TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 56

Sponsored Links

 

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣6️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Zaune yake yana rubutu a jikin allonshi na karfe da sai
lokaci lokaci yakan dauko shi yayi amfani dashi wanda iyalanshi tasan da hakan
sai wani abu na muhinmin yake dauko allon yayi amfani dashi.

    Idan yana hakan
tana bashi natsuwa ita kanta tasan aikine na muhinmanci ya taso mashi dayake
son natsuwa don haka takan jaye ga duk abinda zai iya dauke mashi hankalinshi a
lolacin.

   Ya dauki tsawon
lokaci yana hada rubutun kafin ya wanke ya juye a cikin wani goran ruwa ya aje
gefe ya mike zuwa ban daki inda ya kewa ya fito ya daura alwala a nan ma ya
dauki lokaci yana addua kafin ya shafa.

   Shatu dake zaune
gefe tana zaman kadaici tare da dakonshi ya idarne tayi mai sannu tare da
gabatar mai da abinci.

   Don inda sabo ta
saba yau kusan kwana biyar yana wanan aikin da ita bata san kona meye ba
tadaiga ya tsiri aikin ne kuma kafin ya fara saida ya fada mashi dokokin shi.

  Don kada tazo ta
bata mashi aiki don mace shu, mace sosai idan za ayi wasu abubuwa ba,a son mace
kusa kota saka hannu don a take take karyawa mutum shirin shi.

   Don sanin hakan ya
gargadeta da ta bar komai a yadda taganshi cikin yan kwanakin nan sanin halin
mijin nata yasa ta kiyayye kamar yadda ya bukace ta dayi din.

  A kwana na bakwai ya
dauki ruwan rubutun dayake tarawa ya fice cikin dare zuwa inda yake da bukatan
kaiwa a lokacin.

  Babu kowa a lokacin
don dare ya raba sosai kafa ya dauke gaba daya bakajin komai sai kukan kwarin
dake rayuwa a cikin dare da sauran halittun Allah a lokacin da darene su maraya
garesu.

    Gadan gadan ya
nufi wurin iccen tumfafiyan tun daga nesa yake ganin halittan icen ya juye masa
ya zama kamar wani hallitan kosasshen doki a tsaye.

  Saidai hakan bai
razanashi ba don sanin irin waibuwan da wanan yar hallitan itaciyar yake dashi
kala kala.

  Da sallama a
bakinshi ya kara wurin itaciyan yana fadin icen albarka icen siri nazo gareki
cikin amincin Allah yadda wasu masana kafiran Allah sukai sihiri suka juya
tsakanin da mahaifinsu haka nake son Allah ka juyo hankalinsu su dawo da  alakan dake tsakanin su kamar yadda ka
sharianta a daddinance ya Allah .

    Ka karya duk wani
kulli da minafuncin dake boye tsakanin habu na mazo da danshi Amadu da akafi
sani da Ahmed.

   Ya Allah ka dawo da
alakan a tsakani kamar ko wani da da mahaifi a duniya yana fadin hakan ya mike
ya bude wanan dan goran ya fara zuba wanan ruwan rubutun daya tara na
kwana  bakwai.

   Yana ci gava da
fadin wasu kalamai a bakin shi har saida ya juye wanan ruwan kaf ga icen ya
yayi hamdala tare da godiya ga Alla ya juya don ya koma zuwa gida.

   Ya bada baya yayi
tako daya zuwa biyu sai yaji kamar ana binshi a baya yasan dokan hakan jin
hakan baisa ya juya ko ya dakatar da tafiyan shi ba saima adduan da yakeyi a
bakin shi lokacin na neman tsari daga shedanu da ba ganin su mukeyi ba a fili.

   Can kuma yaji kamar
daga gefenshi anja mashi tsuki a cikin bacin rai tare da fadin kai har ka isa
ka sance kullin dake tsakanin mu shekara da shekaru.

  Lalai ka shiga
hurumin dabai shafeka ba dama kaine kake muna zagon kasa ashe ga aikin, ,
,  kafin ya karasa yaji kamar ana ba
mashi wani azaba .

  Anyi sama dashi har
ya shige gida bai kara jin wani motsi da zai tayar mashi da hankaliba kuma
alwala ya dora yaci gaba da sallah har tsawon wani lokaci.

