TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 13

Sponsored Links

 

 

 

   Don Allah kada kiyi
ko kayi gangancin karata wana  novel din
a audoo don na sayar dashi already ga wasu yin hakan shari,ace tsakanin mu.

    Zaman dai ba dadi
amma hakan baisa mun bar gidan ba muna dakin ta sai shabiyu muka fito zuwa gida
don zamu shiga islamiya lokacin.

    Sai dare na samu
zama da ummah mu a falo naji ta tambayeni wai meya hadaku da hjy yau ibrahim ke
fada min tayi ta maku fada tana zagina da baban ku ?

    Ummah zancen motar
nan daine aka kai mata don mun samu su mama gidan wurinta nasan kara suka kai
wai ashe Abbane ya saya min sai gwaggo uwanice ke dan tsawata mata har ta daina
zancen amma taki sakin fuska damu.

   Sai cewa take ai
Abban zaizo zataji dalilinshi nayin fifiko a tsakanin diyan shi don ita ba zata
lamunci hakan ba tun tana raye ya fara yin haka ina ga ta kawu bata duniya
saidai idan ansa abinda akai mai a karkashin kasa.

   Murmushi naga ummah
ta sauke a fuskanta tana fadin Allah sarki yanzun ne zanwa Alh asiri kuma dacan
baya ashe suma asirin sukai mashi ke nan ko ?

   Little sister
dinace ke min nuni da abinci na diba na bata wanan ya dauke min hankali ga
maganan da mukeyi da ummah din.

    Monday mun shiga
school sam na mance da zancen karatu dan break din da muka samu sai ga mutum
uku da mace daya sai wanan kawar dana samu tunda ita ke aje min wurin zama
kafin nazo dana shigo zata daga min hannu nazo na zauna.

  Oya muje muga guy din
nan don muji ya za ayi tunda  yau yace
damu za,afara wa ke nan na tambayeshi cikin mamaki au har kin manta da zancen
ke nan ?

    Keko zancen
karatun mana da zamu fara ta fada haka suka sani gaba dole na tashi mukaje muka
sameshi yana gyara kayan gwanjon shi a bayan aji.

  Gaisuwa suka fara
mai muna tsaye daga baya kafin ya dago yana fadin yanzun ya kuke son ayi don
gaskiya zaku takura min ga sana,ata kunsan tallaka baiga zama ba naso fita in
zaga da kayan nan nawa cikin hostel ku kuma gaku.

   Hakkuri zakayi
master don kyau alkawari cikawa manir ya fada ok ya fada yana dan kalle kalle
kafin yace mu karasa daga can zaifi wurin ba yawan gittaya sosai don haka sai
yai muna dadin zama.

   Bayani ya soma muna
tun daga farkon yadda zamu gane kan topic din da Munir ya gabatar mai zaka
rantse shi din wani baturene ko babban lectura ke bayani.

    Abinda ya dakatar
damu yan class din nasu ne sukazo mai da wata tambaya hakan yasa muka barshi a
lokacin muka koma namu building din.

    Tallan gwanjo na
maimaita a fili why ga karatu ga kuma sana,a lokaci guda haka au kina mamakin
guy din nan ne ko nima a gaskiya naji mamaki sosai wallahi.

  Gashi Allah ya bashi
amma baiyi girman kai da hakan ba ke da ganin shima kin san yana bukatan
taimako sosai a rayuwanshi ko suturan jikin shi ka kalla.

  Kune yayan manya
irin su ya kamata ku dinga taimako inda halin hakan tunda muma yana taimakon mu
da nasa baiwan da Allah yai masa ai yanzu.

    Ba wanan ba ai da
alaman wahala sosai z tare dashi idan kin dubs ya fada muna zamu takurawa
rayuwan shi amma yanzu kina nufin da wanan sana,an zai rike rayuwan shi ?

    Wata kilama
hardana wasu a karkashin shi yanzu haka idan kin bincika ko yana da aurema a
kansa ai kinsan yadda yake a kasan nan tamu yiwa yara auren wuri su dawo suna
wahala daga baya.

