Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 90

Sponsored Links

90
Idanuwan Ababa Basu gama budewa ba aka jefasa cikin Wani daki me masifaffen duhu da baka ganin komai se dai Kaji murya.

Zare idanuwansa ya fara Yana Neman ganin inda zaiga Dan haske komai qanqantarsa Amma babu cikin murya Mai tsananin bacin ran gaske DD ya sake jefa masa tambayar ya Akai yasan Safnah??

Rawar baki ya fara zaiyi magana yaji saukan Wani masifaffen Marin bayan hannun qato daya sakasa kifewa qasa kunnuwansa na dauke ji diff.

Rarrafawa ya fara Yana Neman inda zai dafa ya tashi aka sake jeho masa wata tambayar wadda kunnuwansa dasuke dauke ji Basu ji ba Dan haka ba amsa take aka sake kifa masa Wani Marin Daya dawo da jinsa take cikin gigicewa da murya me qarfin gaske yace

“yata ce nine na haifeta…

Shiru gurin ya dauka dukkaninsu shiru sukai musamman DD Daya kasa fahimtan me zancen ke nufi,
Shi Kansa dd babba dake kan waya Yana Jin komai sbd yace Sir Ashir bello ya barsa Yana buqatan Jin komai.

Shaqosa officer din yayi cikin qarfi da rashin Imani yace

“Wacece yar taka??
Safnah bulama ake magana.

Shaqar data kusan raba Ababan da numfashinsa yasanyi shi kusan sakin fitsari Yana bubbuga hannun dake wuyansa sai Daya kusa mutuwa officer din ya sakesa lokacin Naseer ya shigo dakin sanyeda glasses din dake saka suna Gani cikin hudun ya kama Ababa ya daga sama tareda mannasa da bango a karon karshe ya sake tambayar gaskiyar Safnah da inda Bena take.

Yana Jin muryansa Naseer ya Bude bakinsa da muryarsa ta shaqe sbd wuyansa Dasha shaqa be dawo daidai ba yace

“Nine na haifi Safnah basheer bulama,
Safnah da Benazir uwarsa Daya ubansu Daya wllahi,
Nine na haifesu duka Kuma Annen Benazir ce ta haifesu duka,
Su hudu ne, Sumayyah,sameerah, Bena da Safnah”

Kallan DD sukai dukkaninsu sbd zuwa lokacin kan kowa ya sake daurewa,
Ababa yace shine ya haifi Safnah,to Kuma Safnah a matsayin ‘yar basheer bulama aka Santa.

dd babba ne yayi shiru cikin zurfafa tinanin tabbas Anne ta sanar dashi yayanta hudu, Sumayyah, sameerah, Bena da Safnah.,

Safnah itace wadda ta gudu tabar gida,
Safnah itace yar Anne Ababa yake nufi kenan?
Safnah da Bena suna auren miji Daya kenan ko me??

Dukan wahala Naseer dake cikeda takaicinsa sukaiwa Ababa shida officer din Amma still Abu Daya yake fada cewan shine ya asalin uban Safnah ba bulama ba.

Ganin taurin ransa yayi yawa ya saka su Basa Daman kawo shedan dayace zai kawo akan Hakan.

Ta bangare Daya kuwa takardarsu suketa Jira cikin matsuwa ta dawo ta email dinsu sbd su kame Safnah wadda sunancan Suma cikin matsananciyar tashin hankalin rashin ganin Ababa da inda yake ga labarin gidansa Daya Kone kurmus ya sakasu sake shiga baqin ciki sbd sunso ne a kamasa da wainnan qwayoyin a gidansa.

Da motar office aka tafi da Ababa har shagon wankinsa inda ya boye jakar kayansa da komai Daya dauka na tafiya porthacort.

Ciro kayan yayi aka karba ana kokarin budewa yaga hankalinsu na Kai ya juya da matsanancin gudu zai tsare cikin rashin wasa da lamarin ba Bata lokaci aka harbe qarasa Daya wadda Bata karye dinba take ya zube a gurin Yana zunduma Wani mummunan ihun azabar daya sakasa somewa take jini na zuba sosai a qafar.

Kaman yankakken rago haka aka washesa aka saka mota Akai asibiti dashi.

Ana zuwa Asibiti bayan ana karbesa anyi ciki dashi bullet akwai aka buqaci Asibitin ta cire a nadesa hakanan a dawo musu dashi suka tafi aka barsa da jamian tsaro biyu suyi gadinsa.

A can office bayan an Bude komai na kayan Ababan anan aka samu duka Wani Abinda Daya saka DD kasa tsayuwa Saida Naseer yayi saurin tareda aka kawo masa kujera ya zauna ana qarawa AC din office din qarfi sbd Bai taba Gani ko Jin tashin hankali ba a ruyuwarsa irin wannan,

Shine duk acikin irin wannan abubuwan da Bai taba ji ba ko a labarai,bare drama ko film sbd bayama kallansu,
Shine yake auren mata biyu dasuke uwa Daya Uba Daya.

