TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 22

Sponsored Links

 

 

 

Don Allah kada ka/ki gangancin juya novel din nan ya koma
audiovisual na saurare don riga da na sayarwa wasu dashi already yin hakan zai
iya jawo shari,a a tsakin ni dake dasu don Allah a kaucewa hakan nagode.

    Zan iyacewa wanan
watan mai alfarma da muka shiga shi yajawo shakuwa da yarda da amincewa kana da
amana gami da sabo a tsakani na Ahmed sosai fiye da tsamani.

  Wanda a waya zamu
tsaya muyi hira sosai kona sana,arshi ko abinda ya shafi karatuna haka wanda
idan a filine ba zamu iya tsayawa da juna muyi magaba mai tsayi haka ba a
tsakanin mu saidai a waya din.

   Saiya kasance shakuwa
mai tsanani ya fara shigar kowan mu tsakanin shi da dan uwa koda kuwa yana gun
sana,ashi zai kirani yana fada min halin da ake ciki.

   Wanda nima hakane
ko zaune nake ni kadai zan iya kirashi kawai naji muryan shi mu danyi magana
sai in kashe wayata haka kuma lokaci lokaci idan yaje kauyen zai yo muna
tsaraban irin su kwan zabbi wataran ma zabbin da ransu kamar uku ki biyu yace a
gyarawa kanwarmu autan mu tasha ruwa dashi.

   Hakama kayan lambu
irin na shan ruwa zai sayo ya tsaya a waje yaba maigadi yace a kawowa Amira
tasha ruwa dashi itako yarinyar ta fara fada da duk wanda ya taba tana fadin
nawane mijinane ya sayo min.

   Da farko daya fara
hakan  ummah ta titsiyeni wata rana a
dakina tana tambayana meye tsakanina da Ahmed da har yake min wanan sayayyan
haka ?

  Kallon ummah din
nayi cikin ladabi a tsigar mamaki nace ummah Ahmed fa ba komai wallahi
tsakanina dashi illa daukan kanwarshi da yake min shine kawai a tsakanin mu
dashi nan nake fada mata kamar yadda ya fada min shi cewa.

  Da yake zumunci damu
yana jin cewa mu din kamar yan uwanshi na jinine sosai don a duniya ba wanda ya
taba daukan shi da muhinmanci har yasan shi di
mutum ne kamar kowa bayan haka ba komai wallahi tsakanina dashi ummah.

   Saida tayi min wani
irin kallo tace ki daibi sannu ummah din ta fada dan ke yarinyace karama har
yanzu kisan kuma yadda ake son ganin bayan mu a cikin mutanen nan don haka ki
natsu ki kama kanki.

    Toh umma na fada
ta juya ta fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya tare da dan tunane a kan
maganganun da ummah din tayi dani lokacin.

    Ko ya akayi mama
ta sanda wanan zancen har labarin Ahmed din yakai kunnen ta oho sai gashi tana
sakewa ummah habaici da fadin kwadan mutum ya kaishi ga halaka.

   Mudai mun godewa
Allah diyan mu suna da farin jini daga mai jeep sai masu benz ke sallama muna
ba fakirai yan ya Allah kuci ku bamu ba kazo ka sayar da akuya ta dawo tana
cima danga a gida kuma.

   Nan ummah ta dago
da zancen da mamakiyi din a lokacin ta gane metake nufi da hakan abinka da uwa
take ran ummah din ya baci da hakan.

    Ita kuma tace da
fakiri da mai kudi duka Allah yayi su yasan da zaman kowa zaman lafiya da
kwanciyan hankali akajawa ba sunan auren mai kudi ba kwanciyan hankali ba.

   Mama din tace kuma
wai ummah da ita takeyi tayiwa diyan ta mugun fata to wallahi ta Allah bata
mutum ba sanan ba hakan akaso ba wai kanin miji yafi miji kyau an dauka yar
zinaroce zatayi sa,an maza don fari da kyau sai gashi Allah bai bada mai abin
hannunsa ba sai wani fakiri ya kawo kanshi don kwadayi.

