Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 100

Sponsored Links

 

*****
Tashi hankalin kowa yayi sbd Umme data rikice ta kasa yarda da ‘danta dayayi shekaru da rasuwa take Gani a gabanta.

Shi Kansa Bilal din cikin tashin hankalin ganin halinda ummen tashiga yake ba shiri ya sake Kiran likita ya dawo dubata.

Dad kaante kuwa tini ya kira dd babba ya sanar dashi halinda ake ciki Shima ba Bata lokaci yasaka Abbakar ya Siya musu ticket din zuwa Abuja a Ranar.

Ris Umme ta kwanta ciwon Nan take hankalin Anne itama ya tashi ganin wannan tashin hankali sbd ita batamasan sun boyewa su dd babba bayyanar Bilal din ba.

 

Sai qarfe 12 da Rabi su DD suka tashi bacci,
Wanka suka fara Yi suka shirya cikin qananun kaya Da dole su aka Siya mata a tsadaddiyar boutique din hotel din.

Abinci suka sake ci batada Wani karfi sosai ko kuzari a jikinta kusan shine yake mata komai sbd shi nasa zazzabin tini ya warware jinsa yakeyi fresh da qarfinsa da lafiyansa.

Saida sukai sallah suka fito tana sanye da slim jeans ajikinta da tsadaddiyar designer silk rigar black,
Shima black kaya ne a jikinsa da Kansa ya Bude mata motar ta shiga ya zagaya ya shiga tareda kallanta sai dayayi kissing gefen fuskarta kafin ya tada motar suka bar hotel din zuwa gida.

Koda suka Isa cikin mamaki suka tararda tashin hankalin da ake ciki Dan haka kan ummensa yayi tareda rungumota jikinsa Yana kokarin dawowa da ita daidai zuciyarsa na shiga damuwa.

Itama Bena gefen ummen ta zauna tana kama hannunta Daya suna kokarin dawowa da ita daidai.

Sumayyah kuwa dole komawa sukai sune suke rarrashin Zeenah da mum Khadija,

Bilal kuwa Se alokacin mahaifinsa ya rungumesa cikin tsananin kewa da son dansa Yana hawaye duk da manyancinsa.

Shi Kansa Bilal jinsa jikin mahaifinsa hawayen yakeyi nauyin zuciyarsa na shekarun Yana gangarewa Yana sauka.

DD da Bena daqyar suka shawo kan Umme ta dawo hayyacinta cikin tsananin kulawa da kauna DD yafara mata bayanin komai ahankali tin be qarasaba ta Kalli Bilal ta miqa masa hannu ya taho ta rungume abinta tana fashewa da kuka me qarfin gaske Daya saka gidan yin tsit.

Ta Dade tana Kuka a jikinsa Shima kukan yakeyi kafin sukai shiru Zeenah ma ya miqa mata hannu tazo ya rungumeta Yana share mata hawayenta.

Anne da sumayyah dai suna gefe tsaye suna kallan iKon Allah kafin daga baya Umme ta dago ta zubawa sumayyahn idanuwanta tanajin tsananin kaunarta tindaga qasan zuciyarta me sanyi.

Hannu ta daga ta kirata da hannun tana nuna mata gefenta.

Cikin sanyi sumayyah ta Tako ta iso gefen ummen ta zauna
Umme ta kama hannunta tareda sauke ajiyan zuciya tana rasa abin cewa.

Itama sumayyahn rasa abin cewa tayi bayan gaisuwar datayi musu dukkaninsu gaba Daya a lokacin.

Amnah dai tinda aka fara tashin hankalin momyn Abdul ta Jata zuwa kitchen ta zaunar da ita ta hado mata abinci tana Bata abaki tana Janta da fira Dan dauke hankalinta daga kan Abinda yake faruwa.

Se yamma dd babba ya iso Nan aka dasa Wani sabon yanayin Dan kuwa yau da Kansa ya ware hannuwansa biyu ya rungume Bilal Abinda be taba Yi ba,
Farin cikinsa da nadamarsa ya bayyanar a fili tareda murnar ganin wanna Rana me albarka da farin ciki garesa.

Sumayyah ma haka ya ringa saka mata albarka tareda aurensu da musu fatan zuria dayyaba me albarka.

