TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 42

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MA

KAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

 

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

 Allah ubangiji ka
zaba muna abinda yafi zama alheri garemu ka saka tausayi da imanin duk wanda ka
zaba muna ya Allah kada ka bashi ikon cutar da bayin ka ka saka mashi tausayi
da jinkan na kasa dashi.

   Allah ubangiji ka
jikan magabatan mu kasa Aljanna ce makomar duk kan musulmai albarkacin kalman
La,illah ha,illah Muhammadan rasulunlillah ya cece mu Amin.

    Allah ya taimaka
tafiyan dare yayi koda ya biyo layin su ba mutane sosai a lolacin don haka ba
wanda ya ganshi dan abinda suke rufe gida dashi ya tura gidan ya bude ya shigo.

   Ya samu Dije ta
kwanta a lokacin yayi shawaran ya kwankwasa mata kofa sai kuma yaga kada ya tashe
ta daga barci don haka yayi shawaran ya aje kayan tsaraban daya sayo din a
kofan ta kawai.

  Bayan ya aje ya
juyane ba tare daya kulaba yayi karo da kwanon data kife daga gefen dakin daga
cikin dakin yaji muryan ta tana fadin wani na nan ?

   Ido ya dan lumshe
kafin yace nine Dije Amadina ya bata amsa daga inda yake tsaye Dije da taji
muryan Amadin a bazata tayi wani tsale ta mike zaune tana sake fadin wanena
shin ?

    Amadi kaina kamin
gizo ko kunuwana na ka min karya haba Dije ga muryana kina ji zakice karya kuma
ko barci kika farane wai ?

    Ji yayi tana
kokarin bude kofan nata daga ciki yasa shi tsayawa ya jira ta bude tako bude
din tana fadin Amadi ina ka shiga haka kabar gida lokaci mai tsawo haka ne ?

   Missa kayi tahiyar
ka cikin duniya kabbanni nan ni kadai shin baka tunanen halin da nii shiga
bayan tafiyan ka ?

   A lokacim ta karasa
bude kofan ta fito don ta tabbatar inshi dine sukai arba yana tsaye daga kofan
saye da taguwan shi da wando baki kaida ganin shi kasan yayo tafiya mai nisa a
lokacin.

   Ina kakshigane
danga tahiya haka mai tsawo baka fadawa kowa inda kakje ba abinda baka tabayi
ba a ruwanka barin gida haka danisa.

   Buhun tsaraban shi
ya nufa ya dauka yana kokarin shiga dashi daki ta jaye ta bashi hanya ya shiga
da kayan cikin daki ya aje kafin ya dago ya fito yana kokarin juyawa don kayan
daya bari waje ya dauko sauran yaji muryan dije din na fadin.

   Shin ina kak shiga
hakane ina magana kayi shiru daniya haba Dije kin san dai bani zuwa wurin banza
ko don ban taba abin banza ba a rayuwana.

   Allah baka hakkuri
amma ka dau alhakin mu dakka daga muna hankali kwanciya asibitina kawai a banyi
ba kowa gari ya dauka wani mugun abuna yassameka.

   Dauri ka fada muna
inda zakana kaga sai mu sani da kyar ya iya budan bakinshi yace kuyi hakkuri
ban dauka zan dade bane haka nima don tafiyan da niyar kwana biyu niyishi ko
uku sai ya kasance haka.

   Awo dama tahiya ita
tagaji haka kafin kayitana kake da ita da zaran kayita ko ita addakai badai an
dawo lafiya ba ta sake tambayan jikan nata don ganin rashi babu dadi a lokacin.

  Bai bata amsa ba ya
kara shiga da kayan ciki tana yada mai haske yaga inda zai aje kayan ta kara
fadin dauri ka bugo wanga abin zamanin ko a makwabtana mu sani.

   Ki kwanta saida
safe zanyi sallahna yanzu Dije ya fada yana daukan buta ya nufi bandaki bayan
yaji akwai ruwan da zai isheshi amfani a lokacin.

   Saida ya kewaya ya
fito har lokacin Dije ta kasa shiga daki ta kwanta kamar yadda yace din da ita
ya duka ya fara alwala yaji tace kaci wani abuna ko a hanya gashi yau ban dahwa
komai ba a gidan .

