TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 46

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/3, 12:41 PM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣6️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Kowa na mamakin ji
ance ai bukin da nine alhalin sunsan ban tsayar da mijin aure ba lokacin
asalima ina karatune a yanzu duk da suma sunata spell a karatun su har lokacin
ba wace ta rike kwalin shedan karatunta.

    Wayana gaba daya
na kashe ban daukan kiran kowa haka ko falon mu bana fita balle zuwa makaranta
ganin haka yasa ummah ta sameni a daki tana min fadan rashin fitana zuwa
makaranta.

   Inda tace dani
kaina zan kullawa sheri don shi Abba baisan ina yiba ma don haka gara in natsu
insan abinda nakeyi zaifi.

    Wanan fadan da
ummah tayi min yasa na shirya washe gari na fita zuwa school nasha tambaya
saidai ganin yadda na rame lokaci guda yasa suka dauka banda lafiyane.

   Sunan nazo school
daine amma ban fahinci komai da akeyi ranan ba don hankalina daya tafi wurin
tunane lokacin ba abinda nake tunawa sai irin matsalolin da rayuwana zai
fuskanta a irin gidan da ban saba rayuwa a cikin shi ba tun tasowana.

   Nakanyi hawayen da
bazan fadi dalilin fitashi ba lokaci guda gashi zance ya gama karade dangi cewa
wani dan talakkawa mara asali da baida galihu nace ina so.

   Su kuma Aisha da
Rukkaiya sai faman rawan kai da sukeyi suna ta zirga zirgan ganin bukin su ya
kawatu kamar bukin ko wace yar gata.

   Inda a bangaren
ummah banga wani shirin da takeyi ba ita ko don zancen yazo mata girshine ko
kuma irin nata fushin ke nan oho.

   Don har an fara
gulman ba aga tana wani shiri ba akan aurar dani din kamar ba yarta na fari
zata aurar ba wanan gulman kuma ya fara fitowane daga bangaren mama har dangin
mu suka dauka suna yadawa.

   Na dawo school a
gajiye rana  ina shiga gida wayana na
ringing ban daga ba sai kusan karshe na daga ina kallon lamban dake kirana din
layin kamar na kasan wajene na gani.

    Dauka nayi ba tare
da magana ba nake sauraren shi naji ana gaisuwa cikin muryan turawa tare da
tambayan nice Zahra na amsa da eh naji yace ko zan iya tuna mutumin da muka
taimaka a baya wanda muka tsunci walet din shi muka kirashi ?

   Har shima ya kira
yana rokon mu nace na tuna yace shine ai yanzu yana Canada ya koma kasan su ya
zama C E O na wani company nasu a dalilin wanan number da muka taimaka mashi
dashi.

  Don hakane yake
gaiyatar mu zuwa kasan Canada wurin shi don ya gana damu yana son yai muna wani
abu muma a rayuwan mu.

   Jin abinda ya fada
nasan abune mai wuya hakan ya kasance yasa na dan sake murmushi ina fadin nayi
mai murna sosai da jin hakan.

   Amma zancen zuwa
Canada a yanzu gaskiya bamu da karfin hakan don muna nan tallakawa lis kuma a
yanzu ma few weeks ya rage muyi aure.

    Dan fito naji yayi
yana tafi tare da fadin yayi muna murnan hakan da yana da dama da zai shigo
Nigeria don mu yazo bukin mu.

   Yanzu shike nan zai
bari sai bayan bukin zai shirya muna shigowa canada din amma mu turo account
zai turo muna da gift din bukin shi nayi mai godiya muka yi sallama na kashe
waya  tare da mamakin hali irin nasu.

    Kamar da wasa na
tura account dina dana Ahmed na juya na bar wayan a gefena karshe na gama
abinda nakeyi na fito falo nan na samu ummah a zaune tare da Tani mai aikin mu
suna zaune suna magana.