Anan gidan Akai duk bayani da tashe tashen zancen da zaayi aka ci abinci lafiyayye da sabon sanin juna kafin da daddare dd babba,dad kaante da Abbakar sukai masaukinsu,

Umme da Zeenah anan gidan zasu kwana,mum Khadija Kuma Naseer yakaita gidan yayarta da zata kwana acan.

Umme da Zeenah a dakin Bena suka kwana Bena Kuma ta koma gurin Annenta itada Amnah suka kwana acan.

Kwana sukai firar kewan juna itada Zeenah da Umme se dare sosai taje ta kwanta sbd dauriya Daman takeyi zazzabine me qarfi a jikinta.

Washe gari haka Suka wuni su kadai mata a gidan Umme na Jin kaman zata hadiye sumayyah sbd so hakama Zeenah Amma dai matsayin Bena a ran Zeenah ita kam na daban ne.

Amnah batasan su sumayyah sune asalin iyayenta ba Kuma kowa be aminta da a fada mata dinba sbd Bilal din da sumayyah dasuka aminta da Hakan.

Wuni cur guda DD yayi Bai saka brown skin matarsa a idanuwansa ba Dan haka da daddare ya ringa Kiran wyaarta a kashe haka ya kwana cikin kewanta da damuwan rashin jinta da ganinta.

Kwana biyu cif sukai a abujan suka tattara gabaki dayansu suka koma gida Wanda tini labarin dawowar Bilal kaante yafara yaduwa Dan haka Koda suka Isa hatta yan jerida da labarai na kaantes haka aka ringa daukansu hotina ana kokarin jeho tambayoyi tako Ina Amma securities Basu bari ba Saida motacinsu dasuka daukosu a Jere tas suka shige aka rufe qaton gate din kaantes din.

Ana parking motocin dukkaninsu suka fito Daya bayan Daya wainda Basu samu zuwa abujan sauran familyn kaantes suka tarbesu ana farin ciki cikin Jin dadi.

Wata qaraman family walima Akai a Kaantes din kafin aka watse da daddare kowa ya kama makwancinsa.

Kafin isowarsu Daman tini aka sauya furnitures da komai na sashen Bilal din Daya koma na DD da Safnah
Dan haka Bilal da matarsa da momyn Abdul a sashensa suka sauka.

Anne kuwa daki na musamman aka ware mata a sashen Umme dakinta kusa dana Bena wadda DD yakusa haukacewa da zai tafi gidansa Shima yabarta.

Washe gari babu Wanda yaje koina gidan hutawa sukai sbd kawuna su sake a sake samun nutsuwar zuciya.

Shi Kansa DD duk yanda yaso ganin matarsa daurewa yayi ya huta yanda ya kamata.

Shima Naseer hutun gaske ya koma gida yana samu da kyau.

 

*******Kwana biyu aka dauka a Kaantes ana hutawa kafin kowa ya koma kan lamuransa Banda Bena da aka dakatar da zuwa Aiki sai bayan ta tare Dan kuwa DD Kai tsaye ya samu dd babba yace a Basa matarsa ta dawo hannunsa.

Murmu kawai dd babba yayi masa Yana cewa ba yanxu ba akwai sauran lokaci.

Dad kaante ya sama da maganar shikuma yace masa babu ruwansa maganar dd babba ce.

Umme ya samu da maganar itama ta zuqewarta sbd ita yanzu su sumayyah da Bilal ne gabanta Dan Suma su samu soyayyar da Basu samuba a baya.

Ba kunya y samu Anne da maganar itama ya nace mata
Ta rasa yanda zatai da ranta sbd kunya da tausayinsa Dan haka ta samu dd babba ta rokesa itama yace ta kyalesu kawai.

Bena da bazata iya binsa su tafi gidan nasa ba kaman yanda yakeson ta hada kayanta kawai su tafi hankalinta itama ta Dan tashi din Amma tasan koma menene dd babban nada dalilinsa,gashi Kuma Bata fita koina bare su hade waje Dan haka iyakacinsa da ita idanuwa,
Gashi Anne na gidan yanzu Wani abin idan yayi Umme cemasa takeyi baa Yi gaban sirika.

