TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 15

Sponsored Links

 

 

DARI BIYAR DARI BIYAR KACAL YAR UWA 👌KADA KI BARI
RASHIN BIYA YAJA MAKI WAHALA, , , ,

 

Suna fita part din mu suka hade da Aisha wace ta kara biyo
sawun su kabir ne yace waitin you come do here amebo ?

  Stop calling me that
yeye name i tell you say i no want that name amebo you na de call me with it!

    Nobe amebo you
come do ? why you de follow us like small kids any where we go har suka shiga
part din mama suna fada haka dashi.

   Mama wace bata son
ran diyanta ya baci ta kasa boye bacin ranta a zuciyarta ta hau Aisha da fada
haka yaja ran hjy Rafat baci don tasan halin mama irin wanan wajen don bata
kaunan ran yaranta ya baci sam.

  Saidai duk abinda
sukai maka kayi hakkuri amma idan kace zaka rama a gabanta zaku samu matsala da
ita duk yadda kuke kuwa da ita.

   Don mama irin matan
nan ne masu ririta diyan cikin su fiye da komai a duniya kema uban wa yace ki
bisune bayan kinsan halin kabir sarai ba kyaleki zaiyi ba.

   Hjy Rafat tace
kabir kasan uwarsu bata son a taba mata yara don gudun irin hakane fa banso ka
biyomu ba kanace sai kazo arewa kaima ka gani.

  Gashi ance kunje
part dincan kun tare har kuna cin abinci tare da zarah a plate daya da ita
kallon Rukkaiya yayi yace mama shiyasa nace yaran nan naku munafukaine wallahi.

   Ni sun sani sun san
halina idan yarinya ta kawo min raini yanzun za ajimu da ita ba ruwana da wai
maman jafar bata son ayi masu mussu yanzu zanwa yarinya one below seven die.

    Ganin abin zai iya
kawo masu matsala don tasan halin kabir sosai baida kunya ko tsoro irin roget
din lagos dinan ne shi don ko kallon shi kayi zaka fahinci koshi waye don
kanshi ya tara wani irin suma hakama kayan jikin shi irin na shegun Lagos ne
yake sakawa.

   Sabanin dan uwanshi
da ba ruwan shi shiru shiru yake shi ko halin irin na yayan farine ke binshi
oho mama din ne tace mai ai ina ganin kaikan kabir wurin damben kokuwa zamu
kaika kawai turai mu huta da haka suka wasance wanan zancen.

    Da suka kebe da
uwar tasuce take kara masu fada take fadin kai Dele ka cire ranka ga yarsu don
komai ya kara rikicewa yanzu gidan nan ga baki daya don dukkan ku nan kunsan
halin mami jafar ta tsani wa yan nan mutane sosai.

   Ba zata taba yarda
a hada ka da zarah ba yanzu ma kokarin hadaka da yarta Aisha naga tanayi bayan
ta sani sarai zarah din kakeso ba Aisha ba.

   Duban uwar yayi ya
nuna kanshi yace wani mama na auri wanan yaran da basu da tarbiya ko kadan
nerve kada ki soma wanan zancen dani don ni zarah nace ina so tun tana karamar
ta.

   Ba zaka auri zarah ba na fadama kada ka bata
min zumuncina da kawata kan wanan bukatab naka don haka ka duba tsakanin Aisha
da Rukkaiya ka zabi daya.

   Ohh really mum da
baki kinki ke fada min haka yau baya
kinsan iri  son da nakewa yarinyar
nan zarah a raina ?

    So so suma zaka so
su ai idan ka zabi daya daga cikin su OK ya fada ya mike ya fito daga dakin kai
tsaye haraban gidan namu  ya nufa tsaye
yayi wuri daya idanun shi a rufe kafin yaji motsi ya bude idanun nasa.

   Nice a duke wurin
motana ina daukan abu sai kanwata karama dake gefena tsaye tana surutu kusan
kamarmu daya da yarinyar na dago ina rufe motar tare da riko hannun yarinyar
muna shirin barin wurin da takardun dana dauko a hannuna daga cikin motar.

   Takowa yayi zuwa
inda naken ganin shi ya dan sani kaduwa lokaci guda zan iya cewa wanan ne ganin
murmushi a fuskanshivtun zuwan su gusau din na
da sukayi.

   Hannun yarinyar ya
riko yana fadin meye sunanta kafin in fadi ta amsa mai da yusurah ya dan rage
tsawo yana fadin sunan ki nada dadi sosai.

