TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 3

Sponsored Links

 

 

 

*Don Allah don annabi duk wadda Bata shirya siyaba kar tamun
magana tabari sai ta shirya tukunna kar mu batawa juna lokaci* 🤗🤗🤗🤗

 

Don Allah kada kiyi gangancin maryar da novel din nan
audiovisual na riga da na sayarwa S ZARIA HAUSA TV idan wata ta karanta audio
din shi hukumace zata rabasu da maishi nagode.

     Da sauri ya biyo
bayan maishi don jin dalilin aika mai da abincin da kudi duk da baya raba daya
biyun cewa fadan da madam tayi mai a bainan jama,a ne ya jawo hakan.

   Tunda ta fada a
kunnen kowa cewa ba zata biyashi kudin aikin ranan ba haka kuma yasan da sanin
baida abinci a ranan hakan na iyasa mai tausayi da imani ya tausaya mashi duk
da bayau aka fara mai irin cin fuskan nan ba ai.

    Aikin wahala kowa
yasan da yana yin shi a shagon madam tun baikai hakan ba saidai kuma haka bai
hanashi ci gaba ba ga karatun shi don kusan shine kurun ajinsu dake zuwa na
daya aduk jerabawa idan suka zana.

    Wanda yasa mutane
da yawa ke mamakin hakan saukin shi daya baya shiga harkan kowa kome yakeyi
wanan ya jawo mashi saukin wullakanci a idon mutane da basu gani basu maganta
ba.

   Ita kanta madam ta
sani cewa zai iya dakatarwa da komai da zaran lokacin  daukan darasinshi yayi yaje aji sai ya gama
ya dawo bakin aikin shi.

  Dan adam da keta da
farko taso hanashi hakan amma ya jajirce yaki yarda da nufin ta don ya gane
bata son cin gabashi saidai tayi ta more mashi ita wanda yasan karshe zai tashi
a tutar babune ta gama moranshi a karshe kuma ta koreshi.

   Mutane da yawa suna
mamakin hakan gareshi ace saurayi kamarshi baya jin kunyar zama yana wanan
aikin ko macece shi abinda kunya ace yana dan jami,a yana wanan aikin zubar da
kiman shi.

    Sam shi bai dauki
hakan wani abu ba tunda burin shi yana cika da sanu da sanu don idan ba hakan
yayi ba ba wani wanda zai tausayawa rayuwan shi yace ya daukin laluran karatun
shi a halin yanzu.

    Gashi a zamanin
nan na rashin taimako kowa kanshi ya sani ba taimako ga al,umma ko tausayawa
tallaka saidai ma kokarin ganin bayan ka koda baka kai karfin mutum ba zai iya
hassada ga al,amarin ka ayanzu.

   Kallon kudin hannun
nasa yayi dubu ukune da dari biyar ta bashi canji wai kyautane daga wace bai
sani ba duk da yasan akwai na Allah har duniya ta nade nagari basu karewa a
duniyan nan.

   Haka yaja kafa ya
koma ciki zuciyar shi cike da zargi da kuma mamakin yin hakan dukda dai yana
samun dan canji wani lokaci saidai basu kai haka din ba .

    Tun dawowana gidan
ina kwance a dunkule dakina wanda ciwon kai dake damuna ya kaini ga kwanciya
haka har baya  magariba ummah taga ban
leko ba yasa ta shigowa da zuman min fada.

  Saidai yadda ta
sameni ne ya daga mata hankalinta a cikin dan tashim hankali take kiran sunana
da kyat na iya bude idona da suka kade sukai wani irin ja kamar garwashi.

   Subbahanallahi
maamaa meke damun ki haka kuma kai na nuna mata na mayar da kaina saman filo
fada ta fara min da cewa wai meyasa kike wasa sa ciwo hakane maamaa ?

   Baki da lafiya ba
zaki fadawa mutum ba sai kishige daki ki dunkule a ciki haka sau nawa zan fada
maki bana son haka din.

   Fita tayi daga
dakin sai gata tadawo dauke da magani da ruwa a hannun ta tana fadin tashi kisa
panadol ko zaki samu relief amma ana zama da ciwo haka a jiki  ?

