TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 33

Sponsored Links

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3️⃣3️⃣

photo 2023 10 04 11 08 23

 

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Suna tsaye inda suka
parker motan a wani dan kauye wani mutum yazo wucewa yake fadin yau tun karfe
goma ai hanyar ba lafiya kunyi arziki da kuka tsaya nan din ai.

    Jin haka yasa
driver fadin sai mu kwana a nan ke nan da safe sai mubi hanya zaifi idan mun
fara ganin motoci sun fara tafiya dama wani lokaci sukanyi haka irin wurin nan
saidai ba ko wani lokaci hakan ke faruwa ba.

  Da zakabi zance na
kawai mu mike in sha Allahu ba abinda zai faru damu dattijon ya fada da sauri
driver ya tareshi da fadin a,a baba kada muyi gangancin yin hakan mu dawo muna
da mun sani mu dai bari ido na ganin ido mubi hanyan da safe kawai.

   A nan suka kwana
cikin motan zaune barci rabi da rabi sai da sukai sallah asuba suka ga wata
babban mota tabiyo ta wuce da kyat suka samu drivern motan ya tsaya suka
tambayeshi yace  hanya da sauki yanzu.

   Suma suka dauki
hanya zuwa hawan mambila lokacin duk suna a takure don sanyin da yaiyawa a
lokacin gashi babu wasu tufafi masu nauyi a jikin su da zai kare masu sanyi a
lokacin.

   Ikon Allah Ahmed
din ke kallo a lokacin don yanayin wanan wajen da bai taba zaton ko tunanen
cewa akwai irin wanan yanayin ba a kasan nan.

  Don dubaga yanayinsu
na zamfara na zafi daya fito cikin shi ga iskan zafi da rana a ko wani lokaci
suna cikin hakan su a zamfara.

    Amma sai ga
yanayin nan din ya bambanta da yanayin su kuma wai a kasa daya duk ake da wanan
bambamcin yanayi din yana faman kiyasta hakan a zuciyar shi.

   Samari mun fara
shiga yankin mambila fa daga nan da ace kasan barin da mahaifin naka ya fito
kaga sai mu ajeka a daidai inda zai sadaka da gurin shi cikin sauki.

    Zama ya dan gyara
don fahintar cewa dashi drivern ke magana a lokacin yace wallahi baba ban san
ainihin garin da yafito ba na dan san cewa ance yace shi din mutumin chedewane.

    Zaka sha wahala
koda zaka gane amma sai ka wahala sosai a gaskiya don gane mutum irin haka bai
yuyuwa cikin lokaci daya haka kai tsaye dole yana son lokaci mai tsawo sosai
don bincike drivern motan ke fadi.

   Hakane kan gaskiya
na gaba motan ya amsa shima yana fadin ai irin wanan tafiyan yana son bincike
sosai kafin mutum ya fito daga gida.

   Amma ka fito haka bakai
bincike ba ka kamo hanya daga kai saikai zuwa neman mutum a irin wanan wuri
haka kamata yayi kazo tare da wani ko ka bincika yadda zakayi saurin ganewa
kafin kazo din.

    In sha Allahu
ganewa zaiyi ai me tambaya baya bata tunda ya fito da niyar alheri a zuciyan
shi Allah zai sadasu a cikin salama wanan tsohon na gefen Ahmed din ya fada.

   Allah yasa don yana
da wuya a wanan zamanin ya iya ganeshi haka kai tsaye babu wani sheda da
zaikaishi inda yake drivern ya kara fadi.

    Gaskiya yana da
wuya kan ya gane haka kai tsayen nan yadda ya fito neman shi nan saidai a gwada
kawai ko za,ayi sa,an hakan daya  mutumin
ya fada.

  Ina ganin aiga baba
nan don yace shi a Gembo zai sauka kaga sai yai masa masauki ko wani taimako ga
hakan don gaskiya idan ba haka ba kan zaka sha wuya gaskiya ga wana  lamarin drivern ya fada a cikin muryan
kulawa.

    Haka ba matsala
bane idan zai iya zama dani mu dai tallakawane sosai ba wani gidan zamanine
gareni ba donshi naga kamar dan masu haline ?