   Kafin ya dago yana
kallona tare da fadin nice name naso su yarda muyi aure amma saboda maman jafar
hakan ba zai samu ba a tsakanin mu.

   They are telling me
now wai na zabi Aisha ko Rukkaiya na aure mamadin ke ni kuma zuciyana ke yake
so zarah ba suba don su din ba zabina bane zabin su mami ne hakan.

   Gobe zan koma da
safe in sha Allahu ina son ki dauki layina a wayan ki don ina son muyi zumuci a
tsakanin mu har yayan mu nidake saboda kada alakanmu dake ya yanke.

  Duk wani abinda ya
sameki don Allah zarah na rokeki kirani zarah muddin ina raye ba zan taba barin
ki wahala ba yadda suke nufi a duniyan.

  Idan sun hanani
auren ki ba zasu hani zumunci dake ba na sani don ba zasu taba sanin ina
taimakoki ba wanan alkwari haka nayi maki zarah.

   Ki natsu kimaida
hankali ga karatun ki don ki zama wani abu a cikin rayuwan ki yadda zaki
taimaki mahaifiyar ki da yan uwanki nan gaba ina maki fatan alheri a rayuwan ki
don sun rabani dake yanzu.

   Ki mi  alkawarin zaki cika min burina na taimakonki
a kaina nan gaba don ba karamin shiri akewa rayuwan ki ba zarah shine dalilin
da basu son kasancewana tare dake a yanzu na gama fahintar komai daga garesu.

    Saidai basu san
cewa kedin kinci sunan ki na Zarah ba kin daga sama fiye da diyan da suke son
su dago din na barki lafiya sai in Allah ya kaddari haduwan mu ya miko min
katin wayan shi da address din shi na dago ido da hawayen daya fara sauko min a
idona ina kallon shi.

    Suka zubo lokaci
daya dan murmushin yake da baikai ciki ba ya sauke a fuskanshi yana fadin don’t
worry take care kada ki bari su san muna tare ina taimakon ki.

   Daga haka ya sake
hannun yusura yana fadin bye ya tafi na bishi da kallon mamaki har ya shige
inda dakunan samarin gidan suke inda a can ne aka saukesu suma.

    Cikin wani irin
yanayi na shiga gida Allah ya taimaka ummah bata falo na samu daman shigewa
ciki na fada saman gado ina sake hawaye masu yawa.

   Ban taba soba ban
kuma fara ba saidai kalama brother Dele din sun tsaya min a raina sosai don na
kasa raba dayan biyun kan abinda yake kokarin son in fahinta daga zancen shi
din .

   Washegari hargowan
su mamane ya tayat damu daga barci wai Dele ya bace tun asubahi an nemeshi a
rasa kuma ya tafi da kayan shi bai fadawa kowa inda zai tafi ba.

   Dole ba shiri suka
shirya tafiya suma a ranan da cewa zasubi bayanshi don me yuyuwa ya koma
lagosne ya barsu nan su zaman me zata zauna yi a garin mutane bata san halinda
dan yake ciki ba .

   Dole muka fito
wajen nasu da zasu tafi ita da drivern su da danta kabir mama sai waya take
faman yi da Abba tana sanar mashi halinda ake ciki.

   Abbah din a karshe
yace su tafi da mama suzo nan sokoto subi jirgi zuwa lagos inyaso sai driver ya
koma da motarsu shi a nan mama ke zage zage tana fadin akan wata yarinyar banza
can yaro yana neman halaka kanshi.

    Duk wanda ke wajen
zai fahinci a fakaice mama ke sake magana da wani a wurin duk da bata fito fili
ta ambaci sunan wanda takeyi dashi ba wurin amma kowa ya gane hakan.

   Kara lafewa nayi
jikin motan danake tsaye kusa da ummah da itama ido ta zubawa mama dake faman
sakin magana a cikin habaici irin na kwararu iya habaici.

    Cikin gida suka
kwasa suka koma suka barmu a tsaye waje yayin da yaranta ma suka mara mata baya
lokacin guda kabir ne daga inda yake tsaye yana magana da drivern su ya tako
zuwa inda nake tsaye ina rike da hannun yusura.

   Baby kema kin
damune don nasan ya fada maki komai jiya ai don na fito na biyo bayan shi na
sameku tare saina koma ciki.

   Amma kada ki damu
fa ban fadawa kowa hakan ba do  kada na
jefaki cikin matsala irin nasu maman jafar gaskiya zan fada maki matan nan bata
son ki keda maman ki.

