TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 64

Sponsored Links

 ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/2, 9:15 AM] +234 703 080 4044: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣4️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Daga school gidan muna na nufa tare da hannatu muka shiga
saidai mun fara zuwa wurin ummah mun gaida ita mukaci abinci bata fada muna
komai ba sai bayan munyi sallah muka shirya zuwa part din mama don mu gaishesu.

   Tun kan mushiga
muke jin  dan hayaniya a part din tunda
nasan an haihu don haka na dauka ai yan barkane suka cika wurin ake hira mukai
sallama muka shiga.

   Mama gwaggo Rakiya
yar dakin mama Rukkaiyan mu da yan uwan mama guda biyune a falon suke wanan
cacan bakin ashe nashiga na gaidasu a cikin fara,ana.

    Ba laifin sun
karba min akai gaisuwan mutunci nace ina maijegon mama tana ciki ta fada cikin
wani irin murya mai sanyi da rashin fara,a.

   Sauran ko sai bina
da kallo sukeyi na kwakwakwan na mike zuwa cikin hannatu ma ta biyoni a baya
tunkan mu shiga dakin nake jin muryansu ita da hjy hakan yasa nagane hjy na
dakin a lokacin don na dauka ta tafi gidane.

   In bako Aisha ba wa
hjy zatazo ta zauna dashi a gida don ya haihu saisu yan gaban goshinta da basu
laifi a wurinta komai sukayi daidaine ko yanzun ma ganinta baisa naji komai ba
irin da danakan dan tsargu don nasan sai ta saka min tsarguwa kafin mu rabu.

  Idon Aisha din yayi
hulu hulu ga hawaye dake gangara a fuskanta tana shara lokacin ba bata lokaci
nace subbahanallahi maijego kuma yaya hakan da kuka ?

   Haba dai meyayi
zafi kike kuka waya taba muna ke kuma barta da tsiyanta an bata hakkuri tayi
shiru kada tajawa kanta wani ciwo taki ya barta mana in iyayyenta sun sa ya
rabu da ita sai me kantane farau irin hakan ko itace karshe.

  Shi kaddara ai yana
kan kowa waye baisan kaddaraba kuma hjy ke fada tana miko muna yar da aka hana
mu dauketa lokacin.

     Na karbi yarinyar
na dan dubata na rasa dawa tayi kama tsakanin uwan da uban na mikata gun
Hannatu ta karba tana bin yarinyar da kallo naga har tana gyara mata hannu.

   Sheshekan Aishan ne
yasani dago kaina na kalleta ina fadin wai meya farune kike wanan kukan naji
hjy na maganan nan.

    Barta wai don
iyayyen mijin sunzo jiya barka sunce basu yarda da yarinyar nan jininsu bace
don haka ba zasuyi suna ba shine take wanan irin kukan kamar ranta zai fita.

   Ashar na lailayo na
sake nace da kazan uba ba yarsu bace dawa yarinyar tayi kama bada shi jamil din
ba don iskaci fadi kedai yar albarka kema ai kya fada.

  Don ga abu a zahiri
kowa nagani amma haka yarshi jiya ta rufe ido tayi muna cin mutunci a gidan nan
kamar ba gobe gareta.

    Muryan hannatu
danajime ya katse min magana tana fadin yar nan fa kamar bata da lafiya nake
gani asibiti mai sukace game da ita ?

    Da sauri najuyo
ina kallon yarinyar gaskiyane nima naga hakan don nufashinta bai sauka sosai a
lokacin hjy tace dannewan cikine yake saka hakan sai hannatun ke fadin a a hjy
gaskiya da kunkaita asibiti zaifi.

    Haka takeyi tunda
aka haifeta nayi magana sunce ba komai bane idan dare yayi ma abin yafi worse
bata ma numfashin wani lokaci kamar ta mutu.

   Anya ba free matual
bace yarinyar nan kuwa hannatun ta kara fada don gaskiya ba normal take sauke
numfashinta ba abinda nake gani ke nan uwarta fada duk shi ya kawo matsalan nan
ai tunda bamu cika Nine months ba.

   Da sauri hannatu ta
kalleni nace ke nan sun sani suke son dorawa mutane laifi akai gaskiya sai an
nemawa yarinya hakkinta kada su batawa mutane suna a banza.

   Ai mahaifinku yana
tafe yace yau din nan idan yazo duk yadda za ayi sai ayita amma basu isa su
taka mutane irin haka a kyalesu  inbanda
ma ita Aishan data nace wa wayan nan mutanen banza aitun farko sun nuna suba
mutanen arziki bane dama.

