TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 34

Sponsored Links

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,

,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3️⃣4️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Bin ko ina yake da kallo shi kadai yasan abinda yake
kiyastawa a zuciyarshi lokacin muryan drivern ke fadin .

    Bani layin wayan
ka don  nima in bincika idan na dawo dan
naga kana bukatan taimako sosai a wana
harkan Ahmed din bai ji ba baima dauka dashi yake maganan ba a lokacin
saida na gaban motan ya dan juyo yana fadin bakaji bane yace ka bashi layin
wayan ka zai taimaka yai ma cigiya wurin diribobinsu shima.

  Yace soryy hankalina
baya tare daku a nan wayan drivern ya miko mashi bai tsaya ba ya fara saka
layinshi a cikin wayan yayi serving.

   Ya mikawa driver ya
amsa yana fadin in sha Allahu zan bincka tsofin direbobin mu inji masu zuwa
arewa ta yamma koda akwai wanda ya sanshi saidai matsalan bansan yadda zan masu
kwatancen sunan nasa ba ko kamanin shi su gane.

   Eh to sana,an
dabbobi yayi da farko akace da suna zaune ne garin ibadan sai harkan ta kawosu
nan zamfara din har yazama kamar dan gari aka aura masa mata mai suna saratu
yar gidan malam ladan na aduwa unguwar labillalabil shekara ashirin da biyar
yanzu da yabar garin ke nan.

  Allah yasa mu dace
ya fada yana aje wayan nasa kafin can yace watau ka gane ne  nasan irin case din nan nasa a baya diyar
wata yayan mu da suka zauna shagamu.

     A can itama suka
hadu da mijin sukai aure daga baya ya barta can da yaran ya koma garin su
karshe ko da zamu gano inda yake gashi dai yayi wani auren a nan kano amma an
samu ya mutu sai yan uwa aka sama kawai.

    Gaban Ahmed din ne
ya fadi yayin da direban yaci gaba da fadin in fadama malam yan uwan nan suka
so ja dasu wai basu yarda ba da yake idon yayan namu a bude sai ta makasu kotu
dole akaje akai gwajin jinin su har aka gane gaskiyan zancen.

    Ido Ahmed ya
runtse yana tunanen idan har hakan ya kasance dashi shi waye zai tsaya mashi
har a sheda hakan sai hakkuri wani sashen zuciyar shi ya bashi amsan hakan .

   Direban ke fadin in
fada ma ma malam karshe fa shi wanan bawan Allah koda ya mutu bai bar komai ba
duk wanan fitinan da akeyi.

   Ita dai yar uwanan
namu duk wanan bai dameta ba bukatanta kawai shine tayiwa diyan ta gata suma su
san yan uwan mahaifinsu kawai shine bukatanta din.

   Ankoyi hakan yanzu
suna zuwa gida suma suna zumunta dasu sosai kaga ta fitar da diyanta cikin
kangin shegantawa ke nan.

    Hira suke sosai a
motan baice dasu ko mai saida yaji tsohon ya fara fadin Alhamdullahi tunda mun
shigo nahiyar mu komai yayi daidai yanzu.

   Kallon tsohon yayi
kafin yakai duban shi ga wayanshi daya nuna karfe goma sha dayan rana gashi ya
soma jin yunwa a lokacin har yana jin yunwar nason yiwa jikinshi illa a lokacin
don yadda ya fara galabaita.

   Idan zai iya tunawa
tun a kano daya karya bai kara saka wani abu a bakin shiba hana rantsuwa ruwan
pure water na leda da yasha a tasha kafin su taso lokacin.

    Baba a ina zamu
sauke ku drivern ya tambaya yana dan waigawa baya a lokacin nan cikin garin
mambilane ko gaba ko kafin a shiga ?

   Cikin mambila din
dai nake da zama amma ni mutumin garba Chedine kowa nawa na nan garin da zama
yanzu haka amma nida iyalina muna a mambilane zaune.

