TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 61

Sponsored Links

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/28, 5:52 AM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

 

Daidai lokacin da nazo gittawa ta gefen shi sai gaji nayi ya
zabura da karfi kamar wani abu yabi ta saman kanshi yasashi tashi firgice har
saida na tsorata daga inda nake nakai kofa na tsaya ina kallonshi

 Ya dan kama wajge
waige kafin ya mayar da kanshi kasa na dan lokaci can kuma ko ya tuna cewa ina
wurin ne sai ya dago ya dan kalleni.

  Lafiya dai na
tambayeshi ya girgiza min kai tare da fadin ba komai anyi sallah ne nace da dan
saura lokaci sai naga ya mike ya shiga daki .

   Ruwa ya watsa ya
dauro alwala ya fito ya tafi massalacin yayi sallah daga can ya wuce zuwa
kasuwa ya karaso sayayyan su ya dawo .

   Ina daki don ni
nasaba da zaman dakin idan ba wani abu ya fito dani waje ba lokacin ko yaushe
zaka sameni a dakina zaune .

    Indana gane ya
shiga kasuwa ledan da nagani dauke a hannunshi lokacin yasa na fahinci hakan
wai ashe tsaraba ya sayo da zamu kaiwa kannena a gida.

    Saida ya fara cin
abinci yake fadin anjima saiki shirya muje gidan mu gaidasu kafin intafi don in
tafi zuwan zai zama maki matsala kuma.

    OK yau din zamu
tafi ke nan na fada ehmana ko zaki iya hawa mashin din garba zuwa ya tambaya
yana kallona don kinga yau din idan mun tafi tare nima sai in samu in masu
barka ai.

   Hakan nada kyau
kuma zanji dadin hakan mashi kuma me zai hanani hawa tunda sunsan ba mota muke
dashi ba dama ba kunya a cikon hakan ai.

   Nasan ke yanzu baki
jin kunyar hakan gaskiya amma ummah ba zataji dadin ganin mu haka ba ai ita ya
fada a cikin wani irim murya mara dadi nace baka ko fahinci ummah ba har yanzu
gaskiya.

    Zahra irin wanan
dalilin yasa kikaga ina jajircewa ga karatun nan don mu samu abin rike kammu
nan gaba dana iyalin mu masu zuwa don kada ki fito daban a cikin yan uwa.

    Ka daina irin
wanan tunanen don Allah Allah fa bai manta damu ba master ko yaushe kaga bawa a
wani hali yana sane da rayuwanshi ko a hakan mungode ai in anfimu mu kuma munfi
wasu ai.

   Hakanane wallahi
irin wanan halaiyar naki zara ke kara kwantar min da hankalina da ace ni wanine
zahra ba abinda zai hana banyi sharia da mahaifina ba don a yanzu shidin wanine
a cikin kasan nan.

   Wananne rana na
farko daya sako min zancen mahaifinshi a hiran mu duk zamana a gidansu dan haka
da sauri nace don me zakayi sharia dashi kaiko ?

   Don an tabo min
inda ke min kaikayi saboda na kasa gane zancen mahaifin nasa gaba daya har
nakanyi konkwanto ince waiko dai zancen mutane akansa gaskiyane wani lokaci.

   Sai naga ya girgiza
kai kaiwa cikin takaici ba tare da yace min komai ba a lokacin yaci gaba da cin
abincin shi yana tunane a zuciyarshi lokacin.

   Nima dai tunanen
nakeyi na cewan da yayi mahaifin nasa wanine yanzu a kasan nan don me ya fita
batun danshi mutum kamar Ahmed ace baya tare da mahaifin shi.

  Wai a ina matsalan
takene nasan dai matsalan ba babba bane don da babbane yadda ake fada Abba ba
zai yarda ya aura mashi niba haka duk da naji su mommy na fadin ba haka a banza
Abba ya daura min aure da Ahmed din ba ai .

    Akwai shige da
ficen da wasu bangare sukayi aka fitar mai da hankali don a tozarta ummah dani
a idon mutane koma meye nidai nasan ina son mijina sosai.

   Muna idar da sallah
magariba muka fito cikin shirin mu na daiji yanacewa Dije zai kaini gida mu
gaidasu bai fada masu yar uwata ta haihu ba don haka nima naja bakina nayi
shiru.