   Na gaishe na mike
zuwa dining din mu don inci abinci naji muryan ummah na fadin ke zo nan na juyo
da sauri don nasan ni ummah ke kira da hakan wani lokaci.

   Daki nawa yaron nan
yace dake ya tanada don muna son sanin komai kada ai min girshi da yawa sai
nace Tani din tace walle hakana na hjy gara dai din a tambaya shiyahi.

   Ummah bamuyi wanan
zance dashi ba na bata ansa  tare da noke
kaina a kasa naji Tani ta sake fadan Allah sarki uwar dakina Allah dai ya shige
muna gaba keji.

  Wadda aka son gani
gareku  Ubangiji Allah Allah ya shi
maisuwaar da wanga aure alheri a gareki kada Allah ya nunawa makiyan ki ke
wullakanta kada Allah ya nunawa makiyan ki
kasawan ki a dakin mijin ki keji.

    Amin naji ummah
tana fadi itako taci gaba da fadin ki zaman ki kiba marada kumya ki zauna
lahiya da mijin ki keji mama.

   Wanga abu anyishina
don aga karshen ku mai ganin haka ga bawa sai Allah komai mukadarine kejiya
shima zan ganai inja mai kunne keji.

    Nidai abinci na
diba na dauka na nufi dakina a saisai lokacin da zan shigane naji sakon massage
na shigowa a wayana ban duba ba sai kokarin zama nayi don in fara cin abinci
naji wayana ya dauki kara lokaci guda kuma.

    Tsuki naja ina
dubawa ga mamaki Ahmed ne ke kirana wanan lokacin gab da magariba haka sai
mamakin hakan ya kamani na mika hannu na dauki wayan.

  Sallaman shi naji na
amsa yana fadin ya school nace lafiya kin koma gidane ko nace tun dazun na dawo
sai yayi dan shiru nima shirun nayi mai yace dama tambayan ki nake son nayi don
na rasa wa zan kira in fada mai abin mamakin dana gani yanzu a wayana.

   Gabana ne ya fadi
jin abinda ya fada din lokacin yaci gaba da fadin yanzu na dawo zan shiga gida
naga wani James daga canada ya turo dz kudi a account dina masu yawa duk da
bansan yawan su ba da kudin Nigeria.

    Har ya turo maka
kudin ke nan nace kinsan da zancen ke nan ya tambayeni nace eh nan na kwashe
yadda mukayi dashi James din na fada mai komai shiru naji yayi na dan lokaci
kafin yace dani.

    Dama kuna waya
dashine wanan wace irin tambayane kake min bayan yanzu nayi ma bayanin yadda
mukayi dashi amma ai da baki fada masa ba don kinga gashi yayi abinda bai tashi
yiba garemu.

    Ok ka mayar mashi
da kudin idan baka so sai naji yace uhumm wai zahra fushi kikeyi dani ke nan
don ban taba jin kina magana da zafi irin haka ba ?

    Wayan na kashe
gaba daya don nasan bai fadi karya ba don a yanzu laifin shi nake gani don
shiga rayuwana da yayi shi yaja muna bacin rai dani da mahaifiyata.

   Wanan tunane
zuciyana ke bani ko wani lokaci na tunda da auren da za a lakaka min a yan
kwanaki masu zuwa insha Allah.

  Shima Abba wani irin
bahagon mutum ne dake da murdaden zuciya amma akan dakin mu kadai nake hango
hakan .

  Don abu ba abu ba
kowa zaiyi yadda yake so a gidan mu amma mu dan kuskure kadan zai hau zancen ya
zauna yace anyi hakan .

   Why mu kadaine Abba
ya tsana hakane wai a gidan nan nasan da Aishace ko Rukaiyya zancen ba zaiyi
zafi haka ba har ya dauki zuga irin haka.

   Abincin da banci ba
ke nan na mike zuwa bandaki na dauro alwala nazo na tayar da sallah don lokaci
yayi na sallah magariba lokacin.

    Na idar na nemi
wuri na in kwanta sai lokacin idona yakai kan abincin dake gefe da banci ba na
mike na dauka nakai kitchen muka hade da ummah .