   Hankalin Ahmed ya
kara kwantawa da jin haka sun dan taba tafiya kafin su isa inda tsohon yace
yake da zama a can dan nisa da gari kadan ya nuna masu wani gida suka gangara
don sai an sauka sosai saman titi din zuwa kofa
gidan .

    Bafilace asali ba
a rabashi da kiwo don haka ko wanan tsohonma dai sun hango shanaye a kofan
gidan nasa an kilacesu a wuri daya manya manya sunci sun koshi sun baje suna
harbin iska sai kiwo sukeyi hankali kwance.

   Sai gashi zancen
tsohon da yace shidin tallakane yasha bambam a idon Ahmed din donshi mai arziki
ya gani don da ace wanan tsohon yasan inda shi yake rayuwan shine da ba zai
kira kanshi da tallaka ba.

    Aka saukewa tsohon
kayan shi dake cikin wani tsohon buhu dayasha jaki sosai ga tsufa tsohon ya
shiga cikin gidan sai gashi ya fito masu da ruwa a kwanon sha sabo mai sanyi da
dasin sha sukayi godiya sosai tare da dan kara tataunawa kan Amadin.

    Nan driver da
wanan mutumin sukai masu sallama suka tafi iso tsohon yayiwa Ahmed din na ya
shiga cikin gidan nasa kada yaji komai.

   Ya daukesu takar
iyayyen shi gidan tas dashi yana jin tsohon yana sallama wata farar dattijuwa
mai tsayi ta fito daga wani daki mai dan rufin kwano a sama.

    Tana masu sannu da
zuwa ta juya kuma ta koma dakin sai gata ta dawo da dauke da tabarma harda filo
a hannunta tana shimfidawa a wani dan runfar shan iska dake tsakar gidan.

    Shima tsohon dakin
ya shiga ya rage kayan jikin shi ya fito yana cewa Ahmed din dake zaune a
takure yarona na fada maka cewa ka saki jikin ka kamar kana gidan kune ne nan.

    Shatu wanan bakon
mune zai zauna damu a gidan nan na kwana biyu har zuwa lokacin da zai gama
abinda ya kawoshi garin nan ya koma.

    Sannu da zuwa
matar ta kara masa tana mashi yaya hanya a cikin kulawa da kauna a gareshi
kafin ta mike daga durkushen da take ta nufi madafin su inda suka kebe a gidan
suna dafa abinci.

    Abinci ta hado a
cikin wani kwana irin na da din nan mai kauri da ruwa  shan data tsiyayo a tulu ta kawo masu nan
inda suke zaune saidata durkusa ta aje tana masu bisimillah.

  Ta mike ta nufi wani
hanya a baya ta dan jima don lokacin har tsohon nan ya matsa masa kan yaci
abincin ya bude tuwone na farar shinkafa da miyar kuka sai kamshin man shanun
data lema saman miyar da kamshin daddawa da kayan yaji.

   Yayi bissimilah ya
fara ci sai gata dauke da nono mai zafi data taso a lokacin ta kawo masu ta
girke a gaban su kallon nonon tsohon yayi yana fadin aiko kon masa dabaran
yunwa kuwa.

   Kasha nonon nan don
hanjin ka ya dan walwale saboda ina kule bakaci komai ba tun jiya duk da ba
wani abinda zakaci a motan amma ina kule da hakan gareka.

    Kwantar da
hankalin ka indai mahaifin ka a cikin wanan nahiyar namu na mambila in sha
Allahu zamu gano makashi tunda naji ka fadi cewa sana,an fita fautaucin dabbobi
yayi a baya.

    Wanan ya kara haska min cewa zamu ganosgi a
saukake ta hanyan tambayan mutanen da sukai irin wanan sana,an a baya su zan
binciko da farko matsala daya zamu samu shine rashin cikakken sunan shi da
sunan garin da ya fito.

