TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 44

Sponsored Links

ZAINAB IDRIS MAKAWA

 

[3/1, 6:22 AM] +234 803 800 7509: 🌱

TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣4️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Abubuwa sun faru a rayuwa da dama wanda ba dole saina tsaya
fayace maki suba kamar yadda rikicin gida kan auku ko ya faru a wani lokacin.

Haka mukan danyi
waya can ba,a rasa ba tsakanina da Ahmed wanda yanzu zumuncin mu dashi yaja
baya sosai wata kila don yanzu bamu ganin juna dashine akai akai.

Wata kila kuma ya
kama kanshi danice don yasan ba ajin mu dayaba dashi kamar yadda Abba ya fada
mai haka haka kuma ko waya zai ai wata dayama ko fiye da hakan bamu nemi juna
dashi mun gaisa ba.

Kamar yadda kowa
ke rayuwa haka shima din a yanzu ya jajirce sosai a wurin neman na kasa kuma
yana samu don Allah yai mai budi ga sana,an da yakeyi din.

A cikin hakane
yayi shawaran tayar da daki ta wani barin gidan don da wanan burin ya taso a
ranshi na ganin ya gyarawa dije dakin da take rayuwa a ciki wanda har itatuwa
ansa daga baya an tangale mata su don kada ginan ya fadi.

Wanan yasa yasha
alwashin idan ya samu budi zai tayar da gina yai masu dakuna su koma ci yanzun
ma din da yaga yan canji na shigo mai sai ya yanke shawaran yin hakan sai gani
kawai akayi ya tayar da gina a cikin gidan nasu.

Ba zargi don kowa
yasan sana,anshi yana samu sosai a yanzu zai tafi gari gari ya dauko hatsi ya
shigo dashi zamfara yabawa yan sari su sara su dora mashi riba gobema zai koma
wata jahar ya dauko ya kawo ya sayar masu da haka sana,an nasa ya fara bunka
sosai.

Ga nauyi ya karu mai
a yanzu mijin mahaifiyar shi ya mutu a sanadiyar macijin nan daya sare shi
zancen su dawo gida akeyi yanzu da iyalinta don ta haifi yan mata biyu da
mutumin gashi ba wurin da zasu zauna a nan din idan sun dawo.

Maigidanshi ne ya
bashi shawaran cewa ya tayar da dakuna biyu gami da nasa da zai zauna ciki da
falo da bandaki ya hada da kitchen ya dinga karasawa a hankali.

Baiki shawaran
maigidan nasa ba ya fara da hakan aka tayar da dakunan saidai lokacin da akazo
fitar da foundation din ginan anyi dashi ya bari a sare iccen  tunfafiyan nan yace sam bai yarda a saremai
ita ba.

Don Allah yasan
dalilin fitowanta gidansu gashi har makwabta yaga sun fara shigowa diban ta ta
baje tayi kyau ta samu wuri gwanin ban sha,awa da ita.

Antayar da aikin
zangazanga an fitar da ginan yadda yake son ya kasance don ya raba barin shi
daban dana su Dije din a lokacin da ginan ya dan tasa sai aka dakata da
nasa  anci gaba da ginawa Dije da
mahaifiyanshi inda zasu zauna su daga dayan barin kuma akaja nasa din kamar
yadda maigidan nasa yace yayi din.

Abinka da kudi
kasa tunda ba wani gina bane nasu dije din na azo agani nan da nan aka kai
linta aka dakata bayan sati biyu kuma aka dora inda aka tsaya da ginan  kafin wata biyu ya gama gina part din su Dije
saiga gidan ya fito ras dashi ba zakace rubaben gidan su bane hakan yadda wurin
ya haska.

Dakatawa yayi da
ginan ya mayar da hankalinshi wurin sana,an shi don yanzu kan bai zama sam a
garin ko yaushe yana wurin sana,an shi yana neman kudi yayin da ginan shi kuma
yake danyinsa a hankali idan ya tara kudi.