Babban Abinda yake sake saka jikinsa daukan rawa da shiga matsanancin tashin hankali shine da mummunan qaddara ta sakasa Wani Abu ya shiga tsakaninsa da Safnah kafin Bena da Bena ana nufin ta haramta garesa kenan har abada???
Zai rabu da ita kenan bashi ba ita har abada??
Shikenan zata rabu dashi taje ta auri Wani namijin???…….Bai qarasa wannan mummunan tinanin ba zuciyarsa ta kasa dauka take numfashinsa ya fara daukewa Kansa na Neman tarwatsewa..

Da sauri akayo Kansa Amma kafin kowane motsi tini ya fice hayyacinsa sbd balain yayi masa yawa da masifa yake ya rasa numfashinsa dole aka kwashesa zuwa Asibiti.

Naseer ma dole yabarwa Abbakar harkar hukumar shikuma ya koma jinyar ubangidansa.

Kafin takardarsu ta dawo daga office Nan suka kira Alh basheer bulama Kai tsaye suka buqaci ganinsa batareda Yi masa Dan taqaitaccen bayanin Abinda yake faruwa.

Shima acan take jininsa yayi mummunan Hawan da dole saida akai gaggawar Nemo likita ya dubasa sbd Dakar zuciyarsa da abin yayi.

Hankalin iyalin Alh basheer din ba qaramin tashi yayiba da halin Daya shiga Kuma cikin rashin sa’a Koda Akai masa Kiran Yana tareda matarsa Daya da me aikinta tana jera musu abincin a dining Dan haka komai a kunnen me aikin akaisa.

Tana ganin halinda Alh basheer din ya shiga ta silale ta koma dakinsu na masu aiki ta shige toilet ta kunna famfon ruwa ta fidda waya ta Nemo numbern momy datake Aiki gidan sbd ita Dan kawai sbd ita,
Tin jiya momyn ke kirana akan idan taga zuwan baqo gidan kowane iri ne gurin Alh basheer bulama ta sanar make dan ta tanadi wainda zasu kawar mata da Ababan Yana Isa batareda ya isar da Abinda yaje fada ba.

Ganin babu baqon dayazo sai Kuma ga wannan mugun sakon wayar ya saka shahida me aikin Kiran momy cikin bayani a natse Dalla dalla tayiwa momy bayanin Kiran da Kuma Abinda akace ankama ‘yarsa ta bogi Safnah bulama dashi wato wasu qwayoyin.

Shiru momy tayi wadda sukafi kwanaki nawa Basu rintsaba sbd tashin hankali da baqin ciki me tsananin gaske tareda rashin sanin madafa.

Kashe wayar shahida momy tayi tana miqewa daga zaunen datake bakin gado shiru tafara kaida kawo hannuwanta na tsananin rawa kaman yanda zuciyarta ke harbawa da matsanancin tashin hankalin da baa saka masa raba ba.

Idan yanda Shahida ta fada ne ance Safnah bulama kawai ne ita baa ambaci sunanta ba Hakan na nufin baa San da itaba aciki ne kokum lissafin be zo kanta bane…

Ta faru ta qare musu kenan,
Yau rana ta batar musu.
Wace qaddararriyar masifar ce ta kaisu Sako Ababa a rayuwarsu suna komai a tsanake hankali kwance yanzu komai ya lalace,

Jinin Rai na kisan mutum nawa ne a hannunsu?
Ita na hajiya Dana Rabi ne a hannunta saina Wanda ta taba yi a bayan aurenta da bulama ya mutu.,

Safnah kuwa jinin ran Wanda tafara kashewa na farko shine Wanda bayan barinta gida ya kamata yaso yimata fyade ta kashesa har lahira Wanda akan Hakan momyn ta hadu da ita ta taimaka mata suka boye gawar daganan suka zama uwa da ‘ya,
Sai Kuma jinin Hande da itace ta kasheta tinda itace ta dura mata qwayoyin a baki.

Idan har baa ambaci sunanta ba to tabbas nata asirin da sauransa Dan haka bazata sanar da Safnah ba silalewa zatayi ta gudu kafin Azo kamasu tabar Safnah a sameta ita Daya.

Sauran qwayoyin karshe dasuka rage musu ta dauko jikinta na tsananin rawa zata Bude ta zubasu a bakinta tashanye itama ta shiga mummunan halinda zaa dauka Safnah durata mata itama tayi Dan ta kasheta idan yaso kafin ta warke dai lokaci yaja case din ya mutu ita ta tsira.

Harta zuba a bakinta taji Bazata iyaba tayi saurin fito dashi tana gobe bakinta ta mayar dashi leda ta jefar tsakiyar dakin tana shiga Sabon tashin hankalin Neman mafita Dan haka gwara dai ta gudu inda zata tsira da rayuwarta.