   Jin hakan yasa ya
dago kai da sauri yana fadin saboda me dije babu abinda zaki dahwane ko me ya
tambayeta cikin son jin abinda zatace din dashi lokacin.

   Sai yaji tace kona
dahwa ma baci zanyi ba shiyasa na hutar da kaina da dahuwan saidai in kai dan
kwano in sayo in dawo gida wani kuka yaji dayasa ya firgita.

  Ba kuma bakon kuka
bane sai sauti  muryan uwar garke  haka
yasashi kaduwa har yaji gaba  shi
ya fadi lokaci guda da sauri ya karasa alwalan ya mike yana lalubo yar wayan
shi daga cikin aljihunshi.

   Yana haskawa ga
dabbobin su biyarne a wurin yagani a
daure kuma tabbas uwargarkene wanan a madaurin ta ta mike tana kiwo.

   Dije yaushe akuyan
nan ta dawo gidan nan daga daki dije ta amsa mai da fadin kaidai bari dan
albarka aini akuyan nan ta wuce sanina yanzu saidai ido da addu,a kawai.

   Akuya sai ta kwasa
ta tafi sai lokacin da taga dama ta dawo ni na kasa gane me wanan yake nufi da
hakan ko wani gidane ta samu take labewa ko wani ke kamata idan taga sarari ta
gudu oho ?

   Bai iya cewa komai
ba sai addua da yakeyi a zuciyan shi lokacin don baima san abinda zai fada ba
game da uwar garke din data zama mai waibuwa a garesu yanzu.

   Haka ya ja kafa ya
shige dakinshi da a yanzu yaji shi daban sai zafin daya doki fuskanshi haka ya
daure ya tayar da sallah bayan ya dan kakkabe wurin yayi shafa,i da wuturi ya
samu wuri ya kwanta zuciyan shi cike da tunane kala kala.

    Ban samu ganin su
yaya musa ba don tun dana shige daki ban fito ba sai washe gari inda na tashi
na samu su yaya din a falo tare da Abba suna magana.

  Suna ganina ko wanin
su ya washe baki a cikkn mamaki da sauri na nufesu na durkusa ina gaidasu ya
musa ke fadin dama kina garin nan ne yan mata ?

   Tana nan tazo hutu
kasan mama da son zaman abuja dama dolene ya kaita gusau ta zauna dama don
rashin mace ce a gidan yasa ban daukota duk hutu don tafi sabawa da nan din.

    Nima nashayin
wanan tunanen cewa na samu lokaci in daukosu dukan su har ummah suzo nan su dan
kwana biyu ko din makwabtan dasuke damuwana da tanbayan su idan sun gani.

   Ai yanzu tana jin
dadin garin tunda ta hadu da wani dan iskan yaro daya fara hure mata kunne a
yanzu Abba ya fada daga inda yake zaune.

   Gaba dayansu suka
kalloni sai ya jafarne yayi saurin magana yace haba dai Abba dama ace su Aisha
ka fada zan yarda don sune rawan kansu yai yawa.

   Gata dai wanan din
yana nunani da cokalin dake hannunshi lokacin yace shiyasa naga gara da anyi
hutu ta dinga zuwa nan kusa dani zaifi.

   Ya musane ya
kalleni yace wai hakane kanwata da sauri na girgiza kaina alaman ba hakana bane
daga inda Abban yake yai min wani irin tsawa yana fadin.

   Karya zan maki kome
ku diba yarinyar nan wai har zataje ta dauko min wani fakirin yaro mara asali
har yana zo min har kofan gidana don uwarta ta daure mata gindi yin haka.

    Abba be cool don
nasan haka kawai Zahra ba zatayi abinda bai dace ba kuma ummah ta sa mata ido
kila dai wani abin ne ya hadasu daban ko ?

   Ya juyo yana ajiye
cibin dake hannunshi da yake shan tea yace zan zauna da ita inji abinda ke
gudana Abba no ai basai ka zauna da itaba don naga tana son ja dani akan wanan
yaron dam matsiyatan.