    Wanan abin bai
kawo kallo ba tsakani ku gwaggo habiba dake biwa Abba wurin haihuwa ta fada don
a gidan hjyn su Abba abin ya faru sunje gaida ita da sallah.

   Kuma amaryan su duk
tana wurin itama don Abba ya tsaya sai su fito su tafi tare su hudu shi yana
waje lokacin da wanan fitinan ya faru din baisan anyi ba.

    Mafari kuwa wata
tobashiyar mu ce ta kawo maganan tana fadin mama ina yan matan kine suwai basu
fitane suna gida ko yaushe kumshe kodai basuyi kasuwa bane a hada su dasu Ali
dacewa yayanta namiji shima abokin wasan mune.

   Shine aka fara ba a
har mama takaiga fadawa umma wanan maganan a bainan jama,a sai ran ummah din ya
baci ta kasa hakkuri ta bata amsa.

   Harda dorawa wai ba
aso dai hakan ba din ba haka akai zato ba gareni an shiga boka an shiga malam
ai farin jini abu taki ummah tace indai wanan ne kanki kikewa terere a fili don
ansan mai mu,amula da shirka .

   Haka suka kwasa
suka dawo gida ran kowa a bace shi Abba ya dauka don fitan da yasasu yi dolene
a tare lokacin yasa kowan su shan toka sai daga bayane amaryan shi ta fada mai
abinda ya faru a can din.

    Ranshi ya baci
sosai da jin hakan ya tarasu a falonshi yana tambayan ba,asin abinda ya kawo
hakan har suke mai cin mutumci a kan diyan shi.

    Ni dai naga sun
dawo inawa ummah sannu da zuwa da kyar ta amsa min ta shige dakinta ta rufo sai
kuma can naga ta fito zuwa sashen Abban mu can ma ta dade bata dawo ba.

    Bayan sun zaunane
Abba ya kalli mama yace maimuna meya jawo fitina tsakanin ki da salma gidan hjy
kuka tonawa kan ku asiri hakane ?

   Daga inda hjy
karima ke zaune tace uhumm tana gyara zama Abba din din ya kallota ya gane me
hakan ke nufi datayi sai kuma ya juya da fadin ke salma yaya akayi hakan ya
faru ?

    Ba ita ka tambaya
ba ta fada maka don ni bansan da zancen da take fada ba sai ji nayu a bakinta
kawai na kuma bata amsa a lokacin don tasan koda tallakane ma dashi da mai kudi
duk daya suke a wurin Allah.

    Meye na wani
kwanaye kwanaye a nan in ma wani ya kawoma gulman haka na fada don abune a
zahiri dana fada kuma ita salma gata nan nace da zarah nakeyi ko me ?

   Zarah zarah fa kika
fada maimuna a gabana yau ita mamana din kike fadin sunan ta haka gatsau a
gaban nawa ?

   Zarah din ba sunan
ta bane ko itace hjy da dole zan dinga sakaya sunan nata ko wani lokaci,  yace yayi kyau yana gyara babban rigar daya
dora saman fatan jikin shi.

    Yanzu dai barin
fada maku kuji idan kuna tsiyatakun ku kubar hada min da diyana don nina
haifesu dukkan su kuma ba wani da dana haifa a gidan nan da ban nuna mai so ba
a cikin diyana.

    Don haka tsiyan ku
ya tsaya iya kanku kuji sanan zancen maza har yaushe aka fara yi min haka a
gidan nan ban sani ba yaushe suka zancen wasu samari can har hakan ya faru ?

   Ke salma wani yaro
ne ake magana a kan shi da yake son zarah sin ina zarah karatu takeyi yanzu
yaushe har ta fara kula maza haka kika barta har wani na zuwa gidan nan wurin
ta.

    Shiru ummah tayi
don takaicin da yake cin zuciyanta sosai a lokacin ba zata iya yin magana ba
don zata iya fashewa da kuka lolacin don bakin ciki.