   Har zamu fita naji
yace yar uwantace ta haihu zamuje barka Dije ke fadin madalla karuwa aka samu
ashe to muna masu barka ita kuma inna sai cewa tayi.

  Kaji mata masu biyan
bashi ba akawo a cinye a juye a masai ba kullun mutum na kiwo ana zama kamar
bata kiwo a gida ko dabbobi keci haka ai suna biyan maishi.

    Nagane nufin ta
sosai amma ban nuna hakan ba don naji Dije tace aikowa yaci bashi da niyar biya
yake dauka Allah ya horewa kowa ya biya da hannunshi sai naji ya lalubu hannuna
alaman mu tafi.

   Mukai masu sai
mundawo muka fice daga gidan yana jaye da mashin dinshi da yake shigowa da ita
har cikin gida saboda tsaro.

  In kuma dare tayi
zai jawota zuwa part din mu ya tura cikin kitchen din mu a kulle idan kuma zai
tafi school dakin Dije yake ajewa duk saboda tsaro.

    Ya tada mashin din
na hau yafara tafiya sai naji yace irin wanan halin na inna nadaga cikin abinda
yasa nake son barin gidan nan zahra duk abinda ya faru da ita kwanaki bata
daddara ba har yanzu.

   Wai kwanaki kinsa
uwar garke ta taba ita kuma tayi mata irin waibuwan su na dabbobi amma har
yanzu baisa inna ta daddaraba ga halin ta ji wanan maganan da take fada yanzu
don Allah .

   Me uwar garke tayi
mata na tambayeshi a gagauce kovya mantane ya shiga labarta min abinda malamin
da aka kaishi wurinshi ya fadamasu.

   Ai dabba taiwa
rashin mutumci wanan uwargarken akuyan namu tunda kinsan in dabbata kosa tana
da waibuwa akace shine nan ta rikide ta bata tsoro a dakin tunda bata tausaya
mata ba.

   Daga bayan mashi
nace what da dan karfi sai lokacin yagane katobaran da yafarayi yace ke bafa
wai ita din aljanna bace ko wani abu ita din a,a wani lokacine dai sai aljannu
su shiga jikinsu su yiwa mutane abinda zai basu tsoro idan sunga ba daidai ba
sai su tsorata mutum shi nake nufi.

   Ai bansan da cewa
tsoro yasa nayi mai wani danka ba a lokacin daga baya inda nake zaune nayi
shiru yana magana banma jishi ba son tunanen da makeyi a lokacin.

   Zahra fa ya ambata
da dan karfi  firgigit na amsa mai yace
ina hankalin ki yaje kuma ina magana kefa kin faye tsoro wallahi wanan maganan
ina abin tsoro a cikin sa kuma ?

   Ba zan kara kaiwa
dabbobin nan abinci ba ko wani abu ko inda suke ba zan kara kallo ba gaskiya
sai naji ya kwashe da dariya yana fadin banda abinki ai kyautatawan da kike
masu zaisa su ganeki su san kamshi ki da muryan ki ko wani lokaci.

   No a dai bari kawai
kaima da kake kyautata masu baisa sun bar mahaifiyarka ba ai balle ni bakuwa a
cikin ku dama idan ina gida naga rana yayi nakan kai masu ruwa in zuba masu
abinci son naga Dije ke wahala dasu yasa nake hakan.

   Don Allah kici gaba
duk na sani wallahi su kadai na gada daga kudin mahaifina daya barmin shiyasa
kikaga dije na kulla min dasu yanzu kuma gaki kin karbeta zakice kin daina kuma
princess ?

  Nifa tundaka fadi
hakan tsoron su nake ji yanzu kuma gaskiya tunda mutum ba sanin ya masu laifi
zaiyi ba kai ina ilimin ki ya shiga kike wanan maganan haka nimafa bawai na
yarda da wanan maganan bane kawai dai abinda mutumin ya fada nake fada maki.

   Daidai lokacin muka
kawo kofan gidan mu ya faka na sauka a hankali muka kwankwasa maigadi ya bude
muna kofa muka shiga muna gaisawa dashi.