   Yanzu kaci abinci
kayi wanka ka shirya saika dan huta zuwa gobe sai mu fara binciken a tsanake
Ahmed din ne ya gyara zaman shi ya dago kanshi dake duke tun lokacin da tsohon
ya fara bayani yace.

    Baba ko hakan ma
nagode ina laifin wanan karamcin da kaimun a yanzu ba zanso daura ma nauyin da
zaisa ka aje tsabgogin kaba kaje yin nawa idan na natsu zan bincika a tsanake
ko Allah zaisa mu dace.

   Kada kaji komai shi
taimako idan kaiwa mutum baka san Alherin dake cikin shi ba ga kuma ladan hakan
a wurin ubangiji nagode baba ya kara fada sai tsohon yace ba komai yaro.

   Saidai kayi hakkuri
da yanayin gidana da irin cimar mu na nan don zaka ji abin daban da yadda ka
saba dashi a  gida ba komai baba aina
gode ya fada.

    Sunci abinci
lafiya wanda saida yasha madaran kamar yadda tsohon ya umurce shi dayi a fatko
kafin ya dora da abinci yaci saida ya koshi ya mike ya dauki kayan zuwa madafi
inda yaga matar tsohon Shattu ta fito da abincin yakai kwanonin a ciki duk da
tsohon ya hanashi yace ya barsu za a kwashe ai.

   Dakin da Shattu ta
gyara tazo ta dauki kayan ta kai mashi wanda dama yar jakkace irin da maza ke
ratayawa a kafada don kala biyu kawai ya cusa a ciki dama sai wanda ke jikin
shi a saye sune yayi tafiyan dashi.

  Shattu ta dawo tana
fadin yaje yai wanka ga ruwan dumi can takai mashi tana nuna mashi bayin inda
zai kewa ya mike yana godiya tsohon ya bishi da kallo har ya shige cikin bayin
don watsa ruwan a jikin shi.

   Tausayi yaba tsohon
sosai don duba da irin yanayin yaron yana da natsuwa da tarbiya gwargwado ya
juya ya kalli matan nasa yana fadin kaiyya wasu mutane suna watsi da daman su
da Allah yai masu.

  Kana da wanan yaro
haka zaka watsar da kimar ka da mutuncin ka ka wofintar da yaro kamar haka ka
banzatar dashi a cikin duniya cikin rashin ko in kula haka kuma kasan kana
dashi a raye ka danne hakan.

    Malam zuciyar wasu
mutanen yana da tauri sosai ai amma wanda yasan yabar yaro haka a wani wajen
zai iya zaman shi a nan ya kyale yaro kamar wanan yanzun haka gorine da
shaguben mutane yasa ya bar gida ya fito neman mahaifin nasa a yanzu.

    Dije kan tashiga
tashin hankali da bai lissafuwa a wanan lokacin ta fara fita cikin yanayinya a
yanzu gashi yan uwanta ba wasu masu karfi bane da zasu iya taimaka mata.

    Haka kuma ita bata
da karfin bin didigin akan hakan yadda mutane keyi abu guda ta samu shine bayin
Allah suna tayata da addua a ko wani lokaci.

   Haka idan anyi
sallah akan saka yaron ga addua don sanin da mutane sukai mashi da hali mai
kyau da girmama mutane yadda ya kamata.

   Yauma malam
tanimune yayi sallama ya shigo suka gaisa yake ba Dije hakkuri yana fadin ni
tun lokacin da naga yaron nan ya fara tasowa haka a dan lokaci guda.

   Saida nayi zargin
hakan gareshi tunda naga ya fara shiga manya yana sana,a nayi mai gudun irin
hakan don mutanen mu ba kyau zuciya garesu ba yanzu.

   Kazo kai magana
kuma sai a dauki hakan a bakin ciki kakewa mutum ai shiyasa banyi wanan maganan
ba tun farko.