    Yau gidan  tsit gashi ba school muna hutu a lokacin da
alama kuma mutanen gidan sun fita a lokacin don falkowan da nayi daga barcin
daya daukeni na safe .

   Na gane hakan ne
don yadda naji wurin ya dauki shiru na dan lokacin dana falko ina sauraren
yanayin gidan don in suna gida ba bace hakan yake ba don zasu cika gidan da
surutusu sosai saboda Allah yayisu da daga murya abinda ba a so ga diya mace ke
nan.

   Don koshi wani
lokaci yakan yi fadan haka dasu don zai fita ya tsawata masu    har hakan kanso kawo sabani a tsakani shi
da mahaifiyar nasa wani lokaci.

    Wanka na shiga na
fito na shafa mai ban tsaya wani gyaran jikina ba sosai sanin master baya gari
yana zaria wurin karatun shi.

   Sama sama nake jin
sallama daga cikin gidan jin hakan yasa na fito ina amsa sallaman na bude kofa
wata mace na gani tsaye kallo daya zakai mata ka fahinci irin matan nan ne masu
zaman kansu.

    Gaisuwa na mutunci
da ban girma nayi mata ta amsa min kamar yadda nagaida da ita din take
tambayana da ko maman Asmau na ciki nace ban tsamani amma barin duba maki su.

   Na dan wuceta na
nufi cikin part din tun daga nesa naga kofan su a rufe sai na Dijene bude
lokacin don haka na nufi can ina sallama daga ciki dije ta karba min tana
kokarin dagowa na leka na kara gaida ita da rana nake tambayanta inna tace tun
safe suka fita ita da yarta Asamau Aishace dai ta fita bada dadewan nan ba wai
ta tafi kitso tace.

    Bakuwace dama inna
din tayi basu gida Dije din ta kara fada matar tana daga tsaye a can kofa na
juya ina fada mata sai bina take da kallo.

   Tace kai ina kuma
ta tafi bayan tasan yaune zanzo munyi da ita hakan idan ta dawo kice mata yar
giwa ce tazo zata gane a, a mama aiba kya tafi haka ko ruwa baki sha ba na fada
.

    Don Allah ki shigo
ki sha ruwa ki dan huta kan ki tafi sai naga ta danyi jim kafin ta sake
murmushi tare da fadin nagode yar nan na bude part dina muka shiga na kaita
daki na dawo kitchen na hada mata ruwan sanyi tare da dan kankara a ciki a wani
jug din tangaran karami tare da kofi na kai mata tana zaune tana bin dakin nawa
da kallo.

    Saidana tsiyaya
mata na mika mata cikin ladabi ta karba na daga na koma gefe na zauna tasha ta
kara ta dago tana fadin nace ko kece sarakuwar nata dama ?

   Dan murmushi nayi
na dukar da kai nuna alaman kunya ga maganan nata taci gaba da fadin kai
gaskiya idan kece ni banga alaman wani matsala a tare dake ba da gyara wandkn
ke fada a kanki ko yaushe gaskiya.

   Har in bakonta
zaizo gidan nan bata nan ai masa wanan taro na mutunci duk da baki sanni baki
san inda na fito ba amma ki karbeni haka hannu bibiyu babu kyama gaskiya na
yaba da hankalinki ba zan boye maki ba.

   Murmushi kawai na
sakeyi itako tana cigaba da fadin kinga ki kara hakkuri tunda baki da matsala
da mijjn ki banga abin damuwa ba a nan din har yaushe akai auren ku da zata
fara  korafin cewa baki samu ciki ba har
yanzu ita aure zata karawa danta ai.

    Nasan yadda kika
min har naji dadin nan haka kikewa kowa a gidan nan amma bata ganin hakan ita
tace kina masu daukan kakai kina juya mata da don kina takaman gidan ku suna da
kudi.

   Bayan tayi bincike
ance bakowa kike ba a gidan naku da sauran dai maganganu irin na bata mutum a
bakinta a kanki.

   Bayan duniya sun
sheda aure irin na soyayya kukayi keda dan nata kowa yasan da hakan ko kallonki
mutum yayi yasan kedin ai ba kallan gidan nan bace amma ita ta kasa gane hakan.