   Ko motsi banyi ba
ayadda nake hannu takai ta dan girgizani da sauri ta dauke hannunta saman jikin
nawa tana min wani irin kallon mamaki.

   Fita tayi dakin ta
nufi part din mama a rude tayi sallama mama na zaune da wata kawarta suna hira
suka amsa mata tare da binta da kallo don tasa
bata damu da shigo mata daki haka ba.

    Hjy maimuna
mutumiyar kice ba lafiya tunda ta dawo school din yau take kwance bata fito ba
shine yanzu na lekata don in bata magani ai jikin yayi zafin da ban taba jinshi
ga wani mahaluki ba yadda jikin yayi zafi.

   Subbahanallahi mama
tace tana mikewa tsaye tana inane ta fada a dan rude tana dakinta a kwance bari
na dubata kafim na kira likita mama ta fada don itace mai kiran likitan mu gako
waye baida lafiya a gidan.

  Ida  mai karatu baki manta ba na fada maki komai
na gidan mu yanzu mamace jan gaba dashi kasancewa mahaifiyar mu batayi boko ba.

  Kuma bata samu haihuwa
da wuri ba yasa mama ta amshe duk wani ragaman gidan ya koma hannun ta hakan
kuma bai damu ummah ba duniyace taje tayi ta kayan shi.

   Ina zuwa hjy karima
mama ta fadawa kawarta dake zaune tana kallonsu kafin kuma ta juyo tana fadin
taso dai mu tafi mu ganta ai dake.

   Dakin suka
shigo  lokaci guda ina kwance yadda ummah
ta barni mama ta fara kiran sunana da maamah maamah meke damun kine tana kai
hannunta a jikina taji zafin jikin da ummah ta fada.

   Da sauri ta jaye
hannun tana fadin meye haka kuma jiki ya gashe kamar garwashi haka lokaci guda
ta fada tana kallon su ummah da hjy karima dake gefenta tsaye.

     Hjy karima ta
matso ta kai hannunta da sauri ta cire tana fadin meke damunta hakane jiki yayi
wanan zafin kamar ba jikin mutum ba.

    Ku bata maganin
maganin tasha mu gani mama ta fada dole ummah ta matso kusa ta tayar dani zaune
ina kokarin komawa na kwanta cikin daurewa Allah ya taimaka na karbi maganin
ina hadewa na koma na kwanta.

   Duk suka kura min
ido na lokaci kafin hjy karima tace dasu anya yar ba iskokaine a kanta ba kuwa
da sauri mama ta tare da fadin a a maamaah bata da komai ciwone kawai ya
ziyarto ta.,

  Allah ya sauwaka ta
fada ta farayi gaba mama din tabi bayanta bayan ta dan kara yi ummah bayanin
cewa idan maganin ya sakeni inyi wanka inci abinci kada ummah ta bari nakwana
da yunwa ta juya tana sauke ajiyan zuciya.

    Godiya ummah tayi
mata ta fita tana tambayan sauran yan uwana ummah tace suna dakinsu suba
assignment ta fice daga part din namu ta nufi part dinta ta samu hjy karima.

   Kai mutumiyar kin
dai tare gaba kin tare baya a dole wanan matar da diyanta su biki batace komai
ba tayi murmushi kawai tana kaiwa zaune.

   Hjy karima ta kara
fadan wanan yar taku tana girma kyauta na dada karuwa haka  wanan ai da gudu wani kusan gwaunati zai
bullo ya dauketa lokaci guda.

    Kun kusa zama
sukan gwauna ko wani hamshakin maikudi a garin nan rass gaban mama yayi amma
sai ta daure ta sake murmushi a fili kawai bata furta komai ba koda amin din
munafuncine kuwa.

   Saidai ta dauko wani
hiran suka somayi da kawar nata har zuwa goman dare data mike tana mata
sallaman zata tafi dare yayi ta rakata har wurin motanta ta dawo.

     Zan iya fada maki
cewa ke mai karatu gidan mu gidan rufin asirine gidane da mahaifin mu nada
rufin asirinshi iya gwargwado da Allah ya bashi don tsonhon ma,aikacin hukuman
kwastom ne na kasa da yai ritaya .

    Yanzu kuma ya fada
harkan kasuwancin kasa da kasa tare da rike siya da karfin Allah yana da tittle
a zamfara da ake kira da MAYANA.