   Hankalin Dije ya
kara tashi sosai tace malam Tanimu ai sai kayi magana tunda yaron nan yana jin
maganan ka kuma na kulla tun lokacin da akai sallah yanayin shi ya sauya idan
nayi magana saidai yace min ba komai.

    Kingani ba tun
wanan lokacin nasan aka harbeshi abin yana masa yawo a kai ke nan toni ina zan
san hakan ka tambayi mutum yace dakai babu komai aisai ka dauka kawai wani damuwace
na daban haka ?

    Duba ga yadda ya
kwallafa rai ga uwar garke yana fadin amana take garemu naso ace ya barta tunda
yanzu ba mallakin mu bace amma yaron nan yaki hakan  .

   Yanzu yau gashi ba
uwar garke ba Amadi din sai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya lokaci
guda hakan yasa shima malam tanimu din yin kuka ya mike ya yafita.

  Nan ta bar Dije din
tana sambatu da fadin wani lokacin shiyasa zama cikin talauci keda dadi son
hankalin ka a kwance yake baka taba kowa ba balle ka tsonewa mutane ido.

    Malam tanimu ko
yana fita ya samu makwabta yana fada masu cewa ai Amadin an rasa inda ya samu
kudi haka yake wandaka dasu har yake dauko wanan kayan da yake sana,a yanzu
lokaci guda haka ?

   Yaron da bai
maganin kwandala abin tausayi za aga yai kudi haka cikin lokaci guda ai hakan
nada ayah tambaya dama gaskiya.

   Mutum dayane yace
kai kada kuyi zargin hakan yaron nan kowa yasan mai nemane shi ko kwanaki ai na
ganshi yana yawon tallan gwajo a gari.

   Wanda ke wanan kowa
ya sani shi kuma yanzu zaku kawo wani zance na daban ku dora mashi shifa Allah
idan ya tashi azurta bawan shi dare dayane yakeyin ikon sa ga kowa da yaga
dama.

   Hakane kuma gaskiya
atoh ni dai shina gani indai wani abin na daban ne na yarda da wanan amma
zancen yayi halin da ba a sani ba wanan gaskiya ban yarda dashi ba ni kan.

   Jin hakan yasa kowa
kama bakin shi don gudun abinda zaije ya dawo a lokacin sai Allah ya kyauta da
suke fada suka watse aka bar malam tanimu shi daya da tagumi a wurin.

    Hakan bai masa ba
karshe ya mike ya shige cikin gidan shi hankalin shi duk a tashe sai faman sake
sake yakeyi a zuciyar shi shi kadai.

   Ga zance sai
juyashi ake faman yi a cikin gari kowa da irin abinda yake fada kan bacewan
Ahmed din wanan yasa har wasu coursemate dina sun fara kirana suna fada min
abubuwa daban daban kan yadda labarin yazo masu.

   Saidai na tayasu
jimamin abin don nima na gwada lamban Ahmed din baya shiga yafi a kirga abinda
kawai ya dan kwantar min da hankalina shind cewa da yayi gashi hanya zuwa wurin
mahaifinshi.

     Kwance take tayi
rub da ciki saman gadon alfarma dake dakin inda kafafuwanta suke dage tana dan
kadasu a hankali tana bin sakon nin waya a facebook dinta ga kida mai taushi
yana tashi cup din drink a gefen ta daya.

    Idontane ya sauka
a kan photon Ahmed din wanda yake tsaye a ranan gama karatunsu yasha kwalliya a
cikin shada da akaiwa dinkin samarin zamani madaidaici dashi inda hasken shi ya
firo fau yana murmushi don Manir dake daukan shi yana mai tsiya lokacin.

   Na cikin photon ta
kurawa ido kafin ta dawo ta fara karanta abinda aka rubuta kamar haka MASTER
NAMU  munyi missing din ka Allah ya
baiyana muna kai a cikin sallama.