Muna zaune  nacewa hanne ta tashi muje ta rakani unguwa
na karbo sako da ummah ke bina na kusan kwana uku ke nan kuma ina jin kiuyan
hakan.

Mun karyo kwanan
wani layi muka hade dashi saman yar mashin din hawanshi daya saya don zirga
zirganshi na gida da sana,anshi kuma.

Yana goye da wata
yar matashiyar budurwa da bazata wuce sha hudu ba da haihuwa Hannece ta fara
ganinsa take fadin ikon Allah ga master namu can fa.

Jin hakan yasa na
dan juya na ganshi goye da yarinyar saman mashin din shi duk ba komai a
tsakanin mu saida na danji ba dadi a raina na danna masa horn yana ji horn din
motana ya juyo ya ganmu da hanne din.

Ya biyo mu baya a
guje ganin hakan yasa na samu wuri na Parker motar ya cin muna daidai saitina
ya karaso da mashin din nasa na sauke glass mukai arba dashi.

Duk ya kara dan
rama don ujulan da yanzu yakeyi din ya fara gaidamu tare da tambayan sai ina
haka yanzu lokacin school hours ne fa kafin nayi magana hanne ke fadin .

Daga can muke yau
malam bai shigo ba ya bamu hakkuru matarsace ba lafiya suna asibiti tun jiya
yasa kaga mun fito yayi Allah ya sauwaka.

Lokacin naji ya
dan juya yana cewa yarinyar daya goyo din ke baki iya gaisuwa bane halan a, a
master ina fa zata gaidamu taga mun cika mata ido haka ?

Dan murmushi yayi
don ya gane me hannen ke nufi yana fadin kai hanne baki da dama wanan sister
dinace hindu kinsan sun dawo garin nan yanzu da zama har mama ai kwanaki na
fadawa kawarki mutuwa  mijin mama din ko
?

Sai lokacin na
dago kai na dan kalli harinyar gaskiya suna da dan kama ta jini saidai shi
yafita haske sosai ba kusa ba yake nayi a fuskana tare da fadin kai amma ai
baka fada min suna garin nan ba .

Da munzo da hanne
mun masu gaisuwa ai a nan ko yanzu ma bai baci ba zamu shigo ai idan muna free
hannatu ta fada daga gefena.

Wanan me tsoron
akuyar ce zata zo gidan mu Dije tun tana tambaya har yanzu ta gaji ta daina
tambaya dana fada mata gaskiya.

Ita wanan wake
maganantane da tsoro ko kadangare ta gani yanzune zakaga tana batun shudewa a
wurin saboda tsoron tsiya na dan harari hannen nace magulmaciya.

Yace well barin
kyale ku kada insa ku makara don naga kamar kuna nisa sai kuma wani lokacin ke
nan idan mun hadu jakkata nake kokarin budewa naji ya tayar da mashin dinshi
yana fadin zan kiraki zahra akai abinda nake son tambayan ki.

Saina jika nace
ina mikawa yarinyar kudin dana dauko tare da fadin yar makaranta gashi tunda
baki gaida muba nina sayi gaisuwan naki yanzu.

Alaman kunya ta nuna
ta amsa tana min godiya naja motan na barsu a wurin kafin yayi magana muka
karbo sakon tare da komawa school.

Sam na mace da
zancen kiran nasa sai bayan kwana biyu har na kwanta naji wayana tana kuka na
dauka na duba ina mamakin me kirana a zatona ma ko maryamce da a yanzu muka
zama kawaye sosai muna waya kai dakai da ita.

Ahmed na gani yadda
nayi serving din layinshi din na daga yake fadin na zata ai har kinyi barci ne
zan kashe don kada in tayar dake daga barcin.

Nayi murmushi tare
da fadin banyi ba ina dai shirin yi yanzu kenan ka kirani muka gaisa sai ya
sanyi shiru kamar yadda nima nayi shirun ina saurarenshi.

Yake fadin Zahra
dama akan zancen kudin kine dake hannuna ina son in mayar maki da abinki yanzu
tunda na samu alheri sosai ta hanyar su.

