TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 50

Sponsored Links

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/15, 3:38 PM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣0️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Sautin kukan ne ya kara dakan kunnuwa lokaci guda zakice a
cikin dakin akuyan ke wanan kukan jin hakan yasa na zabura da sauri na mike na
nufo kofan falon da sauri mukai karo da juna dashi har sai da kowan mu ya kadu.

   Shi yayi saurin
fadin subbahanallahi zahra lafiya kuwa na ganki haka a firgice a daidai lokaci
akuyan ta sake sake wani kukan da karfi kuma jere da juna batako ajewa take
sake wani.

   Ai bansan lokacin
da nayo cikin shiba a firgice na cakume shi ta baya shiko yana fadin wai akuya
kikewa wanan tsoron haka dama zahra ?

    Akuyatace kila
abinci takeso ko wani abin barin fita in dubata ga kayan karyawa nan a falo na
aje maki don na shigo na samu kina barci na fita zuwa wurin su Dije.

   Ganin har lokacin a
tsorace nake don ban sakeshi ba yasa shi fadin dawo nan ki zauna a falo har in
dawo sai in hada maki ruwan zafi kisha.

   Sallaman hannatune
mukaji tana ta kwada sallama daga waje bata kai ga shigowa cikin part din namu
ba,  ba kuma wanda ya karba mata sallaman
ta a lokacin.

   Saishi ya daga
murya daga ciki yana amsa mata tare da dan takawa nima nabishi baya don har
lokacin duk a rikice nake ta turo kofa tana fadin gaku kamar fita zakuyi mana
naganku ?

   Ke san amaryan tawa
motsoraciyata akuya kawai tayi kuka shina kika ganta haka a firgice ta barima
in fita in duba me akuyan keso ta hana yanzu.

   Ashe ciwon kan ya
lafa dan hakane fa na fito don hankalina jiya wallahi ya daga sosai yadda  muka barta a kwance ashema da sauki don gata
na ganta garau yanzu.

    Gaskiya master ka
iya jinya daga dare zuwa yanzu jikin har ya lafa haka a cikin sauki sai naga ya
sake wani shu,umin murmushi a fuskan shi yana kokarin jayewa daga rikon da nayi
mashi

   Sai lokacin na
sakeshi nima don na fahinci me take nufi,
na nufi wurin kujera na zauna ina sauke nufashi koshi don naga hannatu
ne a dakin nasan koma meye zata iya cetona kanshi ai.

    Daga haka shi kuma
ya fice ya barmu tare hannatu din ta kalleni tace aina dauka ko kofa baku bude
ba yanzu har inno tana ce min wai waya fada min ana wanan sakkon haka gidan
amarya da ango ?

    Wani kallo na
watsa mata tare da fadin ai gaskiya ta fada maki uwar gulma kin dako uban
safiya haka kinzowa mutane gida don ki damesu.

   Yar iska da ace
kedin ba matsoraciya bace zakice min haka jiya nan kika tayarwa mutane da
hankali waike ciwon kai don bakin tsoro kawai kin dagawa dan mutane hankali har
yana sabari a gaban abokanshi.

   Tsuki naja tare da
fadin dama shi ya kawoki ko yanzu sai ki kara nadewa ki tashi ki gyara min
wajancan don bamson kura kin sani.

    Ai wallahi baki
isa ba ni fa naman nan nayo samako naci don nasan baki iya cinyeshi duka jiya
tunda tsoro ya hanaki lakka.

   Kaji munafuka amma
cewa kikayi don jikina kikayo sanmako yanzu din kuma kin buge da fadin a baki
ragowan nama kici to anki a baki din .

    Nasan koma zakici
ba zaki cinyesa duka ba don haka ba zan wani damuwa ba don nasan yana nan
nawatsa mata wani kallon takaici nace idan kina so je yau a daura maki aure
kici.

    Ai muma zamuyi
auren nan dai muji don gashi jiya jiya anfara muna gorin akanshi babu ko kunyar
hakan kamar ba jiya kike nan kinawa su mommy raki ba.

  Murmushi na sake
daga inda nake zaune nace kedai kika sani in zaki tashi ki dauko cup kizo ki
karya ki tashi kafin wani ya shigo kuma.

   Ai kuma kin fada
min gaskiya abari ya huce shike kawo rabon wani ta mike tana fadin hakan ta
fita zuwa kitchen din kafin ta dawo nakai kwance saman kujeran.

