TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 16

Sponsored Links

 

 

 

  Allah Allah yake ya
gama ya fita ya koma wurin maikayan yaji ko yaya zasuyi dashi kan wanan kudin
akarshe dole ya maida hankalinshi wurin abinda yakeyi din.

    Dije wace ta dawo
wurin malam tanimu da dan kullin hayakinta data karbo a wurin shi daki ta shiga
ta aje ta fito ta gwama wuta duk abinda takeyi hankalinta na kan uwar garke
dake kwance tana binta da kallo ko ina tabi.

    Ruwa ya diba ya
zaga ban dakin har ya fito yazo ya canza kayan jikin shi lokacin ya fara jin
kamshin hayakin da Dije ta buda yana tashi a cikin gidan.

    Da farko ya dauka
hancinshine ke shako mai kanshin a makwabta kafin ya tun kari kofan Dije din
yaji kamshin a nan yafi tashi sosai ya fara dan sunne sunsune.

   Mikewa yayi tsaya
da kyau yana fadin Dije wai me nake ji yana fitowa ne haka wai kai dan Allah ka
faye surutun tsiya wallahi ta fada a hasale sai yabi kakan nasa da kallon
mamaki a wurin.

    Kayan ya daure yadda
ya saba kafin ya leka wurin Dije yana fadin tau Dije ni zan tafi   ga wanan sai ki kara yana miko mata dari
biyun daya bata da farko.

   Amadi shigo daga
ciki ta fada a sanyaye ya dago yana mamakin tsohuwar ya fada dakin don ganin
bakon yanayi a fuskanta na damuwa daya nuna hakan gareta.

  Dije lafiya kike
kuwa Amadi ba lau ba gidan ya canza tun dawowan uwargarke gidan nan nake jinshi
ba daidai ba sai jiyan kuma na kara tabbatar da hakan.

  Dije uwar garke kuma
tace kwarai uwargarke dai Amadi daka sani yanzu kamar ta hurhura ba ita bace a
gida  nan yanzu don wanan halinta ya
bambanta da wacan.

   Dije don me kikace
hakan yanzu tace kwarai don tana bamu alama saidai ganewa ne bamuyi da hakan ba
Dije don Allah kada ki firgitani ya fada ya juya yana kallon uwargarke dake
kwance tana tuka tana lumshe idonta.

  Bayanin komai daya
faru ta fara mai yace gaskiya zancen ki dutse nima naso gane hakan Dije don ko
yanzu fitan nan naki saida ta ban wani alama ya fadawa wa Dije din komai har
kudin daya tsunta din tace kaji ba na fada ma akwai lauje cikin nadi wanan
lamarin gaskiya .

    Koma dai meye
Allah ya gani bamuyi niyar cutar wani ba kada Allah yaba wani ikon cuta muna
muma ni zan tafi ya fada a karshe ka kula don Allah yace in sha Allahu.

   Ba zaka karya bane
yace ki bari zan karya a waje idan na fita don yau kan ba zancen makara bane a
wurina don nasan na rasa darasin safe kan.

    Har ya fita ya
dawo yana fadin Dije ki rike addua kada kiji tsoron komai in sha Allahu inma ta
hurhura Allah zai karemu ga ko meye tace ai wanan hayakin dana karbo tunda na
turara naji faduwan gaban ya daina.

  Ki dai hada da addua
shine mafita yafi hayaki kaifi duk kikaji wani abu ki karanto addua tsari a
wurin Allah tacw ba komai ai tana kanyin hakan itama.

    Amma kadai yi
shawara kafin ka koma wurin mutumin ka samu wani ka tambaya zaifi yace zaiyi
hakan kasan mutane yanzu ba abin yarda bane yace hakane Dije ya fita.

   Na san na gama
makara saboda rikicin su mana dana tsayawa don ko kannina saida ga baya aka
kaisu makaranta don kawai gudun zuciyar zama tare da ummah keyiwa yaja muna
makaran.

   Na iso makaranta
sai dalibai kadan ne a wurin suke shawagi a nan zama nayi cikin mota ina
kallo  abinda ke wakana a wajen.

   Sam ban san da
zuwan mutum ba don hankalina daya dauku ga tunanen su mama why mama zata dinga
yiwa ummah irin wanan halaiyan hakane ?

   Nocking din window
motan akayi wanda hakan yasani dan firgita kadan ina kallon wanda ke wajen
tsaye.

   Manir ne na gani
yana dariya tare da fadin let coma  yau
ma kin makara ke nan don gaki a waje dan murmushin yake na sake a fuskana
lokaci guda ina fadin wallahi yanzu na shigo nasan na makara na tsaya nan ina
jiran har su fito.

    Ashe mun zama daya
don nima minti daya na kara na samu har ya shiga ko kinga mutumin ki can tafe
ya fada hakan yasani dagowa ina kallon inda yake kallo.

  Watau gaskiya MAYANA
dan uwanan naki ina son rayuwan shi donshi haka yake da simple life bai dauki
karyan duniya ya dorawa kansaba .