  Na rasa hankali irin
na gyara wandon ka me takeso a duniya wanda danta yanzu ya rageta dashi kada
kice na faye zuba daga zuwa na zauna ina sake zance haka ko munafuka nake .

  A,a wallahi abinne
na kasa hadewa a raina ko ita zan mata magana kan hakan idan zata gyara ta
gyara ta barku ku zauna lafiya da mijin ki.

   Don yadda ta dauki
dammaran rabaku tako wani hali yanzu in ance wurin wani malamin nata ta tafi
akanku ba a musu bayan an fada mata tun farko abune mai wuya abinda take so ya
faru tsakanin ku.

   Ni zan tafi na fada
makine don ki sani don nasan ba wanda zai iya taron ki ya fada maki komai
aka  hakan a unguwan nan kaf don sanin
halinta niko kar ta san kar da ita ai.

   Numfashi na sauke
tare da fadin mama nagode kwarai insha Allahu zan kiyayye ta mike nace ina zuwa
na shiga daki na dauko mata turare da sabulu nasa a leda nafito lokacin har ta
fita waje tana bin kitchen dina da kallo tana fadin .

  Idan ba tsiya irin
na gyaran wando ba arziki irin haka yacin ma har gida kai kace baka sanshi ba
sai bakin kishin tsiya da matar danka da takeyi.

  Daga bayanta nayi
magana ina fadin gashi mama ba yawa ki rika da hakkuri nagode sai ga Aisha ta
turo kofa  ta shigo.

  Irin yadda naga ta
kalli mata ta gaida ita a taatsaye ta samu wuri ta zauna ya kara ban mamaki
nake fadin bakuwar innace fa tazo bata sameta ba.

   Tace aina santa
taci gaba da kallon dan wayanta na nokia dake hannunta tafi batu  mu nadan rakata iya kofana mukayi sallama ta
tafi ta barni cike da mamakin maganganun ta.

  Muryan Aisha naji
tana fadin naganeta ai bandai son hurdan su da innace don matar irin matan nan
ne yan karya masu zaman kansu.

   Su innan mu yanzu
take bi suna karya sun girma basu san sun girma ba ga yawan cin bashi da karya
da suka sawa kansu kesan innan mu yanzu wani famfarewa ne kuma yazo mata tun
rasuwan baban mu.

  Koda yake kafin ma
ya rasu din ko acan haka suke fama da ita da yawan dauko mashi magana a wurin
matan nufawa da muke zaune dasu a can.

    Zama nayi gefenta
anan wajen ina fadin ba Djje tace min kinje kitso ba dazun ya naga kuma kin
dawo baki kitson ba kuma ?

   Wallahi naje na
samu mai kitson ta tafi unguwa wai suna bukine yau kila saida yamma idan ta
dawo ko kin iyane ki mun don Allah ta fada tana kallon fuskana.

   Murmushi nayi nace
ban iya kitso sosai ba amma ina dan kamawa tace ko yayane dai don Allah ki mun
don gobe kada in shiga mutane dakaina haka kinsan akwai bukin nan cikin gida da
za ayi goben ko ba a fada maki bane ta dago tana tambayana.

    Wazai fada min
Aisha kila sunga bukin bai shafeni bane yasa ba a fada min ba koma an fada
kinsan Master baya gari ba lalai bane in tafi tunda bai nan.

    Kuma gaskiyane don
nasan yaya yaji labari kin fita zuwa buki baina yana iya yin fada gashi ko
banza ba shiri sukeyi da gidan ba don sun tsani kowa namu.

  Dijece make fada min
dazun cewa abin ya samo asaline tun bayan rasuwan mijinta malam Ladan yan uwan
nasa suka tsani yayanta din har muma abin ya shafemu.

   Balle suna muna
kallon tallakawane a cikin su ko abu sukeyi basu faye saka mu ciki ba tunda mu
bamu da irin tufafin yan gayu irin su.

   Ke Aisha ki godewa
Allah kowa da abinda Allah ya bashi yake shiga yan uwa kin gani nan ban faye
damuwa da irin abubuwan nan ba balle ko bamza ni ba buki nake zuwa ba dama.