   Ta hali akeyi yanzu
ya samu wurin mafaka shine abu na farko da yakamata ya farayi idan ya sauka din
inji diban motan.

   A a fa ai kaji
abinda baba ya fada daganin shi gidan masu hali yake ciwon hakane kawai ya fito
dashi daga gida kaga kuwa aisai hotel irin wanan.

   Ba irin gidan su
baba don baba yace shi tallakane baida hali kaga saukan irin wanan bakon ai
matsalane wanan dayan mutumin ya fada.

    Ahmed din yana
zaune yanajin zancen da kowansu ke fadi a lokacin har saida yaji driver na
fadin kaiko dai ai sauki ake nema mashi yadda zai samu saukin lamarin ba zancen
jin dadi bane a nan kaji yaro.

   Ahmed din yace
hankalina yafi kwanci da nabi baba gidan shi tunda har ya amince da hakan
saukine ai Allah ya kawo min ga hakan.

   Kaji gaskiyan kenan
yaro ka fadi gaskiya ba karya Allah ne ya kawo saukin lamarin ya hadaka da baba
a motan nan har tafiya ya hadaku inji drivern.

    Ya kara da fadin
Allah yasa a dace kaji nasan irin abinda kakeji a zuciyan ka na zafin hakan don
wasu ma na iya shegantaka su kiraka da sunan banza duk da sun san hakan ba
laifin ka bane laifin iyayyen nakane ya jama hakan ?

    Insha Allahu zanyi
iya kokarina kaji yaro ai da na kowane Allah dai yasa mu dace aganshi a cikin
sauki yanzu dai muyi fatan Allah ya kaimu lafiya tsohon ya fada.

   Dijece tunda duku
dukun safiya ta sallamawa malam Tanimu a cikin tashin hankali tana fadin malam
tanimu kasan yaron nan bai taba irin tafiyan nan ba.

  Yaje haka ya dade ba
tare da ansan inda yake ba ko yaje ni abinda nake son ku gane ke nan hankalina
yaki kwanci jiya a raye na kwana ina tunanen ko wani halin yake can ciki ?

   Malam Tanimu ya
nisa yace Dije nima lamarin ya fara dan taba zuciyana don tun jiya nakai dare a
waje ina dakon ko zanga dawowan shi banga ya dawoba har na shiga gida.

    Bakaji ba ina fadi
kuna ganin damuwata yanzu ba a wasa da lamarin batan mutum gashi ya tafi bai
fadi inda zai tafi ba balle aje can din aduba ko lafiya yake ?

    Shike daga min
hankali Tanimu Dije ta fada a cikin wani murya mai rauni yace yanzu dai barin
fita zuwa bakin kasuwan su na yan hatsi in tambaya ko Allah zaisa in samo
labarin shi a can.

    Tare suka fito
cikin gidan malam Tanimu din iyalinshi na masu fatan Allah yasa a gano inda
Amadi din ya shiga bayan sun fito wajene malam Tanimu din yacewa Dije ta koma
gida shi zai karasa zuwa bakin kasuwa din ya binciko halinda ake ciki.

   Ya kama hanya ya
ita kuma ta kasa shiga gidan sai kawai ta juya ta shiga dayan gidan dayafi kusa
da gidan nata ta shiga taba labarta masu halinda take ciki na tashin hankali
din.

    Suma sun nuna nasu
tashin hankalin sosai a hakan sun dai dan jajanta mata sun bata baki ta danji
sanyi ta koma gida tana dakon dawowan malam Tanimu din daga bakin kasuwa daya
tafi.

    Malam tani ko a
kasuwa yayi neman labari amsa daya yake samu shine rabonsu da Amadi kwana biyu
ke nan amma dai yabada kudin hatsin shi ga ubangidan shi kuma an sawo mai har
sun samu shiga sun zama kudi.

    Haka ya juyo ya
dawo zuwa gida a sabule jiki ba karfi don rashin sanin inda yaron ya shiga ya
samu iyalinshi a cikin jimamen maganan.