  Nan ta fara min
fadan rashin cin abinci kafin ta juya
fadan da banci ba naki daukowa tun Tani bata wuce ba ta dauka ta tafi
dashi.

  Ni dai banyi magana
ba sai narai narai da nayi da idona ina son inyi kuka lokacin taja tsuki ta
shige na kai abincin na aje nazo zan shige naji muryanta tana fadin haka zaki
kwanta bakici komai ba ke nan.

    Shiru nayi naji
kanina yazo ya rikeni ta baya yana fadin nazo nakai mai tashan cartoon suyi
kallo kije ki duba akwai sauran madaran su a daki gobe na bayar a sayo wani ki
hada tea kisha

   Na juya zuwa
dakinta na duba na dauko don yanzu kiri kiri Abba ya daina saya gashi kuma
tunda safe saita hada muna tea munsha kafin mu fita.

   Ni bansan dalilin
da yasa a yanzu Abban ya daina sayo muna wasu abubuwan amfani ba kamar da can
baya da yake saya muna ko zuwana abuja ga kayan tea nan nagani wanda keso yazo
ya diba ya hada amma mu nan ya dai saya .

  Saidai ummah din ke
bayar da kudi a dan sayo mata ta aje shine dalilin da yasa take ajewa a dakinta
yanzu don in an aje a falo yaran sha sukeyi.

    Na fito naje wurin
tv na kunnawa yaran naji ummah na fadin kunsan dai gobe akwai school duk wanda
ya tsaya min murzan ido dukan shi zanyi.

    Na wuce kitchen na
kunna gas na dora ruwa yayi zafi na juye na fito zuwa dakina dashi shina na
danji karfin jikina nakewaya na fito nayi shirin kwanciya.

    Wayata na dauko
don in kashe naga massage ya nuna na bude don in karanta naga sakon Ahmed ne ke
ban hakuri na dauki waya muyi magana.

  Sai na biyun sakone
daga james ya turo min da kudi a account dina nima gabana ya yanke ya fadi don
ganin yawan Europe din daya turo min din.

    Kasa hakkuri nayi
na danna kiran layin Ahmed din yana jin kirana ya dauka yana hamdala tare da
fadin har na shiga damuwan kashe min waya da kikayi din.

   Ni ba kashe ma waya
nayi ba nadai ji kana son ka zargeni don bansan abinda zan fadama ka yarda ba
tunda kasan ba halina bane hakan.

   Ba haka nake nufi
ba zahra mutum yau ba abin saurin yarda bane amma ai maganan ya wuce tunda na
gamsu yanzu nace bai wuce ba kan don in zaka mayar mai ka hada da nawa don
yanzun naga ya turo min kidin nima.

  What wallahi yanzu
na daga waya naga sakon shine na duba nagani yace zanso kiranshi gashi kuma
banda layin shi a wayana.

    Ummah tace in
tambayeka daki nawane ka tanada shiru tayi kafin yace Zahra kinsan komai ba
hali nake dashi ba da zanyi gina na alfarma.

    Daki dayane sai
falo da toilet sai kitchen ta waje da dan baranda is ok mana na fada yace nasan
abinda yasa ta tambaya don yanzu ko yar tallakawace yarinya sai kiga an jera
mata daku fiye da daya zuwa uku.

   Balle ke yar gidan
masu gari haka da Allah ya banke a a kyauta ubangiji ya dubi maraicina ya
hadani da yar baiwa salihan mace irin ki mai tausayi da jin kai.

  Ban taba zaton
alakan mu zai kaimu ga aure ba zahra shiyasa har yanzun nake kwankwanton hakan
duk da nasan wani kuline hakan da zai zama muna alheri insha Allahu.

    Zan kwanta na fada
a kasalance yace har kin gaji da hiran nawa ke nan nace No dama nayi shirin
kwanciyane a yanzu zan turo ma wanan kudin sai ka kara kayi abubuwan daya
kamata kayi tunda akwai hidima a gaban ka gashi Allah ya kawo saukin sa.