   Mamace ta shigo yar
mama tayi muna tsaye tana signal kada a fada muna caraf a idanun Hannatu sai
hannatun tayi saurin fadin yanzun dai ayi gagawan kai yarinyar nan asibiti aji meke
damunta shiyafi.

    Wanan yar ne za
akai asibiti yayan mama din ta tambaya cikin mamaki da sauri Aisha din tace ba
rayuwa gareta ba mama itama mama ?

    Ni gaskiya idan ba
zaku   kaita ba naje na kaita a dubata
don hankalina yana tashi gaskiya da yadda yarinyar nan takeyi da dare Aishan ta
fada cikin tashin kunya.

  Ke arrr uwayen ma
naki baki barsu ba shiyasa yar mijin naki keson ta karantawa mutane hauka don
tana yar iska kin nuna kina mutuwan son dan uwansu, kamar mai bakin uwa a kai.

   Nan dai ta bushe
ido tana ba hjy amsa har yar mama din taje ta kira mama a falo tazo ta duba hjy
sai cewa tayi mune da iyayin mu kazo da zancen akai ya asibiti.

   Mama din tace eh
gaskiya hjy yar nan na bukatan ganin likita don yadda take numfashin nan baya
sauka abin a dubane sai hjy din da yar uwan mama suka mere baki waisu basu taba
ganin an kai da asibiti ba haka .

   Mudai bamu fito ba
saida muka tabbatar sun tafi asibitin wai ashe wani cleanic ta haihu dama suna
zuwa asibitin aka hausu da fada kanme suka zauna gida da yarinya haka tana jin
jiki aka dora mata oxygen nan take irin na yara.

   Bayan na koma part
din ummah nake tambaya ashe rikici akeyi tsakanin su mama da dangin mijin Aisha
sunce basu yarda da yar nan ta dansu bane ?

    Fitar da bakinki
cikin zancen nan kada sunan ki ya fito a zancen nan ki saka masu ido suyi
abinsu iyakan ki dasu gaisuwa shine ya dace a tsakanin mu.

   Mutanen da ko barka
na shiga gaidasu suke nuna min wani hali har boyon yar sukeyi suna zaton zan
mata wani mugun abune shiyasa na bar zuwa na gaidasu yanzu tun da naje sau
biyu.

  Shiru nayi ina dan
tunane kafin nace munyi karanbanin fadin yar na bukatan zuwa asibiti don bata
da lafiya kafin ummah tayi magana sai hannatu tace in sun boyeta ai ba zasu
boyewa Allah ba shidaya halicceta.

  Ummah kiyi hakkuri
don mun rigada mun maganta hakan garesu sai ummah din batace damu komai ba ta
dauko wani hiran munayi akabar zancensu.

   Hakan yasa ban dawo
gida ba sai dare karfe tara da wani abu na shigo gidan part dina na nufa kai
tsaye na bude na shiga saidana kwabe kayan jikina na watsa ruwa na fito zuwa
cikin gida don in duba Dije.

    Na shiga da
sallamana suka amsa min na gaidasu don inna bata gidan ta fita unguwa lokacin
don na tambaya inna na dakine sukace ta fita dazun nan saidai Dije.

   Na shiga na gaida
Dije din nayi mata ya jiki tare da tambayanta kota sha maganinta tace tasha
dazun da yamman nan ina zaune muna hiran jaririyan da Dije innan ta dawo tana
fadin har yanzu wanan bata dawo ba ke nan.

    Ta dawo tun fitan
ki gata nan dakin Dije ma zaune suna fira jin hakan yasa na fito na samu inna
din ina gaida ita nace na samu jaririyan bata da lafiya ankaita asibiti yanzu
hakama an bata gadone suna can.

    Ikon Allah
jaririyan aka kwantar to Allah ya sauwaka ta fada tana shiga dakinta ban koma
dakin Dije din ba na nufi part dina har na fara tafiya naji Asmau na fadin kada
ki rufe muna nan shigowa fa.

   Na amsa mata da to
na wuce abina nadai jin muryan inna a lokacin amma ban tsaya sauren abinda take
fadi ba don kona tsaya rainane zai baci a banza.

    Kamar yadda suka
aje goma na safe suna kofan gidan abokin nasu suna jiranshi bai bata lokaci ba
ya fito tare suka zagaya dashi dukkan gidan dan uwa daya kamata yana zumunci
tare da alheri garesu.

   Hakan yana iya jawo
mantuwa ga dan Adam shine hikimarshi na ziyarta wanan karon yana masu alherin
daya dace dasu sai biyu ya dawo gida a gajiye cikinma baije wasu wuraren ba ke
nan don yawa garesu sosai a garin.