   Nan yake fada masu
abinda ya jiyo a kasuwan tare da uwargidan shi suka dunguma zuwa gidan Dije
suje su sanar mata da halinda ake ciki.

    Sunyi sallama sun
samu Dije saman dutse da suke zama suyi alwala a sama ta zauna tayi tagumi da
hannu daya tana faman tunane.

    Sallaman su yasa
ta dagowa tana amsa masu ta gaida malam Tanimu din da dawowa gida tare da
tambayan shi a gagauce da anyi sa,a ab gano inda yake din ?

    Girgiza kai Malam
Tanimun yayi yana fadin wallahi Dije abin ya fara cin tura don  kaf wurin nan nasu na zagaya babu labarin shi
labari daya na samu shine yaba da kudin hatsin shi yace ba zai samu zuwa
daukowa ba a ranan.

  Kuma har sun dauko
mai suma suna dakon zuwan shine a yanzun don har sun sayar mashi dashi kudin
yana hannun shugabansu na wurin da suke aiki tare.

   Kuka Dije ta saka
masu lokaci guda tana fadin shike nan dan marayan Allah ya bata ke nan sun
ingiza min keyan shi ya shiga duniya dan anga ya fara tasowa mun fara fita a
cikin talauci shike nan sun kaimu sun baro.

   Yau in yaron nan ya
bata har ya tabbata kurciya akai mashi me zan fadawa iyayyen yaron nan ni Dije
sai kuma ta sake sake kuka cikkn tasshin hankali da ban tausayi.

   Har makwabta suka
fara shigowa gidan kafin ance haka gida ya cika da mutane masu zuwa jaje labari
ya fara baza gari cewa Amadi ya bata an masa kurciya ya shiga duniya.

   Sai gashi har an
fara sakawa a median cewa ya bata abu ya fara yawo a cikin gari wa yanda suka
sanshi sun shiga damu hankalinsu ya tashi a irin hakane har hanne ta gani a
wayanta ta fara neman layin zahra hankali a tashi .

   Barci nakeyi wayan
hanne ya shigo min da kyar na iya dagawa na amsa sallaman da take min din na
dauka take tambayana wai naga labarin dake yawo a yanan gizo kowa ?

  Ban gani ba hanne na
fada gabana na faduwa tace wallahi nima yanzu nagani cewa wai Ahmed ya bata ya
bar gida an masa kurciya a wurin sana,an shi abokan gaba sunga ya taso sun
batar dashi cikin duniya.

   Ahmed din na sake
tambayan Hannatu din tace wallahi Zahra ashe bakiji ba shine ai yasa na kiraki
yanzu in sanar dake ki san halin da ake ciki.

   Dan murmushi nayi
nace to naga jiya munyi waya dashi da dare yace min yana Taraba state ya tafi
wurin mahaifin shi kinga ko ashe ba bata yayi ba ke nan ai.

   Dan Allah ki bari
Zahra kunyi wayafa dashi kikace nace zan maki karyane kan hakan nikan wallahi
munyi waya yana hanya yake fada min.

  Amma kinga don Allah
ki iya bakinki tunda bai fadawa kowa inda yake ba don yanzu kina furta hakan
sai a canza maganan kuma ya koma wani magana na daban har Abba yazo yaji ya gane
muna tare dashi har yanzu.

   Hakane kuma zahra
Allah ba zan fadawa kowa ba tundama har kinsan inda yake ai dama hankalinane ya
tashi da zancen batan da akace yayi wai an masa kurciya ya bar gari.

   Don Allah dai na
rokeki hanne kada ki kuskura ki furta wani abu har ace nina fadi kinsan Abban
mu zaiji zan kuma shiga cikin matsala ke kin sani.

   Tace wallahi na
fada maki banyin zancen nan da kowa idan Allah ya dawo dashi ai zai nemi wanda
ya bata mashi sunan aji ta fada.

   Nikan muna gama
waya da hanne din nayi ta tirayin din layin shi baya shiga amma hakan bai
dameni ba daga nan na fita zuwa kitchen na samu mutane mukayi ta hira har ma na
manta da zancen.