Zaucewa yake Neman Yi a cikin kwanakin sbd Neman wata Daya akeyi da dawowar tasu.

Shirye shiryen bikin Zeenah da Naseer aka fara ba tareda Jan lokaci ba Dan haka Bena din tayi Dan busy itada Zeenah da sumayyah da itama tayi busy mota ake Koya mata da Kuma karatunta da zata koma farko ta fara itama.

 

******Yawon Kaida kawonsu na Shirin bikin ya saka lafiya tafara gagarar Bena cikin kwanakin kullum da zazzabi me qarfi take kwana Dan haka dole dai aka kira Dr Ashley tazo har gida ta dubata.

Da farko dai kasa yarda sukai da ciki ne a jikin Bena din na kusan wata Daya Dan haka ya dauketa da Kansa ya tafi da ita Asibiti Akai scanning aka tabbatar masa da Hakan.

Tin Bata tashi daga gadon scanning din ba ya bita da Kisses Yana dagota gaba Daya ya Rungume kaman ze cinyeta.

Hanyar highbridge suka kama Yana Kiran Naseer a waya yace ya Siya masa ticket guda biyu Lagos zasu wuce a ranar.

Naseer kuwa ba musu Dan yasan DD din yaji jiki a kwanakin yai musu komai.

Sumayyah ya kira itace ta sato masa passport din Bena da komai daga hannun Bilal ta kawo masa har highbridge tareda Amnah data rakota suka koma gida Amnah nayiwa iyayenta bye bye tanason binsu sumayyah tayi mata dabarar dai suka koma gida.

Batareda sanin kowaba ya dauke matarsa suka wucewarsu Lagos acan ya samu ya Bude babin rayuwar dayakeso da matarsa da sabon babynsu da zasuwa Amnah qani ko qanwa.

Kashe wayoyinsu yayi suna cika sati biyu a Lagos din suka visan ya fito suka wuce Zurich.

Saida suka bar Nigeria da kwana biyu sun huta kafin ya kunna musu wayoyin da zaa samesu.

Dd babba dayaga Abinda DD din yayi kasa cewa komai yayi sbd yasan Daman zaayi Hakan sbd rashin hakurin DD din akan Bena.

Bena kasa mgana da dd babba tayi sbd kunyar Abinda DD yasaka sukai na guduwa.

Anne ma mamakin DD ne ya sake kasheta tai dariya sosai dataji wai ya gudu da matarsa.

Umme da Zeenah basiyi mamakin komaiba Dan sunsan ba komai bane a gurinsa indai DD kaante ne.

ADVERT

*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES_*

*_ASLM ALAIKM_*
*_Yan uwa abokan arziki yan gayu masu bikin alfarma na manyan mutane da son fita kunyar kowane kalar luxury abincin larabawa da qasashen qetare, kuzo ga number 1 best catering services damuke dashi a arewa,_*
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES shine best Abinda muke buqata a gurin hidimar biki da duka Wani occasions na girma da tsari tareda fita kunya indai gurin girki masu tsafta da tsarin ne tareda verities masu dadi,_*
Bikin aure
Bikin haihuwa
Bikin birthday
Picnics
Parties
Walima
Receptions
Hatta a cikin gidanka idan baka buqatan girki zakai ordern abinci daga garesu a kawo Maka har gida cikin tsari da burgewa.

Hakama kalolin abincinsu da services dinsu sun hada da;

Indian biryani rice
Mandy rice
Chinese fried rice
Stir fried spagetti
Chinese noodles
Fried rice
Party jollop rice
Chicken kebab
Beef kebab
Grilled chicken
Chicken cutlet
Kafta
Shredded sauce
Salads

Hatta bangaren snacks masu kyau da dandano da tsari babu Wanda basayi muku kalan Wanda ranka yakeso.

Realtaste 247catering services
08034425662

Instagram@Realtaste 247 catering services

Location:kano,Kaduna and Abuja.
Ga masu buqata su tuntubemu a 08034425662
Mungode.
Karku bari ayi babu ku.