    Ko zuwa kanon nan
da sukayi ace wani dan mutunci yazo neman ta amma yarinyar nan ta rufe ido taci
masu mutunci dagashi har ita hjy karima din karshe ma taso hadata da yan uwanta
a kan maganan fada.

   Wani irin dagowa
nayi na kalli inda Abban yake cikin mamakin jin abinda ya fada din lokacin
kafin nayi kasa da kaina hawaye yana zuba min a idona mai nuna alaman kazafi
akaimin ga hakan.

    Abba yaci gaba da
fada inda yake shiga ba nan yake fita ba sai ya musa ne ya mike ya kama hannuna
zuwa dakina don nan yaga na fito lokacin.

     Har ciki ya shiga
dani ya zaunar dani saman gado yana fadin ya akai hakanga zahra a sanina kedai
ba mai rigima bace zahra ga kuma Abba yanzu yana fadin zance mara dadi a kanki
?

    Da kyar na iya
dago kaina don jin ya sake maimaita min tambayan nace wallahi Allah yaya ba
hakana bane nan na kwashe komai na fada mai har da zancen mommy din ban boye
mai komai ba.

    Zuwa lokacin ya
jafar ma ya shigo dakin yace shi yaron Abba ya fada min wai baida baba ke nan
shegene kome zahra ?

   Kai na girgiza
mashi nace ba gaskiya bane yaya last da mukai waya dashi ya fada min yana
taraba zaije gun mahaifin shi ne.

   Da baida baba aiba
zai fadi hakan ba kuwa ya musa ya amsa daga inda yake zaune is OK ya jafar ya
fada ki bari zanje Zamfara yau zan zauna da ummah akan zancen.

    Da sauri na dago
kai ina fadin don Allah ya jafar ka wuce dani wanan matar makirace sosai bana
jin dadin zaman gidan nan sam wallahi.

    Idan nayi hakan
Abba zai dauka wani abune no kaje kawai zanzo da ita zuwa jibi don na fahinci
wani abu cikin zancen zahra din ni zanzo da ita gida ka wuce kawai zamuzo tare
ya musa ya fada.

    Sai safa da marwa
takeyi a cikin dakin nata kafin can wayanta ya dauki kara kobata duba ba tasan
me kiran nata don shi ta sakawa irin ringing tone din wani wakan larabawa ne da
akewa habibi.

    Ta dauka cikin
saita muryanta yake fadi daga bangaren shi kizo ga sakon yasir an kawo ta karba
da gani fitowa saida ta dan bata lokaci ta nufi falon.

   Mijin nasu ne a
zaune tare da amininshi Jabbi sai tellan yaranta maza dake gefe daya a takure
ta shigo falon cikin isa da izza da takama kamar bataga jabbi din ba ta fara
fadin.

    Yau Isah tellane gidan
eh hjy naji ance kunzo shine nace barin sheko in kawo dinkin nan nasu oga yasir
don yace akwai wanda zaikai mashi can idan na kawo maku.

   Eh nima yayi min
waya kwanaki idan nazo na karbo mashi dinkin yana cirowa yake fadin kai hjy
ashe ana kama a duniya haka ?

    Wallahi shekaran
jiyan nan wani matashi yazo shegona sai ka rantse da Allah yasir din gidan nan
ne sai dai idan yai magana zaka gane bashi bane.

    Wani kallo jabbi
dake gefe yayi mashi amma ya basar don maigidan ya dan daga a lokacin ya shiga
ciki zai daukowa aminim nasa sako tellan ke fadin haka.

  Mikewa tayi tana
daukan kayan tare da fadin jeka zakaji alert tayi tsaye har saida taga fitanshi
daga gidan ta juya ta shige ciki sai jin wani abu takeyi a zuciyanta na tashin
hankali da fargaba.

   Kayan ta jefa a
gefen gado ta jawo waya ta fara neman layin wata yar uwanta dake Gembo cikin
tashin hankali take fada mata abinda ke shirin faruwa dasu.

    Mikewa tayi kamar
a gaban yar uwan nata take ta soma fadin wanan karyane wallahi irin abinda mukayi
muka bizzine za ace yanzu wai yaron nan yazo ya baiyana.