    Ta shigo tana
fadin waini har yanzun ina mamaki na shigo ina ta sallama ga kannen Master ina
gani amma sunki karba min saida naji muryan master na shigo nan.

   Wata kila basu jiki
bane amma ayi sallama su kyaleki kuma a lokacin ya shigo da alama ya dauraye
hannayen shine don ganin damtsen hannun shi da nayi da ruwa.

   Hannatu dake duke
tana hada shayi taji kunya sai cewa taji yayi kinko kyauta min hannatu da kike
hada maku tea din nan bari ni in shiga in dan watsa ruwa in fito.

    Ya shige ya barmu
nan muna hiran bukin wanda hannatun ce ke firan sai jefi jefi nakan dan bata
amsa don irin yadda nake jin kaina a takure a sabon wuri ji nake kamar bakunta
nazoyi a wanan wajen da anan yanzu zanyi rayuwa.

  Ire iren wanan
tunanen ne suka tsaya min a zuciyata inda nayi sa,a shine na kula Ahmed mutum
ne mai tsabta sosai shi da wana  na danji
daman wani a rayuwata yadda nake da tsanda din nan yasa ko a gida kowa baya
shiga dakina ba a kuma taba min kayana.

  Gashi yanzu zanyi
rayuwa tare da wani wanin ma namiji a daki daya tare dashi  kaya kan iyayyena sun kashe min kunya gaskiya
duk da gidan ba wanigidan fada ba amma gyaran wurin ya tsaru da kyau komai an
matsashi an saka min a dan wajen nawa.

    Ya fito tsab dashi
cikin wani sabon dinkin shadda mai ruwan toka sai alaman saura dan ruwan wankan
da kakanga shafin a jikin maza wani lokaci idan sunyi shiri wanda suba mata
bane da zasu tsaya kakale kansu wurin gyaran jikinsu.

    Hannatu kina nan
ko barin dan fita na dawo don Allah ga matana nan ammana na bar maki sai
hannatun tace kai Master ban dauki wanan amanan ba ai saidai ka bar mata ni
amana matsayina na bakuwan ku a yanzu.

    Nikan hannatu
karki kasheni don Allah na fada ina dan murmushi ya dan sake murmushin jin
dadin ganin mu na fara sakewa shugowan hannatu gidan.

  Ya dago yana fadin
to madam Master ni zan fita ko akwai wani abinda kike so a sayo maki idan na
fita ya tambaya yana kallon fuskana na dan girgiza kai ina fadin Allah ya bada
sa,an fita ya dawo min da kai lafiya.

   Amma kuma baka
karya ba naga zaka fita daka dan tsaya ka saka wani abu a cikin ka kafin ka
fita ai na fada ina mayar da hankali a gareshi.

   Wanda na fadi hakan
ne don hannatu don nasan ba zata kyale ba lokacin aiko ban kai ga rufe baki ba
naji muryanta tana fadin a, a, a su aure manya har an fara yiwa miji fatan
alheri irin haka ?

   Da wani
marairaicewa missa baki tashi tun asuba kin hada mai abin karyawan ba zaki
barshi ya fita haka yanzu ?

   To Yarsa ido shiya
kawoki gidan nan tunda safe haka don ki dinga sakawa mutane ido ni har kinsa
ina son auren yanzu shidai ya fita yana murmushi don yasan tsakanin akwai yar
haka dama.

   Yana fita muka
canza topic din hiran mu dan cewa hanne tayi a gaskiya zahra kamar zakiyi aiki
da mutanen gidan nan don fa yanzu da zan shigo nayi ta sallama ba wanda ya amsa
min .

   Saima lekowa da
wata budurwa tayi tana ganina a kofan nan taja tsuki ta juya tun dazun abin ya
tsaya min a raina wallahi.

    To meyasa hakan ke
baki kula ko ranan da sukaje gidan ku da sunan zuwa ganin amarya ai haka sukai
ta wani mere baki suna maganan gidan naku wai ba a darajasu ba don angasu basu
da komai.

    A lokacin ne mommy
ta aiko a kawo masu abin zama da drinks a nan fa suka so raba hali a tsakanin
don sun manta ina wajen don akwai yan unguwar nan dana sani cikin su.

   Har wata na fadin
waisu ba a basu abincin da suka gani ana ta rabone saida wata cikin su ta
tsawata masu tace kada su barwa Master abin kunya don Allah suka natsu.

   Saiga abincin kuma
mommy ta aiko masu dashi suka kuma karba murmushi kawai nayiwa hannatu din
kafin nace kai irin wanan ni bai faye damuna ba yaushema nake da lokacin suni ?