   Kai gaskiya shiyasa
aka bar arewa baya sosai saboda irin wanan matsalan  na tara iyali da wuri kaiba shekaruba ba wani
aiki ba amma an cika gida da iyali.

   Munyi hira sosai
akan matsalan daya shafi nahiyar mu da dalila
dake kawosu har lokacin sallah yayi muka mike zuwa masalaci kafin mu
dawo wani malami har yashiga ko saidai munyi sa,a bai koremu ba don yasan
sallah aka tafiyi.

    Da yamma lis muka
fito sai ban tsaya komai ba na nufi wurin motana ina kokarin budewa na hangoshi
yana fitowa da kumshin kayan shi ta bayan block din mu duk da kayan sun dan
rijayeshi nake gani amma haka ya daukosu ya nufo hanyar da zai fitar dashi
haraban wajen.

    Sai naji zuciyana
nason na taimaka mashi duk da bai kalli inda motana yake ajiye ba lpkacin haka
yasa na tayar da motan na mike hanyar da zai sadani da inda naga ya bi..

   Horn nayi mai
haka  baisa ya juyoba sai tafiya yake da
sauri da kumshin kayan shi a kai lokacin da gani sauri yake sosai zuwa get inda
zai samu abin hawa.

   Ga wasu kayan
rataye a hannayenshi glass na sauke a hankali ina fadin yayana muje in sauke ka
mana don bansan sunan shi ba har lokacin.

   Bai jiyo ba yasa na
kara danna mai horn jin hakan yasa ya dan juyo mukai arba na danyi gaba na
tsaya ya zagayo nake fadin .

   Na bude booth
already na fada yace for what zan saukekane inda zaka dan murmushi ya sake yana
fadin nida zan yawata da kayana ina ni ina shiga mota nagode kwarai da taimakon
ki ya juya yana kokarin cigaba da tafiya a wahalce.

  Binshi nayi da kallo
cikin tausayi na dan ja motan na cin mai hannuna yana cikin jakkata ina lalube
naji kudin a inda na ajesu na jawo tare da fadin.

   Ga wanan sakon don
Allah  ya juyo na mika mai da sauri ina
fadin idan ka bude zaka ga takardane ya amsa yana mamaki na figi mota na na
barshi wurin tsaye yana kallon envelope din dana mika mai din.

   Bai budeba naga
yaci gaba da tafiya yana turowa aljihun shi na halba saman titi bansan yadda ya
karasa va don ni kaina bansan nawa bane ya musa ya ban ba gaba daya na mika
mashi su wanan lokacin.

    Tun daga get din gidan mu nagane anyi baki a
gida saidai yanayin bakin maza ya nuna ba daga nan arewa suke ba ashe kawar
mamace tazowa mama a bazata ita da yaranta daga lagos.

      Saida na shiga
gidane ummah ke fada min zuwan hjy Rafat din nasanta sosai farin sani duk wani
iya shegen bariki itace ta koyawa mamashi zaman su a legas tare.

   Don daya bai wanka
ya bushe yana gidan daya mama ta iya shige shigen yarbawa kamar me haka al,adun
su duk ta iya sosai don haka yaren lagos radau a bakunan mama da yaranta kaf.

   Akwai wani dan hjy
Rafat din daya samin ido sosai idan naje hutu yana cewa wai sona yakeyi wanan
yasa  dana fara girma na daina zuwa legos
wurin su hutu kamar yadda na saba ina karama saina fake ga karatu a lokacin.

    Kai tsaye na nufi
dakina na soma cire kayan jikina sai nayi wani tunane hakan yasa na juya na
fito falo na zauna naci abinci babu kowa daga cikin kannena a lokacin don
hakane gidan yai shiru a lokacin.

   Saidan motsin Tani
dake aiki a kitchen lokacin kadai ke tashi a falon da sallaman zamani Rukkaiya
ta shigo ta hangoni zaune saman dining table din mu ina cin abinci tace min ke
mama na kiranki .