    Duk da yana ganin
duhu a lokacin babu abindake fita bakinshi har cikin zuciyar shi sai kalman
innalillahi baiyi aune ba yaji hawaye yana zubo mashi a fuskanshi lokaci guda.

  Tabbas yasa yana da
yaron daya haifa da matarshi ta farko Rashida basulluba yar zamfara da sukai
aure na saurayi da budurwa a lokacin da yabar gida a baya can da kurciyarshi.

   Ada can baya yana
yawan tuna yaron yana kuma da sha,awa  ya
daukoshi ya dawo kusa dashi ya zaune dashi ya tashi a gabanshi amma sannu a
hankali zancen yaron nasa gaba daya yafita a zuciyarshi.

   A baya yana tuna
yaron amma sai yakanji kiyayyan yaron da uwarshi da tan uwanta ya ziyarci
zuciyar shi a irin hakane har yaji kwata kwata yaron ya fita a zuciyashin baki
daya.

   Shaf ya manta da
zancen shi ga baki daya sai gashi lokaci guda a yan watanin nan ya fara
mafalkin wanan yaron da baisan kowaye ba sai bai kawo cewa wanan dan nasa bane
ruhinshi ke bibiyan shi a yanzu.

    Amma yau zancen
abokan nasa ya tunasar masa da hakan ko yana raye ko yana mace yanzu Allahu ya
alamu don baisan ta inda zai fara nemanshi ba yanzu.

   Tunda an yamusa
garin a yanzu an maida ita jaha mai cin gashin kansa itama yasan a yanzu ba
Gusau din da yasani bane a baya don zasu samu cigaban zamani.

   Kai anya kuwa yaron
nan yana raye shekara ashirin da takwas amma har yanzu ba wanda ya waiwayi juna
da yana raye yasan malam ladan nada wayayyen kai dolene zai nemishi akan yaron
don ko lokacin bawai iyayyen Rashidan na ainihi suka bijirewa zuwanshi da itaba
nan yan uwan haihuwan iyayyen ne suka kawo wanan matsalan.

  Duk da yasan yana
son Rashidan a lokacin yadda yake ji a jikinshi don kiran da akaimai gida na
asiri ba zai iya dakatar da tafiyan nasa ba a lokacin.

   Don kirane na
gagauce a duk inda yake a lokacin dole sai ya dawo gida ko babu shiri kamar
yadda lokaci guda suka turashi cikin duniya ba wanda yasan inda yake hakama
wanan karon aka kirashi ya dawo gida ba shiri.

   Idonshi ya runtse a
cikin takaici yana maijin zafin faruwan hakan a rayuwanshi why da abubuwa suke
zo mashi a hakane cikin rayuwanshi kadai.

   Yasan ya dawo gida
da niyar komawa ya dauko iyalinshi a lokacin amma sai abubuwa suka faru da yawa
bayan dawowan nasa har yakai ya manta da zancensu a zuciyar shi.

  Oh lord ya fada a
fili tareda furta Astangafurallah Allah na tuba ka yafemin kada ka kamani da
wanan babban laifin dana aikata a rayuwana.

  Yasani iyayyen
Rashida da yan uwanta ba wasu masu karfi bane a garin tallakawane tilis inba
Allah yai masu wani budi daga baya bane irin haka dole ke nan yaron a yanzu yana
can cikin wahalan rayuwa.

   Bayanshi yana nan
da nasa iyalin a cikin daulan duniya da jin dadin rayuwan da bai musaltuwa a
lokacin son shidin ba mutum bane mai tauye iyalinshi.

   Yanzu ina zai fara
bullowa wanan matsalan da wani ido yanzu zai baiyana garesu yace yana neman
dansa dan da baisan cinshi da shansa ba har ya rayu yakai wanan shekarun masu
yawa haka ?

   Dolesu jauro zai
nema a asirce kamar yadda yanzun ma suka tunatar dashi hakan asan yadda za a
bullowa maganan da wuri kada ya mutu ya bar baya da kura kuma don yasan halin
matarshi ba yarda zatayi da hakan ba shi yanzu ina zaikai wanan alhakin a
rayuwan shi.