 

******Fadan kalan rayuwar dasuke gadanarwa a Zurich ba me yiyuwa bane sbd ko cikinta Daya fara girma bayan watanni Bai hanasu komaiba,
Bena ta zare kaman yanda DD ya Dade da zarewa ya zarar da ita,

Wata irin tsaftatacciyar rayuwar Jin dadi da hutawa tareda Soyayya suke gudanarwa me Dadi da nutsuwa batareda sun saka ranar dawowa ba.

Daga bikin Zeenah Akai da Naseer sbd kawai Naseer din yafison se DD Yananan a daura masa aure Dan haka su aka tsaya Jira dole hakama kusan dawowan tata zai zama daidai da lokacin haihuwarta.

 

*****Se da cikinta yayi wata takwas kafin suka dawo lokacin sumayyah itama cikinta wata biyar Dan haka haihuwarsu kusan duka kaantes ita ake Jira.

Amnah dataga mummy dinta da ciki kaman zata taka kan gawa sbd murnar zata samu babyn wasa.

Tsakanin Anne da dd babba rasa Akai Wanda yafi Wani farin cikin dawowarsu da ganin tsohon cikin Bena data koma kaman wata halfcast sbd Wani irin Hutu da lafiyayyan rayuwar dasuke gadanarwa,
Shikuwa tini ya sake komawa baturensa kaman Wanda yayi shekaru baya qasar.

Kiri kiri yayi musu wuni kawai tayi ya dauketa suka tafiyarsu gidansa Akai tarewan karfi da yaji ba bikin komai Dan yace baya buqatan bikin.

Dole washe gari su sumayyah da Zeenah suka bita gidanta da kayanta dana yarta da ‘yar ma se Nafisat.

******Bikin Zeenah yazowa kowa da mamaki sbd a ranar da aka daura aurenta a ranar aka daura auren Anne da alh basheer bulama Wanda da Kansa dd babba ya Basa aurenta bayan da Umme ta roki a bawa Dan uwanta auren Annen shikuwa dd babba Hakan yayi masa Dan haka ya sanarwa Annen wadda batada ta cewa se yanda yace.

Su Bena da sumayyah sunsha mamaki sosai Amma Dayake an sanar da mazajensu sai suka fahimtar dasu tareda Nuna musu sune sukai Naam da wannan shawarar.

A cikin highbridge su Zeenah suka tare suma sbd gidan da DD ya siyawa Naseer Zak irin nasa gudummawarsa Dan haka sabuwar Jin Dadin zama guri Daya ta barke tsakanin Bena da Zeenah din wadda itama aka hadota da me aikinta da momyn Abdul ta samo mata ta familynsu me kirki.

Seda akin sato uku da Bikin kowa ya nutsu kafin Anne ta tare nata gidan Alh basheer bulama din Wanda su momy suka fita aciki
An sauya masa komai gidan ya koma sabo komai na cikinsa sabo,
Hatta masu aikin duka sabbi aka Kai wainda Suma duka momyn Abdul ce ta kawosu Dan yanzu ita Kuma itace anintacciyar da aka yarda kawai ta kawo masu aikin familyn.

Da farko kasa sakewa Anne tayi da auren se ahankali da Umme ke Dan sake wayar mata Kai da wasu abubuwan da Kuma yanda Alh basheer bulama din ke nuna mata kauna da kulawa da tattali yasa ta fara sakewa sosai tana karban sabuwar rayiwar data samu kanta aciki.

Ranarda Anne ta cika sati biyar a gidan Alh basheer bulama a ranar aka gama shariarsu Ababa Wanda aka wuce dashi gidan yari da qafa Daya Dan dayar dole yanketa Akai,
Ita Kuma momy hukuncin rataya Akai mata Wanda yasaka Safnah rasuwa itama a cikin dare da aka rataye momyn ta mutu sbd ita har lokacin Bata gama warkewa ha bare ta karbi nata hukuncin Dan haka tsoro da baqin cikin rayuwar datayi mara amfani ya sakata rasuwa a ranar da daddare.

Ranar da zata rasu da rabon su gana da yan uwanta batareda sanin Anne ba har lokacin Bena da sumayyah sukaxo dubata ta nema gafarar Bena Kuma ta yafe mata sunada niyar idan taji sauki zasu kawo Anne ta dubata saigashi Allah be nufaba ta bar duniya cikin baqin ciki da danasani.