   Ya juya wurin mama
yace wani yarone wanan din nace ai gata nan ni ina zan sani nadai san na taba
ganin su a waje suna hira ni zan fita ya tsuguna ya gaidani haka kuma na samu
labarin yana yawan zuwa nan get din gidan nan ya kawo abu yace abawa Amera wai
.

    A gidan nawa har
wani zai kawo abu yace abawa yata salma ni ban sani ba me kuka rasa a gidan nan
yanzu ko a wani fanni na rage ku dashi wurin kula da iyalina ?

   A,a Alh kowa yasan
hakan ba gazawa bane duk da banso saka bakina cikin zancen ku ba amma ya kama
dole saina saka yanzu shi alheri ki kyautatawa gun mace ba duban wanan a cikin
shi.

  Sanan idan zakayi
adalci ba wanan yar kadai ake kawowa alheri ba a gidan nan ga nawa fahintar
zancen da sukayi kamar kowa saurayi na zuwa wurin shi saidai wani yafi wani
shine zancen nasu.

    In ma magana ne ai
zance zakayi akan su waye suke neman yayan naka kasani idan da gyara sai a
gyara a zauna lafiya ina ganin shi zaifi ai .

   Gara dai da tun
farko kikace zancen bai shafeki ba don haka banga abinda zaisa ki tsoma bakin
ki a cikin wanan zancen ba saiki jira idan kin haifa sun girma sai ki tsoma
baki a zancen diya tukun.

   Duk da dai ba
lsifin ki bane hakan shiyaja muna shidake kokarin nuna cewa bamu da muhinmanci
ya kiramu nan gaban ki don kikai mashi gulma ya zaunar damu yana muna wanan
tambayan haka a gaban ki.

    Dakata maimuna
koda yanzu tazo cikin mu ya zama dole maganan gidan nan a zauna da ita ayishi
tare a agama don itama yanzu zancen ya shafe ta.

  Mikewa mama tayi
tana fadin badai dani maimuna ba don bata kai mun can ba wallahi ita din nan
saidai ta gigitaka amma ba dani ba kallon ku kawai nakeyi wallahi.

  Au haka zancen yake
idan baki kallemu ba yaya zakiyi yanzu maimuna barin fada maki duk abinda kike
ji ina jin shi ina daga maki kafane don Alh amma ke din nan kinyi mun kadan
wallahi.

    Ai dole kice hakan
ba dole   ki daga kafa don Alh ba tunda
ke kikasan shige da ficen da kikayi har kika kamoshi saidai saukin abin iyashi
kika tsaya badai da maimuna ba ko ?

    Fada sosai sukayi
tsakanin mama da karima karshe tashi ummah tayi ta barsu a falon ta koma part
din ta ta shige daki duk ina dakina ina barci don dan hutun da muka samu na
sallah muna gida bamu fita.

   Duk abinda yake
faruwa nikan ban sani ba amma su Aisha sun sani don suma sun dauki zafi sosai a
kan hjy karima har ma da ummah da akace tayi masu mugun bakin a gidan aurensu
don haka suka dauki zafi sosai da ummah din suma.

    Fahintar ummah
bata cikin yanayi mai dadi yasa na bita dakinta bayan sallah magariba na sameta
zaune a kasa saman sallaya ta hade jikinta da gado tana jan tasbaha a hannun
ta.

   Sallama nayi na
shiga ta dago kai ta kalleni gaida ita nayi ina zama nace wai ummah anyi wani
abune dazun da ku fitan.

 Don tun dawowan ku
naga yanayin ki ba dadi haka na kura mata ido ina son jin amsan da zata bani
lokacin don na gama fahintar cewa akwai matsala.

    Maamah na fada
maki kada ki fada tarkon soyayya a yanzu kada ki biyewa su Aisha don ba daya
kike dasu ba yanzu gashi zancen yaron nan da ake ganin ku tare har yakai gaban
Alh ko .

   Wani yaro ummah na
tambaya cikin rudewa dama kuma fahintar cewa bakin cikin da ummah ke ciki ashe
ta dalilina ne hakan ya faru.

    Kasa na sauko inda
take don dama a saman godo na zauna sai gani na zube kasa gaban ummah sallaman
da akayine yasa batace dani komai ba nima din ban samu fadin komai ga ummah din
ba.

