Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 38

Sponsored Links

38-Shiru Malik yayi amma yana ji a ranshi, tabbas akwai matsala wanda yake bibiyar rayuwarshi ba karamin Sani yake da shi akan shi ba. Lumshe idanun shi yayi kafin ya buɗe. “Kasan me Elbashir?” Juyawa yayi yana kallon Malik. “Da fatan ba sharri zaka min ba?”. “kai dai baka da hakuri! Wanda yake bibiyata. Izuwa yanzu yasan ina barikin sojojii me yasa bai kawo min hari ba?” Kallon Malik yayi kafin ta ce mishi. “Me yiwa yana tsoron farmakin sojojin Keivroto ne? Me yiwa kuma yana son sai ka fita zai dauki matakin da ya dace!” Kawai bai san me yasa zuciyarshi taki yarda da Elbashir ba, gani yake kamar akwai hannunshi a cikin abin da yake faruwa, don haka ya mike tare da ɗaukar kayanshi yana faɗin. “Bari na fita cikin town na ga me zai faru?” Rike shi Elbashir yayi yana zaro idanu. “Baka da lafiya ne?” “Ras nake da lafiyar kawai jikina ne, yake bani fitatta shi ne karshen rikicin da yake faruwa!” “A’a Malik ba mafita ba ne, don Allah kayi hakuri ka bar fitar nan, kai Uba ne yanzu, ko dan Yaranka ka tuna da halin da Zainab take ciki ya zata ji idan ta kuma jin labarin wani abu ya same ka?”
“Zata ya min, amma bari na tafi dai!”
“Don Allah kada ka je, yau nake son fara amarcina don Allah kada ka bata min daren yau da tashin hankali.” Ware idanu Malik yayi yana kawai Elbashir duka. “Kai dan iska dama ajiyeta kayi kamar hoto?” “Hmmm kawai ban yarda da ita bane, amma yanzu naga duk abin da yake faruwa bata sani ba, shi ne nake son mu!”
“Ai kuwa kasan ba zan zauna a cikin gidan nan ba, Gara na fita.”
“Haba Malik”
Elbashir ya rike kafarshi, yana dariya.”wallahi baka barin gidan nan, haka kawai ka ja min masifa a wurin matarka da take can bata waye a kanta ba.”
“Tow uwar me zan maka?” “Ka zauna dai mu ta ganinka wannan ma arziki ne!”
“Kai bani zama a cikin gidan sabin aure, ku lalata min tsufa na.” Ya faɗa yana dariya, kusan don dole Malik ya hakura da fita. Amma a ranshi yana shirye da ya fitan, don haka ba tare da Elbashir ya sani ba, ya shirya wani fita na musamman, Cikin dare inda tare da wasu zakwakuran sojaji.

Abin da suka fara shi ne, bibiyar shiga da ficcen mutanen da suka ziyarci 3stars a cikin kasa da wata shida, a watanni shidar an raba shi gida uku, wata biyun farko. Sai wata biyun tsakiya, sai wata biyun ƙarshe. Sannan baki ɗaya, an ga mutanen da suka shige da ficce a unguwar kasancewar sojojin akwai masu kaifin basira, suka tattara kome, suka bar wurin da Malik. Wani abin mamaki sunyi bincike a daren har zuwa gari ya waye.. sannan suka mikawa Malik sakamakon da basu samu wani gansashen bincike ba. A lokacin ya kira Yasir Aswad da Zulfah ya basu aikin domin ya gama shirin fuskantar makiyin shi.
Su suka cigaba da binciken daki-daki da har inda aka yi abin, wanda akala xai dauki wani lokaci. A gefe guda kuwa Elbashir murza amarci yake babu ruwanshi, sanin haka yasa Malik yaki zaman gidan domin kada ya ga abin da zai dame shi. Kuma ko ba kome ya basu damar su sarara da junansu. Binciken da suke yi ne yafi daukar hankalin shi. Domin kuwa a cikin kwanakin da ake binciken nan. Da dare aka buga gidan Zulfah Allah yasa akwai yan sanda a kofar gidan, aka ajiye mata wani kwali a kofar. Ba ita ɗaya ba hatta yan sanda sun sha mamakin yadda aka kawo kwalin aka ajiye.