    Ai dole kiyi
lokacin su tunda yanzu dasu zaki zauna ya zama dole kiyi taka tsantsam da kowa
ki fahincesu kada kiyi saurin sakewa dasu tundai kanen nan nasa da alaman
rashin kunya a fuskan su.

    Shiru nayi ina
tune kafin na nisa son na hango alaman wani matsala kuma a nan bayan wanda na
baro a gidan mu can anayi wanda har yanzu
ummah tana cikin fuskantan shi.

   Da farko dai ki
mayar da hankalin ki sosai Zahra wurin yiwa mijin ki biyayya ki nuna masa kauna
kamar yadda shima yake nuna maki a gaban kowa don tsakanin daren jiya zuwa yau
na fahinci wasu abubuwa game daku.

  Kada ki yarda koda
wasa a samu matsala a gurin ki zahra don mutane sun bude kunnuwan su sun kuma
baza ido sugani ko zaki iya zama da master a hakan.

  Ko ita mama data
masa sunyi hakane don su bata maki suna a karshe a koma ana zagin ki cikin gari
wanda kuma su da kansune zasu baza maganan naki a gari.

   Sun dauka ba zaki
iya rayuwan talauci irin haka ba don idan anyi daga baya kin kasa zama a dawo
ana maki lissafin dakin auren ki.

   Hausawa sunce idan
ka kure dakin farko yanada wuya ka sake samun irinshi a rayuwan ka din haka
zahra ki kwanta ki bisu da halinsu ki kara hakuri bisa ga wanda kike dashi a
baya.

  Shi aure dama dan
hakkuri komai dacen mace da gidan hutu ko inda takeso saifa ta hada da hakuri a
zauna lafiya don haka ki zamawa Master diya .

  Shima haka ya zama
maki da don kinyi mai abinda bako wace yarinya bace a yanzu zata iya hakan ga
namiji duba ga yadda rayuwan ya koma yanzu kowa na son jin dadinsa.

   Amma in akwai ci
dasha da sutura duk wanan mai saukine sai mace ta zauna tayi hakuri don ba
wanda yasa ya gobe zatazowa bawa karshe.

    Haka ki jajirce
dkn Allah ki kula wurin bashi hakkinshi na da namiji ki kawar da komai a
zuciyar ki kada ki dauka wai kin fishi gata a gidan ku a, a zahra ki kwanta
mashi Allah ne ya basu su maza wanan matsayin.

   Haka karki yarda
koda wasa kiyi rauni a wurin girki don ko ba komai kiyi kokari ki girka masa
abinci ko wani irine don kinsan an camfa matan yanzu a wurin girki an barsu
baya.

   Don haka yanzu an
saka ido an baza a dandana girki aji dama kuma an dauka diyan masu hannu da
shuni baku iya aikin komai ba hakane ke yawan jawo matsalan aure da yawa yanzu.

   Zama na gyara na
lumshe idanuna ina jin maganganun hannatu din kamar na wani babba can a kunnuwa
kiyi hakkuri wata rana sai labari insha Allahu dan hakin daka raina shike
tsonema ido.

    Shiru nayi sosai
ina sauraren ta don nasan iya gaskiyan da duk mai kaunata tsakani da Allah zai
fada min ke nan irin wanan zance da hanne ke fada min a yanzu din.

    Sallama akayi a
kofa hakan yasamu katse zancen mu su mommy ne dasu mama Geshuwa yar ummah
sukazo don na daukama sun tafine don naji a ranan ne zasu tafi.

    Saidai basu shigo
part din direct ba kamar yadda hannatu tayi su sun wucene part din mutanen
gidan suka gaisa dasu tare da masu ya gajiyan taro kafin su fito zuwa nawa part
din.

    Suna shigowa na
mike ina gyara mayafin kaina na rungumesu daya bayan daya ina gaidasu suna min
ya jiki ya kuma kwana a bakon wurin ?

    Na danyi murmushi
kawai bayan sun dan zauna can mama Geshuwa ta mike mommy ta bita da sauran
mutum hudun da suka shigo dukkan su bakine sunzo sha,anin bukin ne lokacin.

  Kitchen suka shiga
sun dan dade a ciki kafin su fito da wasu buhuhuwa suka hada da kayan da sukazo
dashi mommy kubura tace oya tashi mu shiga ki kimtsa mu kaiki wurin sararkanki
ku gaisa.