  Godiya da tasbihi ya
shiga yi a zuciyan shi yana mai lumshe idanuwan shi kadai yasan yadda yake ji a
zuciyanshi yasan alhakin hakan dole ya kamashi a wani bangaren rayuwa.

    Hjy Yabi ce ta
shigo part din a lokacin jin motsin mutum yasashi dago kai ya kalli mai shigowa
dakin a lokacin matarshi ya gani hakan yasa ya sauke kanshi kasa daga kallonta.

   Barka da hutawa
yaji bakinta na fadi yau karo na farko azamansu kunuwanshi ya jiyo mai hakan a
bakinta a ciki ya amsa mata ta samu wuri ta zauna tana mai kallon fuskanshi
dake daure lokaci guda.

   Alh wai da wani
matsalane ka canza gabadaya cikin yan kwanakin nan mu bamuji dadin kaba kai kanka
bakaji dadin kanka ba kuma kaki fada muna abindake faruwa mu sani ?

  Lafiya nake haka dai
naga shine daidai yanzu don naga kina kokari dake da diyanki ku maidani mace ke
ki zamo miji a gareni yasa na daukarwa kaina matakin hakan shine kawai ya fada
yana dago kai tare da kallonta.

    May ya kawo wanan
zance kuma ana zaune kalau zaka fadi haka a cikin mu waya nuna maka cewa baka a
matsayin ka na ubangidan nan yamzu ?

   Nina gani na
fahinci hakan don haka nake shirin daukam matakin daya dace dani a yanzu wanda
shine daidai gareni gako wani magidanci kuma.

  Gaban hjy yabine
yake wani irin faduwa don abinda take tunane shidin take ganin ya faru a
lokacin hakan na nufi duk wani shiri na sihiri da kulli da sukai mai suka
daureshi abin ya karye a yanzu haka ke nufi.

  Cikin karfin hali
irin na hamshakan mata tace dashi kai Alh wanan zance ai bai kamata a bakin ka
wani power naka zan dauka ko yaran nan su bani bayan kowa yasan a karkashim
innuwan ka muke rayuwa a gidan nan.

    Idan ma Baku sank
ba said Ku fara sank son Abubakar din da kuka sank a baya bashi bane yanzu kuke
kallo wanda kuka mayar dashi da banza duk days a wurin Ku.

   Shiru tayi tana Dan
kakaro murmushin dole a fuskanta don tunanen ta ya wuce abinda takeji a gareshi
yanzu dole wani aikinsu na baya ya samu matsala a wani bangaren .

  Inko haka tasan
akwai aiki a gareta babba yanzu don’t yaushe zata iya tuna wani abinda akai
mashi a baya ga kuma hjy Korau uwar rikon nasu sun samu matsala yanzu da ita
akan yayanta.

    Zakace ba haihuwa
akayi ba a lokacin don’t yadda naji gidan shiru koda yake darene a lokacin
watakila kowa ya nufi gidansa sai kuma gone su dawo ga yadda nasan aal,adan yan
uwan my ko garin mu

   In an haihu kai
maigida ka shiga uku don yawancin yan uwa a nan suke tarewa kullun suna gidan
sai dare za a watse said bayan suna kafa ya dauke.

    Shine abinda ya
bani mamaki a was a wanan karon data kofa muka tsaya muna sallama kusa sau ukku
ba a amsa muna ba kallonshi nayi ganin haka yasashi daga muryanshi da karfi ya
kwada sallama a daidai lokacin aka bude kofa.

   Mama hafsice zata
fito tsci karo damu tsaye a kofan dakin cikin mamaki ta amsa muna sallaman tana
fadin ashe bakine daga can ciki naji mur I an mama tana tambayanta da su wayene
a kofan ?

   Nice mama nayi
saurin bata amsa kafin mama hafsi din ta bata amsa ta bude muka shiga au
Zahrace ashe yanzu like tafe aina dauka bakiji haihuwa  ba ma son ban ganki ba ?

   Naji mama dazun nan
ummah takirani tana fada min anty Aisha ta haihu barkan mu da arziki ubangiji
Allah ya rays muna bisa kan sunna amin.

   Nafada freely da
murmushi a fuskana tace amin gaba daya hankalinta na kaina tana kallona daga
samana har zuwa kasana lokaci guda nikuma na fahinci hakan.