  Yanzu fa kayan
gwanjon sayarwane ya dauko haka abinshi ba tare da damuwa ba wallahi gayen na
bala,in ban tausayi sosai idan na ganshi.

   Wai me zamuyi mai
kan karatun dayake karamune naso mu hadu a hada mai wani abu ina ganin hakan
zaifi don kada mu takura ma rayuwa  shi
wana  ba matsala bane idan kun shirya
saina bada nawa dana Hannatu ai.

  Ah Master salamu
alaikum ya fada lokacin daya dan karaso inda muke tsaye din yana washe baki
kamar yaga mastern gaskiya a gaban shi.

    Bai amsa ba sai
cewa da yayi lafiya dai na ganku ana  ana
class yanzu lokacin nake kokarin fitowa daga motar sai cewa da Munir yayi
wallahi master mun makarane.

   Kasan halin malami
nan da rashin nasiha gara kawai mu tsaya waje har sai ya fito mu shiga sai kuma
hankalinshi ya dauke ga wasu daya sani ya nufi wajen su ya barmu tare da master
din a wurin .

    Meyasa kike son
makarane hakan zai iya jawo maki matsala ga karatunki fa naji ya fada nasan
dani yakeyi yasa nace yau mun tashi babu dadine a gidan mu wasu baki mukayi sai
dayan ya bata ana neman shi hakan yasani zuwa yanzu.

    Allah ya baiyana
muna shi na amsa da amin ya juya kamar zai tafi kuma sai yaja ya tsaya nadago
na dubeshi muka hada ido yace dama son Allah wani zance siri nake son yi dake
ko zaki fahince ni ban sani ba.

  A take naji gabana
ya fadi girman shi na batun barewa a idona a cikin daurewa nace ina jin ka sai
naga yana tura hannu a aljihunshi ya ciro wani dan wallet a ciki na fata ya
bude ya zaro dollars din Europe ya miko min yana fadin don Allah ko kinsa  wanan kudin wace kasane ?

  Jiya baya na zaro
kayana na tsunceshi a ciki har guda goma gasu nan harda address din mai shi a
ciki na karbi kudin daga hannun shi na duba Allah ya taimake mu nasan kan kudin
don rana  mun zauna da yaya musa muna
hira falon mama yai muna bayanin yadda suke.

    Nace ai wanan
kudin ketarene kudine masu daraja da kima a idon duniya kudine wanda sunfi
kowani kudi daukaka a nan duniya naga alama ya fada .

  Kinga wanan katin
kuma ina ganin na mai wanan kudine ya mata ya sako kayan a cikin gwajo ko wata
kila ansace mai sune suka shigo nan din.

   Kallon mamaki nayi
mai yaci gaba da fadi cikin muryan damuwa da ace da hanyar da zanturawa mai
kudin nan da kudinsa su koma wushi danayi hakan na sauke nayin hakkin shi a
kaina.

   Haba dai kaiko
wana  ai kamar kyautane ubangiji ya
bakasu don a matsayin rabo sukazo hannun ka duba nisan tafiyan da suka sha a
cikin duniyan amma ba wanda yasan da kudin nan saika.

 Eh to nasan da hakan
amma kuma shi maishi kamar bada sanin shi ya bar kudin a ciki ba ai nidai da
zan samu a kira min layin naji saina fadawa mai shi cewa kudin yana hannuna
zaifi.

   Wai wanan ai long
process ne idan har kudin basu kwantama a raiba zaka iya yin sadaka dasu ka
huta ai wanan kuma kin kawp shawara babba zan kara bincika inji ya matsayin su
suke a wajena.

    Ban katin mugani
ko za a samu lanban maishi a ciki sai kayi magana dashi to kina ganin hakan ba
zai ja muna matsala ba ko babu wani matsala indai zai fahinci abinda kake fada.

   Katin ya sake miko
min nabi katin da kallo na dan lokaci kafin na gane lamban da aka rubuta na
waya a ciki nasa na danna kira yana tsaye yana kallona.

   Turancin da ake min
yafi karfina na mika mashi wayan tawa kiran iPhone ya karba yana saurare sai
kawai naji ya buge da turanci kamar wani wanda ya tashi a kasan waje.

   Turanci sosai yake
bugawa da mutumin saida yai mai bayani dala dala baturen ya gane sukai magana
ta fahinta dashi yayi maigodiya suka kashe wayan ya miko min wayana yana
godiya.

    Mai karatu wanan
abin ya kara jawo shakuwa da yarda a tsakanin mu don a tare mukai shawara har
na binciko mai inda zaikai a canza mai cikin mutunci ta hanyar bashi lamban ya
musa sukai magana dashi.

   Na karbi kudin muka
tura mai Abuja ya canzo mashi su in naira sai gashi ya tashi da wurin dubu dari
hudu da dan kai wanan ba karamin tsoron hakan yaji ba.

   Kallona yayi da mamaki
yace kanwata kin san me ki rike wanan kudin a hannunki ki ban dari na fara
juyashi ta wani hanya zan dan dinga zuwa kauye ranan sati in sayo kayan
masarufi na kawo cikin unguwar mu in kasa.