   Nima juyowa nayi
jin yadda tayi min magana na mayar mata da fadin wa,ni ina nuna kaina da
hannuna tace ke mana ok idan na g

hada zanzo na bata amsa nima.

   Kamar zata sake
magana sai tayi shiru ta wani irin juyawa kamar a hasale lokacin ne tace ina
zakizo kizo don ba mama bace ke son ganin mami Dele ne tazo dama akace akiraki
ta hada da tsuki ta tafi.

 A daidai lokacin umma
tana fitowa daga kingun shiga dakunan kwanan mu na part din ta bita da kallo
saida ta karaso take tambayan meya kawo wanan nan ?

   Wai inzo inji hjyn
Lagos ta fada ai dama zaki kigaida ita tunda batai maki komai ba koda tayi kuma
ai bata fitar a fili ba angani.

  Saiki tashi kije
kada kuma taje ta fada masu wani abin daba
don karamin aikin Rukkaiyane hadin fada kindai san halinsu ba sai na
fada maki ba.

    Dole na mike nabi
bayan ta na shiga da sallamana falo suke zaune gaba dayan su jin sallaman nawa
yasa suka juyo suna kallona banda mama da yan uwana da suka hade rai a wurin.

   Hjy Rafat da diyan
ta uku suka fara sake min murmushi tare da fadin see u you na your face be dis
kowan su fuskan shi dauke da fara,a a gareni.

   Da dan sarsarfa na
karasa gun mami din saidai na dungumeta kadan na saketa nakai kasa tare da
fadin your welcome mah ta shafo kaina tana fadin ji yadda kika koma wata babba
dake haka Zarah?

   Na danyi murmushi
kadan tare da tambayanta ya hanya na dago kai ina gaida yaya nata da duk suka
zubo min idanuwan su a kaina lokaci guda.

   Bayan na gaidasu
mama data mike tun shigowana ta dawo ta zauna kusa da mami din na dago a cikin
fargaba ina gaida ita ta amsa min da fadin lafiya kalau kun dawo ke nan ?

   Eh na fada na dukar
da kaina kasa muryan mami Dele dince ke fadin u no see you man Dele, he de
worry me asking you yanzu kuma ya ganki ya noke kamar bashi ba.

    Nayi murmushi sai
kanin nasa yace shima yaji mamakin girman tane haka ta koma wata babban mace da
ita shekaran ki nawa yanzu a jami, a ?

    Bai samu kanshi wanan yinin ba balle ya tuna
da zancen envelope din ba don haka har yamma bai san meke cikin envelope din
nan don bai koma ta kanshi bama alokacin.

  Don yana raragewa
kasuwa ya koma don ya saro wasu kayan da zai fita dasu da safe yakoyi sa,a ya
samu an bude a gaban shi.

   Don haka dilace mai
kyau na kayan maza ya samu giredi kamar anzabo mashi sune daga can ya taki sa,a
matuka don yana zuwa ana bude dila saidai kudin shi basu kai ya saye dilan duka
ba lokacin.

   Don haka ya
zaba  tare da rokan mai kayan ya aje mai
zuwa safe ko yamma zai dawo ya saye sauran ga baki daya .

  Mutumin yai shiru na
dan lokaci kafin ya duba sabo da kwazon yaron yace amma idan bakai bane banayin
haka gaskiya tunda inada masaya.

  Ida  har bakazo ba zuwa biyar zan sayar dasu duka
gaskiya yana magana yana hada sauran kayan a wuri daya don ya adana mashi kada
wani yazo ya dauka bai sani ba.

   Ya bashi kudin tare
da godiya kan karancin da yayi mai saboda sabo da juna da sukayi ya dauko kayan
shi zuwa inda zai samu abin hawa da zai kaishi unguwarsu.

   Da kayan shi niki
niki ya shigo bai tsaya ba sai kofan dakin Dije data riga ta tayar da sallah
magariba a lokaci  shima buta ya dauka ya
fara alwala kada ya rasa jam,i.