    Jin hakan da hjy
Korau tayi cewa ai yau Dan gaske ziyara yake kaiwa yan uwanshi yana kuma masu
alheri sai hassada da bakin ciki irin na kishiyar uwa mai mugun nufi ga dan
kishiya ya darsu a zuciyanta.

   Abinda bata son ji
ke nan ace shine ya zama tauraron gida yana tallafa masu harda diyanta da yan
uwa duk dako wace uwa nason hakan a dakinta ai.

   Sai ranta ya baci
sosai ta shiga daki tasa jikanta ta kira mata yarta hjy Yabi duk da a yanzu
Yabi din ta dan bata baya amma hakan bai hana tana aiko mata da alheri irin na
uwaye.

  Ba kuma wani abune
ya hadasu ba sai yadda taso ta juya hjy yabi dinne da irin mulkinta taki yarda
dashi shine ya kawo masu sabani a tsakaninsu suka bata baya suna abu tsakaninta
da yan uwanta yanzu tunda sun bude ido da hakan dama.

    Tana daukan wayan
take fadin bayan sun gaisa yau dai ga irin abinda nake fada maki nan yana
faruwa da mijin ki dama ta yaro kyau yake baya karko.

   Na fada maki kada
ki yarda ya rabi yan uwan nan nasu ko abokansa su Jauro amma kin nuna ban iya
ba don komai da mukayi an fada muna har in hakan ya faru komai zai lalace muna
tun farko.

    Hjy ban fahince
kiba hjy yabin ta fada daga bangarenta nan dai ta koro mata irin hidiman da
yayiwa yan uwa da abokan arzokinsa na baya yadda rahoto yazo mata daga bakin
babban data da aka bashi ya raina abinda dan uwan yayi mai don haka yaji zafi
yazo yana fadawa uwar nasa.

    Komai ma ina ganin
yanzu ya lalace don ko wanan tafiyan bai sanar dani ba zaizo gida saida ya iso
mukai waya yake fada min tun jiya hankalina a tashe yake don ina gudun yaje
Gembo wurin wa yan nan yan uwan nasa.

  Yaushe kuma dan Amo
ya fada min yaga sun dauki hanyar zuwa Gembo din nasan kuwa har Garba Chedi sai
yakai a can ne komai zai karasa lalacewa kuwa kuma kinsani .

 Don suma ba zama
zasuyi su zuba masa ido yana haka su fita batun shi ba tundai wanan malam Amadu
da baya kaunan mu ko kadan.

     Sunyi waya sosai
da tsohuwar don itama hankalinta a tashe yake lokacin suna neman mafita akan
hakan kada abinsu ya koma masu daga baya.

    Karfe shida da
wani abu na safe ya kira wayana na dauka muka gaisa yake fadin yaya zamuyi ki karbi
sako a tasha don driver zai kawo maki kaya yau din nan.

   Kaya na tambaya
cikin mamaki yace eh kayan da zakisaka wurin fita sunan yar uwanki na sayo maki
tare da takarduna na hado don naga kamar ranki ya baci ranan.

    Bai baci ba tunda
kaine maiyin aikin bani ba yace naji zaki bar wayan ki a gidane Aisha taje ta
karbo maki ko yaya za ayi din nasan zaki shiga school yau.

    Zan dai zauna har
drivern ya iso da sakon na karba da rana sai in shiga school kasan wayata bana
ba kowa su halaka min  ita.

   Hakane kuma why note ki shiga school din idan
ya kira ya iso sai ki fito ki karbo eh ko hannatu saita karbo min amma da baka
wahal da kanka wurin saya min kaya ba tunda ina dana sakawa ai.

    Haka nayi ra,ayi
saidai idan kin raina amma ba zanso su ganki da wasu kayan da suka sanki dashi
ba a wurin ya fada cikin wani irin murya.

   Idon na lumshe tare
da jin tausayin kanmu a lokaci guda a raina nace Allah sarki master yagama min
korafin baida kudi yanzu kuma ko ina ya samu kudin da har ya saya min kayan fita
suna oho ?

   Watau shidai master
sam baya son yaga na kasa a cikin yan uwana ko yaushe yana dai iya bakin
kokarinsa dani yadda kowa zai fito aganshi fes a wurin taron shima haka yake
son a ganni ke nan ban bambanta da yan uwana ba.

   Na dade zaune ina
tunanen zuci kafin na mike na fara shirin fita zuwa school ina kuma tunanen
yadda zan samu in karbo sakon ba tare da an samu matsala daga gareni ba don
saura kwana biyu sunan yar Anty Aisha.