   Allah ya tsare muna
kai a duk inda kake ka dawo garemu lafiya innalillahi ta fada kafinta fara bin
comments din yan group da kalman da kowa ke fadi a kanshi.

    Wurin mahaifiyan
ta ta nufa da wayan a hannunta tana fadin mama don Allah ki duba wanan kamar da
yasir da wanan guy din kamar tasuma har ya baci wallahi.

    Uwar bata daki
hakan yasa ta nufi falo inda ta samu mahaifiyan nasu zaune a falon tare da wata
yar uwansu da tazo gidan.

     Bata fasa fadin
abinda take fadin ba ta zauna kusa da uwar tana nuna mata photon cikin kaduwa
karba tayi tana fadin a ina yasir ya dauki wanan photon haka kamar bukin yayye
dalibai akeyi ai nan ?

   Mommy ki duba da
kyau ba yasir bane fa kamane kawai wallahi wanan sunan shi Ahmed wai ya bata
yau kwana uku ke nan ba a san inda yake ba.

  Wanan din uwar ta
fada tana kara kallon fuskan yaron sosai tace duba min nan tasallah wanan kaman
yayi yawa da yasir din gidan ya Yusuf din Jimeta.

    Wayan ta karba
wace aka kira da Tasallah din tana kallo tace wanan yasir ne mana ku duba da
kyau kugani mana bashi bane wallahi gwaggo wanan wanine ya bata ne wai ba a
ganshi ba yau kwana uku ke nan akace.

     Wai ana kama a
duniyan nan wanan  ai idan sun ga yasir
sai su dauka cewa dansune shi aiko zan turawa ya yasir da photon nan ya gani
shima nasan zaiga kaman su da wanan din.

  Ta mike zuwa dakinta
tabar iyayyen nata a zaune suna magana kan batan matashin da suka gani a
lokacin cikin wayar yar tasu.

   Itako tana komawa
daki ta canza network zuwa whtsf ta aika mashi da sallama kafin ta tura mai
photon matashin daga haka ta kashe data don taga baya online a lokacin.

     Tun safe muka
karya aka fara shirin tafiya inda har kowa zamu tafi a gidan sai Tabitha da
jennet ne kadai za a bari da Abban mu da zai biyo daga baya.

   A gabana mommy ta
bugawa ummah har da mama waya ina kwana biyar da zuwa abujan ta sanar dasu
zancen bukin kanin nata naji yadda ummah take mata fatan alheri da Allah sanya
albarka a auren.

    Hakama mama ba
laifi tayi mata Allah ya watse taro lafiya a sukayi sallama sama sama bandai
san ya suka karasa ba har gashi yau mun dauki hanya zamu tafi buki a garin
kanon dabo din.

    Tafiyan mota
mukayi don haka sai karfi shabiyu da rabi na rana muka isa kano din duk da na
taba zuwa tare da ummah amma bai hana in kalli garin ba.

    Bana son tafiyan
mota mai nisa don nafi yin tafiya a jirgi tun tasowana haka yasa na jirgata a
tafiyan da kyat muka kai kano din don har na fara amai a mota koda muka kai a
wahace na iya fitowa wuri na samu na kwanta don yadda nake ganin wuri a lokacin
ba zance ga tsarin gidan da muka tafi ba din.

    Barci na samu nayi
sosai a dakin da aka saukeni har wani lokaci don sai hudu na iya tashi nayi
sallah a lokacin.

   Bayan na sallamene
aka kawo min abinci na dan taba kadan na koma na kwanta don duk jikina banjin
karfin shi mommy ta shigo dakin ta kalli abincin take fadin.

   Wanan dan abincin
da aka zuba maki zahra kin kasa cinyeshi duk kada fa hakan yaja maki matsala
ace tun karin safe ke a cikin mutum gashi kuma har amai kinyi dazun a hanya.