   Gara dake ko banza
ku yan gayune ba wanda zai maki wanan kallon amma ita innan mu bata damu da
hakan ba haka take kokarin cunamu cikin su wai sune dai yan uwan nata.

   Ko wanan bukin
kafin yaya ya tafi saida ta matsa mashi ya bata kudin da zata bayar na bukin a
cikine naga ta sai wani atamfa ta dinka waishi zata goben muko kinga haka zamu
shiga da tsofin kayan mu suna muna kallon banza.

   Mikewa nayi na
shiga daki na dauko cumb da tsinken kitso ina fadin zauna nayi maki kafin innan
su dawo ta samu kin shigo nan din.

    Wai ashe kema
kinsan tana hanamu shigo wurin ki yanzu Dije tayi maganan hakan tace wai bata
son wullakcine kada ki dauka don abinki muke binki nan.

   Aiko hakan ma
nagode kisan kowa da nasa irin fahintar ai daga hakan naja bakina nayi shiru
Allah ya taimaka mukai kitson har lokacin bata dawo har muka dora indomie a
wuta mukaci tare a plate daya muna hira tana ban hiran zaman su Niger.

   Bamu dade da gama cin abincin ba sai mukaji
shigowan su gidan ta tashi ta tafi lokacin nayi sallah na gyaro part dina na da
muka dan bata.

   Na koma zaman
kadaici don Aisha din ta dan debe min kewa da sato hanyar da takeyi din ta
shigo wurina nakan ji dadin hakan sosai a raina.

  Don zaman kadaici
baida dadi ga mutum ko ya yake kuwa gara kana dan magana da wani duk da bawai
ina samun hakan bane ko wani lokaci kuma daman hakan ba damuna yayi ba.

  Amma kuma gashi uwar
su yanzun tana skn sakani wani hali a rayuwana wanda bansan dalilin hakan ba a
yanzu.

   A wanan zaman ne
naji zancen wanan matar kawar inna data kira kanta da yar Giwa zancen tane
tiryan tiryan yake dawo min a zuciyana.

   Naga laifin me
nayiwa innan su Ahmed haka ta tsani sai naji ina son yin wanan zancen da wani
ko zan samu mafita duk ban taba yin wani zancen ta da kowa ba ni kadai nake
shanye abina a raina duk abinda akai min din na cin fuska.

   Saida ba zan iya
wanan maganan da ummah ba don nasan itama tana can da nata tarin matsalolin datake
fuskanta gidan wanda kullun bai karewa garesu.

  Hannatu ya kamata na
kira zuciyana ya bani hakan duk da shekarun mu dayane ba wani shawaran zansamu
da zai gamsheni ba amma ita din ya kamata na kira na fara jin me zata fada min
kan hakan.

   Kiran dana danna
mata sai gashi ya shiga ta dauka tana fadin yar halak yanzun nan nagama zancen
kifa a raina wallahi tun shekaran jiya ba muyi waya dake ba.

   Wai kina inane
yanzu ko kin samu tafiya sokoto din ne na tambayeta don mu katse zancen data
dauko din a lokacin nasan tana iya bata muna lokaci da surutunta a hakan.

   Wallahi ina gusau
dai ban tafi sokoton ba har yanzu don wanda zanbi din baizo weekend ba nace kai
hanne akwaiki da son banza yanzun don dan kudin motan da zaki biya kike garin
nan nan har yanzu ?

   Bayan kin sakawa
gwaggo ran zuwan ki yanzu ki zauna kina jiran bati a nan tace ke an fada maki
kowa irin kine da Master ya kamawa kina yadda kikaga dama.

    Humm wani master
ni dama na kira najine idan kina gari akwai zancen da nake son muyine dake don
abin ya daure min kai sosai wallahi.

   Da sauri naji
yanayin muryanta yai kasa tana tambaya meke faruwa kuma zahra nace sai kinzo
zakiji komeye but kada ki damu ba don ba komai bane mai yawa.

   Da haka muka kashe
zancen da ita akan washe gari zata shigo wurina mukai sallama ta kashe wayan
har lokacin ina faman sake sake a zuciyana nako in fada mata ko kuma nayi shiru
kawai in bar zancen a ckkin raina.