   Don wanan da kika
ban da wanda na sayar da uwar garken Dije sune yanzu nake harkan gwanjona dasu
muna samun rufin asiri a ciki kuma sosai.

  Idan ban fadi karya
ba ke alherice don haduwana dake dana rabe ki na samu alheri sosai a rayuwana
ba zan boye maki ba.

    Kai haba brother
kawai dai nazo a daidai lokacin abine kawai yace ba zaki gane hakan bane kawai
abar zancen nace shike nan.

   Sam yanzu banda
matsalan kan karatuna don muma haduwan mu dashi ya zama muna alheri a karatun
mu sosai sai gashi ana hada babban group yana kara muna darasi saidai ba kulun
hakan ke faruwa ba don hankalinshi ya kara daukuwa ga sana,an shi yanzu sosai.

    Kusan sati daya
bamu sashi a ido ba gashi karatu ya dau zafi sosai muna yawan test lokaci
lokaci sai hakan ya tayarwa yan uwan karatuna da hankali.

   Suka yanke shawaran
cewa mu hada kafa muje har gidansu a dubashi ko lafiya da bama ganin shi dole
yasa ba bisu don bani zuwa ko ina daga makaranta.

   Munir ne ya binciko
muna sunan unguwarsu din da kwatancen gidan nasu a inda zamu samu isa a saukake
ga sayayan da muka hada kudi akayi za a kai gidan nasu.

  A motana muka shiga
saita munir din da maza suka shiga sune a gaba muna biye dasu a bayan su zuwa
gida da dan nisa sosai da school din mu.

    Dije ne kadai a
gidan ban daki ta zagaya ta fito ta tsaya tana wanke hannayen ta idon ta ya
sauka kan tsiron daya fito daga gefen dan gatangan kasan daya zagaye gidan nasu
.

    Ido ta kurawa
wurin kafin ta taka zuwa gaban dan tsiron ta kara kura mai ido sosai hannu
takai zata cire don kada haki ya jawo masu sauro don hakane gidan ko yaushe fes
yake a garesu.

   Wani kuka uwargarke
tayi wanda yasa Dije firgita tana fadin ke yanzu nasan kukan ki da ma,ana yake
watau kina nufin na nabarshi kada in cire ko ?

  To Allah ya sauwaka
ta fada tana barin wurin da sauri don lamarin uwargarken ya fara bata tsoro
yanzu sosai yasa ta kara rike addua da karban magani a wurin malam tanimu da
har saida ya shigo da kanshi kallo
uwargarke.

  Inda ya kara tsora
Dije da fadin indai ba sun shigeta ba to tana da shafansu a jikinta gaskiya don
alamu sun nuna hakan sosai ga dabban.

   Haikan dije ta
tsani uwargarke yanzu saidai tana tsoron nuna hakan afili don gudun wani abu
yazo ya sameta wanda ya shafi iskokai.

    Da tambaya Allah
ya kaimu gidan nasu a kofa muka tsaya inda ba iya gidan ba kusan unguwan nake
karewa kallon mamakin ashe akwai irin wanan unguwar tallakawan a cikon gari
haka har yanzu.

    Kofan gidan da
naga munir din ya tsaya sai mamakina yakaru lokacin layin shiru sai motsin daka
da mukeji a wasu gidan unguwan.

    Fitowa yayi daga
motanshi kiran honda ya nufo inda muka tsaya yana fadin to ai saiku fito ku
mata ku shiga kuyi muna sallama ciki muji dole muka fito na tako da kyar ina
bin bayan su zuwa cikin gida .

 Hannatu ce a gaba
muna biye da ita kusan nice fa karshe don haka akaji sallamana daga bayan su .

  Wani kuka mai ban
tsoro mukaji saida kowan mu ya kadu saboda sautin kukan nata har zamu juya  muryan tsohuwar daga ciko tana fadin sannun
ku da zuwa su waye ?

   Nikan tsakiyansu na
shige don ga bakidaya tsoro nakeji mama Ahmed muke nema mama Hannatu ta fada
Ahmed a gidan nakuwa eh mama nan akai muna kwatancen gidansu.

    Wanda ke karatu a
jami,a babba kamar yadda yan gari ke fada kodai Amadi tsohuwar ta fada kai
tsaye sai hannatun tace shi mama Amadi kuke ce masa ko ?

   Ai saiki yawace
unguwan nan kaf kuna neman shi da sunan nan ba a gane ba amma dakunce Amadi
kowa yasan nan ne .

    Yanzun nan ya dawo
daga kauye kwana biyun nan duk bai fita don ciwon kafana daya tashi yana gidan
nan yana kula dani.

  Yaune dana danji
sauki ya tafi kauye dauko hatsi kuma har sun dawo don naga an fara shigo da
kayan su daga bayan mu mukaji suna shigowa yana fadin tunda kunzo aisai kun
shigo kunga kakata Dije.

  Turus yayi don ganin
mu gaba dayan mune ashe mukazo don bai farga da motana dake can gefe dana
parker ba a unguwar don samun saukin fita idan zamu koma.

Leave a Reply

Back to top button