   Nasan ba komai take
kallo ba sai shigana na lokacin duk da ba laifi amma ita taga kasawa a hakan
dama shi take son gani a gareni don’ komai daya shafeni baya burgeta ita.

   Ki shiga suna ciki
tare da hjy tsohowa cewa kakan mu sai nace a cikin kunya tare muke dashi yana
kofa yazo yai maku barka shima OK tare da mijin naki kike ashe ?

   To kije ki shigo
dashi ciki mana ta fada a cikin izza da isa iron nata na mike na fita ta bini
da wani kallo mai kama da harara tana jan tsoki tare da kawar da kai gefe daya.

   Nayi masa iso da mu
shiga daga ciki na juya zan shige naji ya dan jawoni na juyo kudi ya danka min
bansan ko san ko nawa bane nayi godiya yace No da sauri.

   Ina gaba yana biye
dani a bayana zuwa ciki yayi sallama suka amsa mai su ukune zaune a falon
lokacin har kasa yakai ya gaidasu kafin ya fara masu barka da karuwan da aka samu
din.

    Rakiya kira masu
hjy nan su gaisa ta fada a gadarance don mama badai magana a gadara ba kan
balle ta samu wurin yi a yanzu.

   Jin hakan yasa
nasan ba sai mun shiga ciki ba kenan a nan zasu zo mu gaisa dasu son azato har
maijegon din amma sai naga hjy ta fito ita kadai dakin itama saida ta jima ta
ja muna rai tabarmu a zaune shiru a falon
kafin can ta fito tana Dan dingisawa irin na manyanta.

   Su waye ke neman ta
fada a gyatsire tana kaiwa saman kujeran farko dake falon bayanta kalle mu gata
nan takwarankice ita da mijinta sukazo barka mama ta fada har lokacin tana mike
a saman dogon kujera da waya a hannunta.

   Waye takwaran nawa
ta fada kamar bata shedani ba tana wani gimtse fuska a cikin daurewa mama tace
gata maisunan kicefa ta nan gidan.

    Yanzun taga daman
zuwa ita issasa duk yan uwa dake nuna farinciki sunzo sun tafi wani iri naji a
lokacin,  bansan lokacin da nace muma ai
farin cikin mukazo nunawa kedai hjy duk da kin dade bakiga mutum ba sai kin
yaba masa magana son ranki.

   A,a makka kikaje
karshen dadewa ina kina cikin garin nan dai karshen dadewa unguwar
sullubawa  da kika zabi zama.

    Sai naga mama ta
kalloni ban fasa maganan ba naci gaba da fadin yanzu da naji din bagashi munzo
tun ba,a kwana ba ?

   Ke kada ki shiga
min ido ana magana kinayi har wani aure kikayi na gwadawa tsara da kike ganin
wuyan ki yakai yanzu da zaki fadawa mutane magana yadda kike so .

   Tashi muje ya fada
a hankali daga bayana inda yake zaune din itako taci gaba da fadin masu manda
da uhumm basu  rawan kan aure.

    Naji zafi naji
ciwo a raina amma saina dake INA fadin in auren banzane kije kiyi mana ai
naggidan ai zawarawan fake sonki had yanzu na mike da zuman shiga dakin naji
mama Rakiya na fadin Aishan ko ta samu barci fa.

    OK in ta tashi a
gaida mun ita muna mata barka da sauka lafiya ya mike yace mama zamu tafi Allah
ya raya muna na mikawa mama rakiya kudin daya bayar abawa jaririya nace ga
wanan inji shi asaiwa jaririya kwali.

   Kai haba dai kana
fama da kanka da iyali cikin Dan kunya yace ba komai mama ayi hakkuri dashi son
Allah to an gode ta fada nayi mask saida safe muka fito zuwa part din mu.

  Nan ma bamu dade ba
min gaida ummah ta tambayemu mutanen gida na barsu tana kara mashi nasiha na
shiga wurin kannena har sunyi barci a lokacin.

   Mukai mata sallah muka fito bar muka hau
mashin din my banji yayi magana ba a lokacin zuwa gida don haka nasan ranshine
ya baci sosai nima nayi shiru.

Leave a Reply

Back to top button