  Ummah ta mike ta
fito zuwa falo wasu makwabtan mune da take abin arziki dasu suka shigo lokacin
gaida ita da Sallah.

    Sun dade tare
hakan yasa na koma dakina na kwanta jiki a mace don abinda ummah ta fada min na
shiga tashin hankali.

    Abinka ga wauta
irin nawa wai Ahmed din nayi niyar kira in fada mai ko zan samu shawara a wurin
shi don sam ban yarda in magana  gidan mu
da Hannatu kawata ba.

  Saidana danna kiran
nakuma ga rashin dacewa  hakan na kashe saidai
kiran ya shiga sai gashi ya kirani dole na dauka yake fadin zarah yau lafiya
kuwa naga flashing din ki a wayana ?

   Sorry bakai naje
kira ba saina danna sunan ka na samu kaina da fadin hakan gareshi murmushi naji
yayi kafin tace duk dadin naman sallah da kike cine yakai ki ga hakan ina mama
ina kannen mu.

    Duk suna lafiya na
fada a kasalance lokacin yace a gaida min su saina kawo masu goron sallah su da
sauri na tare shi da fadin no ka barshi don Allah.

   Cikin mamakin jin
hakan yace lafiya kuwa kikace min hakan ina mungama wanan maganan dake ko raina
abinda zan basu kikayi ?

   No ba hakana bane
akwai abinda yasa nace hakan kasan Abban mu na gari ba fita mukeyi ba koda kazo
din koda nazo ai ba tsayawa zanyi ba don ina son zuwa in gaida mama da sallah .

   Na sake fadin don
Allah kayi hakkuri kada kazo don yanzu haka case akeyi da ummah din mu saboda
wani abu so kada kazo gidan mu don Allah.

   Abinda ya fada ya
daure min kai don cewa yayi saboda nine ko zarah an fadawa mahaifin ku kina
kulani dama nasan da wana  ranan yana
tafe komai dadewa.

    Amma tunda kince
kada nazo din na fasa zuwa ni kaina nasan baki cancanci mu,amula da mutum irin
naba mara galihu da asali na kwarai.

   Kiyi hakkuri shiga
rayuwan ku yaja maku matsala har ummah da bata taba sanina ba na jawo mata
matsala a rayuwan ta nace ba yadda kake zato bane kawai dai an samu wanda ya
fadawa Abba zancen kane na karya.

   Murmushi naji yayi
yana fadin nasan za ai hakan zasu dauka soyayya muke dake zarah har shakuwa ya
shiga tsakanina dake hakan.

   Abinda na guda ke
nan garemu tun farko nake ta kaucewa hakan kada azo a yiwa mu,amulana dake wani
fahinta na daban gashi kaddara ya riga fata har an samu wanda ya tsegunta
hakan.

   Ko kudinshi ya kare
a lokacin ko kuma dai shidin ya kashe naji wayan ya katse lokaci guda duba  wayan nayi na aje ina gyara kwanciya don
lokacin gaba daya jikina ya mutu sosai da maganganunshi da mukayi ga na ummah
kuma da ban san me zata fada ba a kan hakan.

    Tun ina dakon
ummah ta sallami bakin nata har barci ya daukeni ban sani ba a haka har gari ya
waye bamu samu zama da ummah din ba kan case din.

  Saidai na kasa
sukuni da sakewa a gidan don haka na zauna dakina ina jiran tsamani har barci
ya daukeni can cikin barcin nake jin muryan ummah na kiran sunana na bude
idanuna.

   Tana tsaye a kaina
take fadin kinsan kuwa karfe nawa yanzun baki je kin gaida mutane har Abba  ku yakai ga tambayan ki yanzu .

    Jin hakan yasa na
sauko a gurguje saman gadon ban daki na shiga na watsa ruwa na fito na shirya
ba wani kwalliya nayi ba sai idan nadawo zan zauna in gyara kaina.