Hoton Zeeno da Yaranta aka saka alamar (×) da jar pen. Shiru tayi a lokacin ta kira Malik da Yasir ta gaya musu, kai tsaya headquarter yan sanda suka nufa, duk da dare yayi. Malik bai hana shi zuwa ba. Yaranshi guda Uku. Da matar shi da yake so kamar me? Hmmmm. Ya faɗa yakai sau ba adadi, yana kallon al’amarin kamar wasa, sai zaga cikin office din yake yana kara kallon hoton Yaran.
“Ku yi min hanyar magana da shugaban yan sandar Nigeria, ina son magana da shi.” “Yallabai zata yiwu barazana ce!”
“Barazana da rayuwar iyalina? Barazana da rayuwar Yarana? So kake na koma gefe nayi ta kallon abubuwan da suke faruwa kamar wasa? A hada min waya da shugaban yan sanda Nigeria, su rubayya tsaronsu kan iyalina idan ba haka ba.” Ya juya ya bar office din yan sanda.

Tabbas abun yana son shan kanshi, jifa daga kanshi zata fada kan Yaranshi. Kafin gari ya waye Yasir Aswad yayi magana an kara tsaurarra tsaro a asibitin domin halin da ake ciki. Lokacin da gari ya waye Malik ya fito da shirin zai fita Elbashir ya kalle shi. “Jiya da kafita baka dawo da wuri ba!”
“Matata da Yarana suna cikin hatsari!”
“Innalillahi wa inna illahirirajuun, kuma dai?” “Tow me zan ce maka? Matata da Yarana suna cikin hatsari ina fatan ka fahimta. Koma waye yake bibiyata idan na yi idanu biyu da shi, sai na aika shi lahira. Domin haukar shi da shirmenshi ya tsaya a kaina kawai!”
“Malik ka nutsu!”
“Taya zan nutsu! Me bibiyar rayuwata, yana can ya raba mana aiki. taya zan yi barci matata da Yarana suna cikin masifa! I will turn myself, shi kenan Yarana da Matata su samu yanci!”
“But why Malik!”
“Na hakura da kome, amma matata da Yarana bana son su fuskanci ƙaddarar da ma fuskanta, Ina son suyi rayuwar yanci da Mahaifiyarsu.”
“Tow Malik ya zayi kenan?”
Zama yayi ya lumshe idanunshi kafin yaƙ ce .
“Ban san me zanyi ba, kawai ina kan nazarin abin da zai yiwu ne ” “mu barwa Allah kome, mu ga abin da zai faru.” “Allah ya kawo min dauki” “Amin Ya Allah!” A cikin kwanakin nan, idan ka ga Malik sai ya baka tausayi, domin ya masifar laushi da shiga tashin hankali. Sannan damuwar tayi mishi yawa. Wanda yaja shi faduwa bai shirya ba, domin har kullum barazanar da ake mishi kara yawaita yake sosai, domin har an kai, an turo mishi da cewa.
*Likitocin da suke asibitin babu wanda ba zai min aiki domin kudi ba*
Lumshe idanunshi yayi, kafin ya mike tare da ɗaukar top dinshi ya fita, bai tsaya ko ina ba, sai tsohon gidan lauyan Babanshi. Gidan ya koma kango, babu kome a cikin gidan sai ciyawa, shiga yayi yana nufar cikin gidan. A bakin kofar tsakar gidan ya tsaya. Sakamakon hango mutum zaune da bakaken kaya, an juya mishi baya.
“Gani nan, free my family!”
★★★
Tun da ta farka, kusan bata da abokan hira sai Yaranta, idanunta yana kansu. Daukar wanda ya dan fi sauran girma tayi, tana kallonshi yadda yake kama da Malik. “Kuyi hakuri! Ni ce na raba ku da shi, na kuma kashe muku shi. Kada ku tsane ni don Allah.”
“Madam idan kin gama basu nonon, zamu mai dasu cikin wurin kwanciyarsu.”
“Tow!” Ta ajiye shi, tana me gyara mishi kwanciyarshi. Sannan ta dauki dayan ta rungume shi, tana shashekar kuka. Sannan ta ajiye shi ta dauki macen tana shafa fuskarta. Wani irin kaunar Yaran take ji. Haka ta fito a hankali ta nufi dakinta. Dake babu nisa da ward ɗinsu. A hanyar ta na komawa dakinta ne. Wata mata ta bangajeta. Har ta kusan faduwa. “Ke tinkiya baki gani ne?”
juyowa matar tayi, hannunta dauke da karamar wuka. Gyara tsayuwa tayi tana kallon matan, yadda ta nufota a shirye. Yasata kura mata idanu. Tana isowa, ta kai mata wukar da sauri ta goce matar ta fadi. Sake juyowa tayi a fusace ta kuma kauce mata, a karo na uku ne, ta koma asalin yar kunamarta, wato Xnoo, tana kawo mata wukar zata yanketa. Tayi maza ta rike hannun tare da murgud’a mata shi, sai da ya karye. “Da alamu turo ki,aka yi idan har nice ki gaya musu su shirya irinki, goma.” Ta karya hannun, sannan ta take kama kafa sai da ta targad’a yatsun.