   Saidai wanan zancen
tafi karfin na barwa cikina shi don in dan tuntubi wani inji wani shawara zan
samu na sake cusa kaina gun uwar mijin nawa da nake ganin hakan shjne mafita a
lokacin.

    Sun fito daga
lectures yana sauri ya koma masaukin su don azumin daya wuni dashi a bakin shi
ga azumi ga kuma faduwan gaba da yake ji a ranan yana damun shi wanda hakan
yasa shi kara zama shuru a lokacin. 

   Ya iso gidan da
suka kama suna zama shida abokin shi babu kowa haja yasa ya bude dakin ya shiga
ya samu wuri ya kwanta don akwai sauran lokaci da zai dan gangara bakin titi ya
dan sayo abinda zaiyi buda baki dashi lokacin.

    Barcine ya
daukeshi a hakan ba tare da niyar hakan ba a lokacin can ya fara mafalki da ya
bashi mamaki    don mahaifin shine ya
gani a gaban shi yana tsaye nisa dashi kadan .

   Sunawa juna kallon
kallo kafin yaga ya miko mashi hannu alaman yazo gareshi sai yaga wata mace
tazo da sauri ta shiga tsakanin su yana ganin hakan shi kuma juya ya bar wurin
da sauri kafin mahaifin nasa ya farga da hakan .

   A daidai lokacin
kuma ya mike zubur daga barcin nasa tare da wani irin zufa dake karyo mai duk
da yabar kofan dakin nasu a bude amma zufa yakeyi har yana tsiyayo mashi ya
jike sharkaf duk jikin shi.

   Zai iya cewa wanan
ne karo na farko daya taba mafalki da mahaifin nasa irin haka sai abin ya fara
bashi mamaki gashi shi kadai a dakin nasu lokacin.

   Macen nan fara da
yaganine ta fado mashi a rai yake mamakin ita kuma wacece a garesu datazo ta
shiga tsakanin su a lokacin da baisan abinda mahaifin nasa keda niyar fada
mashi ba.

    Daba don yamma
yayi a lokacin ba da zai koma barcin ko zaiyi sa,a yaci gaba da wanan mafalkin
da  baisan dalilin zuwan shiba gareshi a
wanan lokacin.

   Haka yasha ruwa a
dadare ranan bai samu tabukawa kanshi komai ba don ko dan karatun da yakayi
bita a lokacin bai samuyi ba don yadda yake jin kanshi cikin damuwa a lokacin.

   Waya dai ya samu
yayi da sahibarsa Zahra yaji lafiyanta dana mutanen gida a bakinta a nan take
dan fada mai zancen bukin da za,ayi a cikin gidan nasu da suke kira da babban
gida a wajensu.

   Take ya katse ta da
zancen yana fadin Zahra kibarsu da bukin su don mutanen nan ba kaunata sukeyi
ba zahra kinsan sani ba wanda cikinsu da yake nuna damuwan shi a kaina don haka
kija nisa dasu kamar yadda nima nake nisa dasu a yanzu din.

   To amma Master
kasan akwai hakkin zumuci tare da hakkin makwabtaka dasu ba zasu dauki hakan da
laifinsu bane sai suga namu laifin ne a yanzu.

   Haka kuma Allah ba
ruwan shi da wanan dalilan donshi ya sharada da ayi zumunci a tsakanin zumu
kaga hakan sai, , ,

    Zahra ki barsu
idan lokacin yayi zamuyi zumuncin dasu amma ba yanzu da suke muna kallon
fakirai ba a idanun su.

    To shike nan ta
fada a sanyayye yadda tai maganan yasan zancen bai mata dadi ba a ranta amma
gudun bacin ranshi yasa ta amsa mashi kamar yadda yake son ayi.

  Irin wanan halin
nata yasa yake kara jinta a rashin don zahra ta daukeshi a na gaba da ita sosai
yake jin sonta a ko yaushe yana kara shiga zuciyar yadda bata nuna cewa ita din
mai gatace fiye dashi a zaman su na aurataya tana tsayawa a inda ya ajeta a
rayuwan ta.

 

 

Leave a Reply

Back to top button