Da wanan da muka
tsunta din kema zance maki wani abu daga cikin kudin tunda an juya an kuma samu
yanzu don gaskiya Alhamdullahi.

Uhumm kawai na iya
fadi na dora da cewa aini ban baka din ka dawo min dasu ba taimaka maka nayi ka
kara jari dama dasu don haka don Allah ka bar zancen nan please.

Zahra kudine masu
yawa fa ko har kin manta yawansu ne wai nace ban kuma son in sake tunasu ko a
yanzu in ma kana son wasu zan iya baka iya karfina don har gobe Abba yana bamu
dakuma su yaya musa suna nan min ajiye din bana sayen komai ni.

Yanzun dai kina
nufin naci gaba da juyasu ke nan baki da bukatansu yanzu eh ka juya din na fada
a gajarce idan kin bukata lokacin da bandasu fa ya fada.

Don gina nakeyi
yanzu ina tsoron kada kudin naki ya shige ciki dan murmushi nayi din jin meya
fada kafin nace ayi gina mai kyau dai Allah ya bada ikon gamawa lafiya.

Zahra kin daureni
da yawa bansan me zance dake ba yanzu nima haka don ban baka kudi da sunan aro
ba sai don ka samu binda zaka tallafawa rayuwan ku .

Yanzun kuma wani
nauyi ya kara hawa kanka tunda ga su mama sun dawo karkashin ka kuma yanzu don
haka ni kyauta na baka kada mu kara zancensu dakai don Allah ina fadin hakan na
kashe wayana.

Na barshi rike da
waya da mamakina saiga text dinshi ya shigo min yana fadin zahra muna magana
dake kin kashe waya godiyanane bakya son ji to nagode Allah ya bar zumunci a
tsakanin mu ya karawa baba lafiya da mama.

Wani iri naji har
hakan yasa nadan runtse idanuwana tausayi ya ban naga duk irin cin mutuncin da
Abban mu yayi mashi hakan bai hanashi yiwa Abba din addua mai kyau  haka ba.

Har muna batun
fara exam banyi zancen zuwa gidansu Ahmed ba ganin hakan yasa hannatu ta tuna
min zancen zuwa gidan banyi magana sai washe gari na dauketa mukaje wani shago
muka danyi sayayya a shagon .

Da kwatance muka
iso gidan saidai yaran muka samu manyan basa gida tun waje suka taremu suna
fada muna muka mika masu kayan da muka sayo din hannatu tace idan sunzo a fada
masu cewa abokan karatun Ahmed ne suka zo masu gaisuwa.

Muka ja mota muka
tafi ina godewa Allah da bankai ga shiga gidan ba muka samu wucewa don na tsani
ganin wanan bakar akuyan dake gidan.

Gashi su sunki
rabuwa da akuyar kamar ta tsafi a gidan ina wanan tunanen har bansan lokacin
danaja tsuki a fili ba har hanne ta juyo tana tambayana ko lafiya ?

Just forget about
it wanan bakar akuyan tasu nake tsoro nake godewa Allah da ban shiga ba na
ganta yau daba zan iya barci ba sai nayi mafalkinta a karshe.

Lokacin da Ahmed
ya dawo ya shiga gaidasu ne Dije tana washe baki tana fadin yau da alaman yar
arzikin nan ta shigo wai tazo yiwa uwarka gaisuwa bama nan.

Har suka kawo muna
wanan abin arzikin haka wai ace muna abokan karatun kane suka zo da motar su
yaran nan na fadin abun gwanin ban sha,awa.

Dan Dije ina kasan
yaran masu kudi haka har suna zuwa da wanan irin alherin mai yawa haka uwar ta
jefo mashi tambaya daga inda take zaune kofan dakinta tana cin abinci.

Yace mama gashi sun
fada abokan karatunane su din yar gidan wani mai kudine a garin nan jinin mu ya
hadu dasu muke cin alherin su haka.

Dan Dije kabi sannu
banson daukan magana ka tsaya matsayim ka da Allah ya ajeka kada ka dauko muna
fitinan da yafi karfin mu don hurda dasu tonon asirine a gareka karshe.