   Wanan ma karyane
wallahi in ko har haka sai mu canza mu koma wani hanya me zamu tsaya jira dama
kin daiji abinda ake fada cewa muddin ya baiya zai doke duk zatin da taurarin
diyan ki ga baki daya zai dushe.

    Shi nakewa tsoro
ya Lantana idan ina kaunan mutuwana ina kaunan yau in bude ido inga wani da a
gidan nan da sunan dan Alh ne shima koda kuwa diya macece ita bana kaunan
hakan.

   To kingani inda
mukaje aka bawa kare mahaifar wanan gajan kishiyar taki aka daureta can zamu
koma mu kara matsesu a saka masu duhu a tsakanin su har abada.

   Don haka kiyi
dubaran da zakiyi ki fito gobe mu sanu muje wanan kauyen don kinsan wuyan zuwa
ke dajin arnan nan don hawan dutsen nan dake wajajen .

  Na sani idan ba dole
ba wallahi ban son zuwa wanan wajen saidai ba yadda na iya tunda ina son biyan
bukata in sha Allahu gobe din dai zansan yadda nayi nafito muje wurin.

    Allah ya kaimu ta
fada suka dan taba hira aka kashe wayan kowa ya zauna yana cicika a zuciyan shi
tare da tuna irin kudin da suka kashe a baya.

    Yallabai ina zuwa
zanje in dawo yanzu jabbi ya fada yana saurin tashi daga inda yake zaune Alh ya
bishi da kallon mamaki yana tunanen inda zaije haka da sauri har yana tunanen
ko lalura ya kamashi.

    Allah ya
taimakeshi ya samu wanda yake son gani din a lokacin har ya tare mashin zai hau
ya tare shi don haka ya tsaya .

  Ya sanshi farin sani
don customer shine a wurin dinki sosai bayan sun kara gaisawa ne ya dan duba
baya kafin ya fara fadin.

  Ka gafarceni kan
maganan da nake son muyi yanzu in har hakan ya zama kamar katsalandan a garejku
don zakaji maganar kamar ina son maka kutse a cikkn sa yanzu.

   Kan isa tella din
ya daure kafin yace Alh lafiya dai ko don ban dahinci inda zancen ka ya dosa ba
yanzu yace eh hakane gaskiya ba zaka gane ba sai na fada.

    Dama game da
maganan nan danaji kana fadawa hjy shine a yanzu na yaron da ka gani sunyi kama
da yaron wurin Alh don Allah ko ka san inda zamu sameshi.

    Kallon mamaki isa
din yai mashi kafin yace dashi Alh wallahi ban sanshi ba nima haka kuma ban san
daga ina yake ba illa abinda na sani shine.

   Sun kawo dinki
shagona munyi dasu su dawo gobe jumma,a su karba da karfe hudu na yamma shine
kadai abinda na sani game dasu din.

  Amma bayan haka  bansan komai a game dashi ba wallahi zaka
taimakemu don Allah nan dai ya fada mai abinda yake son yai masu na taimako
kuma iya shi yasan da wanan zancen ya kama bakin shi.

  Insha Allah in har
ya yaimaka masu akwai goron da zai samu kuma ba zasu taba yarda hjy tasan da
zancen ba don kada su hana mashi hanyar samu daga gareta da diyanta.

    Basu kai ga kare
maganan ba kiran hjy ya shigo a wayan isa din ya dauka ba sallama ta fara fada
dashi kan baida hankaline ko wayau zai fada mata magana irun haka a gaban wani.

  Hakkuri ya fara bata
saida kyar ta yarda tayi shiru tare da fadin to ka iya bakin ka don nasan wanan
munafukin zai bincike ka akan maganan nan watarana duk daya nuna ba komai a
hakan daya nuna a falon dazun yace insha Allahu zaiyi yadda tace din.

  Kallon juna sukayi
ya kashe waya ya dan murmusa yana fadin aina fadama wanan marar akwai abinda
take boyewa wanda bata son asani.[2/28, 6:40 AM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

Leave a Reply

Back to top button