  Hakane wallahi Zahra
kedin  alherice gareni don tun haduwana
dake na fara ganin haske a rayuwata amma ki dan ban minti daya naji yaushene
Abba zai shigo garin don iyayyena da yace in turo mashi.

 Ok ina ganin this
weekend zai shigo don naji ya musa yace tare zasu shigo da Abba din idan zaizo
sai naji yace Allah ya taimakeni na tambaya da wuri don kinsan ba nan kusa suke
ba sai sunyo tafiya mai nisa.

    Munyi sallama
dashi na kashe wayan ina faman tunanen daga wani kasa iyayyen nasa zasuzo na
dai bar komai a cikina sai sakon ko daki nawa din da yace a bari ya gani ko za
a tayar da wani idan ba,agama ba din.

   Zaune yake gefe
daya yayin da Dije da mahaifiyan shi ke dayan barin dan barandan zaune suna
sauraren shi eh Dije wanan dai yarinyar da kika sani wace suka zo nan gaidani
da yan makaranta mu din in zaki gane ta.

   Yar gidan wane na a
garin nan Dije din ta tambayeshi tana mai kura mashi ido don son jin abinda zai
fada mata din lokacin shima a bakin shi.

   Ya danyi shiru
kafin ya dago kai yace yar cikin manyana maici yanzune Dije wane mayana mayanan
garin nan wadda nas,sani mai kudin nan da akace yana da arziki sosai ?

  Shiya dije  ya fada yana kallonta tace wai shi yar rikone
ko yar cikin shi ta Amadi hwada min in jiya da kyau don Allah ?

   Walle yarshi ce ta
cikin shi Dije ina miki karyane akan mi zan hwada maki abinda bashi ba ?

   Dan Dije yar
cikinshi hwa kace ina kai ina yan gidan manyan mutane irin haka ko dai yar yan
uwanai na kaka hwadin diyatai kasan yanzun haka akayi niggani.

  Walle mama Diyatai
ta cikinai na wai a,a zan maku karyane wai Amadi ina kaga kudin auren yar wanan
babban gidan ?

    Dije zancen kudine
wai wanga abu kekin san mukaddarina kwai daga Allah amma ni ko dan ga aikin
gidan nan na isa inyi balle intai neman yarshi nihin Allah na kawai.

   Yanzun dai yace in
turo mai magabata na suzo ya gana dasuwa a aje ranan buki don so yake a wanke
su dai rana akai ko wace gidan mijinta .

   Wane gida zaka kai
ta kanka daya kuwa kake wani zagewa haka kasan abinda kake hwadi kuwa ina kaga
kudin auren yar manyan mutane haka ?

   Ko so kakai ka tonawa
kanka asiri cikin garin ga a samu abin hwada muna bayan wanda muka hwama da
shiya kace sunce katuro iyayyen ka waka zuwa ma wanan gidan neman aure ?

    Kasan dai irin
zaman da mukeyi da dangin uwarka garin nan ko bakin ciki na hana masu zuwa inma
sun sani zuwa sukai su hana su aibanta ka wurin su.

   A,a dangin ubana
dai ka zuwa min ai ko wane da da ubana yaka kuri nima insha Allahu kamar kowane
da haka yan uwan mahaifina ka zuwa min neman auren.

   Kkagansu ina wanda
ko kamanin ubanai bai kawowa ko haya zaka kayi ka tudar muna da mutunci a gari
yace a a muna zaman mu lahiya.

   Shin dije in bansan
suba ina hwadin haka ki bari ki gani kina zaune zasu shigo nan su hwada maki
komai ki kijiya kila ki yarda dasu.

    Wayan shi yai kara
ya ciro gaba  aljihun shi yana dubawa ya
mike tsaye ya nufi hanyar fita yana fadin gani tafe nan ya barsu dije na
mamakin maganan shi din.

