Hausa Hip HopLatest Musics

[Music] Mr 442 ft. Murja Ibrahim – Yaga Yaga Mehn

Sponsored Links

Yaga Yaga Mehn
Duniya juyi-juyi, daga barbadancin tiktok yau kuma Murja ta yi juyi wanda yafi juyin juya hali ta koma waka.

Hoh! Ina daukacin masoyan Murja Ibrahim Kunya? Mutuniyar fa ta takarkare ta suburbudo muku sabuwar waka ita da mawakin Hausa Hip Hop, Mr 442.

Mr 442 mawaki shugaban tawagar Dream Chasers Record tare da Murja Ibrahim sun saki sabuwar wakarsu mai taken, “Yaga Yaga Mehn” (mp3 download).

Ban dai samu nutsuwar sauraron wakar nan ba amma dai kai da ji an sako murja ka san wakar za ta matukar nishadantar.

Wannan ce wakar Murja Ibrahim Kunya ta farko, za ku iya sauketa, ku saurareta sannan ku yi sharhi a kanta.

Leave a Reply

Back to top button