   Part din mama na
fara zuwa su Aishane a falo suna breakfast na gaidasu da kwana ta hanyar fadin
ina kwana  ku nasan da wuya su amsa min
da dadin rai don haka na hada da fadin mama fa?

  Tana ciki kwance
Rukkaiya ta bani amsa nace idan ta tashi na shigo na fice zuwa part din mommy
amaryan Abba don wanan zuwan ta gyara part din ta daga kano masu hada wuri
sukazo kwana biyu suna aikin gyaran wurin nata .

  Nasan ranan da
sukazo ummah ta turamu muje mu gaida ita da zuwa kashe gari kuma sallah kowa
yana hidimar shi ban samu zuwa ba can saida ta shigo gida ummah da sallah muka
gaisa a part din mu da ita.

   Sai yanzun da zan
shiga saida nayi sallama nasa kai na shiga ban sameta ba sai wanan matar da
sukazo tare da naji tana kira da Altine.

    Nagaida ita na
fito ina fadin in ta fito a fada mata cewa nazo tana ciki na fita na nufi part
din Abban mu yana zaune saman daning yana karyawa lokacin nayi sallama na
shiga.

   Bayan nakai wurin
shi nakai gurfane kasa ina gaidashi da kwana ya amsa min yadda ya saba amsawa
saidai ba wani wasan ko zancen daya biyo bayan haka din.

    Na danyi jim na
dago zan fice har nayi tako biyu naji ya ambaci sunana na amsa na dawo na
tsunguna gaban shi ina fadin na,am Abba .

   Bai dago ba na dan
lokaci sai can ya dago yana fadin wani yarone ke zuwa wurin ki maamah kuma shi
din dan gidan waye a garin nan ina kuma kika hadu dashi ?

   Cikin mamaki na
dubi Abban din kafin nace yake zuwa wurina Abba ni ba wanda ya taba zuwa wurina
wallahi Abba.

  Murmushin takaici
naga ya baiya a fuskanshi lokaci guda kafin yace kinsan banson karya kuma
maimuna ba zatayi maki karya ba tunda tace da idonta ta ganki dashi gidan nan ?

    Ahmed ne Abba kuma
ba wani abu bane ya kawoshi lokacin sai takardun shi dayazo amsa a lokacin
wurin shi kawai na sani.

   Shi din dan gidan
waye a garin nan kuma wani sana,a yakeyi dashi da mahaifin shi wani mataki yake
ga karatun shi yanzu ?

  Duk wanan tambayab
Abbane ya jero min su lokaci guda na kara dago kai a gigice ina fadin Abba
bansan komai ba kanshi abinda na sani shine kawai yana koya muna karatu mu goma
idan muna free wanan kadai na sani game dashi.

   Kallon mamaki Abba
yai min wanda ke nuna rashin yarda dani lokacin ya kalloni da kyau yana fadin
ki turo min shi kafin na koma cikin satin nan.

   A tsorace na dago
kaina nace wallahi Abba ba abinda kake tunane bane a tsakanina dashi tashi ki
ban wuri ki tabbarar da kin turo min shi kafin na koma idan ba haka ba zamu
saka kafan wando dake gidan nan ki tashi ki ban wuri..

   Na mika da kuka zan
fita muka hade da hjy karima wace ke shigowa tana fadin a maamah ance kinzo
gaidani ina wanka sai kuma tayi shiru ta bini da kallo.

  Me kuma ya farune ta
riko hannuna tana tambayana na kasa budan baki in bata amsa sai sautin kukan
dana kara a lokacin.

  Kallon Abba din tayi
tana fadin Alh meya sameta ne take kuka haka wani abu ya farune kuma da ita
kodai wancan maganan ne kake har yanzu din ?

  Bai bata amsa ba sai
kallon shi da takeyi saketa  ra fice min
daga falona sakariya kawai mara hankali ya fada daga inda yake zaune.

   Jin hakan yasa ta
sakeni tana fadin jeki part din ku zanzo in sameki can muyi magana ta fada tana
bina da kallo na fice daga falon na barsu da Abba.

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/17, 5:49 AM] +234 701 497 9567: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣3️⃣

Leave a Reply

Back to top button