koda zaiyi auren shi nina bashi shawaran yayi ?

    To bari kiji in
sha Allahu alheri zan gani don nani ganin komai sabanin hakan da kike fada din
don haka ki fitar dani a cikin zancen ku.

   Au haka kika fada
ummah tace kwarai kuwa ke baki iya hanashi ba nice kike son na hanashi ko me ko
ya shawarce nine lokacin da yayi shawaran hakan ?

   Itama ummah din ta
hayayyoko mata lokaci guda ta juya tana fadin aimu zuba shege ka fasa zaki gane
baki da wayau don ke ba makira bace dama ai a zuben yake ummah ta bata amsa
tana juyawa zuwa ciki taci gaba da fada har naji tayi shiru nasan ta tada
sallahne lokacin.

   Shigowan kannena
yasa nace suyi wanka muje mu gaida hjy suka shige suna ihu na bi bayansu nayi
masu wanka na shiryasu muka fito nake fadawa umma zamu gaida hjy.

   Tana zaune tana
lazumi ta amsa da kai na juya zan tafi naji tace dani gaskiya da badon kun saba
zuwa irin ranan ba da sai ince kada kuje gidan nan yau amma ku tafi kada dai ku
dade idan kunje.

    Mukai mata sallama
muka tafi mun samu dakin a cike da mutane don muna ta sallama ba,a amsa muna ba
saida karamin yaron ya leko yana amsa muna.

   Ya koma saiga
gwaggo ta leko tana fadin aiyah su maamahne ku shigomana muka kara sallama zamu
shiga hjy ke fadin me kuma ya kawosu yau gidan nan gulma ko me kuma ?

   Haba hjy maamah ce
kuma zaki fadawa haka yau yaran nan duk sati suna gidan nan wurin gaidake fa
don Allah dai hjy kibar wanan halin gaskiya hakan baida kyau.

  Tsohuwar tayi wani
irin da fuska tare da kawarda zancen ta hanyar fadin ke miko wancan ledan a
zubawa gidan Tella nasu .

   Kayane dakin irin
na buki baja baja a falon hjyn cikin manyan robobi sai rabawa sukeyi wasu kuma
nacin nasu a tsaye muka gaidasu da kyar hjyn ta karba muna hankalinta na kan
kayan da take rabo din nabuki .

   Gwaggo shafa ta
debo t mikowa kannena sai hjy din tace a, a haka kuma ga nasu da za a kai
gidansu nan a raba zaki dauki wanan ki basu kuma ?

   Haba hjy gwaggon mu
daya ta fada wai missa kike haka don Allah mi aan ciki don an basu waga din don
Allah dai ki bar wanga halin.

    A daidai lokacin
na fisge na hannun yaron na mayar inda gwaggo ta ballo ta basu nacewa kannen
nawa su tashi mu tafi muryan su gwaggone ke fadin ke maamah mi ?

  Mi halan halim hjy
na a baki sani ba kuma yanzu gwaggo ta dauko tana mikawa yaron da sauri ya
girgiza kai don munada kwabo sosai mun samu tarbiya daga wajen mahaifiyar mu.

   Nake fadin gwaggo
sai anjiman ku mun barku lafiya wai har zaku tafi yanzun da shigowan ku kai ku
dawo ku zauna kunji ku kyale hjy ai kun saba da halinta.

   Ku barta dan Allah
karku zauna mana ta fada tare da kirana da ja,ira ta kara min da ubanki ma
baikai yayi fushi dani ba balle ke ko iyayyen naku basu kai can ba.

   Hakan baisa na
tsaya ba sai murmushin da nayi nasa kai kannena nabina a baya muka fice daga
gidan ummah na zaune falo tana kallo muka shigo ta dago tana fadin.

  Bakuje bane ko mey ?

     Mun tafi ummah
mun dai dawone yau gidan nasu a cike yake da mutane yasa muka dawo  bin kujera tayi ta kwanta ba tare da magana
ba .

   Nikan na shige ciki
abina na barsu a falon kallon hannun kanin nawa dake rike da alkaki tace kai
kuma nan yaran sukai mata bayanin komai.

   Duk da ran ummah ya
baci amma bata yarda ta nuna min hakan ba koda alama haka na wuni a daki ina
karatu rabi tunane har akai sallah na fito bayan nayi sallah.

  Missalin uku da
rabin na rana mukaji dawowan Abban gidan ana ta bude get ta ko ina kara  motoci mukeji Alh ne kuma da rana haka yau ya
dawo ?

   Sai ga Tani da
sauri tana fadin hjy Alh nefa yazo da Amaryan shi yadda naga ummah ta dan
kadune yasani natsuwa don cewa tayi Amarya fa ?

   Tani din data kawo
mata gulma tace saima kinganta ai yar gayuce sosai itama kamar ku haka saidai
ba yarinya bace don da gani ta dan manyanta.