   Wace suka shigo
dakin da mommy dinne tace bata da lafiyane dama tun a gida tace wallahi lafiyan
ta kalau ban san meyasa hakan ba.

   Kinsan wasu hakane
tafiya bai karbesu ba saisuyi ta tafiya wahala a hanya da kyat na bude baki ina
fadin bana tafiya mai nisa haka a mota sai a jirgi .

    Toow kinji abinda
yajawa yarki ciwo ashe dayan matar ta fada dama saida daddyn ku ya fada min baki
taba tafiya mai nisa haka ba ai a mota shima yayi korafi kafin mu taso din zuwa
nan.

   Ba yadda zamuyine
don kaya da muka dauko dolene mu biyo mota din zuwa nan don nima bana son  tafiya mai nisa haka sun juya sun fita zuwa
magariba ina idar da sallah naga mutane suna zuwa gaidani .

   Wai ashe wanan
matarce take masu labarin cewa wai sabida gata anyi tafiya dani a mota nake
kwance ina wahala tun zuwan mu.

   Wata mai yawan
surutuce da tashigo take fadin yarinya yi abinki don gaskiya akwai kyau ga kuma
naira wanda baidane yake ganin haka wani abu kana da kudin ka a duniya meye ba
zakai ba yanzu don iyalinka.

  Nikan shirin
kwanciya nayi saiga mommy ta shigo tana fadin badai har zaki kwanta ba zahra ko
duk gajiyan hanyane haka har yanzu ?

   A,a mommy zan dai
kwantane don in tashi da wuri tace gashi kuma nazo kije ku gaisa da hjyn mu
yanzu don an dan rarage a dakin nata nace OK ina duban inda na aje hijabb dina
don sallah asuba.

  Hijjab din na dauko
na zumbula a jikina wanda yarufe min rigar barcin dake jikina lokacin tana gaba
ina biye da ita a baya har zuwa wani part dake daban da wanda muke.

    Muka shiga da
sallaman mu wa yanda ke cikin dakin suka juyo suna kallon mu su ukune sai
tsohuwan dake zaune tayi irin daurin tsofi din nan na da duk da darene tana
sanye da glass din ido a fuskanta a lokacin.

    Daidai kafatanta
na zube a kasa ina gaida mutanen dakin da naga yawan kaman su da mommy sosai a
idona don basai ka tambaya ba kasan yan uwan haihuwanta nesu.

    Suka amsa dayan ke
min ya jiki na amsa da naji sauki nagode kafin naji Mommy tace tau yaudai gaki
ga hjy a gabanki zahra.

    Kai na dago na
kalli tsohuwan nayi murmushi ina fadin ina wuni hjy mun sameku lafiya ya gida
ya taro lafiya kalau yar nan banda kafa ance kinzo ba lafiya.

    Ashe bakya tafiya
a mota haka mai tsawo ya jikin naki a raina nayi mamakin jin hakan daga bakuna
yadda maganan yayi saurin yaduwa a kunnen kowa lokaci guda haka.

  Mommyce ta tare da
cewa ai nayi arziki da fari da har aka yarda ta biyoni zuwa nan yadda yar nan
take yarso ba ita kadai ba duk yaran nasu yan gatane ai.

   Murmushi kawai nayi
ina gyara zama tare da fadin  zanje in
kwanta a sanyaye zakace sallone hakan idan ba kasan yadda nake magana ba dama
zaka zaci haka din.

  Au ai inace a nan
zan kwana da kawar tawa a ina kuka sauketane ta dago tana tambayan yar nata sai
mommy tace a dakina mana hjy can zatafi sakewa ai a, a kunyi yawa a dakin ina a
nan su hauwa zasu sauka suma idan sunzo ?

   Ku barsu nan ita da
wanan sarkin laudin su zauna tare dani a kuryana ai zaifi a lalai yar nan kinci
da fari tunda har hjy yau ta bukaci bakuntan ki a dakin nan

Leave a Reply

Back to top button