Gurin drawer na aje kudinsu ta nufa ta Bude jikinta na wata irin rawa tahau diban kudi ta cika qatuwar handbag dinta babba ta dauki passport dinta ta saka tareda sauran id cards nata.

Tana fitowa Safnah dake dakin itama nata idanuwan kaman na Panda duk sun fito sunyi baki sbd tashin hankali da rashin rintsawa ta fito sukai Karo a palon.

Kallan juna sukai ta kalli momyn a tsanake itama momyn ita ta kalla tana boye tashin hankalinta ta kalleta tana Dan bayyanarda kulawa tace

“Bari naje na dawo yanzun Nan nayi Miki bayanin Wani abin mamakin kiji.”

Gaba tayi tana Hana yanayinta bayyana.

Harta fice Safnah batace mata komaiba sai jakar hannunta data hango kudi masu tarin yawa aciki musamman daloli.

Mamaki ne ya kamata Dan haka ta Bude dakin momyn ta shiga ta nufi inda suke ajiye kudi taga babu komai se yan canja,

Passport din momyn ta duba Bata gansa ba nata kawai ta Gani Dan haka ta sake shiga matsanancin mamaki da tashin hankali.

Juyawa tayi zata fice ta hango ledan robar qwayoyin dasukai amfani dasu tsakiyar dakin take ta fahimci akwai babban Abinda yake faruwa.

Fitowa tayi da sauri daga Palo ta nufi harabar gidan har momyn ta kusa ficewa da kota ta tsayar da ita ta qarasa gurinta tayi qasa da glass Safnah tace

“Momy nesa ne zakije??

Cikin girgiza Kai tace “aa yanzu fa zan dawo,Dana dawo zakiji komai fa.”

Jan motar tayi ta wuce Safnah ta bita da Kallo tana goge hannunta daga ledan qwayoyin data sakawa momyn bayan motarta batareda ta saniba.

Momyn na ficewa itama motarta ta dauka ta fito da sauri tabi bayan momyn.

Sun ficewa motacin jamiaan tsaro gudu uku suka iso gidan maigadi ne ya nuna musu motocin su Safnah dasuka fice yanzu Dan haka take suka bi bayansu Suma.

Hanyar barin gari momyn ta kaman tana kallan madubinta ta lura da motar Safnah dake binta Abaya.

Wani mummunan faduwan gaba da zufa ne ya keto mata sbd Safnah taci gaba da binta akwai babbar matsala zaa iya kamasu duka tare Dan haka suna sake ficewa daga mutane ta tsayar da motarta tana kallan motan Safnah datai parking bayanta.

Fitowa mota Safnah tayi cikin tsananin baqin ciki da takaici tareda tafasan zuciya sbd har lokacin ta kasa Gane me momyn ke Shirin aikatawa.

Tana tahowa momy sai dataga ta fito motar ta nufota kafin tayi gaba kadan da motarta tayo reverse cikin Wani mummunan gudu ta taka Safnah din da motarta Bata tsayaba ta buga da mugun speed tayi gaba tana Hawa titi sosai da gudu.

Cikin mummunan yanayi na karywar qafarta Daya da fita fit a take jamian tsaron suka iso kan Safnah wadda ke cikin halin Rai ko mutuwa Dan hatta fuskar kusan tayi dameji suka kwasheta sauran motacin kuwa suka bi bayan momy.

Asibitin da aka Kai Ababa Wanda tini Shima gurin cire bullet an qarasa lalata qafar acan aka kaita itama da qafarta Daya Bata hayyacinta sbd fuskarta datai damage.

Momy gudu takeyi sosai tana qarawa hankalinta na tashi tana waya da qaninta dazai Siya mata ticket a Daren ta wuce Lagos daganan zata Bema visa tabar qasar gaba Daya.

Checking point na sojoji ne suka tsayar da ita ganin yanda take gudu sosai tana mace.

Jakar kudin dake qarqashin qafafunta suka fara gani take suka buqaci tayi parking.

Parking tayi tana Dan kame kame tana murmushin karfin hali kafin tafara magana saiga ledan qwayoyin abayan motarta.

Koda jamian dasuka biyo motarta suka iso gabaki Daya kamanninta sun sauya daga hannun sojojin Dan haka take case dinta ya girmama aka fara daukanta hotina mutane ana korarsu sbd harda bindiga a Jakarta.

Kamata Akai babu tausayin halinda take ciki da mummunan dukan datasha da kan bindiga a hannun sojojin aka saka mota ko tafiya Basu fara ba itama ta sume kaman matacciya hancinta da bakinta suna jini hakama idonta Daya ya tsiyaye.

Same Asibitin itama aka kaita inda su Ababa da Safnah suke babu Wanda yasan inda Kansa yake haka itama aka Bata gadon batasan inda kanta yakeba jininta na tsiyayewa.
saisun farka su samu Daman karban hukuncinsu.
##MAMUH#

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Leave a Reply

Back to top button