    Wanda asalin yan
garin suke kiran duk wani dan gidan mu da wanan tittle din na mahaifin mu
tundaga waje zaki fahinci naira ya zauna a gidan namu.

   Duba da irin ginan
gidan namu da irin motocin dake haraban gidan wanda duk wata mace da yarin
gidan daya kai munzalim jami,a ana mika mai mota don bukatanshi na yau da
kullun .

    Mahaifin mu yana
da gidaje a garuruwan anan gida Nageria har wasu na fadin yana dasu a wajema
saidai ni shekaruna bai kaiga nasan wanan zancen ko gaskiya ake fada ba a nan.

    Kamar yadda na
fada ummah itace matsrshi ta farko daya aura saidai ummah batai boko ba wanan
yana cikin dalilin koma bayan da umma din ta samu a gidan mu.

    Sai mama da kamar
yar uwa take a wurinshi don suna da dangantaka da ita wajen ubananan su ita
tayi boko har ta fara FCE a lokacin da sukai aure.

    Mahaifin mu ya
hadu da mahaifiyan muce yar katsina lokacin dayaje bautan kasa a kaduna tana
wurin kanwar mahaifiyar ta dake tasheta nan ya ganeta a unguwar rimi ya nuna
yana sonta aka bashi ita lokacin tana da shekara goma sha shidda batai wani
girma ba sosai ya aureta ya ajeta Gusau shi yana tafiya wurin aikinshi a can
Lagos saidai ya dan kawo masu ziyara a lokacin.

    Amma shigowan mama
gidan namu da kuma samun rabo da tayi gata kuma da alaka da mahaifin mu sai
asanu da sannu komai ya koma hannun mama din da yanzu ita ke mulkin komai.

    Tun yan gulman
gefe na magana kan yadda ake mulkan mama din har suka daina ganin ita bata
dauki hakan a komai ba don ko haihuwa mama tayi itace ke kula da yaran har
girman su sai idan sun fara wayone mamake rabata da yaran nata a cikin hikima
irin na wayayyu kuma ta haifo wani ta danka mata raino bai hana ummah ta karba
da zuciya daya ta rike matasu inda duk wani wahala da yaro zaiyi na goyo itace
wahalan su a lokacin.

     Amma halin dan
Adam lokacin da mama ta kyala ido taga ummah da ciki a fili ta nuna mata bakin
cikin hakan saida wata yar uwanta ta fadawa uwanta ta tsawata mata tace .

   Amma idan kikai wa
salma haka bakiwa kanki adalci ba matar da a tare kuke wahalan ciki da goyo
agidan nan tare da ita don yau Allah ya tuna da ita ya bata nata rabon zaki
nuna fushi gareta.

    Wallahi ki janye
wanan gabar taku kada duniya tasan da kinayi a zageki don salma ta gama dake
maimuna ta rikeki dake da diyan ki rikon Allah da Annabi me kuma kike nema gun
kishiya wanda salma batayi maki ba a yanzu.

    Ai idan kinyi haka
kamar kina fushi da ubangijin kine don saida ya fifitaki kafin salma a gidan
don yanzu ya tuna da ita ya bata zaki nuna bakincikin ki ga hakan.

  Wanan fadane yasa
mama ta danne zuciyar ta wayence da fadin salma aini fushi na dake wai ace mun
samu alheri amma kika iya boye min baki fada min sai kawai gani nayi a jikinki
?

    Murmushi Salman
tayi tana fadin haba dai ai da kunya na fadi abu haka kai tsaye ballema ba  tabatarda cewa cikine ko ciwo ba a jikina nidai
baki kyauta min ba tunda baki bari na nunawa yata ko dana farin ciki ba tun
yana ciki yadda kike nunawa diyan ki.

     Wanan ya jawo ake
kirana da diyar mama duk da maman ta kasa yin yadda ummah ke mata dawainiya da
nata diyan lokacin haihuwansu don tabar ummah da kula da abinta karshe ma tabi
Abba zuwa lagos ita da diyanta sukayi shekaru a can tare saidai idan sunzo yin
wani abu ne zasuzo gida cewan mama takai yaranta su sami ilimi ingantattace a
lagos din.