Wane irin magana
kikayi haka mara dadin ji don suna mutunci shina ka zama tonon asirinai ?

Ba hakana bane inna
ke san yadda duniya yanzu ta koma kowa baison ka rabai ka karu yar mai kudi sai
dan mai kudi irin ta hakama dan tallaka ya tsaya matsayinai.

Yafiki sanin haka shida
a namiji yana jin irin abubuwan daka hwaru a gari yace maki soyayya yakai da
ita ina zai fara haka gwalmadiya,i ya debowa kainai ruwan dahwa kaine .

Wane uba ka tsaya
mai duk garin nan a bashi yar gidan mai kudi dan dama dama da ubanai ya tuna
dashi har ansanshi a dauki mata a bashi.

Nina dade ina
jiyowan wan ga ranan gare mu don nasan a lokacin nan za a tayar muna da tsohon
hwamin daka zuciyoyin mu anyi haka dauri balle yanzu da kan kowa ya waye.

Wani iri yaji a
zuciyar shi daga shi har mahaifiyan tasa sai da kibiyan tsoro ya caki zuciyar
su lokaci guda uwar tasa ta dauka da fadin .

Yanzu ai kin gane
abinda naka nufi ke nan ni rigimana banison ya dauko wa kanshi da abinda yasan
bashi yuyuwa garai.

Wanda ko ubane bai
taba gani ba sunan kana dan halal ne kawai kaka zuwa gidan masu hannu da shuni
kakai kan ka ?

Wa hwada maki
bansan ubana ba saukin abindai ina da uba da yan uwan uba don haka kko hwada
min ina bashi amsa yanzu.

Ya mike tare da
saka takalmanshi ya fice a gidan Dije na kiranshi yazo yaci abinci baiko tsaya
kulata ba ya wuce don rashi daya baci fa baki daya a lokacin.

Wuri ya samu ya
zauna a gaban gidan su baisan lokacin da hawayen bakin ciki ya soma fito mashi
ba sai ranan ya tuna da malam musa.

Waya ya ciro a
cikin aljihun shi da niyar ta kira tsohon don sun kwana biyu basuyi waya da
dattijon ba da yanzu ya zame mai kamar mahaifin shi yake jinshi a ranshi.

Ya kira bai shiga
ba ya sauke ajiyan zuciya yana sake kiran dattijon sai tayi sa,a kiran ya shiga
ya dauka suka fara gaisawa yake tambayanshi shattu .

Sun dan jima suna
magana kafin su kashe wayan suyi sallama da junan nan su ya bike ya buga mashin
dinshi ya bar unguwar bai dawo ba sai cikin dare sosai ya shigo gidan ya samu
wuri ya kwanta.

Lalai kan naji
labarin cewa su Aisha sun tsayar da mazajen aure kuma na tayasu murna sosai ga
hakan sam ban kawo rai da cewa wai don sunyi hakan nima na fitar da miji kona
fara kula samari ba don ba rasasu nayi akwai su saidai babu fuska gareni ne don
irin tsawatawan da Abba yai min a baya.

Yasa yanzu na kara
mayar da hankalina sosai wajen karatuna ban yarda koda wasa ma in tsaya da wani
wai ina zance.

Allah sarki ashe
duk da hakan ba tsira nayi ba a wajen mama don sun hada min bom nida ummah
dayasa zukata baci a gidan namu don ko Abba yai wani zuwa gaisuwa .

Don anyi rasuwa suka
zo hardasu yaya musa da ya jafar lokacin nan mazajen su Aisha suka zo gaida
Abba din kuma suyi masu gaisuwa.

Bayan sun wuce ne
da dare suna falonshi da yayyunmu maza ana maganan a kai har aka jefo zancena
cewa ni wana tsayar ya musa ne ya tare da fadin.

Haba dai Abba Zahra
fa karatu takeyi yanzu bawai lalai bane ace sai tare za ai masu aure dasu kafin
ya karasa mama ta haushi da fada tana fadin to uban mu.