   Don ban dauki
zancen da ma,ana ba a zuciyana haka yasa banji komai ba a lokacin kan zancen
har zuwa lokacin dana daidaici cewa mutanen gidan sun kusa dawowa na shige daki
daga sunan sallah ban sake fitowa ba nayi wanka na fito nayi sallah na sake
komawa na kwanta.

    Sai shida na fito
gaida mommy don nasan ta dawo gida a lokacin saidai ashe shigowan ta ke nan
gidan wai ta biya wurin tellan data bawa dinkunan buki ta karbo.

   Tana zaune a falo
sai gani na fito da fara,a a fuskanta ta na karasa wurinta ina mata sannu da
zuwa tace come come my daughter yanzun nake zancen in tura a kiraki.

   Kizo ki gwada kayan
nan ko zasuyi sizes din ki don kwatancen ki kawai nayi mashi ya dinka maki duk
da naso yazo ya ganeki ko kije amma yace aiki yayi masu yawa sosai.

    Na karasa zama ta
miko min leda da kaya a ciki na dadu dasu sunsha guga na karba ina fadin thanks
mom haba dai gwada mu gani ko zasuyi maki idan ba matsala  ga dinkin.

   Karba nayi na fara
budewa tace yawa kinga wanan shine za a saka ranan kamu namu ankone na gidan
ango wanan din.

    Abu na farko dana
fara dubawa shine dinkin bujen don ban saka bujen daya matseni sosai don haka
Allah yayini ni bana son kaya su matseni tam a jikina sai in  koma ban walwala ko sakewa karshe ma saidai
in kyautar da kayan.

    Naji dadin ganin
akwai space a dinkin tellan koda ya matse zan iya budeshi haka nayi ta dagasu
har kala biyar tana min bayanin kayan da ranan da za a sakasu din.

     Bayan na gama
ganine na hada a wuri daya na mike daga inda nake zaune na durkusa a gabanta
ina fadin mommy na gode tare da dan fadawa saman jikinta ta dafa min baya tana
fadin haba haba dai ki bari don Allah zahra .

  Kkme nayi maki kin
cancanci hakan gareni tunda kun yaba dani har kuma kun yarda da zamana a cikin
ku ba tare da nuna min hassada ba ko kishi don me nima zan gaza daku yanzu.

   Shigowan Abba yasa
na mike da kayan a hannuna bayan na gaidashi na shige ciki ina tunanen irin
hakin mommy dana kasa fassara manufabta a kaina yanzu.

   Daki na shiga na
fara gwada kayan a jikina gaskiya kayan ba laifi ba dinkin ba ba kayan da
akaiwa design din ba duk ko wani abin a yabane.

  Tunane yazo min
bayan na gama ganin kayan shin me wanan matar take nufi dani hakane abinda ban
yarda dashi ba shine dole akwai manufa ga zuciyan wanan matar a kaina.

  Saidai ban gane me
take nufi ba take min hakan dole dai nasan akwaishi amma zan  bita a hankaki har in gano hakan inda na
godewa Allah shine banda rawan kai da zai hanani gane hakan da take min din.

   Gashi ga lissafina
saura kwana biyu mu wuce zuwa kano kamar yadda ta fada min a baya dole gobe in
bayar da kayan da zantafi dasu a kara wanke min a goge hakan yasa na lalubo
wayana na kira ummah ina fada mata komai daya faru.

    Ki dai kula da
kyau kuma ki natsu ki kula da kanki banda rawan kai Allah ya tsare tunda ba
yadda zamuyi don Alh ya tsaya mata nan kuma suna ganin kamar wani munafuncine
na kulla ga yin hakan.

  A sanyayyena amsa da
toh ummah in sha Allah zanyi yadda kikace min din muka dauko hiran kanne da ita
har ta basu wayan na gaisa dasu din .

   Saidai na yanke a
raina muna dawowa zan koma gida don nagaji da zaman Abujan ba yan uwana da mahaifiyan
mu a kusa saboda hakane nake zama a takure gashi ba wani sabawa nayi da mommy
din ba sosai kamar yadda na saba da mama a baya.

 

Leave a Reply

Back to top button