   Wai danga kanshi
dayana kome yaka hwadi kamar almara mutumin da yai tahiyanai tun kana goye a
raga kaka hwadin ka ganai har yan uwanai ka zuwa maka neman aure .

   Barshi dai ya dawo
mu jiya ai mara rai akewa karya indai ba hauka yayi ba shin ina danga ina yar
irin gidan saidai in bata da lahiyana suka bashi ita uwar nasa ta fada.

  Shi naka tunane a
raina amma in har ba matsala agareta ba su da suka dace da diyan gwaunoni ko
wasu hamshakan masu kudi a,a suka daukan diya suba mutum kamar Amadi.

   To walle ban yarda
ya daukowa kanshi jarabar tsaya  yazo duk
dan zarahinai da aka gani su kare ga gindinta suka koma yi mai gwi Allah.

    Akwai dai magana
amma haka zikau mai kudi bai daukan diyanai ya bashi don jin dadinai ko wani
shaharanai wurin karatu nai.

   Barshi dai ya dawo
ai zama mukai dashi mu jiya kaka haka yya hwaru ina kuma yanemo ubanai da shika
hwadin wani shirmey yanzu.

   Basu daga wurin ba
sukaga ya shigo dame awo suna auna fili tare da kara fasalin ginan dake wajen
suka kwasa kuma suka fice daga gidan lokaci guda.

 Duk suka bishi da
kallkn mamaki basu samu karin zama dashi ba sai baya  kwana biyu da yazo masu da kayan abinci da za
a dafawa bakin shi da zasu zo wanda yace yan uwan ubanshine.

    Dije kan ta kasa
boye mamakinta dakinshi ta bishi ta sameshi tana fadin wai kai da gaske kake
zancen ka dangin ka zasu zo garin nan nema maka aure ina ka samu dangin naka ?

   Kai tsaye ya bata
amsa da garin mu naje kwanaki da kuke shelan cewa an saceni naje na nemo
ubanane kuma na ga dangishi ya ganan yanzun
yan uwanshina zasu taho su tsaya mani .

    Ikon Allah yanzu
Amadi dama neman ubanka katahi yi ka kasa hwada muna ka barmu nan mun shiga
tashin hankali aina hwada maki tahiya zanna kuma kin sani amma kika biyewa
malam Tanimu tayi ta rudaki a gari.

  Yana fadin haka ya
rabata ya fice daga gidan ta dawo tana sallati take gayawa yarta abinda ya fada
mata din duk suka dauki sallati mahaifiyar nasa cewa tayi waya hwadamai inda
zai samai ?

   Dan yau da zamani
ki barshi kawai kai inna ni ban yarda ya samo mutumin nan ba dije tace nima
abinda zuciyana ya bani yanzu ke nan.

    Sayayya yayi sosai
don bakin shi don kowa bai yarda da abinda ya fada ba an dai dauka wasu mutane
na daban ya dauko suzo su tsaya mashi matsayin dangin ubanai don sunsa babusu
ba kuma wanda yasan inda ubanai ya hito.

    Abinci kan anyi
unguwa ya dauka ai yan uwan mahaifinai na zasu taho nema mai auren da ya
kakabawa kainai auren diyan mai kudi shina yayo hayan ubanan banza.

   Mota biyu ras
sukazo dashi kana ganin su kaga fulanin usuli dogaye farare dasu tas ga kama na
jini da suke dashi da mahaifninasa basai an tambaya gaduk wanda yasan habu dan
filo kamar yadda suke kiranshi a zamfara din.

    Nan su malamTanimu
aka fara kus kus lailai yan uwan ubanai na lalai suna sai wani kanin malam
ladan yace meye shedan ku na yarda da hakan.

    Sai kuma aka koma
aka sare ai babu tabas dasu din ne daya ya dauko hoton mahaufin nasa ya nuna
sai kowa jkkkn shi ya mutu aka yarda da zancen su.

Leave a Reply

Back to top button