Zama zarayi gidan
ku jikata kusha ko me yarinya da wanda take so zaka wani kawo tsurku ka tare
kana fadin wai tana wani karatune yanzu.

Suma din ai karatun
sukeyi bawai sun gama bane ko wanene take so yanzu din Abban ya tambayi mama
din tace a wanan yaron daine na kwanaki mana don basu rabu ba tunda shi take
so.

Yaron da baida
asali din dana rabata dashi ashe ta nace saishi mama tace a toh suna dai tare
don basu rabu ba gaskiya tunda bata ba wani fuskan zuwa ba.

Abba baida asali
kamar yaya ya musa ya fada cikin dan bacin rai yace ta fada min fa ubanshi dan
shiyoyin gabas din nan nd kuma har yana zuwa garinsu .

Mama tayi saurin
fadin kaji ba Alh ai na fadama ka barta kawai tayi don kada ta jawo muna abin
kunya don Allah shi aure ai mukaddarine in Allah yayi shine mijin ta ba makawa
sai anyi auren nan Alh.

Da rabo yazo ya
kashe ai gara ka yarda ka aura matashi a zauna lafiya haba haba mama wanan
maganan bai dace ba haka ga zahra don kowa yasan irin natsuwan zahra din.

Wanan yarinyar na
gane abin kunya take son ta jawo muna kawai Abban ya fada cikin bacin rai mama
tace ai shi nake fadama wa yan nan sakarkaru suna wani tarewa kada in fada.

Karshe in wani mugun
abu ya faru duk laifin mu za azo agani ace mun saka ido akai barna a gidan nan
yadda take magana zakace wani mugun abu nakeyi a rayuwana.

Abba yai shiru na
dan lokaci kafin yace shiyasa kwanaki da sukaje kano karima ta samo mata wani a
can yarinyar nan taki zancen nan .

Kadai fada kaima
yanzu ai indai har abu ya kwabe wanan kuma kai kajawa kanka Alh Abba din bai
iya cewa komai ba a lokacin sai shirun da yayi.

Bayan kwana biyu
abin yana cinsa sosai a ranshi ya kira maigadin gidan mu yana tambayan shi
wayaga yana zuwa wurina ?

Mamakine ya kama
maigadin yace Allah ai mama boyar Allah ce don ban taba ganin wani yazo gidan
nan ba wurinta da sunan hira ba.

Idan ta dawo ta
shige gida ta shige ke nan sai kuma idan zata fita da safe gata bata kara
lokaci ga yadda ta saba dawowa kullun.

Tashi kaje kawai
Abba ya fada ya mike yana mashi godiya ya fice daga falon Abba ya dade zaune
yana tunane kafin ya yanke shawaran abjnda yake gani daidai a gareshi yabarwa
cikin shi sauran zancen.

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Sun dai gagauta
tsayar da zancen sukai sallama ya tafi shi kuma ya juya ya koma ya samu Alh
yana fadin ya dan kewayane sukaci gaba da hiransu a wurin.

Hjy ta fito kamar
tana neman wani abu a lokacin shi jabbi ya gane me take nufi da haka  yai kamar bai fahinci komai da hakan ke nufi
ba.

Kamar yadda suka
shirya da isa din hakan ya faru bayan dan bayaro yazo yake tambayanshi ina
abokin shi yake fadin ai bayanan ya koma garin su ko.

Daya karbi
dinkin ne ya hau mashin shima ya hau yabi bayan shi har zuwa unguwar su dan
bayaro din yaga gidan da yashiga din.

Ya juyo ya dawo
shagon shi ya zauna ya kama bakinshi har zuwa tashi ya samu wuri ya kira wayan
Alh Jabbi yai mashi bayanin unguwan da siffan dan bayaro din.

Yai mai godiya ya
kashe wayan yana kiyasta yadda zai bullo idan yaje unguwan don wanan lamarin
yana son taka tsantsan a cikin sa.

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/1, 11:33 PM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMF

Leave a Reply

Back to top button