Wani irin tsoro ne ya kama matar, “ki gaya musu. Ni ba kanwar lasa bace, ban yi wannan lalacewar ba” ta kai mata naushi a fuskarta, matar ta sume a wurin sai lokacin yan sanda suka karaso, a hankali ta jingina da bango. “Da fatan kina lafiya, ku kama matar ku tafi!”
“Lafiya lau,ita ce zaku duba domin ta suma. Kuyi magana da shugaban asibitin nan, a mai da min Yarana dakina.”
“Tow!”
Daga haka ta wuce dakinta, tana haki domin baki daya ta gaji, rabonta da ta motsa jini ta jima. Tun kafin Malik ya aureta. Yau kuwa tayi da hujja. Kafin ta gama hutawa, An dawo mata da Yaranta, tunda gansu, barci me nauyi ya dauke ta.

Washi gari yan sanda, suka zo tambayarta, ta fadi abin da ya faru. “Ban san me yasa ta farmake ni ba, amma kuma nasan ba mamaki daga Keivroto zata zo domin daga can ne, kawai abin da na sani haka kawai ba zata kawo min farmaki ba, sai da dalili meye dalilinta?”
Shiru suka yi, kafin suka ce mata. “Mun tambaye ta, amma har yau bata bamu amsa ba” shiru tayi kafin hawaye ya zubo mata, wato tun daga ranar da ta rabu da Malik bata cikin nutsuwa, yau gashi nan an fara bibiyarta.
“Ba mamaki suna haka ne, saboda abinda ya faru da mijina, ko nace don mijina suke bibiyar rayuwata. Amma bayan nan nasan bani da wata mummunan alaka da wani, sai ta alkhairi. ”
“Tow tace an turo su ne, domin an biya su iya adadin da zasu kashe ke ko Yaranki, sannan wannan abin da muka fahimta tana aiki ne anan don haka zamu mai da ki gida, ki cigaba da jinya a can saboda rayuwarku tana da muhimmanci!” Hawaye ya zubo mata, ta saka bayan hannu ta goge, tana faɗin. “Shi ma ba laifinshi bane, wasu suka daura shi a haka, da zasu fahimci yadda rayuwar shi take baza su tsane shi ba, babu ruwanshi kawai ƙaddara ce, don Allah su bar mishi Yaranshi, idan ta kama ni ce, su hukunta ni da abin da ya aikata na amince na yarda. Amma Yaranmu babu ruwansu.”
“A’a Madam, zamu duba al’amarin nan, ba zamu bar su, su bata mana gari ba domin yin haka kamar tozarta hukumar tsaro ne, don haka zamu mai da ki gida, ki cigaba da jinya”

Fita suka yi, bayan Ammyn sun hada mata kayanta, suka fita suna jimami. Ita kuwa kuka take, tana karawa kaunar yaran kamar me ya cika mata rai. Yanzu kalaman Malik ya dawo mata, dama yasan haka zai faru ne yasa shi cewa.
*Zan baku kome zan baku damar kome, amma ki sani ba zan tab’a cire idanu akan ku ba, ko ƙarƙashin ƙasa kuke. Idanuna sa zuciyata tana tare da ku. Kune Duniya ta, kune rayuwata, farincikin da nake yana tare da ku ne, amma zan hakura da nawa farincikin na baku kuyi, na barku Ku rayu cikin aminci da salama, na san kinyi fushi ne idan kika yi sanyi zaki fahimce ni, Albashir zai kawo miki duk abin da kika bukata, duk abunda kike so akwai ki bukata kawai, sannan na amshi number Kawunki na can Maiduguri, zan saka a tura duk abinda zaki bukata na haihuwa. Zainaba don Allah, kada ki cusawa Yarona ko yarinya ta, kiyayyar da kike min. Don Allah na hadaki da shi.”*
Wani irin kuka ne ya kamata tana yi tana karawa.

★★★
“Gani nan nazo ka kashe ni, ka bar min zuri’a ta, sun zauna lafiya bayan nan shi kenan! Ina magana ne kaki kula ni waye kai? Nace waye kai?”
Ya kai hannun kenan zai tab’a, aka juyo gare shi, with all surprise ya ce.
“Ke ce??……..
Happy weekend 🤗🤣🙄
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button