Rasuwar Safnah ta tabasu kaman yanda ta taba Alh basheer bulama sbd Yana son Safnah har cikin ransa Dan haka yaji ya qara son Mahaifiyarta da batasan ta rasa yarta ba.

Daga qarshe ma dauke Annen yayi suka bar qasar ta rakasa Wani aikin da zashi Dubai suka share kusan wata biyu a qasar Koda suka dawo Bena ta haifi lafiyayyan baby boy dinta Wanda sukai naquda tareda Daddynsa Dan kuwa duk ihun da Akai hannunsa na cikin nata Yana share mata zufa Yana binta da Kisses hardai aka samu aka haihu lafiya.

Babyn sunan dd babba aka saka masa Wanda aka sake samun Wani DDD din a family.

Farin cikin da familyn kaantes suka shiga na samun wanna babyn duniya ma seda ta tabbatarda dashi Dan haka sati shida kawai sukai da haihuwar ya dauke matarsa da yayansa Amnah da little D suka bar qasar.

Basu dawoba se da sumayyah ta haihu ita namijin ta Haifa yaci sunan dad kaante daganan suka zauna aka Bude babin dasa sabuwar rayuwa.

Anne duniyarta ta sauya gabaki Daya zuwa duniyar da Bata taba mafarkiba,
A yanzu gidan aurenta wata aljannar duniyarta ce tareda mijin da Bata taba tinanin akwai irinsa a duniya ba sbd so da kaunar Dayake mata,hakama gidanta tarin masu aikinta kawai take kalla Wani lokacin taji tana godewa Allah da tarin niimar da yayi mata ta samun Yaya mata dasu kawo mata Yaya mazan da sirikai mazan masu albarka suma.

Littafin zafin Kai ya rufe ne daga ranar da Zeenah ta haifi ‘yan biyu ita Kuma mace da namiji Wanda ya saka family sake shiga cikin murna da farin cikin samun wata qaruwar.
#MAMUHGEE#
#ZAFIN KAI
#ALHAMDULILLAH

BABU WANI ABINDA ZAN IYA CEWA A YANZU DA MUKA KAWO KARSHEN LABARIN ZAFIN KAI WANDA NA RUBUTA SAI ALLAH YA SAKAWA KOWA DA KHAIRAN YA YAFE KURAKIREN CIKI DA MUKA RUBUTA,
NGD WA MABIYANA SOSAI SOSAI ALLAH YABAR KAUNA.
MASU YABAWA DA MASU ZAGI DA MASU BAQAR FATA DA MASU SATA DA MUGAYE DUK ANGODE ALLAH YA SAKAWA KOWA DA ALKHAIRI.
SAIMUN HADE A SABON LABARI
THANK YOU.
MAMUHGEE

*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES_*

*_ASLM ALAIKM_*
*_Yan uwa abokan arziki yan gayu masu bikin alfarma na manyan mutane da son fita kunyar kowane kalar luxury abincin larabawa da qasashen qetare, kuzo ga number 1 best catering services damuke dashi a arewa,_*
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES shine best Abinda muke buqata a gurin hidimar biki da duka Wani occasions na girma da tsari tareda fita kunya indai gurin girki masu tsafta da tsarin ne tareda verities masu dadi,_*
Bikin aure
Bikin haihuwa
Bikin birthday
Picnics
Parties
Walima
Receptions
Hatta a cikin gidanka idan baka buqatan girki zakai ordern abinci daga garesu a kawo Maka har gida cikin tsari da burgewa.

Hakama kalolin abincinsu da services dinsu sun hada da;

Indian biryani rice
Mandy rice
Chinese fried rice
Stir fried spagetti
Chinese noodles
Fried rice
Party jollop rice
Chicken kebab
Beef kebab
Grilled chicken
Chicken cutlet
Kafta
Shredded sauce
Salads

Hatta bangaren snacks masu kyau da dandano da tsari babu Wanda basayi muku kalan Wanda ranka yakeso.

Realtaste 247catering services
08034425662

Instagram@Realtaste 247 catering services

Location:kano,Kaduna and Abuja.
Ga masu buqata su tuntubemu a 08034425662
Mungode.
Karku bari ayi babu ku.

Leave a Reply

Back to top button