   Ta sani sarai
brother Dele ke yakeso kamar yayi hauka amma yanzu munzo kan zancen ku ta dauko
zancen hadi da yarta ta kawo mashi shine dalilin da yayi fushi ya tafi ya barmu
nan.

   Amma kinsa da ace
nine yau da sun gane basu da wayau a garin nan amma shi yana da sanyin hali
sosai kinga ya tafi ya barmu a na  ita
mami tasan halinshi idan yai zuciya zai iya barin kasa  nan ga baki daya yanzu haka shiyasa kikaga
sun tayar da hankalinsu haka.

   Ummah ce ta juyo
inda nake tana fadin dauki Yusura mu koma ciki ta kalli kabir tana fadin Allah
ya kaisu lafiya ya amsa da amin nima kallonshi nayi ya rigani fadin ban layinki
sai mu djnga gaisawa.

  Na karanto mai
number na yayi serving mukayi sai watarana na juya na shiga vida don ummah har
ta shige ko a lokacin ita.

   A falo na samu
ummah zaune ranta a bace sai hankalina ya tashi sosai ganin yanayin ta kallona
tayi tana fadin maamah zoki zauna kuma ki fada min gaskiya don banson karya kin
sani.

   Wallahi umma zan
fada idan abinda na sanine zaki tambayeni a kanshi tace dakyau me kika sani
game da tafiyan yaron nan kuma meye hadin ki dasu ?

   Ummah ni babu komai
a tsakanin mu ku ban san komai a kantafiyan shi ba sai jiya daine yake ce min
na kawo duk yadda mukayi dasu tundaga farko har wanan maganan da kabir ya fada
min a waje na fada mata komai.

   Oh wanan dama take
kullawa naso in fahinci hakan amma sai na dauka kawai hakan shakuwane a
tsakanin ku amma ai ita hjy mama din tayi kuskure tunda ta mata da Allah ke
komai ga bawanshi.

    Idan shi Dele din
ya kasance mijinki ita bata isa ta hana hakan ba sai anyi balle ban fatan hakan
a gareki a samu abin fadi cewa kin kwaso bare kabila kin kawowa yan uwa.

   Ita zata hada ita
kuma zata dawo tana kulla sheri a cikin dangin ki don a samu abin zagi da
barnan suna a garemu ni fatana kullun shine ubangiji Allah ya baki miji mai
albarka mai mutunci da sanin ya kamata ba tarana arziki ko kwadayin duniya ba
maamah.

   A, a ki natsu kiyi
karatun ki don gaskiya Dale ya fada maki nan gaba dakene zan fara alfahari a
cikin gidan nan shine dalilin maman ku nason dakushe rayuwan ki kota halin
kaka.

  Ummah me nayiwa mama
haka yanzu take jin haushina ba yanzu ba kawai tun haihuwan ki take jin haushin
ki maamah  bado  komai ba kuma don kawai kin kasace yar
kishiyanta da bata kauna wace tafi tsana yanzu a duniya.

   Ummah kin mata wani
abune haka me kuwa nayi mata idan ma yine itace tayi mun tunda a gidan nan tazo
ta sameni ban daki zafi da ita ba akan mijina sai itace zata dauki zafi dani
daku har yakai yanzun bata kaunar taga mun rabi Alh ko kadan.

      Tanice ta shigo
falon jiki a sanyaye tana fadin sun tafi har da hjy maimuna wai tare zasu haka
ya dace dama ummah ta fada kafin tani din ta sake fadin amma hjy ta fada maki
zasu tafine ?

   Allah dai ya tsare
hanya yasa su ganshi a can din shine fatan mu yanzu mu don hakan ba karamin
tashin hankali bane tunda ba a san halinda yaron ke ciki ba yanzu duk inda
yake.

  To wai ina zashine
ko ya taba zuwa arewane dama ni shi nakewa mamakin inda yaje ga hjy kuma sai
wani zance takeyi a dunkule wai daman haka akeso dasu aga bayansu,  towa ke son ganin bayan nasu take nufi ?

    Wai Amadi kasan
dabbobin nan ganinka yasa suke wanan kukan haka toke Dije ba kuna wuni gida dasu
ba ko wani lokaci suna ganin ki ni kuma sai wanan lokacin idan na shigo.