   Bai dawo gidan ba
sai yamma lis ya dawo duk a gajiye yake sosai a lokacin hakan bai hana shi zuwa
wurin uwar garke dake kwance ba ita da yayan ta..   

   Duban abin abincin
su yayi babu komai a cikin kwanon haka yasa ya fita gidan ba tare da sanin Dije
ba yaje gidan da ake sayar da abincin dabbobi unguwar don ya sayo masu.

   Dije wace taji
shigowan shi gidan saidai bata karajin motsin shi ba a zatonta yana dakin shi
yana hada kaya ta fito tana magana taji shiru.

   Yau ga ja,iri
kafita ne koka kewaya ban dakine wai ita kadai take maganan a tsakar gida sai
gashi ya bullo a cikin duhu har saida ta dan kadu dan ganin shi a lokacin.

   Tambaya yayi lafiya
kike nan a tsaye cikin duhu wai kai na fito nema naji motsin ka kuma nazo naji
shiru ashema kana waje.

   Naje nan gidan malu
ce na karbowa dabbobin nan abinci don naga basu da abinci saidai dusan
gwaunatice na samu na gargajiyan ya kare tace.

   Dadina dakai Amadi
akwai kula duk da wanan gajiyan daka kwaso bai hana ka tuna da bayin Allah nan
ba a ranka Dije dole mu kula dasu tunda mun turkesu a wuri daya idan bamu basu
abinci ba sai Allah ya tambayemu hakkin su akan mu.

    Yana bata amsa ya
duka yana zubawa dabbobin abinci kafin yakai hannu ga uwar garke yana fadin
uwar garke tashi kiyi kiwo kada ki kwana da yunwa kinji kuci sai na sayo maku
haki gobe insha Allahu.

    Zakace da mutane
yake wanan maganan yadda dabbobin suka mike suka fara kiwo lokaci guda abin
shan ruwan su ya dauka ya daure guntun jarkan da aka yanke ana zuba masu ruwan
sha a ciki yaje har randan ruwan su ya debo ruwa lokacin ya farga da basu sa
ruwa a gidan ashe.

    Yana gamawa da
dabbobin ruwa ya fara diban masu yana cika kayan zuba ruwan Dije duk ya samu ya
cika don ya samu ba mutane sosai wurin ruwan.

    Sai goma da wani
abu ya samu kanshi ya sauya kayan jikinshi ya nufo dakin Dije wace ke shirin
kwanciya hannu dauke da takardan da yarinyar nan da sunan gidan su ya sani na
MAYANA.

    Zama yayi yana
bude takardan don ganin meke ciki kudine suka zobo daga cikin takardan zuwa
jikin shi sabi dasu kar saida ya dan kadu da ganin hakan.

    Kai din da yace yasa Dije juyowa inda yake
tana kalloshi idonta ya sauka saman kudin da yake tattarawa a jikinshi.

   Amadi ina kafito da
wanan kudin sabbi haka kar dasu tana tambaya take tsureshi da ido a cikin tsaro
da son jin ina ya fito da wa yan nan kudin masu yawa.

  Bai dago kaiba don
tsayawa da yayi kidaya kudin dubu darine cif din su a mike dinsu suna daukan
ido tambaya ta jefo mai da ina kafito da wanan kudin Amadi ?

   Wallahi Dije ina
wanan yarinyar da matar nan tazo gidan nan karbawa magani wurin malam tanimu
ranan to itace dazun ta bani shi tace don Allah na karba kada in bude sai nazo
gida.

  Nina dauka ma wani
takardan wani abune a ciki ai ashe kudine ta saka haka a cikin takardan nan ta
bani har tana fadim nayi hakkuri dashi don Allah.

   Amadi kudi lafiya mace ce zata baka kudi haka
kuma yarinya karama kadafa ta jawo muna matsala muna zaune kalau a yanzu ?

 

Leave a Reply

Back to top button