   Don tun jiya suka
fara korafin wai ba a kaiki ba kun gausa an basu darajansu gareki Allah yasa
naji na dawo ba basu hakkuri kan baki da lafiyane.

    Ta tafuto hannatu
tace zo mu shiga ki tayata kimsatsawa hannatun ta taso muka shiga dakin tare
shiga na kwarai na alfarma mommy da hannatu sukai mun.

    Muka fito gaba
dayan mu zuwa part din nasu suna zaune da wasu baki mukayi sallama aka shiga
nan suka fara kame kamen gyaran wuri da kyar muka samu inda zamu zauna.

    Nan aka shiga
gaisawa kafin mama Geshuwa tace dasu to inna ga jikanki nan kuma yarki mun kawo
maku ita amana don Allah idan tayi ba daidai ba a tsawata mata a sakata a
hanyan daya dace.

   A,a ga uwayen su
nan zaune tsohuwa Dije ta fada nikan kakace garesu amma ba laifi ai wanda yace
yanayi da danka ya gama maka komai a duniya.

    Zahra ki saki jiki
nan kamar gida kikazo ga uwar mijin ki nan ga kannensa muyi zaman mu lafiya
keji kaina a duke yake kasa kuma na dunkule a tsakankanin gwiwana sai hawaye ke
zubo min lokacin.

   Wanda ba zan iya
fadin kona meye ba gadai hawayen ina zubarwa zan baka tausayi sosai a yadda nake
zaune can sai naji muryan mahaifiyarshi na fadin.

   To kesan dai muna
da yara mata a gidan nan dole sai kin hada da hakkuri wurin zama dasu mommy ce
ta katse ta da fadin ai ko gida tana da kanne itama .

  Iyaka dai kowa ya
tsaya matsayin shi su bata girmanta na matar wansu itama haka ta dubesu a
matsayin kannenta saikuyi zaman ku lafiya dama hakane.

    Me zai kaisu
wurinta in ba sa ido tana gefenta suna nasu kudai Allah ya bamu zaman lafiya ya
kawo kazantar daki da wuri tsohuwa dije ta fada kamar tana katse zancen da aka
dauko din lokacin.

   Nan dai naji mama
Geshuwa tace ga dan abinda ya samu nan daga waje na uwayen miji kuyi hakkuri
dashi hakana gaba dayansu suka juya suna kallon kayan da aketa shigowa dashi
part din.

   Daga nan naji mommy
ta dagoni muka mike zuwa nawa part din mommy kamar tana jurane mu shige naji
tana fadin.

   Zahra sai kin
jajirce a wanan gidan kada ki kuskura ki koyi wanan halin   nasu ko kusa gida da kazanta haka kamar ba
mata a cikinsa harda yaran mata amma kaya haka gajal ko ina.,

    Ai ba zata koyi
wanan halin nasu ba tunda bata taso a cikinshi saidai idan taso amma yaro na
tashi wurin sallama bai koyi tsabta ba.

  Wace saboda
tsabatanta har muna tsamanin shiya hanata samun haihuwa da wuri maman Zahra
akwai tsabta kan gaskiya don komai nata tsab yake.

  Mommy ta amsawa mama
Geshuwa din data fadi hakan kafin su dawo kuma kaina suna fadin yanzu idan mun
tafi ki tashi ki dora girki ga kawarki nan ta kama maki ku hada abinda zakuci.

   Hannatu ta amsa da
fadlin dama zamu dora ke nan kuka shigo hakan nada kyau gaskiya kada ki yarda
kiso jikinkin ki ki jajirce sosai kinji Allah yaiwa auren ki albarka aka amsa
da amin

   Na kuma ji wanan
uwar mijin naki na wani zance kan yayanta kada ki yarda ki basu fuska da zasu
raina ki ki tsara girman ki bawai sai kin sake masu yadda raini zai shiga ba
don su din kinga kamar jahilai suke.

    Don in raini ya
shiga tsakanin ku daga baya ko kinso gyara hakan ba zai yuyu ba shi kuma
mijinki ba zaiki yan uwanshu ba ya goyi bayan ki don haka kisan yadda zaki
zauna da kowansu.

    Sun kai wani
lokaci kafin suyi min sallama su tafi muka mike muka gyara gidan nida hannatu
muka dora girki kamar yadda sukace nayi din .

   Sai yamma lis
hannatu ta tafi nima nayi wanka na canza kayan jikina zuwa wani dogon riga mai
laushi a jikina na saka kamshi a jikina da dakin na zauna ina jiran a tayar da
sallah.

Leave a Reply

Back to top button