   Yasa na taso a
hannun mahaifiyata lokacin dana isa karatu kuma sai mahaifin mu ya dauki ummah
ya mayar da ita abuja da zama don a sakani karatu har Allah ya azurta ummah da
diya uku bayana lokacin mama tana da haihuwa shidda a duniya.

   Komawan ummah Abuja
yasa ta waye har ta dan shiga karatu a can a wani women center na matan aure da
haka itama ummah tayi nata ilimin shiga cikin manyan mata ya tallafawa ummah ta
fara kwato incinta a gidan mu yanzu.

    Duk da dama ta
sani tana dai barin su da Allah ne kawai don son da takewa mijin ta shima in a bayan
mamane yana nuna mata kulawa irin wanda ya dace.

   Mama ta raina abuja
a lokacin don sun dade basu hadu ba wani sallah da suka hadu a gida taga yadda
ummah ta sake a lokaci zama da manyan mata ya juyar da ummah ta zama mace mai
yancin kanta sai hankalin mama ya tashi sosai da ganin hakan.

    Nan ta matsa itama
Abuja zata dawo da zama Abba yace karatun yaran fa gasu sunyi nisa ga karatu ba
kunya tace su dawo abujan suyi duka a inda nake.

     Duk kamanin
mahaifiyata na kwaso a wurin kama don hakane duk mama ta kalleni takw jin wani
iri game dani saidai tana danne zuciyarta ne kawai a zauna lafiya saboda
mutane.

    Gashi kum sunn
mahaifiyar Abban mu aka samin yana kirana da mamangida wanda mama bata yarda ba
sai ta mayar dani maamah kawai a takaice da sai mutune sun tambaya da suna wa
aka saka minne ake kirana da maamah ?

   Akwai shakuwa na
musanman tsakanina da mahaifina da yan uwana maza na sakin mama matan ne dai
sam.bamu shiri dasu da ba wanda yasan dalilin hakan.

  Hakama kakan mu
danaci sunanta muna shiri sosai da ita don tun muna abuja zaune nakan zo
wurinta hutu a gusau amma tare da mai hidimana.

   Lokacin dana kare
secondary zan fara jami,ane mama ta kawo cewa sai mu koma gida tunda yanzu yara
duk sun girma gara dai su koma gida cikin yan uwa su koyi irin al,adan gida
acan kuma.

    Abba yaso ya nuna
mata bai yarda da hakan ba amma sai ta nuna mashi cewa yanzun fa yana da tittle
a masarautan zamfara zai iya son wani abu a nuna masa ai ba a gida yake zaune
ba har iyalinshi da wanan mama taci galabanshi muka dawo zamfara da zama .

  Don kawai kada yayan
ummah su samu karatu ingantattace da zai amfanemu kamar diyanta a nata tunanen
ke nan.

   Sai gashi Allah
yaba yan dakin mu baiwa na ilimi don gaba dayan mu na daya muke ci ga jerabawan
mu idan munyi exam.

    Kokai waye idan ka
shigo gidan mu ba zaka fahinci akwai wani zama na daban ba a gidan mu zakace
zamane mai tsabta a tsakanin don yadda ake nunawa a fili.

    Har wasu sukanyi
kwantace da irin zaman lafiyan da akeyi a gidan mu tsakani  mama da ummah d basu nuna haukan kishi akan
junan su sai zaman lafiya zallah.

    Saidai abinda basu
sani ba shine irin wanan zaman yafi cutarwa ga irin zaman da ake haukan kishi
din afili tsakanin kishiyoyi.

   Shiyasa zancen hjy
karima ya dagawa mama hankali da har yakai ta kasa barci kan wanan maganan a
ranan sai faman sake sake take a zuciyarta.

   Hankali a tashe ta
wayi gari don ba karo na farko ke nan ba da take jin irin wanan zancen a
bakunan mutane saidai har yakai kawarta tun na kurciya kuma aminiyarta ta fada
mata haka a gabanta tasan akwai abinda hjy karima din ta hango game da yarin
yar ke nan.

     Tana idar da
sallah ta jawo waya ta danna kiran layin anty Asmau yarta dake aure a Silami
wace suke kashewa su bisa tare da ita.

  

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

Leave a Reply

Back to top button