   Kallon ummah din
nayi kafin na mike da kanwata a hannu na shige dakina na rufo naji ummah ta
kwala min kira na dawo take fadin kika sani ko zasu shigo nan din duk da part
din bai wani dattiba ku dan gyara keda tani tana fadin hakan ta shige ciki ta
barmu nan muna kara gyara falon take muka gama muka saka kamshi ta ko ina a
falon har zuwa ciki .

   Kamar yadda ummah
bata sanda zance ba hakama mama don Abba auren bazata yayiwa su ummah din kuma
yazo da matar gida kowa ya ganta.

    Ranan kan mama
kamar ta hade zuciyarta tana jin tare suke tace aja mata kofanta tashige daki
ta kira maman Dele abokiyar cin mushen ta suka hau tsara mafita a garesu.

    Muryan su gwaggon
mune a falon suka shigo suna suratai da fadin ina hjy salma din ina falon zaune
na natsa yan kanne muna kallon cartoon suka shigo na fara gaidasu gwaggon namu
daya tace ina hjy salma din ta shiga ga Amarya nan zata shigo gaida ita.

  Tana ciki na basu
amsa take kira muna ita kodai barin lekata da kaina gwaggon mu daya ta fada
tare da nufar dakin ummah din kai tsaye suka barmu a falo.

  Ke kuma ja,ira dazun
sai kikai fushi da hjy kija kannen ki kuka taho ana fadin ku tsaya gwaggo
abinda hjy ke muna dinne ba dasi wallahi laifine don muje gaida ita kuma , .

   Fitowan su ummah da
gwaggo daga dakin ne ya katse mu ummah na fadin baku sanarda mutum ba sai kawai
muji wai ga Amarya nan zuwa gaidani ku dai baku dauki cin amana bakin komai ba
wallahi suna ta cacan baki mukaji muryan Abba na sallama zasu shigo ashe shine
tare da sabuwar matar nasa .

 Da murna kanne suka
nufi Abba suna mashi oyoyo da zuwa kamar yadda suka saba yana shafan kansu zuwa
wurin kujera matar tana biye dashi a baya.

   Yes farace bata kai
ummah na fari ba saidai tafisu tsayi da jiki ma,ana tana da nata irin kiran
itam mama wankan tarwadace ita don ita ba baka bace kuma ba fara ba.

    Daga inda nake
zaune na mike na nufi wurinsu na dan rage tsawo ina fadin sannu da zuwa Abbah a
a mamana kece nan yau ba school ke nan ya tambayeni yana riko hannuna.

   Na dan juya wurin
matar dake bina da kallo nace sannu da zuwa tace yauwa sannu ko idonta tar a
kaina daga cikin glass din idon ta tana karemun kallo.

    Hannuna rike dana
Abba din ya nufi kujera ya zauna ni kuma na zauna a makarin kujeran sai kuma na
daga ina fadin ga wuri ina nuna mata dayan kujeran dake kusa da wanda Abba din
ya zauna.

   Tace na gode takai
zaune tana gyara lafayan jikinta data lalaye saman wani rantsatsen lace dake
jikinta  daga can inda ummah take zaune
take fadin sannuku da zuwa.

   Yauwa Abbah ya fada
ya juya wurin sabuwar matarshi yana fadin hjy karima ga salma nan uwargidana
itace matana ta farko ga yaranta nan kuma kina ganisu.

    Iya makirci sai ta
dan zamo daga yadda take zaune da farko tana fadin mun sameku lafiya ummah ta
amsa daga can da fadin Alhamdullahi ya hanya ya akabar mutanen gida kuma ?

  Lafiya kalau ta fada
tana dan murza hannun ta tare da  fadin
akwai nisa kan nan da Abuja gaskiya na dauka tafiyan ai ba wani mai nisa bane
sosai yadda yake fadi.

   Da akwai nisa sosai
gaskiya aiku  isa ku huta sai a kawo maku
abinci daga can gwaggo shafa ke fadin ai akwai abinci da aka kawo daga gidan
hjy ma.

  Au to ai shike nan
har ina zancen a shirya wani a nan din akai masu tunda mungama tun dazun Abba
ya juyo yana fadin daga gida hjy kuma nan din ba akwai abinci ba tace sunyi wai
dama don zuwan kune ai aka hada din acan tunda su nan basu sanda zuwan kuba.

    Ba,a fada masu
cewa yau zamu zo ba nika ina jin haka na mike tsam na bar falon bansan ya suka
karasa ba a wajen don ban sake fitowa ba sai da dare da zanci abincin dare din
na fito.

    Amadi azzumin nan
duk da ya samemu a cikin walwala in sha Allahu amma  sai naga kamar bamu fara mai tanadi da wuri
ba don gaskiya irin gab da azumin nan komai kara kudi yakeyi farashi na hau
hawa sosai na kayan masarufi.

   Kukan uwargarke ya
dakatar da Dije ga fadin abin da tayi niya fada lokacin me kuma uwar garke kewa
kuka yanzu kuma , ?

   Allah ya gani kukan
uwar garke a yanzu tsoro yake ban don yanzun haka wani alaman take nufi da
hakan….

Leave a Reply

Back to top button