   Duk da suna asibiti
ummah ta fada min da mukai waya za ayi taron sunan mama tace ba a janyeshi ba
yadda yake nasan mama da bidi,a kam.

   Don  hakane muke tashirin suna mukan da sauran yan
uwa son naji ance su Abbama sunzo har da hjy karima da yanzu ta daina zuwa
gusau din ban kuma san dalilin hakan ba tunda ba hurumina bane sanin halin da
suke ciki.

    Gashi kuma
washegari nake son in zauna gida inyi kitso da kumshi da badon hakan ba da
ranan na zauna gida ban fita ba ko don sakon dake tafe mani din.

   Sakon ya iso lafiya
kuma hannatuce taje ta karbo min din kakken atamface barauniyar super an mashi
dinki half gown dinkin ya kwanta yayi kyau sosai dashi don yan zaria badai
dinki ba kam sai in baka da kudin dinkin kwarai.

    Da wuri na dawo
gida don Aisha ce zata tsafe min kaina na wanke washegari aimun kitso da kumshi
a nan makwabtan mu wata mace ce muka samu yar maiduguri matar wani police take
kitson da kumshi koshi yan gayun garin sun bata ta yanzu don sai anyi bucking
dinta kafin ka samu .

  Don haka sammako
zanyi zuwa gidan nata ta gyarani bamda niyar girki don haka na nufi part din
nasu da kayan tsefe kan nawa.

   Wurin Dije na fara
shiga muka gaisa ina fada mata nazo Aisha ta tsefe min kaine gobe ba zan fita
ba zan tsaya gyaran jikine zuwa rana sai in leka gidan mu din.

   Muryan inna naji a
kofan tana magana na fito ina gaida ita nace Aisha gani nazo zancen tsifan kai
din tace a nan zamuyi ko a part dina lokacin naji inna tace Aisha.

    Ki dauko wanki ki
fara min kafin ku zauna kuma ki dora girki idan kin gama jin haka kawai yasa na
juya zuwa part na zauna na fara tsifan kan sai ga Asmau tace na kawo tayi min
yanzu ta dawo Aisha ke fada mata abinda ya faru ita inna kome yasa take haka
oho ?

 Ni dai ina jinta ta
gama min a cikin lokaci na wanke na dunkule don yanzu ba zancen zuwa saloon
bane gareni gaskiya don duk wasu abubuwan rayuwa na rage yinsu a yanzu din.

    Don kada yace sai
ya matsawa kanshi yai min tunda nagane halinshi na kwatantawa ban faye yin abin
da nakeyi a gida ba yanzu.

    Washegari sammako
nayi zuwa gidan kitson yaran sun nuna min suma suna so saidai suna kame kame
nasa akai muna tare dasu aka gama na biya karfe biyu muka dawo gida.

   Don mune na farkon
zuwa munyi sa,a an gama muna cikin lokaci don inna bata da kunya sai gata tana
jin dadi har tana nuna na diyan yafi kyau a gabana ni dai ban tsaya kulata ba.

   Washegari suna suka
kuma nuna zasuzo gidan namu nikan goma na safe ina gida don ina son inga Abba
ingaishi don mun dade bamu hadu ba.

   Nayi sa,a sai gashi
ya shigo ina daki da kanne na nan na fito ina gsidashi da mamaki ya juyo yana amsawa
tare da dan kura min ido kafin yace dani .

   Yaya maigidan naki
nace yana lafiya yana can school zaria yace har yanzun bai karasa karatun ba ke
nan na dan amsa da eh Abba.

  Badai kuna lafiya ba
nace lafiya kalau muke Abba ya danyi shiru har ya bude baki kamar zaiyi magana
sai kuma ya juya yana magana da ummah.

  Na daga daga inda
nake zan wuce naji yace kina dai kula da karatub ki yadda ya kamata ko nace eh
Abba to ki kula zai maki amfani wata rana koda koyarwa ne ki samu nace nagode
Abba.

   Daga hakan shima ya
fita wani iri naji a raina bayan fitan Abba din part din hjy karima naje muka
gaisa da ita itama din dai wani kallo take min da har na tsargu.

   Daga wurinta na
nufi part din mama ina gaida mutanen dana sama kowa dai idon shi akaina na rasa
meyasa hakan sai kawai na tsargu na tashi na koma part din mu a nan su hannatu
dasu Aisha da sukazo min suka sameni nadai kaisu sun gaisa da me haihuwa kafin
yamma muka amshi abin sunan mu ummah ta kara min da wanda aka bata muka dawo
gida.

Leave a Reply

Back to top button