   Haba dai wani sabon
abu dai suka samu hakan gashi uwargarke gabadaya tun dawowanta gidan nan sam
ban gane mata abubuwa takeyi yanzu dabo dabo kamar , , , ,

   Shiru tayi domin
idon ta daya sauka kan uwargarke irin kallon mutum uwar garken kemata a take
taji tsikan jikinta ya tashi lokaci guda sai gabata ya dinga faduwa.

  Mikewa tayi tana
fadin innahu sulaimana wa innahu bissimillahi rahamanin rahim Amadi nikan nayi
nan idan ka gama ka sameni a daki ta fada ta wuce sa sauri zuwa dakin nata tana
sake labulen kofan da sauri.

   Ranan abinda bai
taba faruwa ga Dije ba shine ya faru don Dije ta kwana a wahalce tana mugun
mafalki da tsoro a zuciyar ta har gari ya waye kiran sallah asalatu a kunnenta
tafito tayi alwala ta koma daki don sai ya kasance tana jin tsoron gidan nata a
ranan.

   Tana jin fitowa
jikan nata dafa dakin shi sai dai batayi yunkurin ta sake fitowa ba a lokacin a
inda tayi sallah ne barci ya dan dauke ta bata falkaba sai da gari ya haska ko
ina rana ya fara fitowa lokacin take jin motsin mutum a cikin gidan.

   A hankali ta mike
zuwa wajen bata yarda ta fito  gaba daya
daga dakin ba lekowa tayi daga ciki sai ta gango Amadi ne ke faman wanke kayan
sana,anshi yana shanyawa a rana.

  Hakan yasa ta fito
tana fadin a, a yau ba bokon ne ko ka daga kafan ga zuwane yau din yana buga
kayan dake hannunshi don su mike  yake
fadin .

    Akwai Dije kawai
na tsayane in wanke wa yan nan kayan daga nan sai in dan fita da wa yancan dana
kulle amma lafiya kika kwanta haka har wanan lokacin.

   Kai dai bari saita
daga ido ta kalli garken dabbonin ta kuri idon uwar garke a kanta hakan yasa
tace munaga rasulu Annabi sidi farin gani mazon Allah.

  Shiru tayi har yaje
yayi shanyi ya dawo yanayin da yaga Dije din acikine ya daga mai hankali yake
tambayan ta wai kuwa yau lafiya kike Dije ?

   Lafiyata kalau
barin dan je nan makwanbta tunda kana gida na samo muna dan kamu nazo in kashe
muna kunu yau a gidan mu karya dashi.

    Idan da saura ki gyara
kawai Dije ba sai kin wahalal da kanki ba ai kayyah yau ban jin cin tuwon kunun
dai nafi son insha yau tana fadin hakan ya tura hannu cikin wandon dake jikin
shi yana lalubo kudi ya dauko dari biyu ya mika mata.

  Tace barshi akwai
canjin jiya daka ban suna nan banyi komai dashi ba zan sayo dasu ta fice da
sauri daga gidan yaci gaba da wankin shi.

    Wandunan daya
dauko zai tsoma a ruwa a daidai lokacin uwar garke ta aza wani kuka dayasa ya
kallota inda take din ya tsame hannun shi ya nufi wuri  su yana jaye masu igiyar da suka harde dashi
ya kara masu abinci da ruwa duk lokaci guda ya juya ya koma wurin wankin nasa
wandon ya kara dauko wa ta sake wanan kukan nata irin na farko.

    Zai aje wandon
hannun shi yakai daidai aljihun wandon yaji abu da dan karfi a ciki ya tura
hannu a cikin wallet irin na maza mai kyau ya zaro a cikin wandon .

  Cikin mamaki yake
kallon wallet din kuka sosai uwar garken tayi ya juya ya kalleta sai yaga ta
koma ta kwanta lokaci guda hankalin shi ya mayar kan wallet din ya dauraye
hannayen shi ya fara budan wallet din.

   Kudine a ciki irin
na kasan waje da sai a photo yake ganin su sune a hannun shi ya ciro da sauri
yana duba kudine masu yawa sun kai guda goma a ciki sai dan katin sheda dake da
rubutun wani address din kasan waje
sunan maishi da lamban wayan maishi a cikin katin.

   Ya karanta
wana  address din yafi a kirga kafin ya
aje wandon a gefe daya tare da mayar da kudin yadda ya gansu ciki yaci gaba da
wanke sauran kayan yana dubawa.

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA AHH, HAYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃👠👜💍👡👛  🥿👘👗🧤

Leave a Reply

Back to top button