Canjin Kudi: Kada Ku Mayar da ‘Yan Najeriya ‘Yan Iska – Atiku Abubakar Ga FG
Dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shaida wa Gwamnatin Tarayya cewa kada ta bari a mayar da ‘yan Najeriya ‘yan baranda “a yakin da ake yi na gani-kasheni kan sake fasalin Naira.
Mista Atiku ya yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da masu taimaka masa kan harkokin yada labarai suka fitar a Abuja ranar Talata.
Ya ce ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ganin cewa bankunan kasuwanci ba su sanya kansu cikin tarnaki ba wajen dagula kyakkyawar manufar sauya fasalin Naira daga kyakkyawa zuwa mummuna.
“Abin yabawa ne yadda Gwamnatin Tarayya ta gwammace ta yi aiki a bayan fage, bisa ga bayanan sirri da ake kyautata zaton ta samu, dangane da zargin da ake yi na cewa wasu ‘yan takarar shugaban kasa sun yi boye biliyoyin Naira domin sayen kuri’u.’ ‘
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya koka kan yadda ake samun tashin hankali a fadin kasar, sakamakon rashin aiwatar da manufofin sauya fasalin Naira da bankunan kasuwanci a kasar ke yi.
“Kasuwanci da ’yan kasuwa masu dogaro da kuɗaɗe duk suna cikin mawuyacin hali a halin yanzu. Ya kamata a magance wannan cikin gaggawa domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa”.
Mista Atiku ya ce, a ranar 28 ga watan Janairu, ya taka muhimmiyar rawa wajen sake fasalin kudin Naira, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma babban bankin kasar CBN, da su tsawaita wa’adin ranar daina karba tsohuwar Naira, domin magance kalubalen da jama’a ke fuskanta.
Ya kuma kara da cewa, ana gudanar da manufofin ba kamar yadda aka samu a wasu sassan duniya ba, inda aka aiwatar da irin wadannan manufofi.
A cewarsa, miliyoyin ‘yan Najeriya ne ke jefa su cikin matsanancin halin kaka-nika-yi da yanke kauna saboda gazawar da aka samu wajen sakin sabuwar Naira ta zagaya ta wadata.
“A ‘yan makonnin nan, abubuwa na kara tabarbarewa a fadin Najeriya, saboda rashin gudanar da tsarin sake fasalin tsarin Naira,” in ji mai fatan shugaban kasar.